• This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

ZAN ƘARA AURE... 01


*💑ZAN QARA AURE // 01🙆🏻🕺*

Aure a rayuwar malam Bahaushe na nufin wata rayuwa da ake kullawa tsakanin namiji da mace, wace ake sa rai da cewa mutuwa ce kadai za ta iya raba tsakaninsu, tare da sanin cewa in wani zarafi ya datso kowa na iya kama gabansa, ko dai shi maigidan ya sauwaqe mata, ko kuma ita ta kai shi inda za a shiga tsakaninsu. Da zarar an daura aure komai na amaryar ya tashi daga kan mariqinta ya koma kan maigida, hada da ci da sha, matsuguni da wasu abubuwan rayuwa da suka zama dole, ciki har da ilimi da addini.

A duk inda aka ji cewa ana daura aure za ka ji ala-san-barka ga ma'auratan guda biyu, koda kuwa mutum bai san daya daga cikinsu ba, ango da amarya da uwayensu da sauran tarsashin jama'a duk sukan yi ta murna, sashin ango na farin cikin cewa dansu ya zama babba, shi ma yanzu ya zama magidanci, uwayensa ko ba su fadi ba dai dayan abubuwa biyu ne ke bayya musu: Kodai yanzu zai taimaka musu a kan al'amuran rayuwa, ko kuma zai kama gabansa su ji da sauran qanninsa.

Duk da haka fahimta kan bambanta a lokacin da mutum ya ce zai qara aure:-

1) 'Yan boko wadanda ba qanin iya bare na baba, su ke fara tofin ala-tsine da kawo wa angon talauci kusa, wasu har da maganar karatun yaran da za a haifa da kama musu hayar dakin da za su riqa kwana da gazawa wurin tarbiyantar da su duk da cewa ko auren ba a daura ba bare ta sami ciki bare kuma a kai ga wadannan abubuwan da suke zayyanowa.

2) Wasu daga cikin yayyin angon, maza kenan, masamman ma wadanda suke da mace guda, su ma sun kasu kashi biyu, wasu suna kallon zarafin angon ne, da kuma irin qarfinsa na qara auren ko gazawa, wasu kuma sun kulle idanunsu kan cewa bai isa ya qara aure a wannan lokacin ba, koda kuwa ba su da wata kataimaimiyar hujja a hannunsu.

3) Sai yayyin angon wato mata, su ma sun kasu zuwa kashi biyu, wasu kamar mazan ne ta wurin lura da yadda mutum yake riqe da ta gida, in gazawarsa ta bayyana sai ka iske suna yin fito na fito da qarin auren, wasu kuwa shaquwarsu da matarsa take sawa su taya ta kishi, a irin wannan yanayi angon kan jima kafin ya shawo kansu, wani sa'in lamarin kan kai ga murje idanu don dai ya isa zuwa ga manufarsa.

4) Sai 'yan sa ido, wadanda ba wani abinda ya hada su da mutum, amma su shiga tsakiya su nemi bata komai, koda kuwa ba wata riba da za su ci.

5) Uwargida kuwa (sai daidai) samsam ba ta qaunar ta ji an ce za a yi mata kishiya, duk kuma wani bayani da za ka yi mata don ka gamsar da ita cewa auren zai iya zama alkhairi a gare su bata lokacinka kawai za ka yi, ko fahimtarka ba za ta yi ba, in ka ji mace ta tsani wani malami, ko ta kira shi munafuki, qila ya kwadaitar da maza ne kan qarin aure, qiyayyar mata da qarin auren ya kai ga yi wa uwargida jaje na masamman kamar ta rasa wani, a hankali ya bayyana a matattararsu cewa qarin aure ko yin kishiya tamfar wata fitina ce wace ba yadda za a yi da ita.

6) Uwayen uwargida kan tsaya a gefen diyarsu ne, shahararriyar hujjarsu ita ce ba a san abinda amaryar za ta shigo da shi ba, koda kuwa yarinya ce qarama wace ba ta ma gama sanin duniya ba, ko wata saliha da maqwabta suka shede ta kan zama lafiya, wasu uwaye mata ba sa maganar cewa amaryar za ta kore su, matsalolin gida ne suke fitowa da su, masamman inda mijin diyarsu ya gaza, in ba a yi sa'a ba nan za su rada wa diyarsu yadda za ta bata auren ta wajen fadin gaskiya da qarya a kan maigidan don dai su bata sabon auren, in shedan ya sanya wa aikinta albarka sai ka ga sun ci nasara.

7) Akwai halin da mutum kan yi jinkirin qara aure har 'ya'yan da suka haifa tare da uwargidan su girma, a irin wannan hali in lamarin ya zo da matsala sai yaran su goya wa uwarsu baya a yi ta kwasan rigima, ita da yaranta a hannu guda, maigidan kuma a daya hannun, yaran kan tsaya kai da fata kan cewa uban bai isa ya kawo wata matar cikin gidansu ba, na taba ganin wadanda suka saka masa sharadin sai dai ya auro sa'ar mahaifiyarsu, wasu kuma suka turje kan cewa ba za a yi wa mahaifiyarsu kishiya ba, a kan ci nasara wani lokaci, amma ba kullum ake kwana a gado ba, galibi idan namiji ya yi niyyar qara aure zai yi abinsa, koda kuwa zai yi fito na fito da kowa.

A cikin wannan dan littafi da za mu bi, muna so ne mu ga wasu dalilai da suke sanyawa mutum ya yi sha'awar qara aure, tare da sanin cewa abubuwan da yawa matuqa, duk yadda ka lissafa wa mutum dalilan qara aure in ba ka yi sa'a ba sai ya ambato maka wani abin daban wanda bai da alaqa da abubuwan da aka lissafa, mu dai za mu lissafo su, amma mun sani cewa namiji in ya rasa dalilin da zai ce dominsa ne zai qara aure hakan ma wani dalili ne mai qarfi da zai yi din, a taqaice komai ma na iya zama dalilin da zai sa namiji ya qara aure, kenan wannan rubutu zai taimaki mata sosai ta wurin sanin yadda za su kare gidansu.
Share:

ABOKAI NAGARI

✍🏻 *SHEAKH AMINU IBRAHIM DAURAWA KANO*

ABOKAI NA GARI 

Abokai iri uku ne :

1- Abokin tayi daɗi, abinda ya kawo shi abota da kai domin ya amfana da kai, ranar da yaga babu amfanin zai kama gabansa. 

2- Abokin aiki, wannan abota da shi, iya wajan aiki ne da zarar am gama aiki shi kenan sai kowa ya kama gaban sa. 

3- Abokin mai daraja mutunci, wanda zai kasance tare da kai, a dukkan mawayacin hali, ko kana da shi ko babu, shi yana kaunar ka saboda Allah kawai, ba domin wani abu na duniya ba. 
Wannan irin abokin yana da wahalar samu, idan ka samu irin sa ka riƙe shi da kyau. 

Idan za kayi abota kayi da masu hankali
Domin 
idan baka nan zasu kare mutunci ka. 
Idan basu ganka ba zasu nemeka. 
Idan ka samu zasu tayaka murna. 
Idan kayi kuskure zasu gyara maka. 
Idan za suyi addu'a ba zasu manta da kai ba. 
Idan baka da lafiya zasu duba ka suyi maka addu'a. 
Idan ka shiga wani hali zasu nuna damuwa da alhini. 
Idan sun ganka suna murna. 
Idan kayi kuskure za su yi maka gyara, cikin hikima. 
Idan zaa cuce ka zasu taimake ka.
Idan ka mutu zasu yi maka addua, kuma su taimaki iyalanka a bayanka.
Wanda ya rasa abokai na gari yayi asara. 
Allah ka bamu abokai na gari.

Shin muna da irin waɗannan abokan?

Share:

SHARHIN FIM ƊIN KABIR SINGH DAGA MAHANGAR NAYAAK

daga Mahangar NayaakBhai:Sharhin Film din
# Kabir_Singh
kamar yanda Muka sani Kabir Singh shiri ne daya amsu matuka awanan shekarar..harya kaiga matakin kololuwar Karshe a Box Office wato All Time Blocbuster...wanda shine shirin Shahid Kapoor na farko daya kai wanan matakin a tarihinsa.....a bangare guda shirin yasamu matsakaicin yabo ne daga masana masu shrhi wato Critics daga masu bashi tauraro 3 sai 3 da Rabi cikin Taurari Biyar.harma da masu 2 da Rabi....shidai sharhi gami da bayarda taurari ya danganta ne ga ra'ayi, Nazari gami da Hangen masana dakeyi bayan sun kalla domin su ankarar da masu shiga Silm kallo gudun karsuje su zuba kudinsu wajan siyan tikitin kallo daga vaya su koma suna nadama...sau da yawa masana kan yabi shiri yakasance beyima makallata va, haka zalika masana kan kushe shiri sukuma makallata ya kayatar dasu suyita zuwa kallo....
nasama kallan shirin Kabir singh ainahin dauka mai kyau wato original copy ba na yaren indiyan ba fassarar hausa ba wanda yake kunshe da English Subtitle inda na kalla rabi a shekaranjiya na kammala da sauran rabin a jiya....nasan mutane dayawa sun rigani kallo wasu kuma basu kaiga kallo ba na rigasu... wani ya buqaci inyi sharhi a mahangata...sanan danayi posting zan nasoma kallansa a shekaran jiya wasu sunce beyi kyau ba yayinda wasu sukace zan kayatu.dan akwai wanda yace ma intanajo Popcorn wato gurguru wajan kallan shirin saboda ingancinsa... kar inja surutu da nisa bari inkaiga Sharhin Film din Kabir Singh bayan na kalla bisa mahangata.....
kabir Singh ba shiri bane na kallan yara masu kasa da shekaru 18 saboda yawan sumbace sumbace da shaye shayen barasa datayi yawa...wanda bana tunanin na taba kallan wani shiri da aka nuna shaye shayen barasa kamar ruwa dakuma sumbace sumbace ainun kamar shirin ba....so ko a kasar indiya hukumar tace finafinai tayi hani da barin yara su kalla a gidajen silma....a gsky shirin bashi kunshe dawani darasi mai kyau kwatakwata....dan dabi'ar shahid kapoor na Kabir singh acikin shirin babu ko daya mai kyau dan ya raina manya be ganin kowa da gashi har iyayansa ya rainasu ainun fiyeda yanda aka saba nuna indiyawa na raina iyayansu acikin finafinai...sanan tauraruwar shirin Kiara Advani ta bayyana ne cikin shirin amatsayin yarinya saliha mara hayaniya yar aladah...ammh yanda aka nuna kabir ya lalata mata rayuwa ya sauyata kwatakwata daga tarbiyar iyayanta ta daina ganin mutuncinsu abin beyi ba...sanan tunda ta hadu dashi bata tabayi masa musu ba...sanan be tabayin abu tanuna rashin dacewar hakan tundaga haduwarsu duk munanan dabi'unsa abun beyi tsari ba...ansancewa so hana ganin laifi ammah ayanda aka nunata a saliha bekamata ace daga haduwarsu har soyayya ta afkata fagenda zata lalace cikin sanshi haka ba harta koma fitsararriya ta sosai ba...sanan lalatarsu na farko ita dakanta ta nuna bukatar hakan bayan ta sama rauni ya mayarda ita dakinsa na hostel din maza da zama ba...
Kabir singh shiri ne na yara yan bana bakwai masu san rayuwar holewa zasu soshi shiyasa yayi kasuwa....domin inka kalla rayuwar kabir singh bayan ya rasata an aurar da ita yakoma rayuwar shaye shayen giya kwayoyo hodar iblis da sauransu duk wadanan abubuwa dayayi daga karshe ya sami abunda yakeso hakan zai karfafa matasa suje suyita rayuwar dasuka ga dama domin suna iya tunin zasu sama yanda sukeso a karshe kamar yanda kabir singh yasamu duk tsiyar daya tsula...saide matasa masu san rayuwar holewa da basa iya banbance abu mai kyau da mara kyau ne rayuwar dabi'ar shahid kapoor na kabir cikim shirim ka iya burgesu.....dabi'ar kiss wato sumba dasukeyi na baki da baki kace kace dasukeyi ne yasa sanda kabir yaje gidansu Preeti dan naiman iznin mahaifinta wanda bayanan suka haye saman gidan suna sumbatar juna har babanta ya kamasu ya tafasa matuka ya hanashi auranta wanda kowana mutumin kirki na iya aikata hakan...ammah daga karshen shirin sai gashi Baban ne wai yake basu hakuri...sanan yarinyarsa data kangare auran daya mata taki zama kwanaki uku dayim auran ta gudu.....
zamu iya cewa salon dabi'ar rawar da shahid kapoor ya taka ta kayatar yayi kokari dama sauran dabi'un taurarin shirin....saide wasu abubuwan hankali bazai dauka va kan labarin shirin in anyi nazari sosai....duk me shi'awar rayuwar holewa, rashin kunya, saurin fishi gami da rashin ganin girmab kowa shirin Kabir singh na iya kayatar dashi yakuma nishadantar dashi ainun.....ko a indiya har yau ana cece kuce kan bambancin ra'ayi a kafafen sadarda zumunta har tsakanin ainahin taurari daga bollywood kan shirin....
so shiri dai ya amsu a Box Office ainun dan shine shirin dayafi amsar kudi wanan shekarar kafin War ya bige shi...
banga laifin masu sharhi ba da basu bashi daurari sosai ba har ya samu matsakaicin yabo ba....
NayaakBhai a kankin kaina dakuma ra'ayi na Kabir Singh shiri ne da bana shi'awar kara kallansa...dukda nasan ya kayatarda wasu dayawa wanda ra'ayinsu ne.nima wani abu na iya min kyau sukuma bai yi musu va ..
nabama shirin taurari 2 cikin 5 a mahanga taaa


Share:

KODAI GASKIYA NE KATIN GAYYATA NA BIKIN RANBIR KAPOOR DA ALIA BHATT?


KO DAI GASKIYANE KATIN GAYYATA NA BIKIN RANBIR KAPOOR DA ALIA BHAAT?


Daga Jiya Zuwa Yau Wani katin Gayyata (Invitations) Yake Yawo Kan Za ayi Auren Rabir da Alia a 22, Watan January 2020.

Mutane Sun Kasa Tabbatarwa Amma a Daren Jiya Wasu Yan Jarida Sunci Karo da Jaruma Alia Bhat Acikin Airport ta sauka Daga Mata Inda a Video din Me dauke da Sakonni 50 Tana tafiya tare da Masu Tsaranta Kawai Acikinsu Wani yake Tambayar ta da Hindi " Suno Na Ma'am ek khabar mili hai, confirmed hai kya? Watau MADAM MUN SAMU LABARI SHIN AKWAI TABBACI AKANSA KUWA? Sannan ya Kara dacewa 22, ga Watan January Ake Cewa Zaku Angonce Kawai Jarumar Ta KyalKyale da Dariya Har Ta Kusa Shiga Wajen Kawai ta juyo ta kalle Shi tace "Kya Batoon" Watau Me Zance? Shi Kuma Yace Madam a fada Mana.


By #AbbaIndiaDala
Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN DHOOM

Fassarar Kalaman Fim Din Dhoom

Shekarar Fita- 2004

 1. Mere rules koi nahi todh sakta ... main bhi nahi
 
Babu wanda ya isa ya karya min dokoki na, ko da ni ne 

John Abraham

 2. Tezzi goli mein nahi ... chalane waale mein hoti hai

 Sauri ba a jikin Harsashi yake ba... A jikin Maharbin yake 

 John Abraham

 3. Agar tum chor na hote to hum zaroor dost hote

Da ace kai ba barawo bane to da lallai mun zama Abokai 

 
Abhishek Bachchan


 4. Joh bhi karenge ... style se karenge
 
Ko me zamu yi... Zamuyi shi ne a cikin salo. 

 John Abraham


 5. Nothing is permanent ... na tum, na main, na plan, na time
Babu wani abu Dauwamamme... Ba kai ba, ba ni ba, ba tsarin ba kuma ba lokacin ba. 

 John Abraham

 6. Tumhari kismat badal rahi hai ... tum bhi badal jaoge
Idan Kaddarar ka ta canja... Kaima sai ka canja 

John Abraham

 7. Jail jaana meri kismat mein nahi hai
 
Magarkama ba Kaddara ta bace 

 John Abraham

 8. Main criminals se baat nahin karta
Bana magana da 'Yan Jagaliya 


Abhishek Bachchan

 9. Burai chahe jitni bhi aage chali jaye ... hamesha achchai se peeche rehti hai
Duk iya nisan da Zalunci yayi... Adalci na gaba dashi 

Abhishek Bachchan


 10. Bahut jhankaar beat aadmi hai woh

Wannan fa Kasurgumin mahaukaci Ne 

 Uday Chopra


<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring

Share:

INTERROGATIVE PRONOUNS IN HINDI

LESSON TWELVE (12)
INTERROGATIVE PRONOUN

In previous lessons, we discussed about three types of pronoun, in this lesson we shall discuss interrogative pronoun.
In Hindi it is called Prashanvaachak Sarvanaam. Interrogative pronoun is a pronoun that is used to ask a question.
Examples :
Who = Kaun
What = Kya
Whom = Jisi (non-human)
Whom = joh (human)
Which = Kis
Whose = kiska

Lets see their examples.

Who is sleeping there?
Kaun so raha hai vaha?

To whose house did you go yesterday?
Kiska ghar gaya tha kal?

What is on your head
Tumhara saar par kya hai

In sankhya me kis chunayega
Which one will you choose among these number

This is the soldier whom slapped me yesterday
Yeh hai phojee joh mujhe Kal thapar mara tha

This is the cat whom has died yesterday
Yeh hai billi jisi kal mar chuki thi

If you find the lesson useful, don't forget to like, share, comment and invite your friends to like the page on Facebook
LEARNING HINDI
_

Share:

GIVING CHARITY TO WARD OFF CALAMITIES


Giving charity to ward off calamities

In the Name of Allah, the Most Gracious, the Most Merciful.

Abu Hurayrah, may Allah be pleased with him, narrated that the Prophet said, 

“There is no day in which the slaves rise in the morning except that two angels descend; one of them says, 'O Allah! Compensate the one who spends.' The other angel says, 'O Allah! Destroy the wealth of the one who is stingy.'” [Al-Bukhari and Muslim]

It is also confirmed that charity repels calamities, as stated in the hadeeth, “Doing good (to the people) protects one from misfortunes, secret charity extinguishes the anger of the Lord, and keeping ties with kinship increases one’s life span.” [At-Tabaraani - Al-Albaani classified it as hasan (good)]

Also, Anas, may Allah be pleased with him, narrated that the Prophet said, 

“Doing good (to the people) protects one from misfortunes, calamities, and destruction; and the people of goodness in this worldly life will be the people of goodness in the Hereafter.” [Al-Albaani classified it as saheeh (sound)]

Moreover, the hadeeth reported by Al-Bukhari and Muslim about the solar eclipse reads, “The Prophet said,

'When you see that [i.e. the eclipse], supplicate to Allah, say Allahu Akbar, pray, and give charity.'”

Ibn Daqeeq Al-‘Eed , when interpreting this hadeeth, said, “This hadeeth is evidence that charity is desirable when someone fears something in order to repel the misfortune that he fears.”

Imaam Ibn Al-Qayyim said in ‘Iddat As-Saabireen, “In charity, there are numerous benefits which no one can enumerate but Allah, among which is that it protects one from misfortunes and repels trials to the extent that it repels tribulations off an oppressor (i.e. charity repels tribulations even if it was given by an evil or an oppressive person). 

Ibraaheem An-Nakha'i said: 'They (the righteous predecessors) held that charity protects the oppressed man, wipes out the sin, preserves wealth, brings forth sustenance, brings joy to the heart, and necessitates having trust in Allah and thinking well of Him in the same manner that stinginess is mistrust in Allah.

Charity repels the devil, purifies one’s soul and develops it, endears the slave to Allah and to His creation, and conceals all his defects in the same manner that stinginess conceals every good trait.

Charity increases one’s life-span, incites people to supplicate for the person and to love him, repels the torment of the grave from the person, provides shade for him on the Day of Judgment, intercedes for him with Allah, eases the difficulties of this world and the Hereafter for him, and makes it easier for him to do all good deeds; indeed, its benefits are many times more.'”

Therefore, there is no harm in giving charity in order to attain what is confirmed in the Sharia as a promise to repel a calamity from the person who gives charity.

We ask Allah to make us charitable and save us from calamities. Aameen.

Allah knows best.
Share:

HIKAYAR WASU SARAKUNAN HINDU


HIKAYAR WASU SARAKUNAN HINDU

Tare da Sadiq Tukur Gwarzo

A wani zamani mai tsawo daya shude, lokacin da ake cewa mutane na magana da dabbobi, anyi wasu sarakuna biyu manya a kasar hindu, kowannen su na mulkin garin sa daban da dayan, sannan dukkansu sun kasance masu yawan kyauta, amma dayan su yafi daya kyauta.
Sarki na farko sunan sa Karna. A kullum yana rabon dinare dari ga mabukata. Har ma yasha alwashin cewa bazai taba cin abincin safe ba a kowacce safiya har sai ya kammala rabon dinare darin daya saba. Sai dai inda yake samun wadannan dinarai ya zamo abin tambaya da mamaki a wurin jama'a.
Na biyun su shine Vikram. Wannan sarki shahararre ne a wurin kyauta. Domin yana bada kyautar duk abin da aka tambayeshi tun daga kan gwala-gwalai, azurfa, gidaje, kuyangi da sauran su. Ance babu abinda ake tambayar sa ba tare da an samu ba, kuma wai har dabbobi na rokon sa abu.
Wata rana Sarki Vikram na shakatawa a lambunsa, sai ga wasu tsuntsaye mace da namiji sun dira a gabansa.
Namijin yace "Ya sarki mai kyauta, ka ceci rayuwar mu, yunwa zata kashemu".
Sarki yace "Abinci kuka rasa ko yaya? Idan kunaso zan rinka aiko muku da tsabar abinci a kullum".
Ta macen tsuntsun sai tace "Ay bazamu iya cin tsaba ba. Muna rayuwa ne can saman wani tsibiri, kuma 'ya'yan itatuwa ne wadanda ba'ai wa tabo ba kadai abinda muke iya ci"
Sarki yace " To babu matsala". Nan take yasa aka kawo musu zababbun 'ya'yan itatuwa masu kyau aka basu. Sannan aka ce kullum safiya suzo su amshi irin wadannan 'ya'yan itace masu kyau suci.
Hakan ne yayi ta faruwa. Kullum da safe tsuntsayen na samun abinda suke so kamar yadda aka alkawarta musu. Sai dai wata rana, ta-macen tsuntsuwar nan ta lura da cewa an kawo musu 'ya'yan itatuwa wadanda aka gatsa. Sai tace da namijin "kalli da kyau kagani.. Anyiwa wadannan 'ya'yan itatuwa tabo. Don haka sarki bazai iya ciyar damu ba, zaifi kyau mu tashi mu tafi wani wurin daban".
Da fadin haka sai gano su akayi sun shilla sama suna karkada fuka-fukin su tare da fadin "mungode maka Sarki Vikram, kaine mafi kyauta a sarakunan duniya".
Tsuntsayen basu gushe ba suna wannan yabo ga Sarki Vikram har sai da suka yi nesa sosai da garin izuwa wani babban tsibiri. Ashe a hanyar su ta wucewa sun gushe ta saman fadar Sarki Karna har kuma yaji abinda suke cewa, abinda ya sashi kishi, yake tambayar kansa tayaya za'ace akwai wani sarki da ya d'ara shi kyautayi a duniya?
Ai kuwa sai ya umarci wasu sadaukan sa da subi bayan wadannan tsuntsaye kuma su tabbata sun kawo masa su.
Kafin wani lokaci kuwa sai ga dakaru sun zo da tsuntsaye cikin keji ga Sarki Karna.
Sarki ya dube su cikin annushuwa yace " Naji kuna kiran wani sarki a matsayin wanda yafi kowanne kyauta, shin meye dalilin ku na fadar haka?"
Namijin Tsuntsu yace" Sarki Vikram ya kasance yana ciyar damu 'ya'yan itatuwa zababbu kullum da safe kuma baya daure wadanda basuyi laifi ba acikin keji".
sarki karna yace "Na kasance kullum da safe ina rabon dinare dari ga mabukata. Ashe ban fishi ba?" Sannan ya dubi dakarun sa yace "Ku kawo kwandon zababbun 'ya'yan itatuwa zan ciyar dasu yanzu".
Da aka kawo sai ya kalle su yace "Yanzu zan sa a ciyar daku da zababbun yayan itace, shin ban fishi kyauta ba?"
Sai ta macen tsuntsuwar tace "Ai shi sarki vikram da hannun sa yake ciyar damu".
Hakan yasa shima Sarki Karna yayi yinkurin ciyar dasu da hannun nasa, ya bude kejin zai mika musu tuffa. Sai dai kuma cikin hanzari ta macen tsuntsuwar tayi wuf ta fito daga kejin, sannan ta tashi sama. Bata zame ko ina ba sai gaban Sarki Vikram.
Da zuwanta ta fadi gaban sa tana afi, tayi masa bayanin abinda ya faru tare da rokon sa ya 'yanto mata mijin ta.
"Zan 'yan to miki mijin ki". Abinda sarki Vikram kurum ya fada mata kenan.
Kashe gari yayi shigar tsummokara, ya nufi birnin da Sarki karna ke mulki. Da zuwan sa ya wuce fada gaban sarki.
Ya fadi yayi gaisuwa, sannan yace " ya wannan sarki mafi kyauta a duniya, naji labarin karimcin ka da kyautatawar ka, don haka ina neman izinin ka don na zamo maka bara mai maka hidima."
Jin haka sai yasa sarki Karna yaji dadi a zuciyar sa. Sannan yace masa babu komai, " Duk abinda kaji a bakin mutane game dani gaskiya ne, kuma zaka shiga cikin masu dauko mini dinaran da nake rarrabawa kullum da safe".
Da gari ya waye kuwa Vikram da wasu bayin sarki suka kamo mazubin dinarai niki-niki. A kan idon sa Sarki karna ya raba guda dari ga mabukata.Shi da kansa vikram sai daya raya a ransa cewa Sarki karna ya fishi kyauta. Amma kumà sai yasha alwashin sanin inda Sarkin ke samo wadannan dinarai.
Tun daga nan Sai vikram ya ke ta leken asirin aiyukan Sarki Karna. Watarana da dare yayi, vikram ya wanzu leka kofar dakin sarki karna don yaga ko zai ga fitowar sa. Ai kuwa da gari ya dauko wayewa sai Vikram ya hango Sarki Karna ya fito daga dakin sa, yana waige-waigen kada wani ya gansa, sannan yabi wata hanya wadda zata fitar dashi daga cikin gidansa.
A hankali vikram ya rinka bin bayan sa yana labewa don kada ya juyo ya ganshi. Sai da suka fita daga gidan izuwa bayan gari, sannan Vikram ya hango Sarki karna ya nufi wata Bukka, kafin isar sa kuma sai ga wani tsoho irin masu kawwame kawunan su a wajen gari don bauta, ya nufo sarkin. Da haduwar su sai tsohon ya dukursa ya gaishe da sarki karna.
Sarki Karna ya tube kayansa daga shi sai gajeran wando, sannan ya dauki wata sanda ya nufi karkashin wata bishiya dake wurin. Ya rera wasu baitoci kamar haka:-
Ka_s_u_s_u_w_a_ d_a_ d_a_d_i_, a_m_m_a_ b_a_ k_a_m_a_r_ n_a_m_a_ b_a_.
Ka_b_a_ s_h_i_ r_a_y_u_w_a_, n_i_k_u_m_a_ z_a_n_y_i_ a_g_a_j_i_.
Da gamawar sa sai ya zunguro wata shigifa dake saman bishiyar. Nan take sai ga dinarai nata zubowa. Sanna ya karbo mazubi daga wurin tsoho ya zuba, yayi sallama da tsohon nan ya juyo izuwa gida yana dauke da tulin dinarai akansa. Anyi wannan duk akan idon Vikram. Da ganin haka, sai yace "yawwa, yanzu na gano yadda zan ceci Tsuntsu."
Kashe gari da sassafe vikram yayi sammako ya riga Sarki karna fitowa. Yazo wurin dattijo tare dayin duk abinda yaga sarki karna yayi. Tsoho bai iya gane shiba, abinda kurum ya iya tambaya shine sammakon da yayi, tunda yazo ba a lokacin daya saba zuwa ba. Vikram ya make murya ya ce masa uzuri ne ya fito dashi. Da Vikram ya gama yin duk abinda yaga sarki karna yayi, sai yace yau yana son tafiya da wannan shigifar gida, saboda kwana biyu wani uzuri zai hana shi zuwa wannan wuri. Tsoho yace to ba matsala. Sai kuwa vikram ya hau sama ya ciro shigifa yayi gaba da ita.
Anyi haka ba jimawa sai ga Sarki karna ya iso. Tsoho ya kamu da mamaki, ya kuma kwashe labarin abinda ya faru ya shaida masa. Nan take sai sarki karna ya cika da matsanancin bacin rai, lallai yasan cewa wanine yayi shigar sa ya tafi da wannan shigifa ta siddabaru.
Ya gama fadace-fadacen sa ga tsoho akan don me zai bari a tafi da shigifa, sannan ya koma gida. Kwana biyu sarki baya kyauta, kullum cikin bacin rai yake, har abinci ma baya iyaci.
Rannan kwatsam sai Vikram ya faki idon mutane ya shiga dakin Sarki karna. Yace masa "abokina, ka kwantar da hankalinka, shigifar ka na wuri na. Kuma zan dawo maka da ita matsawar zaka saki wannan tsuntsun da kake tsare dashi."
Sarki karna yayi tsallen murna, sannan yace ai a shirye nake na baka duk abinda kake so akan wannan shigifa. Amma yace yana rokon ya sanar masa da labarin sa.
Vikram ya labartawa karna ko shi waye da kuma labarin sa. Wannan abu yayi matukar kayatar da sarki karna. Shine ma har yace hakika tsuntsaye sunyi gaskiya. Ni ina iya yiwa talakawa kyauta don fidda su daga talauci, amma kai ka fini kyautatawa tunda kana iya sadaukar da kanka don 'yantar da tsuntsu."
Ai kuwa sai suka dunguma izuwa kejin da tsuntsu yake a tsare. Sarki karna ya bude kejin, tsuntsu yayi fir ya tashi sama inda ya hadu da matar sa wadda a kullum take rayuwa a boye a saman wata bishiya cikin bakin cikin rashin sa, tana mai fatan ganin ran da zai samu 'yanci.
Tsuntsayen suka wanzu cikin farin ciki suna waka ga sarki vikram, suna cewa " mungode, mungode, mungode wa Sarki vikram, wanda yafi dukkan sarakunan duniya kyautatawa"
Daga nan sai raha ta barke a tsakanin sarki Karna da sarki Vikram. Sarki karna ya tashi runduna don tayiwa sarki vikram rakiya izuwa birnin sa, sannan yasha alwashin shima idan ya samu lokaci zai kawowa Sarki vikram ziyara a birnin sa, zai kuma labarta masa labarin wannan shigifa mai ban mamaki wadda take aman dinare.
Share:

I WILL NEVER MARRY A IMAM!

I WILL NEVER MARRY A IMAM!

Yesterday was Friday, I was in the mosque and everyone looked gorgeous and glorious as we are all listening to Eld-ul sermon... 
The Mosque Service was just fantastic. My Imam was delivering the message with so much passion...
His words were hitting me right where I sat. Suddenly my stomach did a flip flop. So I went out to answer the call of nature.
Before I could head back into the Mosque building, I could bet I was hearing sobs...
Sobs coming from the back of the Ladies' Restroom. I followed the sobbing sound and guess who I met!! Mutmahinah, my Imam's beautiful 6 year old daughter crying and Cherish, a 9 years was trying to calm her down.. 
I tried to find out what was wrong. Even though it took a long time before they voiced out.
They were hungry... Mutmahinah said to me, "Aunty, when I grow up, I will never marry Imam, so that I won't be hungry... My Dad is an Imam and we are always hungry, but my friends' dads are not Imams and they never go hungry. Even mummy is hungry, we didn't eat yesterday."

I couldn't tell how tears flowed down my face, and God's word struck me like an arrow in my heart.

How could I explain to these little girls that being an Imam was a noble work and that the reason why they were going hungry was not their father's fault but the fault of we the members....????
We were not following Allah's order... 
A lot of us eat delicacies and forget the levites who were interceding for us before Allah... 

We forget the men and women who spend sleepless nights digging deep into the holy scriptures in order to get out secrets to move our lives forward...

 The angel technically raised my head up as I saw the array of executive cars owned by the members which was a big contrast to the rickety car my Imam drives... Now I understand why my Imam's wife wore clothes that were not fashionable. 

Friend, it's high time, we started taking the material needs of those who are blessing us spiritually seriously... Would it be wrong to personally placed your Imam on a monthly allowance... 
Would it be wrong to support your Imam in paying his children's school fees... 
Anyone who blesses you or ministers to you spiritually, make it a duty to bless them materially... 

Our Imams are hungry.... 

Do this for any Imam in your area and see how Allah will add His touch of blessings to your ways... 
Remember a soldier who defends a nation and fights for a country does not have to do a side job in other to meet his needs.... The Army provides for him and his family... Let's provide for our spiritual soldiers.... 
Have a blessed week. 

Compiled by *ComradeTAB*.............. Copied

Share:

KI ZAMA SARAUNIYA A FADAR MIJINKI

KI ZAMA SARAUNIYA A FADAN MIJINKI

💏Nana Aisha (RA) abun koyi ce ga ko wacce mace. In kika ɗauki rayuwarta kika koyi nagartattun halayenta. Sai kuma ki koyi kissoshinta, soyayyarta da salon zamantakewarta a gidan mijinta Nabiyur Rahma (SAW).

💏In kika ɗauki kissanta to ba kan mijin kaɗai zaki samu ba, a'a har da gangar jikin, kayan miya da spices din dafa shi ya dahu luguf, ki cinye shi tsaf, ki kora da ruwa 😋

💏Zaki samu dukiyar da gidansa, da soyayyarsa baki ɗaya ba tare da malam ya amshi kuɗinki ba In sha Allah. Mai wuyan dai mu gyara halayenmu, mu koyi hakuri da kyautatawa. Mu bawa kanmu tarbiyyan zamantakewa da koyi da magabatan kwarai, da cire son zuciya, da biyewa huɗuban shaiɗan la'ananne. Maza a yi koyi da Annabi (SAW) wurin soyayya da zamantakewa mai daɗi, domin ba zamu iya ba in baku bamu haɗin kai ba. Don Allah ku bamu dama mu dafa ku mu cinye 😆

💏Ka ji ka turawa matarka ko budurwarka. Ki ji ki tura duk wacce kika sani. Allah Ya bawa duk ma'aurata dawwamammen soyayya da zaman lafiya. Marasa aure ya azurta su da abokan zama na gari alfarmar wannan watan.

💏 *DAGA ƳAR'UWARKU SADEEYA LAWAL ABUBAKAR*

*💽KU SHIGA LINK DAKE QASA DOMIN DOWNLOADING DA SAURARO.*
                 👇🏾👇🏾👇🏾

http://darulfikr.com/s/50149 ___________________________________

 *💽Shiga sink dake ƙasa kuma domin downloading wasu nasihun da da suka wuce.*
                 👇🏾👇🏾👇🏾

http://darulfikr.com/m/scholar/sadeeya-lawal-abubakar-

=============================

*-Darulfikr>>> Taku ce domin yada Sunnah.*

Share:

SARKIN SARAKAI BOOK 2. 06

 SARKIN SARAKAI BOOK 2. 06

Al amarin sarki sahibul hairi da aljani
dabarus kuwa sai da suka shafe sa a
hudu
suna tafiya a can kololuwar sama
sannan sahibul hairi ya umarci
dabarus daya sauko kasa ba tare da
wata gardamar komai ba
kuwa sai aljani dabarus ya cika umarni
har suka sauko kasa suka
dira a cikin wani tafkeken jeji mai
dogayen bishiyoyi da manyan
tsaunika da fadamomi da koramai
gimbiya shukura da bawa haluf basu
farfado daga dogon suman
da sukayi ba koda ganin haka
sai hankalin sarki sahibul hairi ya
dugunzuma ya fara jijjigasu don
tsammaninsa sun mutu ne aljani
dabarus ne ya dubi sahibul hairi
yace ya shugabana ka kwantar da
hankalinka ba mutuwa sukayi ba
dogon suma sukayi kaje ka samo ruwa
ka yayyafa musu ni kuma sai
nayi musu fifita da fuka fukaina in muka
yi haka zasu farfado
koda jin wannan shawarar sai sarki
sahibul hairi ya ruga izuwa
cikin wata korama ya tsoma wani
mayafi nasa a ciki sannan ya daw
a guje ya daddana mayafin akan
fuskokin su shi kuwa dabarus sai
ya kamayi musu fifita da fuka fukansa
bayan dakika biyar
da faruwar hakan sai duk su biyun suka
farfado suna masu yin tari
da atishawa koda ganin haka
sai farin ciki ya lullube sarki sahibul
hairi shukura da haluf
suka kama kalle kalle da waige waige
suna masu mamakin yadda aka
yi suka tsinci kansu a cikin wannan daji
koda sarki sahibul
hairi ya fahimci halin da suke ciki sai ya
bushe da dariya yace kuna
mamakin ne bisa yadda kukazo nan?
Shukura ta dubeshi tayi masa
murmushi tace bana mamaki da
al amarinka ya kai jarumi uban jarumai
amma ina so ka gaya mini
abinda ya faru tsakaninka da mijina
shinka kashe shine??
Koda jin wannan tambaya sai sarki
sahibul hairi yayi ajiyar
zuciya sannan yace ai a rayuwata ban
taba haduwa da sadauki
mai tsananin karfi ba kamar mijinki
tabbas in ba don ina da nisan
kwana ba da tuni ya hallakani ina sanar
dake lambo nayi masa kamar na suma
sannan na shammaceshi na dokeshi
daga kan. Daga kan aljani dabarus ni
dai naga sa adda ya fado kasa
kansa ya bugu da wani rusashshen
tubalin gini harma
goshinsa ya fashe jini ya zuba abinda
ban sani ba shine
shin suma yayi ko kuwa mutuwa yayi sa
dda gimbiya shukura
taji wannan batu sai tayi ajiyar zuciya
cikin takaici tace yakai
wannan sarki kayi sani cewa kayi
babban kuskure da baka
tabbatar da mutuwar mijina ba ai kaima
kasan cewa manyan
mazaje basa saurin mutuwa ina
tabbatar maka da cewa
sarki barusa na nan a raye kuma zaiyi
gagarumin shiri
ya biyomu duk inda zamu je ko shakka
babu duk sa adda
muka sake yin arba da shi sai ya sami
nasarar hallakamu
yayinda sahibul hairi yaji wannan batu
sai yayi murmushi
yace yake shukura kiyi sani cewa a
rayuwata ni
,utum ne mai tsananin sa a bisa duk
abinda nasa a gabana
don haka ina tabbatar miki da cewa
komai RINTSI DA
TSANANI sai na cika burina na zama
SARKIN SARAKAI
na duniya lallai sai mun dauko yarinya
alfila a
cikin gidan boka shamzubul azwas
kuma sai na sadu
da sadauki Awaisu ya taimaka mini
mun nemo
wadannan yan mata guda uku wadanda
zan auresu
na sami daukakar dana ke nema
Koda jin wannan batu sai gimbiya
shukura ta jin jinakai
tace tabdijam ashe kuwa kana da
gagarumin aiki
agabanka ina tabbatar maka da cewa
wahalar da
kasha a baya tamkar kaso daya ce
daga dubun wacce
zaka sha a nan gaba yakai wannan
sarki kayi sani
cewa nemo wadannan yan mata uku
dai dai yake da
nemo jaki mai kaho domin babu wanda
yasan inda suk )
saboda sun boye kansu da karfin sihiri
irin na
sadauki awaisu tabbas in ba sadauki
awaisu ba
babu wanda zai iya laluben inda suke
shi kansa
babu tabbacin cewa zai iya gano inda
suke a cikin
karamin lokaci yakai wannan sarki idan
har dukiya
kake bukata da kuma daukaka aiko a
yanzu ka
samesu
domin wannan gatarin sihirin kadai
daka mallaka
ya isa ya baka duk abinda kake bukata
ina tabbatar
maka da cewa idan kaje ka ajiye
wannan gatarin
a cikin gidan sarautarka saika sami
dukiya mai
yawan da tafi cikin RIJIYA GABA DUBU
arba'in
kasancewar kayi babbar bajinta wacce
babu wanda ya
yi ta a wannan zamani don haka dole
ne labarinka
ya bazu ko ina
a cikin duniya mai zai hana yanzu ka
koma kasarka
kaci gaba da sabuwar rayuwa?
Amma ina mai rokonka alfarma guda
daya
Alfarmar kuwa itace ka daure muje
gidan boka
shamzubul azwas mu dauko yarinya
Alfila
ka mallaka min ita
koda jin wannan batu sai sarki sahibul
hairi
ya bushe da dariya sannan ya dubi
gimbiya
shukura yace kai duniya ba gaskiya
wato dai kina
nufin duk wahalar da nasha a baya ta
zamo ke nayi wa kenan
idan na hakura da gatarin sihirin kadai
ke kuma
na baki yarinya Alfila ne zaki sami
wadannan
sirrikan tsafi
guda dari idan kuka samesu kuwa sai
kinfi kowa
arziki da daukaka a duniya shin kin
manta ne
cewa nima matsayin da nake nema
kenan?
Ai so nake nafi dukkan sarakunan
duniya dukiya
mata da daukaka ya kasance ana
kirana da suna
SARKIN SARAKAI
Hakika ba zan taba samun wannan
matsayi ba
face na auri wadannan yan mata uku
kamar
yadda boka hadimul Asur ya yi mini
bayani
ke yanzu na san so kike nayi miki
wahalar banza
ki samu abinda kike nema kin taimakeni
a cikin
gidan sarautar sarki barusa na sami
nasarar dauko
gatarin sihiri nima na ceci rayuwarki
dana
daukoki daga can domin inda na baroki
a can
din sarki barusa ya farfado ya ganki da
tuni kin
zama gawa
guyson naci gaba da cewa
ina mai shawartarki da mu rabu anan ki
tafi can
wani bangare daban na duniya kici
gaba da bina
har mu dauko yarinya Alfila ki iya rabani
da ita muje
zuwa mahaukaci ya hau kura' ai wanda
baiji
bari ba shine yake jin hoho !!!
Sa adda sarki uban sadaukai sarki
sahibul hairi
yazo nan a zancensa sai hankalin
gimbiya
shukura ya dugunzuma
nan take idanunta suka ciko da kwalla
taji
gaba daya ta
tsani kanta kuma ta tsani rayuwar
duniya
gaba daya
domin ta fuskanci cewa zatayi biyu
babu
ma ana bata ga tsuntsu
kuma bata ga tarko... !!!!!!!
.
SHIN SARKI SAHIBUL HAIRI ZAI SAMI
NASARAR SHIGA CIKIN GIDAN BOKA
SHAMZUBUL AZWAS HAR YA DAUKO
YARINYA ALFILA??
.
YAUSHE NE SAHIBUL HAIRI ZAI HADU
DA SADAUKI AWAISU??
.
SHIN IDAN SUN HADU SADAUKI
AWAISU ZAI YARDA SU TAFI NEMAN
YAN MATAN UKU?
.
SHIN SU WAZIRI AKIYANU ZASU SAMI
NASARAR SATO WANNAN DOKI NA
SARKI AMINUL HAS SU KAIWA BOKA
SHUBURUL UZUB?
.
IDAN SUN KAI MASA DOKIN ZAI CIKA
ALKAWARIN YAGAYA MUSU HANYAR
DA ZASU BI SU SAMI NASARAR
HALLAKA AMINUL HAS?
.
YAUSHE NE BURIN SARKI SAHIBUL
HAIRI ZAI CIKA YA ZAMA SARKIN
SARAKAI?
.
SHIN SARKI AMINUL HAS DA
MATARSA SHULAIBA ZASU SAMI IKON
YIN KWANA SITTIN AKAN GADON
SARAUTAR BIRNIN MISRA DON SU
SAMI HAIHUWA?
.
Marubucin littafin yace mu hadu a
SARKIN SARAKAI3
Littafi na uku
don jin karshen wannan kasaitaccen
labariShare:

SARKIN SARAKAI BOOK 2. 05

 SARKIN SARAKAI BOOK 2. 05
LOKACIN DA SAURAN JAMA'A DAKE
CIKIN FADAR SUKAJI FADAR NATA
GIRGIZA KAMAR,
zata rufta cikin kasa sannan karar
haduwar makaman su sarki sahibul
hairi,
ta cika musu dodon kunne sai suka rude
suka firgice aka kama iface iface,
da guje guje domin ba a taba ganin
tashin hankali ba irin wannan,
kafin a jima wannan tashin hankali ya
isa har cikin gari ko ina da ina,
don haka sai gaba daya birnin ya
hargitse kai bama mutane ba hatta,
dabbobin gida da na daji saida suka
firgice suka kama koke koke da,
guje guje tsuntsaye kuwa tashi suka
rinkayi suna barin shekarsu suna kaara
nausawa cikin daji,
domin neman maboya manyan dabbobi
irinsu kura zaki damisa da sauransu,
cikin ramuka da koguna suka ringa
shigewa suna boye kansu,
kai a wannan rana duk dabbar dake
cikin ruwa bata yarda ta leko saman
ruwa ba,
tun sa adda aka fara azababben yakin
tsakanin sarki barusa da sarki sahibul
hairi,
sai bawa haluf ya yanke jiki ya fadi kasa
sumamme saboda tsananin razana,
ko kadan gimbiya shukura bata lura da
halin da haluf ya shiga ba domin,
gaba daya hankalinta na kansu sarki
sahibul hairi sa adda sarki barusa,
ya ga an shafe kusan sa a uku ana
wannan dauki ba dadi amma ko sau
daya,
bai sami nasarar taba jikin sahibul hairi
ba sai ransa ya baci zuciyarsa tayi
bakikirin,
kawai sai yai jifa da takobin hannunsa
yai nuni da hannunsa guda,
izuwa ga sahibul hairi take wadansu
masun tsafi suka fito daga cikin,
hannun nasa kimanin guda dari suka
tafi da gudu kamar an cillosu daga
cikin kasa zasu cake a cikin jikin sarki
sahibul hairi kawai sai shukura ta nuna
masun da yatsantsa guda take suka
tsaya kyam a cikin isa kuma suka kone
kurmus suka ruburbushe, koda ganin
haka sai sarki barusa ya kara fusata
ya juyo kan shukura suka fara musayar
tsafi a tsakaninsu kowa na jefawa
kowa mugayen abubuwa shi kuwa
sahibul hairi sai ya zama dan kallo .
Sai da barusa da shukura suka jefi
junansu da muggan makamai sama da
guda dari
amma dayansu bai sami nasarar
lahanta dan uwansa ba daga nan kuma
sai
suka jefawa juna wata irin iksa mai
karfin tsiya sai gashi suna wujijjiga
juna a sama suna ta katantanwa a cikin
iska a wannan lokaci iskar sarki barusa
tafi ta shukura karfi don haka sai tayi ta
wulwulata da karfin tsiya cikin
kankanin lokaci shukura ta fita daga
cikin hayyacinta kawai sai iskar ta
makata
a jikin gini sannan ta saketa sai ga jini
yana zuba a goshin shukura ta fado
kasa
magashiyan babu alamar tana numfashi
koda ganin abinda ya faru sai
hankalin sarki sahibul hairi ya
dugunzuma shi kuma sarki barusa sai
ya
tuntsure da dariyar farin ciki yace yanzu
na gama da wannan munafukar maci
amana
saura kai karamin alhaki ina mai
shawartarka daka bani wannan gatarin
sihirin
dake hannunka kuma ka durkusa bisa
gwiwoyinka ka tuba gareni muddin
kana son kaci gaba da rayuwa a doron
kasa in ba haka ba kuwa yanzun na
zan yi daga daga da sassan jikinka na
batar dakai yadda har abada babu mai
iya shaida barin jikinka guda
yayinda sarki sahibul hairi yaji wannan
batu sai yayi murmushi irin na manyan
mazaje
wadanda basa karayar zuci yace yakai
tsohon azzalumi kayi sani cewa
babu wani da mai jini a jiki wanda ya isa
ya firgitani walau mutum ko aljan
domin ban san tsoro ba kuma ban san
jada baya ba ina tabbatar maka da
cewa
babu wani bala'i ko wata masifa da ta
isa ta rabani da wannan gatarin sihirin
dake hannuna don haka ina mai
shawartarka daka kauce ka bani hanya
na fice daga cikin fadarka salin alin in
ba haka ba kuwa zaka riski ajalinsa
koda jin wannan batu sai sarki barusa
ya bushe da dariya kawai sai ya
watsawa
sahibul hairi kibiyoyin tsafi da nufin su
cake dukkan jikinsa koda kibiyoyin
suka diro a kan jikin sahibul hairi sai
duk suka narke suka zama jini shikuwa
jikin nasa ko kwarzanewa baiyi ba ko
da ganin haka sai ran sarki barusa ya
baci ya dubi sahibul hairi yace amma
kayi farar dabara daka sha jinin
dodannina
a dakin azaba na karkashin kasa ba
don haka ba da tuni yanzu kibiyoyin
tsafina sun nutse a cikin gangar jikinka
tabbas yanzu ba zan iya hallaka ka ba
da karfin sihiri amma idan ka ci
maganin kaifi da tsini ai bakaci na karfin
damtse ba koda gama fadin haka sai
sarki barusa ya daka tsalle daga kan
aljaninsa ya dira akan aljani dabarus
ya gwabzawa sahibul hairi naushi a
baki saboda karfin naushin saida
sahibul hairi
ya baje a kan aljani dabarus wani irin
gudan jini yai tsartuwa daga cikin
bakinsa sai yai shame shame kamar ya
suma sarki barusa ya raba kafafunsa
akan sahibul hairi kuma ya dunkule
daya hannun nasa da nufin ya yiwa
sahibul hairi fashin albasa aka bazato
ba tsammani sai yaji sahibul hairi
ya gwabza masa naushi a fuskarsa
sarki barusa ya tafi da baya taga taga
kamar zai rikito kasa daga kan aljani
dabarus take idonsa guda ya kumburo
saboda karfin naushin da sahibul hairi
yayi masa amma sai ya sake rugowa
kan sahibul hairi yaci gaba da
tumurmusashi yana naushinsa hannu
da kafa. Cikin zafin nama ba
kakkautawa
tun da sarki sahibul hairi yake fada da
sadaukai
bai taba haduwa da sadaukin daya yi
masa mahaukacin
duka ba irin wannan har saida ta kusa
cewa sahibul hairi baya iya mai da
martani sai dai kokarin
kare duka kai da dukan ma yayi masa
yawa saiya
kasa karewar yanaji yana gani sarki
barusa yayi laga
laga dashi ya hada masa jini da majina
sahibul hairi ya
sake yin wanwar akan aljani dabarus ya
zamo tamkar
gawa sai numfashi yake yi dakyar
hakika barusa ya fi karfin
sahibul hairi
nesa ba kusa ba domin ko tsaywa
sukayi mutum ya dubi
girmansu da kirar sadaukantakarsu
yasan cewa banbancin a bayyane yake
lokacin da sarki barusa ya ga ya sumar
da sahibul
hairi a karo na biyu sai ya sake zuwa
kansa ya tsaya ya sunkuyya
da nufin ya kamo kansa ya karya masa
wuya
koda ya kai hannunsa zai kamo kansa
sai yaga sahibul hairi
ya goce cikin zafin nama yayi dungure
ta karkashin kafafunsa
ya bulla bayansa kafin dabarus ya juya
tuni sahibul hairi ya
naushi bayan barusa da dukkan
karfinsa nan take sarki barusa
ya fado kasa daga kan aljani dabarus
fadowar da zaiyi kuwa
sai ya fado kan wata rusashshiyar
dirkar gini koda buguwar
kansa sai ya sume a wannan lokacine
sahibul hairi ya mike tsaye da kyar ai
kuwa sai ya hango bawa haluf
da gimbiya shukura kwance a sume
cikin tsawa sahibul
hairi ya umarci aljani dabarus daya
dauko gimbiya da bawa
haluf ya fitar dasu daga cikin
wannan fada kafin dakika biyu tuni
aljani dabarus ya cika
wannan umarni tuni sun luluka sama
cikin gajimare
bayan kaamar dakika dari da ashirin da
bacewar su sahibul
hairi sai sarki barusa ya farfado daga
suman da yayi cikin
razana ya mike tsaye zumbur ya kama
dube dube baiga kowa ba
a wajan face wadannan narkeken aljani
nasa zaune waje daya yai
tagumi sarki barusa ya dakawa
aljanin tsawa yace ya kai shumakaru
ina abokan gabata
shumakaru ya risina yace ai tuni
wannan aljani nasu ya kwashesu
yayi sama dasu sun bace a cikin
gajimare cikin tsananin fushi sarki
barusa ya sake dakawa shumakaru
tsawa yace me yasa ka kyalesu suka
gudu shumakaru
ya ce ya shugabana ai bana zartar da
aiki face da umarninka
koda jin wannan batu sai sarki barusa
ya takarkare ya kwarara uban ihi
mai tsananin firgitawa cikin nuna takaici
tamkar ya fashe da kuka
sannan ya sunkwi da kansa kasa yace
yanzu yau ni aka zo har fadata aka cini
da yaki hakika mata
shaidanu ne in ba don shukura taci
amanata ba da babu yadda
za ayi sarki sahibul hairi ya sami
ikon satar gatarin sihirina na sani cewa
yanzu babu inda zasu nufa face gidan
boka shamzubul azwas
don dauko yarinya Alfila abinda zanyi
kawai shine nayi gagarumin
shiri nabi bayansu in yaso sai na labe a
kusa da gidan shamzubul
azwas sai bayan sun gama shan
wahalarsu sun dauko alfila ni kuma na
taresu na kwaceta na hallakasu
koda gama wannan zance sai sarki
barusa ya kama kyalkyala dariyar
mugunta yaci
gaba da yin dariyar kamar ba zai daina
ba nima kuma saina
ci gaba da tayashi wannan dariyar ni
guyson muje zuwa
wannan shine abinda ya faru tsakanin
sarki barusa da sarki
sahibul hairi bayan sahibul hairi ya sami
nasarar dauko gatarin sihiri
Al amarin sarki sahibul hairi da aljani
dabarus kuwa....
Zan Cigaba insha Allah

Share:

SARKIN SARAKAI BOOK 2. 04

 SARKIN SARAKAI BOOK 2. 04

Koda jin wannan tambaya sai boka shuburul uzab ya bushe da dariya sannan yace yakai babban waziri ka sani cewa amsar wannan tambaya tana bukatar a saurareta a cikin nutsuwa ku kuwa yanzu gashi babu nutsuwa a tare daku domin kun gaji ainun kuma kuna bukatar abinci da abin sha don haka zaifi kyau mushiga daga cikin gidana ku zauna ku sami nutsuwa tukunna.
.
Ba tare da wata gardama ba sai su waziri Akiyanu suka bi boka shuburul uzab a baya har izuwa cikin turakarsa da zuwa suka iske an tanadar musu shimfidu da abinci da abin sha irin nasu na sarakai.
Kawai sai boka shuburul uzab ya umarcesu da su zauna su kintsa cikinsu shi kuwa sai ya wuce zuwa wani dakin daban bai fito ba sai bayan sun gama kimtsa cikinsu boka shuburul uzab ya zauna a gefe daya yana mai fuskantarsu boka shuburul uzab yace yaku wadannan manyan baki na sani cewa kuna cikin matsanancin bakin ciki bisa rashin samun nasarar hallaka sarki Aminul has?
.
.
Tabbas ba zaku taba samun nasara ba face kun rabashi da wannan sandar tsafi da takalmin sihiri duk duniya babu wanda zai iya taimaka muku ku sami nasarar rabashi da wadannan abubuwa face mutum biyu.
Na farko shine boka hadimul Asur sai kuma ni din nan ni kuwa ba zan taimaka muku ba face kunyi mini wani abu guda daya.
Cikin matukar mamaki waziri Akiyanu ya dubi boka shuburul uzab yace kai kuwa menene abin da kake son muyi maka.
Boka shuburul uzab yayi murmushi sannan yace ina son ku sato mini dokin nan na sarki Aminul has wanda yai tafiya dashi a can karkashin teku,
domin na ciri wani sinadarin tsafi a jikinsa wanda shi ne zan cika burina na duniya.
Cikin mamaki Akiyanu ya dubi boka shuburul uzab yace to ai wannan doki bashi da wani sihiri a jikinsa,
boka shuburul uzab ya kyalkyale da dariya yace kaine dai baka sani ba ai sakamakon daukan da wannan guntun Aljanin yayi masa yanzu ya sami sirrikan tsafi guda dari ba daya irin na sadauki awaisu.
Akiyanu ya sake tambaya wane ne kuma sadauki Awaise?
Boka shuburul uzab yace sanin wannan bashi da wani mahimmanci a gareku yanzu saiku amsa mini muradina kafin na gaya muku hanyar da zakubi ku raba aminul has da ababan dogaronsa.
Shin kum amince zaku sato mini dokin.
Waziri akiyanu yace kwarai kuwa ai sato wannan doki a garemu abu ne mai sauki tamkar wanke hannu da ruwa,
boka shuburul uzab yayi dariya sannan yace to shi kenan sai ku tashi ku tafi izuwa birni na baku kwana biyu rak ku sato wannan doki ku kawo mini kuna kawo mini shi nayi Alkawarin zan gaya muku yadda zakuyi ku raba aminul has da sandarsa da kuma talakawansa na tsafi don ku sami damar hallakashi.
Koda gama wannan jawabi sai boka shuburul uzab ya lumshe idanunsa ya bace bat daga cikin turakar koda ganin haka sai suma suka hau dawakansa suka nufi birnin misra.
Basu isa cikin gari ba sai da dare ya soma maimakon su rarrabu kowa ya tafi gidansa sai suka sake dunguma gaba daya suka tafi izuwa gidan waziri Akiyanu suka sake sabon zama na musamman don tunanin hanyar da zasu bi su sami nasarar sato wannan doki na sarki Aminul has,
abinda su waziri akiyanu basu sani ba shine boka shuburul uzab yaudararsu zaiyi kawai amma a zahirin gaskiya ba zai iya raba sarki Aminul has da abubuwan nan biyu ba.
Sihirin da yake so ya cire a cikin jikin dokin Aminul has kuwa shine irin sihirin dake jikin yarinya Alfila yar sadauki Awaisu kuma irinsune a jikin wannan sanda da takalmi na aminul has.
Duk abinda wannan guntun Aljanin ya taba da hannayansa sai ya sami wannan sihiri dalilin haka ne dokin Aminul has ya sami wannan sihiri.
++ ++ ++
Acan birnin Askandariyya kuwa lokacin da sarki sahibul hairi yaci gaba da labewa a cikin fadar sarki barusa yana hangen abubuwan dake faruwa kawai sai ya gga wata kyakkyawar mace ta gaban kwatance ta baiyana a gabansa tana mai yi masa murmushi.
Har ya yunkura zai bar wajan ta dakatar dashi tace tsaya na nuna maka hanyar da zaka bi kaje inda gatarin sihiri yake in kuwa kabi wata hanya daban halaka zakayi cikin matukar mamaki da rashin yarda sarki sahibul hairi ya dubeta yace ke kuma wacece kuma saboda me zaki nuna mini inda gatarin sihiri yake alhalin kuna son wannan gatari fiye da komai a cikin birnin nan?
Kyakkyawar tace babu isashshen lokaci da zan iya maka bayani yanzu amma bayan ka sami nasarar dauko gatarin sihirin zanyi maka bayanin komai.
Koda gama fadin haka sai ta jashi izuwa wani sako daban sukaci gaba da tafiya suna ratsa wadansu manyan dakuna har saida suka shige cikin dakuna dari koda suka isa gaban kofa ta dari da daya sai kyakkyawar ta tsaya tace gatarin sihiri na cikin wannan daki a rataye a jikin bango kuma akwai dakaru mutum dubu uku a ciki masu tsaron gatarin wadanda suka kasance karfafa kuma sadaukan gaske yanzu saika shiga cikin dakin ka yaki sadaukan dubu ka karkashesu sannan ka fito na saka a hanyar da zaka fita daga cikin gidan sarautar nan sannan kuma nayi maka jagora izuwa gidan boka shamzubul azwas don dauko yarinya Alfila yar sadaukin duniya Awaisu''. An ya kuwa nima ba zan bisu ba kuwa ganin yadda mace take son raka sarki sahibul hairi?.
Koda jin wannan batu sai sarki sahibul hairi ya cika da tsananin mamakin yadda akayi wannan kyakkyawar budurwa ta san dukkan shirinsa har ya budi baki da nufin ya sake yi mata tambaya sai tace dashi.
Na gaya maka cewa bamu da isashshen lokaci a yanzu wanda zan yi maka bayanin komai don haka kayi sauri kaje ka dauko gatarin sihirin nan.
Koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya bude wannan kofa ya kunna kai ciki ba tare da fargabar komai ba yana shiga kuwa ya hango gatarin sihiri a rataye a jikin bango sai sheki da walwali yake tsaitsaye a gaban bangon da aka rataye gatarin wadansu murza murzan kartine majiya karfi su dubu uku kowannansu a tube daga shi sai kamfai.
Kuma duk suna rike da manyan makamai ababan tsoratarwa wani makamin ma tunda sarki sahibul hairi yazo duniya bai taba ganin irinsa ba su dai wadannan karti sun ninka sarki sahibul hairi sau uku a girma da cika ido gaba dayansu kansu daya tamkar tagwaye kai kace mace daya ce ta haifesu rana daya.
Koda kartin sukaga sarki sahibul hairi ya shigo cikin dakin sai suka yi masa kawanya su duka kowannansu ya kama gyara makaminsa shima sarki sahibul hairi sai ya gyara tsayuwarsa a cikin farin kayan karfe yana jiran yaga wanda zai fara afko masa..
Kamar hadin baki sai suka tasammasa gaba daya a lokaci guda ya zamana kowa na kai masa sara da suka shi kuwa sai ya zama tamkar shaidani a tsakiyarsu yayi ta kare kansa yana mayar musu da martani nan fa aka yi ta gumurzu dauki ba dadi da fafatawa tsakanin sarki sahibul hairi da dakaru masu tsaron gatarin sihiri.
Sai da aka shafe sa a biyu a haka subasu barshi ya sami damar isa inda gatarin yake ba shi kuma ya kasa hallaka koda daya daga cikinsu domin idan ya samu sa ar sarar jikinsu ma sai yaga kaamar dutse ya sara babu abinda yake samun su wani abu daya kara firgita sarki sahibul hairi shine ko kadan dakarun basa gajiya kuma basa alamar cewa zasu gaji sarki sahibul hairiya tabbatar da cewa idan akaci gaba da wannan fada a haka zata kai cewa ya gaji sun samu lagonsa
.
Don haka ya zama wajibi a gareshi yayi tunanin mafita ba zato ba tsammani sai dakarun sukaga ya sauya salon fada dabarar da yayi kuwa itace ya fara tsalle tsalle yana taka kawunansu yana karawa gaba a haka suka rinka kaiwa kafafunsa sara amma saboda zafin namansa sai suka kasa cimmasa bare samunsa
.
Kafin su ankara ya daka tsalle ya dira akan gangon da aka rataye gatarin sihiri nan take ya yarda takobin hannunsa ya suri gatarin
duk da cewa gatarin nada matukar nauyi amma sai gashi da hannu daya ma sarki sahibul hairi ke jujjuyashi.
sa adda dakarun sukaga sarki sahibul hairi ya suri gatarin sihiri sai suka sake yin caaa a kansa da nufin su ragargazashi shi kuwa sai yayi amfani da gatarin yaci gaba da saransu wohoho
a wannan lokacine labari ya sha bambam domin duk wanda ya sara da gatarin sai dai kaga ya faskarashi gida biyu.
..
Sarki sahibul hairi yaci gaba da ragargazarsu tamkar mai yanke kabewa kafin a jima yai fata fata da su babu sauran mutum daya a tsaye gabansa koda yaga ya sami wannan nasara sai ya cika da tsananin murna kawai sai ya saba gatarin a kafadarsa ya bude kofar dakin ya fito.
.
A wannan lokaci duk jikinsa yayi kaca kaca da jini hatta fuskarsa kuwa sai da ya cire hular karfen dake kansa sannan ya goge jinin akan idanunsa fitarsa ke da wuya sai yaga wannan kyakkyawar budurwa a tsaye tana jiransa koda ta gasnhi rike da gatarin sihiri sai ta tareshi da farin ciki ta kama hannunsa
.
Faruwar hakan keda wuya sai suka face bat a tare suka bayyana cikin wata babbar turaka wadda akayi matukar kawata da kayan kawa iri iri daga can kuryar kudu an ajiye wani shimfidadden gado na alfarma irin na sarakai kwance akan gadon kuma a lullube cikin mayafi ba wani bane face bawa HALUF yana ta sharar barci tamkar wanda ke dakin matarsa.
.
Nan fa sarki sahibul hairi ya cika da tsananin mamaki domin shi a saninsa ya baro bawa haluf a can bayan gari toyaya akayi ya shigo har ma ya sami jiki yana barci mai nauyi haka.
Koda kyakkyawar budurwar ta fahimci cewa sarki sahibul hairi na mamakin ganin bawansa haluf a cikin wannan turaka sai tayi murmushi sannan ta zauna a gefen gadon tana mai fuskantar sarki sahibul hairi tace dashi.
.
Yakai wannan jarumi uban jarumai ai saika zauna don ka huta sannan na baka amsoshin tambayoyin da kayi mini dazu sarki sahibul hairi ya dubeta cikin kaduwa yace yanzu ni ina na ga lokacin zama alhalin nayi sata a cikin wannan gidan sarautar kuma na tabbatar da cewa da zarar an ankara cewa an dauke wannan gatari dole ne a bazama nemana''
.
Koda jin wannan batu sai kyakkyawar ta dubi sarki sahibul hairi da wani irin kallo mai tattare da alamomin tambaya tace ka kwantar da hankalinka yakai mai birnin Misra ka sani cewa kana tare da wadda tafi kowa sanin sirrin gidan nan.
Gama fadin haka keda wuya sai ta mike tsaye taje kan wani tebul ta dauko tambulan na ruwan inibi tazo Gaban sarki sahibul hairi ta ajiye kofunan ta tsiyaya ruwan inibin a ciki sannan ta dauki kofi guda ta mika masa guda take ta kai kofin bakinta ta fara shan ruwan inibin
ya yinda sarki sahibul hairi yaga ta sha ruwan inibin sai shima ya sha nasa kyakkyawar tayi dariya tace ai nasan cewa in ban shaba kaima ba zaka sha ba domin akwai alamar cewa kana zargi zan iya ha intarka''
.
Sarki sahibul hairi yayi murmushi ya ce ai a duniya idan akwai abinda nake tsoro bai wuce kaidin ya mace ba domin zata iya sawa mutum ya rasa mulkinsa dukiyarsa da rayuwarsa gaba daya.
.
Kyakkyawar tai murmushi tace hakika zancenka dutse ne to amma ina sonka saki jikinka dani domin nai maka alkawarin ba zan cutar dakaiba.sarki sahibul hairi yace to shikenan na gode.
Yanzu kafin ki bani labarin komai ina son ki gaya min yadda akayi bawana haluf ya shigo cikin wannan turaka taki har ya kama barci haka tamkar yana cikin dakinsa 
kyakkyawar na jin wannan tambaya sai tayi murmushi tace na yarda zan baka wannan labari amma dole sai na fara da gabatar da kaina a gareka da farko dai ni sunana gimbiya shukura kuma nice matar sarki barusa mai mulkin wannan birni na Askandariyya.
.
Koda jin wannan batu sai tsoro ya kama sarki sahibul hairi ya mike tsaye daga inda yake zaune ya danja da baya yace ke kuwa menene dalilin da ya sa kika ci amanar mijinki har kika taimaka mini na dauko wannan gatarin nasa na sihiri??
.
Sa adda gimbiya shukura taji wannan tambaya sai ta bushe da mahaukaciyar dariya tace ai cin amanar maci amana ibadane yakai wannan jarumi kayi sani cewa asalin sarautar birnin nan ta mahaifinace amma tun ina cikin mahaifiyata uban sarki barusa ya kashe mahaifina alhalin ya kasance babban amininsa kuma wazirinsa don wai ya gaji dukiyarsa da karagar mulkinsa
A wannan lokaci sarki barusa baifi shekara bakwai ba ni kuwa kamar yadda na gaya maka ko haihuwata ba ayi ba amma mahaifiyata na dauke da cikina wata shida bayan shekara bakwai sai uban sarki barusa ya mutu sakamakon cutar ajali don haka sai barusa ya gajeshi yana da shekara goma sha bakwai a duniya ni kuma a lokacin ina da shekaru goma kacal.
.
Tun kafin sarki barusa ya hau kan karagar mulki ya shaku dani ainun kuma yake nuna min tsananin kauna A zahiri ina nuna masa kauna amma cikin zuciyata na kanji na tsaneshi kamar yadda na tsani mutuwata mahaifiyata ta bani labarin cewar a gaban idanunta mahaifin barusa ya kashe mahaifina ya haye kan karagar mulkinsa amma bai san cewa tana labe tana gani ba
.
Dama mahaifiyar tawa ta lura da cewa baruwa na sona don haka saita rokeni da na yarda na aureshi ko don na samu damar daukar fansar ran mahaifina akansa da wannan manufa a zuciyata na girma na isa aure a lokacin da aka daura mini aure da sarki barusa tsawon shekara shida ina tare dashi bamu samu haihuwa ba kullum sai nayi yunkurin hallakashi amma sai na kasa bisa wannan dalili ne na fake da batun tafiyar neman maganin haihuwa wajen bokaye amma a zahirin gaskiya ba maganin haihuwar nake nema ba 
..
Dama nake nema wacce zan iya hallaka sarki a cikin yawona neh na hadu da wani shahararren boka wanda ya sanar dani wai ba zan taba samun damar hallaka sarki barusa ba face na mallaki wadansu sirrikan tsafi guda dari ba daya su kuwa wadannan sirrika suna nan a jikin wata karamar yarinya mai suna alfila
.
Yar wani mashahurin matsafi kuma jarumin gaske ana kiransa da suna awaisu koda naji wannan batu sai na tambayi bokan nace yanzu ya za ayi naje inda wannan yarinya take har na sami sirrikan tsafi daga gareta?
.
Bokan ya kyalkyale da dariya sannan ya murtuke fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa yace ke yarinya baki isa kije inda wannan yarinya take ba domin tana can cikin wani gida dake tsakiyar tekun bahar zallus mallakin sarkin bokayan aljanu na duniya mai suna shamzubul Azwas.
.
Yarinya ke dai baki isa kije wannan wuri ba har ki sami ikon shiga cikin wannan gida amma idan kikayi hakuri nan da wadansu yan shekaru kadan akwai wani jarumin sarki da zaizo birninku neman gatarin sihirin da kuke bautawa idan kika taimaka masa ya mallaki gatarin sihirin za ki iya tafiya tare da shi izuwa tsuburin bahar zallus ku shiga har cikin gidan boka shamzubuk Azwas ku dauko yarinya alfila a sannan ne saiki biya bukatarki ta samun surrikan jikinta''
.
Lokacin da bokan yazo nan a zancensa sai na tambayeshi nace tayaya zan iya cire sirrikan tsafin daga jikin yarinyar?
Koda jin wannan tambaya sai bokan ya bushe da dariya yace ai wannan kuma aikinmu ne na bokaye ba naku ba kedai da kinga kun dauko yarinyar saiki san dabarar da zakiyi ki raaba abokin tafiyar taki da ita ki kawota gareni.
.
Tunda naji wannan batu sai naji hankalina ya dugunzuma naji cewa ko kadan ban yarda da wannan boka ba da ga wannan rana na dada jajircewa wajan neman ilimin tsafi nayi yawo kasa kasa gari gari ina ziyartar bokaye ina yi musu alheri mai yawa suna koya mini tsafi sannu a hankali nima na zama gawurtacciyar bokanya a sirrance ba tare da mijina ya sani ba.
.
Don haka a yanzu ina sanar dakai cewa hadimul asur so yake kawai ka Kawo masa wannan yarinyar don cika burin rayuwarsa amma ba dan ya biya maka bukata ba ni a yanzu nayi maka alkawari indai ka taimaka mini muka dauki alfila na ciri sirrikan tsafinta guda dari ba daya zanyi tsafin da zaka zamo attajirin da babu kamarsa a duniya zaka auri wadannan yan mata uku da babu kamarsu a duniya kuma sunanka da mulkinka zasu shahara ko ina cikin duniya.
Sa adda gimbiya shukura tazo nan a jawabinta sai sarki sahibul hairi yayi shiru ya shiga tunani mai zurfi yana juya al amarin a ransa daga can saiya dago kai ya dubeta yace.
Na gamsu da duk jawabinki kuma na amince zan baki hadin kai domin mu cika burin rayuwarmu yanzu saiki amsa mini tambayar da nayi miki akan yadda akayi bawana yazo cikin turakarki
.
Har ya kama barci mai nauyi akan gadonki na alfarma nan take gimbiya shukura ta kwashe labarin duk abinda ya faru tsakaninta da bawa haluf ta zayyana masa har izuwa sa adda ta yaudareshi da batun zata ceci rayuwarsa da ta maigidansa dalilin da yasa ya bata kansa kenan suka kwanta tare shukura tace maganar gaskiya ban tara da bawa haluf dan na samu haihuwa ba sai don kawai naci mutuncin mijina 
.
Kuma naci amanarsa saboda yadda nasan cewa yana tsananin tsanar bakar fata a rayuwar to yau gashi matarsa da yake matukar so fiye da komai a rayuwarsa ta kwanta da bakin fata kuma bawa.
.
Lokacinda gimbiya shukura tazo nan a zancenta sai takaici da mamaki suka kama sarki sahibul hairi ya jinjina kai yace hakika ku mata ababan tsoro ne domin dafinku da kaidinku yafi na maciji saurin tasiri a jikin dan adam hakika sai yanzu na fuskanci cewa ba karamar ni ima nake ciki ba da banyi aure ba
shukura na jin wannan batu saita bushe da dariya tace haka kuma ba karamar ni ima kayi asara ba domin duk mutumin da bai taba yin aure ba ya rasa kaso tamanin cikin dari na dadin duniya.
.
Zama da su fitina rashinsu kuma asara sarki sahibul hairi ya ce har yanzu dai ban fahimci wannan karatu naki ba abinda nake so dake yanzu mu ajiye wannanzancen komai a gefe daya kawai ki fitar damu daga cikin gidan sarautar nan mu tafi izuwa tsibirin bahar zallus don shiga gidan boka shamzubul azwas mu dauko yarinya alfila gimbiya shukura tayi murmushi tace yanzun nan zan aikata haka amma dai ina mai dada yi maka tuni da cewar ka manta da batun bokanka hadimul asur cewar zai taimakeka idan ka kai masa yarinya alfila tabbas yaudararka zaiyi kawai ya biya tasa bukatar abinda nake so dakai shine ka bani wuka da nama indai muka mallaki alfila tamkar burinmu gaba daya ya cika ne sarki sahibul hairi yayi murmushi yace ai shi kenan na amince da duk abinda kika shirya na baki wuka da nama..
.
A zuciyar sarki sahibul hairi ko kadan bai baiwa gimbiya shukura amana ba don haka duk yadda zaiyi ba zai yadda ta rabashi da alfila ba bayan sun daukota daga gidan boka shamzubul azwas acan karshen zuciyar sarki sahibul hairi sai yaji yana wasu wasu dangane da al amarin boka hadimul asur yaji cewa shima bai yarda da shiba kawai akawai alamun cewa shima akwai wani abinda yake so ya mallaka shiyasa yake son mallakar yarinya alfila
.
Abinda sarki sahibul hairi ya yankewa kansa hukunci shine indai ya sami nasarar dauko yarinya alfila kai tsaye zai tafi da ita zuwa ga mahaifinta sadauki awaisu sannan ya nemi taimakonsa bisa nemo wadannan yan mata uku
.
Sahibul hairi yace a cikin ransa idan idan har sadauki awaisu ya cika dan halak wanda yasan mutunci kuma har idan kaunar da yake yiwa yarsa dari bisa dari ce to lallai ba zaiki taimakonsa ba idan ya sada shi da alfila 
.
Sahibul hairi na cikin yin wannan tunani gimbiya shukura ta runtse idanunta ta fara karanto wadansu dalasimai na tsafi fara hakan keda wuya saiga wata jibgegiyar halitta ta ratso ta cikin saman rufin dakin kamar haske ta fado a gaban shukura wannan halitta ba komai bace face ALJANU DABARUS.
ALjani dabarus na da siffa irin ta bil adama wato yana da hannaye kafafu kirji wuya da kai sai dai kansa rabkeke ne yana da wangamemen baki cike da hakora hancinsa ma wawakeke ne amma idanunsa yan kanana neh ko yaushe jawur suke kamar gauta yana da dogayen kunnuwa wadanda suka kara masa muni fuka fukansa manya ne guda biyu
.
Koda saukar aljani dabaru a gaban gimbiya shukura sai ya rusuna ya kwashi gaisuwa sannan yace ya shubata me kike bukata daga gareni?
Ki sani cewa a shirye nake na sallama rayuwata don faranta miki shukura ta dubi aljani dabarus tace bukatata dakai kawai itace ka daukeni da wannan jarumin ka kaimu can tsibirin bahar zallus inda gidan boka shamzubul azwas yake koda jin wannan batu sai aljani dabarus ya kwalla ihu ya fadi kasa.
Yana birgima da tuba yace kiyi min rai ya shugabata ki yi sani cewa tsakanin mutum ko aljan duk wand aya kusanci gidan boka shamzubul azwas take yake narkewa ya dige ya zama ruwa don haka ina mai rokonki daki sauya min aiki da wata bukatar amma ba wannan ba
.... Koda jin wannan batu sai gimbiya shukura ta dakawa aljanu dabaru tsawa tace kai sha saha sha banza ai ba cewa nayi dole saika kaini har kofar gidan ba zaka iya ajiye mu nesa da gidan koda ya kai tafiyar rabin sa a ce
mu mun san yadda zamu karasa can kai kuwa saika jiramu a baya inda zaka iya tsayawa Aljani dabarus ya saki murmushin murna yace yauwa yanzu naji kan zance wannan ai ba matsala bace saiku hau bayana mu dau hanya
.
Koda jin haka sai shukura ta bude wata akwatu ta dauko wata garkuwa ta zinare ta mikawa sarki sahibul hairi tace ka ruke wannan domin zata maka amfani a gidan boka shamzubul azwas ba tare da gardama da fargabar komai ba yasa hannu ya karbi wannan garkuwar da hannun hadu 
A hannun dama kuwa ya damke gatarin sihiri nan take shukura ta taba kafadar bawa haluf kawai sai ya farka daga barci ya mike zaune zumbur a firgice,
amma da yaga sarki sahibul hairi tsaye a gabansa ruke da gatarin sihiri da bakuwar garkuwa sai murna ya kamashi gimbiya shukura ta dubi sarki sahibul hairi tace ai saika hau kan aljani dabarus ka zauna daga gaba dani da haluf mu zauna a bayanka.
Sarki sahibul hairi yace wannan ba laifi bane nan take kuwa ya hau kan bayan dabarus ya zauna faruwar hakan keda wuya sai haluf da shukura suka yunkura da nufin suma su hau bayan dabarus:
bazato batsammani sai sukaga bangon dakin ya dare gida biyu saiga sarki barbusa ya ratso ta ciki sanye da bakaken kayan yakin nan wadanda sarki sahibul hairi ya gani a gidan karkashin kasa a sakale a jikin bango tare da fararen daya sa da kuma jajaye.
ni kaina bayyanar sarki barusa a wannan lokaci ya razanani kamar ba zan iya ci gaba da typing din ba amma nayi ta maza naci gaba...
Sarki barusa ya dubi gimbiya shukura cikin tsananin bakin ciki idanunsa cike da hawaye yace yake bakar annamimiya maci amana ki sani cewa karyarki tasha karya domin baki isa ki ha inceni ba har ki hada kai da makiyina don a nakastani a rabani da abin dogarona wato gatarin sihiri.
.
Na dauki so da kauna na gaskiya na baki tun muna yara kanana ashe ke ba kaunata kike ba asalima so kike ki hallakani to kin makara domin na gaba yai gaba na baya sai labari ki sani cewa duk hirar da kukayi yanzu tsakanin ki da wannan sarki duk na gani a cikin madubin tsafina don haka naji dalilin da ya sa kike son ki hallakani don ki dauki fansar mutuwar mahaifinki.
.
Haba shukura ni idan kika ce dole a kaina zaki dau fansa bakiyi mini adalci ba domin babu sa hannu na akan mutuwar mahaifinki
asalima sa adda aka kasheshi ina yaro karami ban san abinda yake faruwa ba ba wai ina fadin haka bane donki janye ra ayinki sai donki sani cewa ke kin cika butulu maci amana haka kuma naji da bakinki kina cewa kin kwana da wannan bakin bawa don kawai kici amanata ki tozarta mutuncina tabbas kin sami nasara bisa hakan amma ki sani nima sai na tozartaki irin tozartawar da ba a taba yiwa wata ya mace ba a duniya kuma saina wulakantaki fiye da kima a cikin wannan birni namu na askandariiya yadda duk mai kaunarki idan ya tuno da abinda nai miki sai ya gwammace bai zo duniya ba yanzu a gaban idanunki zan yiwa wannan sarki da bawansa kisan wulakanci irin wanda baki taba gani ba.
.
Duk wannan bayani da sarki barusa ke yi sarki sahibul hairi na zaune akan aljani dabarus ya zuba musu idanu kawai ko gyara zaama baiyi ba maganganun da yake yma jinsu yake kamar tatsuniya ( kunji fa yarda da kai wajan sarki sahibul hairi) ita kuwa gimbiya shukura sa adda taji barusa ya gama jawabinsa sai ta kyalkyale da dariya lokaci guda kuma ta murtuke fuska tace kai barusa dakata kaji ka yi sake dan zaki ya girma ina tabbatar maka da cewa baka isa kayi mini komai ba domin dama na dade ina yin tanadinka.
.
Nima kuma a yanzu ban isa nayi maka komai ba tunda ban mallaki sihirin tsafin da zan iya ganin bayanka ba kafin na tareka mu gwabza yanzu ga dan uwanka nan sarki SAHIBUL HAIRI GAGARA BADAU saiku fara karawa mu gani ko zaka iya dashi ''
koda jin wannan batu sai sarki barusa ya juya ya dubi sarki sahibul hairi ya bushe da dariya sannan kuma ya murtuke fuska kawai sai yaga wata irin walkiya ta fito daga cikin idanun barusa ta bugi jikin sahibul hairi take rigar karfen da yake jikin sahibul hairi ta bace bat barusa ya bushe da dariya a karo na biyu yace yanzu saimu gwabza gaskiya da gaskiya.
.
Kafin sahibul hairi yayi wani yunkuri tuni barusa yayi tsafi saiga wani narkeken aljani nan ya bayyana a gabansa wanda a girma da kwarjini ya ninka Aljani dabarus sau uku.a lokacinne kuma wata katuwar takobi ta bayyana a hannun sarki barusa.
Cikin abinda baifi kiftawar ido ba sarki barusa ya haye kan narkeken aljanin suka afkawa sahibul hairi.
Nanfa aka fara azababben yaki ya zamana cewa sahibul hairi na kaiwa sarki barusa sara da gatarin sihiri shi kuma yana karewa da wannan katuwar takobin yana maida martani
wannan fada dai a sama suke yinsa bisa aljanun biyu cikin isa gimbiya shukura da bawa haluf kuwa sai suka daga kawunansu sama suna kallon abindake faruwa a cikin sararin samaniya.
Al amin ne sunana. Sa adda takobin sarki barusa ta hadu da gatarin sihiri sai kaji wata irin kara mai firgitarwa tamkar saukar aradu sannan kuma sai tartsatsin wuya gami da hayaki sun tashi al amarin da ya janyo girgizar gidan sarautar kenan gaba daya jama ar dake cikin gidan sai da hankalinsu ya dugunzuma saida aka shafe sa a uku ana wannan gumurzu dayansu bai sami nasarar taba jikin daya ba amma tuni sun rugurguza ginin fadar domin a duk sa adda dayansu ya kaiwa daya sara ya goce duk abinda ya sama sai wannan abu ya rabe gida biyu koda kuwa dirkar gini ce shi kansa tartsatsin wutar da ke zuba daga jikin makaman fadan nasu sai da ya haddasa gobara in ba don gimbiya shukura na kashe wutar ba da karfin sihiri da tuni fadar ta kone gaba dayanta. ....
Zan Cigaba Insha Allah

Share:

SARKIN SARAKAI BOOK 2. 03

 SARKIN SARAKAI BOOK 2. 03

Sarki sahibul hairi ya ci gaba da cewa 
yauwa fari kalace ta adalci da nuna alamun tausayi don haka su zansa ba tare da fargabar komai ba sai ya dauki fararen kayan ya sanya a jikinsa tsaf
wohoho duk wanda yaga sarki sahibul hairi a cikin wannan shiga ta fafaren kayan yaki dole ne ya bashi sha awa kuma ya bashi tsoro saboda sunyi masa kyau matuka kuma sun kara bayyana kwarjininsa a fili
.
Gama sa tufafin ke da wuya sai yaga wata kofar ta bayyana a jikin bango kai tsaye ya nufi kofar ya shiga cikinta sai gashi yana ratsawa ta cikin wadansu kofofi wannan na bin wannan tun yana irga kofofin har sai da ya gaji ya daina nan fa sarki sahibul hairi yayi ta ganin abubuwan tsoro iri iri da abubuwan mamaki kala kala amma duk inda yazo sai yaga ya wuce lafiya ba tare da wani abu ya same shi ba mamaki ya turnuke sarki sahibul hairi
.
Abin da bai sani ba shine duk wanda yasa wadannan fararen kaya na yaki babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai iya ganinsa kai hatta tsuntsaye da dabbobi ma bazasu iya ganinsa ba face mutum daya kwal a duniya ba wani bane face sarki barusa mai birnin Askandariyya
.
Sai da sarki sahibul hairi ya wuce kofofi dubu tara da dari tara sannan ya iso gaban wata matattakalar kasa koda ganin wannan matattakalar sai murna ta kama sahibul hairi
kai tsaye ya khau kanta ya kama tafiya har ya iso karshenta inda yaga wata kofar koda ya bude kofar saiya hango cikin fadar sarki barusa ga jama a nan a cike an kewaye sarki barusa ana fadanci
.
A lokacin wani mai baiwa sarki labari na zaune a gabansa yana ta sharara labari mai ban dariya sarki barusa na ta kyakyatawa saboda karfin dariyar tasa ma kiris ya rage bai fado kasa ba daga kan karagar mulkinsa cikin sauri sarki sahibul hairi ya fito daga cikin dakin ya kulle kofar ba tare da kowa ya ganshi ba sannan ya kama labe labe yana tunanin hanyar da ya kamata yabi yaje inda aka ajiye gatarin sihirin inda matsalar take shi bai san a ina aka ajiye gatarin sihirin ba haka dai ya ci gaba da labewa a cikin wani sako mai duhu yana tunani a lokacin da hadimai da dakarun gidan sarautar ke kai komo wasu mata gabansa suke wucewa amma basu ganshi ba.
**
wannan shine abinda ya faru ga sarki sahibul hairi bayan ya sha bakar wahala a cikin gidan halaka wanda ke karkashin kasa a masarautar sarki barusa
++
++ ++ ++ ++
ACAN BIRNIN MISRA KUWA kashe gari da sassafe fada ta cika makil da jama a tare da dukkan fadawan sarki kowa ya zuba idanu yana jiran fitowar sabon sarki wato mai rikon karaga AMINUL HAS.
don aga yadda zai tafiyar da nasa tsarin mulkin ana cikin wannan haline aka hango shi a tafe shi kadai a bayansa kafarsa sanye da wadansu tsofaffin takalma wadanda saboda tsufa har sun fara lalacewa sannan kuma yana rike da wata tsohuwar sanda itama duk ta fara farfashewa rigar dake jikinsa ma ba wata mai kyau bace rigace irin wadda kowanne irin talaka zai iya sawa
.
Koda ganain Aminul has a cikin wannan shiga sai su waziri suka shiga duban junansu suka fara dariyar farin ciki jama ar gari kuwa sai suka cika da dumbin mamaki suka kurawa aminul has idanu a lokacin da jama a suka dare suka bashi hanya ya nufi kan karagar mulki dama a wannan lokaci kowa a tsaitsaye yake har saida aminul has ya zauna a kan karaga sannan fadawa suka zazzauna a mazaunansu suma mutanan gari sai kowa ya nemi wuri ya zauna take fadar tayi tsit kamar mutuwa ta gifta
.
Cikin nutsuwa sarki aminul has ya mike tsaye ya dubi jama arsa cikin fara a da walwala yace yaku jama ar birnin misra kuyi sani cewa adalin sarkinku wato sarki sahibul hairi wanda yai tafiya bai tafi ba yana nan
.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama kowa da kowa fadar ta sake rude wa da hayaniyar jama ah koda ganin haka sai Aminul has ya daga hannu aka yi tsit sannan yace nasan kun shiga rudani bisa jin abinda na fada yanzu to amma abin da na ke nufi anan shine sarki ya tafi amma ni wakilinsa ne duk irin mulkin da yasaba yi akansa zanci gaba ba zan sauya komai ba
.
Ban yarda mai mulki ko wani attajiri ya zalunci talaka ba duk mutumin da yayi laifi za a hukuntashi kamar yadda za a hukunta kowa da kowa.
Sa adda jama a sukaji wannan batu sai suka barke da shewa suna tafi kowa ka dubi fuskarsa sai kaga ta cika da annuri amma ban da ragowar fadawa su waziri Akiyanu wadanda suka murtuke fuskokinsa sai muzurai suke kamar zasu fashe da kuka don bakin ciki musamman waziri Akiyanu ji yayi kamar ya tashi yaje ya soke aminul has da takobi yayi juyin mulki nan take
.
Sarki aminul has yaci gaba da bayani yana mai tabbatar da cewa za aci gaba da yiwa jama a adalci da kuma taimakon marasa shi haka dai yayi ta bayanai har ma yana kirkiro sababbin abubuwa don farantawa talakawa haka dai taro ya watse kowa yana farin ciki aminul has ya mike tsaye ya shiga cikin gidan sarauta inda ya wuce kai tsaye izuwa cikin turakar sarki sahibul hairi.
Da shigarsa cikin turakar sai ya iske matarsa shulaiba zaune a gefen gadon taci ado fuskarta cike da annuri ya yinda ta dago kai suka dubi juna sai kowannansu ya Kama murmushi saboda tsananin farin ciki aminul has ya matsa gareta ya zauna daf da ita sannan ya ajiye sandarsa akan gadon a gefe daya koda ya sunkuya da nufin ya cire takalman kafarsa sai tayi wuf ta tare hannayansa tace A kul ka cire wadannan takalma lallai dasu zaka yi barci akan wannan gado mai Albarka.
Yayinda Aminul has yaji wannan batu sai yayi murmushi yace ki gafarceni yake abar kaunata hakika na sha afa da dokokin da kika shimfida mini bisa wadannan takalma da kuma wannan sandar amma ba komai bane ya haddasa hakan ba face tsananin farin ciki kasancewar yau ne zamu shafe dare daya daga cikin dare sittin na farin ciki akan wannan gado na sarauta 
.
Yayinda shulaiba taji wannan batu sai tayi dariya sannan ta mike tsaye taje ta rufe kofar turakar ta kuma kashe gaba dayan fitilun dake cikin turakar dakin yayi duhu matuka yadda ko tafin hannu mutum ya daga ba zai iya ganiba.
++ ++ ++
Al amarin waziri Akiyanu kuwa sai suka kasa tashi daga filin fadar saboda tsabar bakin ciki ya zamana cewa kowa ya watse an barsu a zaune su kadai a cikin fadar har dare ya raba basu koma gidajensu ba sai da suka tabbatar da cewa babu kowa a cikin fadar sai su kadai a lokacin ma masu gadin kofar fadar sunrufe kofa sannan suka fara tattaunawa akan yadda zasu ga bayan sarki Aminul has.
Waziri akiyanu ne ya fara magana yace yaku yan uwana yan majalisa kun gani kuma kunji abubuwan da babban makiyinmu ya fada lallai ya zama wajibi muyi saurin kawai dashi in ba haka ba kuwa gaba dayanmu zamu wulakanta sai mun kaskanta a idon talakawa saimun talauce mun zama abin tausayi
.
Yayinda yan majalisa sukaji wannan batu na Akiyanu sai duk sukayi shiri aka rasa wanda zai ce kala daga can sai tsoho kilzam yayi gyaran murya yace yakai waziri Akiyanu kayi sani cewa dolene a dawo kan maganata ta farko wato dolene mu yiwa aminul has juyin mulki a dare daya idan ba hali kawai muje mu kashe shi yanzu yanzu a cikin wannan dare
.
Waziri Akiyanu yayi murmushi yace kai kuwa dadina dakai kenan ka cika gaggawa na yarda da shawararka cewa mu sa a kashe shi a cikin darennan amma ba mu da kanmu za muyi wannan aiki ba domin aikin ne mai hadari manufa ta anan inda bamuci nasara ba asirinmu zai tonu a hallaka mu amma idan wasu muka sa sukayi wannan aiki kome za ayi musu ba zasu fadi cewa mune muka sasu ba
.
Abinda za ayi kawai shine yanzu idan muka bar nan zan tura a kirawo mini manyan yarana amintattu bakwai wadanda zasuyi wannan aiki a gobe da daddare ina tabbatar muku da cewar sai dai a wayi gari sarki ya mutu kun san kuwa yana mutuwa nine zan hau karaga kasa ta zama tamu
.
Koda jin wannan batu sai gaba dayansu suka bushe da dariyar mugunta dariyar da suke ce masu gadin kofar fadar suka jiyo suka fahimci cewa akwai mutane a ciki dan haka sai suka rugo da gudu suka bude kofar suka haska fitilu koda sukayi arba dasu waziri akiyanu sai suka zube kasa suka kwashi gaisuwa nan dai su waziri Akiyanu suka tarwatse kowa ya tafi gidansa cikin farin cikin muguntar da suka kulla.
.
Lokacin da waziri Akiyanu ya isa gida sai ya tsaya cikin wani babban falonsa inda ya saba ganawa da jama arsa ya zauna nan take ya kira wani bawanda mai suna JAMASI ya umarceshi daya hau doki a cikin wannan dare ya tafi izuwa gidajen wadansu barade su uku musabu, Akaifu da samar yace ya gaya musu cewa suzo yanzu yanzu yana son ganinsu a gidansa cikin rawar jiki jamusi ya fita daga cikin falon ya tafi cika umarni
.
waziri akiyanu na nan zaune a falonsa har tsawon kusan rabin sa a sai ga musabu da akaifu da samar sun bayyana kamar wadanda aka jefosu daga sama cikin biyayya su duka suka zube kasa gaban waziri Akiyanu suka kwashi gaisuwa.
Su dai wadannan barade uku sune manyan mayakan birnin misra wadanda sarki sahibul hairi ke takama dasu domin duk sa adda zai bita yaki sune suke take masa baya kasancewar waziri akiyanu mai dukiyane saiya dinga siye zuciyoyinsu da abin duniya ya zamana cewa yana yi musu kyauta da alheri mai yawa fiye da tunaninsu su kansu sun dade suna mamakin dalilin da yasa yake musu wannan alheri bisa dalilin haka ne suke matukar yi masa biyayya duk abinda ya umarcesu dayi ba zasu ketara ba A zahirin gaskiya ba wani abu bane yasa yake musu alheri ba face tanadin irin wannan rana wacce ya san cewa ko ba dade ko bajima zatazo amfaninsu zai taso.
.
Bayan su barde musabu sun gama kwasar gaisuwa ga waziri akiyanu sai ya dubesu cikin murmushi da girmamawa ya yi musu izinin zama akan kujeru na alfarma ba tare da gardamar komai ba kuwa suka zauna cikin nutsuwa ya sake dubansu yace yaku wadannan zaratan jarumai kuma dirkokin misra ina mai mika godiyata gareku da kuka amsa wannan gayyata tawa ta bazata kuma a cikin wannan dare na san zakuyi mamaki matuka to amma idan kuka dubi sabon yanayin da muka shiga na mulkin kasar nan bai kamata kuyi mamaki ba ku duka kun sani cewa sarkinmu yayi gagarumar tafiya mai tsananin hadari da kowa ya san ba zai taba dawowa ba hakane ko ba hakaba!?
.
Gaba dayansu ukun suka amsa da cewa wannan haka ne gaskiya kam Waziri Akiyanu yayi murmushi sannan yaci gaba da cewa a halin yanzu galadima Aminul has ne sarkinmu maimakon ace nine na hau karagar mulkin.
Ina tabbatar muku da cewa idan yaci gaba da mulkinmu ba zan iya ci gaba da muku alherin da na saba yi muku ba domin kuwa zan talauce na zama fakiri..
Abinda nake so daku shine ku bani hadin kai mu kawar da gwamnatin Aminul has mu kafa tamu idan har mukayi nasarar hakan nayi muku alkawarin zan sanyaku a cikin manyan yan majalisata kuma na baku dukiya mai yawa irin wacce baku taba mallaka ba a rayuwarku idan aka sami akasi akan wannan aiki to kada ku kuskura ku fada sunana domin kun san illar da hakan zata iya haifarwa ina mai dada tabbatar muku da cewa dani da sauran yan majalisa duk bakinmu daya muna da goyon bayansu dari bisa dari
.
Lokacinda su barde musabu suka ji wannan jawabi daga bakin waziri sai duk suka bushe da dariya a lokaci guda kamar hadin baki Al amarin da ya bashi mamaki kenan
musabu ya dubi Akiyanu cikin nutsuwa yace ya shugabana kayi sani cewa yadda muka yarda da kanmu ko sarki sahibul hairi kace mu yiwa juyin mulki zamu iya bare galadima Aminul has wanda bashi da jarumtaka kuma bashi da karfin sihiri na kare kansa muna tabbatar maka da cewa cire silin gashi daga cikin tandun mai yafi wannan aiki wuya a daren gobe zamu je har cikin turakar sarki mu kashe shi salin alin ba tare da kowa ya ganmu ba hatta iyalansa kuwa
.
Cikin mamaki waziri akiyanu ya dubi musabu yace tayaya zaku iya wannan aiki alhalin ciki da wajen gidan sarautar a zagaye yake da dakaru masu tsaro dare da rana
musabu ya sake yin dariya shi kadai a karo na biyu yace ai kowa akan aikinsa sarki ne wannan aikinmu ne ba naka ba.
Don haka ka kyalemu muyi aikinmu kawai sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba'
waziri akiyanu ya zazzaro ido yace wanne hanzari ne daku?
Musabu yace duk da cewa wannan aiki mai sauki ne a wajanmu amma hadarinsa na da matukar yawa dalilina anan shine koda bayan ka zama sarki ne idan bisa tsautsayi wani ya ganmu a sa adda muke wannan aiki tofa sai sirrinmu ya tonu har abada jama aba zasuga kimarmu ba da mutuncinmu ba sbd haka ba zamu fara wannan aiki ba face ka bamu dukiya mai yawan gaske ta kimanin rakuma dari dari da shanu hamsin hamsin da kuma gonakai goma goma
.
Koda jin wannan batu sai waziri ya bushe da dariyar farin ciki har da tafa hannaye sannan yace gobe da safe zan dankawa kowannenku wannan dukiya a hannunsa idan aka wayi gari na samu labari cewa galadima ya mutu zam kara muku rubi uku na wannan dukiya yayinda su barde musabu sukaji wannan lafazi sai suka cika da murna nan take suka yiwa waziri sallama suka tafi.
Kamar yadda waziri akiyanu ya yi alkawari haka al amarin ya kasance wato kashe gari da safe ya sake turawa aka kirasu baradan uku ya basu wannan dukiya su kuwa suka tafi suka zauna suna ta shirye shiryen yadda zasu sami nasara bisa wannan gagarumin aiki dake gabansu
.
Lokacin da dare ya fara rabawa sai musabu Akaifu da samar sukayi wata irin shiga ta bad da kama gaba dayansu bakaken kaya suka sa sama da kasa suka fufe fuskokinsu da babaken rawani ya zamana cewa idanunsu kadai ake gani hatta kufen takubbansu da kakalminsu bakake ne bayan sun gama wannan kimtsi sai suka nufi gidan sarautar yayinda suka isa daf da gidan sai suka hada hannayansu waje guda sukayi kawanya faruwar hakan keda wuya sai ga wata guguwa ta zagayesu guguwar ta suresu a sama ta rika yin katantanwa dasu nan take suka rikide suka zama guguwar ta bace dasu bat !!
A can cikin gidan sarauta kuwa yaune dare na biyu ga sarki Aminul has tare da matarsa da samun wannan kwanciya yin barci a gadon sarauta tun a farkon darensuka yi barci suna ta shara mafarkai masu dadin gaske shulaiba na cikin yin mafarki ne ta farka daga bacci kawai sai taji bawali ya kamata don haka saita sauko daga kan gadon ta shiga kewaye ta bar Aminul has a kwance bisa gadon yana ta shara barci abinsa
.
Shigarta cikin kewayen keda wuya sai ga guguwa ta bayyana tana mai kewaye gadon karfin guguwar yasa gashin kan Aminul has ya kama tashi sama maimakon ya farka daga barci sai ya kara gyara kwanciya saboda jin dadin iskar guguwar da ke kadawa nan take kuma sai guguwar ta rikide ta zama su musabu suna zagaye da gadon kowannansu na rike da takobi ya dagata sama tsininta na kallon kasa
.
Lokaci guda suka dubu juna kawai sai suka yunkura da nufin su tsire cikin sarki aminul has da takubbansu bisa mamaki sai sukaji an ruke hannayansu tamau a sama sun kasa saukesu kasa nan fa suka ci gaba da kokarin sauke hannayen amma sai abu ya gagara sai da suka jarraba soke cikin shi sau uku amma suka kasa bisa dole suka hakura suka rikide izuwa guguwa suka bace bat faruwar hakan keda wuya saiga shulaiba ta fito daga cikin kewayen duk abinda ya faru bata sani ba koda ta hau gadon da nufin ta kwanta sai taga gashin kan Aminul has duk ya tarwatse kuma matashin kai ya fado masa mamaki ya kama ta amma dataga cewa Aminul has ya sauya wuri daga inda ya ke kwance saita yi tsammanin cewa garin mirgin murgin Ne ya jeho matashin kan kasa har gashin kansa ya barbaje kawai saitayi kwanciyarta taci gaba da barcinta
Al amarinsu barade kuwa lokacinda suka zama guguwa suka bace bat sai suka bayyana a can nesa da gidan sarautar su ukun suka dubi juna cikin matukar mamaki da razani masabu yace yaya akayi aminul has ya sami tsari da sihiri.
Akaifu yai ajiyar numfashi yace ni dai a tunanina kafin sarki sahibul hairi ya bar gida ya taimaka masa samar yace sam sam ba haka bane shin kun mantane cewa sarki sahibul hairi ya taba gaya mana cewa babu wani mahaluki da zai taba yin amfani da irin sirrikan tsafinsa 
ai duk yadda akayi ya sami wannan tsari ne daga wajan wani mutum daban kun san cewa tun da ya zama sarki dole ne shima ya mike tsaye ya nemi tsari musabu yace to yanzu menene abin da zai fishshemu?
.
Akaifu yace bamu da abinyi face muje mu sanar da waziri akiyanu duk abinda ya faru kuma mu bukaci ya bamu dama ta biyu in ba haka ba kuwa kun san cewa duk dukiyar da ya bamu karbeta zaiyi.
Ai kan wannan shawara baradan suka rabu kow aya tafi izuwa gidansa
Kashe gari da safe tun kafin alfijir ya keto su musabu sukaje wajan waziri akiyanu suka zayyane masa duk abinda ya faru sa adda sukaje hallahaka aminul Has
koda jin wannan batu sai bakin ciki ya turnuke Akiyanu zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone har saida kallar takaici ta fado masa cikin tsananin fishi ya dubi su musabu yace ku tashi kuje na bamu dama ta biyu lallai kuyi tunanin duk hanyar da zaku bi kuga bayan wannan mutum kafin nan kafin kwana bakwai in ba haka ba kuwa duk dukiyar da na baku sai kun dawo mun da ita.
Cikin sanyin jiki da tsananin damuwa su musabu suka mike tsaye suka tafi sai da su musabu suka shafe kwana uku suna tunanin hanyar da zasu bi su hallaka sarki Aminul has amma basu sami mafita ba a rana ta ukuce da yammaci suka tsinci dami a kala a wannan lokaci suna zaune su ukun a can bayan gari suna tattauna wa matsalar kawai sai suka hango sarki Aminul has tare da mai dakinsa da kuma dakaru kimanin mutum dari kacal sun fito ran gadi.
Da yake suna labe ne a bayan wani dutse babu wanda ya hangosu har tawagar sarki ta wuce bayan wucewar sune musabu ya dubesu yace.
Yauwa ga tsuntsu daga sama gasashshe yanzu menen abinyi Akaifu yai ajiyar zuciya yace ai ba hawan ba saukar kun sani dai cewa koda munyi gaba da gaba da sarki ba zamu iya hallakashi ba tunda mun jarraba mun gani
duk su ukun sukayi shiru suka shiga tunani mai zurfi daga can sai dabara ta fadowa samar yace ku bani dama na san abinda zanyi Ni kadai zanje na aiwatar da wannan aiki bana bukatar taimakonku.
.
Hm cikin matukar mamaki musabu ya dubesu yace haba samar tayaya zaka iya yin aikin da mu uku ya gagaremu samar yace ai ka san ance kowanne mutum da irin tasa hikimar kuma ai ita hikima baiwace don haka saiku kyaleni na jarraba sa ata
musabu ya dubi Akaifu yace yaka gani Akaifu yace aiba a kwacewa yaro garma mu bashi dama mu gani
koda jin wannan batu sai samar yayi girgiza ya bace bat su kuwa sai suka ci gaba da labewa a bayan dutsen suna jiran dawowar samar.
.
Lokacin da tawagar sarki aminul has sukayi nisa da bayan gari sukayi nisa da bayan gari sukayi nisa a cikindaji sai suka yada zango a bakin wata koramar koramar mai kyawun ruwa garai garai nan take aka kafawa sarki tanki aka sauke kayansa aka zuba a ciki
.
A rayuwar Aminul has babu abinda yake sha awa sama da harbin tsuntsaye dan haka ana sauka a bakin wannan korama sai yaga tsuntsaye iri iri suna ta shawagi a cikin dajin nan take yasa aka dauko masa kwari da baka ya fara kaiwa tsuntsaye hari bisa sa a kuwa sai yaga yana harbo tsuntsayen suna fadowa kasa ana debewa ana tarawa a cikin wani babban kwando Al amarin da ya jefashi cikin farin ciki kenan yaji zuciyarsa tayi fari ana cikin wannan hali ne samar ya baiyana a wajan ba tare da kowa ya ganshi ba cikin sanda ya isa inda dokin sarki ke daure.
Ba tare da kowa ya ganshi ba sai ya fiddo bakar ciyawa ya baiwa dokin ya cinye koda fruwar haka sai samar ya bace .
Sarki aminul has yaci gaba da harbo tsuntsaye cikin farin ciki da nishadi har sai da ya harbo guda dari a sannan gajiya ta riskeshi ya bada umarnin a tashi a tafi gida nan da nan kowa ya haye kan dokinsa aka juya da baya don a koma cikin gari koda fara tafiyar sai kawai aka ga dokin sarki yai turjiya yana mai dag kafafuwansa sama yana haniniya tamkar ya ga wani abin tsoro da ya firgitashi.
.
Kafin a yi wani yunkuri tuni dokin ya juya da baya sarki na kansa ya zabura da gudu ya nausa cikin dawa cikin tsananin tashin hankali dakaru sukabi bayansa a sukwane don su tsayar da dokin.
Ita kuwa gimbiya shulaiba kida taga abinda ya faru da mijinta sai ta sulale ta fado daga kan dokinta a sume saboda tsananin razana.
Guyson ke magana
dakaru da dokin sarki aka kasa tsere suna ta kokarin cimmasa amma abu ya gagara domin na gaba yai gaba na baya sai labari.
Aminul has yayi ta jan linzamin dokin don ya tsaya amma kamar ma kara masa gudu yake yi don haka sai ya rungumi kaddara ya zuba ido yaga inda...Ya zuba ido yaga inda dokin zai kaishi dokin yaci gaba da azababben gudu ya zamana cewa ya baiwa dakarun tazara mai yawan gaske babu yadda za ayi su cimmasa babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda dokin yake ratsawa ta cikin kwazazzabai da kayoyi ba tare da wata damuwa ba rami kuwa komai girmansa yana yin tsalle ya haye shi 
.
A iya sanin Aminul has bai taba ganin doki mai tsananin karfin gudu ba kamar wannan doki amma abin da ya bashi mamaki shne ya mallaki wannan doki fiye da shekaru ashirin kuma babu wanda ya taba hawansa face shi kadai yaya akayi wannan doki ya zama maguji haka alhalin bai taba yin tseren gudu da shi ba dokin yaci gaba da gudu irin gudun da idan aminul has yace zaiyi gangancin dira daga kansa sai iya hallaka kansa.
.
Haka dai dokin yai ta tsala gudu har ya iso bakin teku suka lume a cikinsa su biyun a dai dai wannan lokacin dakarun suka iso wajan bakin tekun sukaja tunga cikin thanzari wadanda suka iya ninkaya suka sauka kasa daga kan dawakansu suka fada cikin tekun suka hau lalube.
Saida aka shafe sa a uku suna lalube a cikin tekun amma ba a ga sarki da dokinsa ba bisa dole aka hakura aka fito daga cikin tekun aka juya da baya,
.
Lokacin da labari ya riski gimbiya shulaiba cewa da sarki da dokinsa sun lume a cikin teku an nemesu sama da kasa an rasa sai ta fashe da kuka da kyar kuyanginta suka dauketa suka dorata akan doki aka tafi da ita gida,
.
Nan da nan labari ya cika gari cewa sarki da dokinsa sun hallaka a can bayan gari cikin teku nan fa hankalin jama a ya dugunzuma aka kama kuka cikin kankanin lokaci fada ta cika makil da jama a ana ta koke koke da zullumi cikin tsananin bakin ciki ba komai ne yasa jama ar gari suke wannan bakin ciki ba face sanin cewa yanzu fa mulkine zai koma hannun waziri akiyanu idan kuwa mulkin ya koma hannunsa talakawa sun shiga uku babu wadanda zasuji dadi face masu mulki da tajirai.
Lokacin da labari ya riski waziri akiyanu da mukarrabansa cewa sarki ya hallaka a cikin teku sai farin ciki ya lullubesu sukaji kamar su zuba ruwa akasa su sha tun kafin su iso fada suka fara rabawa makada da mawaka dukiya suka shiga aikinsu kafin a jima kuwa tuni su waziri Akiyanu sun hallara a fadar don kaddamar da bakin nadin sarautarsa kafin ya hau karagar ne makada da mawaka wuka yi ta cashewa bayan nan sai waziri akiyanu ya mike yayi bayanin tsautsayin da ya sami sarki Aminul has har ma ya matso hawayan karya yana mai nuna bakin cikinsa duk da ya san cewa jama a sun san cewa murna yake da faruwar tsautsayin
.
Bayan ya gama jawabin sai ya tafi izuwa kan karagar mulkin don ya zauna ba zato ba tsammani sai aka jiyo sukuwar doki gaba daya jama ar dake fadar suka waigo suka dubi bakin kofa saiga sarki Aminul has bisa wannan dokin a sukwane
.
Da shi da dokin duk a jike suke sharkaf da ruwa Al amarin da ya jefa kowa a cikin mamaki kenan shi kuwa waziri akiyanu sai ya kasa zama a kan karagar mulkin ya kame kamar gunki sbd tsananin mamaki da jin kunya,
Da shi da mukarraban nasa duk sai ido ya raina fata sarki Aminul has yazo har gaban karagar mulkin fuskarsa cike da annuri da zuwa sai yaja tunga ya sauko daga kan dokinsa ya nufi kan karagar
.
Waziri akiyanu ya matsa gefe daya ya bashi hanya
a wannan lokaci gimbiya shulaiba na can cikin turakarta tana shara kukan bakin ciki tana cikin hakanne wata kuyanga tazo ta tabbatar mata da cewa ai ga sarki can ya dawo a cikin koshin lafiya koda jin wannan batu sai ta mike zumbur ta ruga izuwa fada da zuwanta bakin kofar fada saita hango Aminul has a zaune bisa karagar mulki jama a na kewaye da shi suna tayashi murnan tsira da rayuwarsa
.
Kawai sai ta tsaya a bakin kofar ta na ta kyalkyala dariyar farin ciki bayan sarki Aminul has ya gama karbar jajen murna sai ya mike tsaye ya fuskanci jama a yace'
yaku jamar wannan birni na misra na fuskanci cewa kunyi matukar mamaki da kuka ga na dawo gareku a raye?
Hakika akwai alajabi a cikin wannan al amari don haka akwai bukatar nayi muku bayanin yadda akai na kubuta da rayuwata
da farko lokacin da dokina ya zabura dani ya kama gudun tsiya dani sai hankalina ya dugunzuma ainun domin nine nayi kiwon dokin tun yana karami kuma ko sau daya ban taba jarraba yin gudu dashi ba haka kuma babu wanda ya taba hawa dokin in baniba
.
Ko da naga na kasa sarrafa wannan dokin don na tsai dashi sai na rungumi kaddara na zuba ido kawai naga inda zai kaini ban ankara ba sai gani nayi ya afak dani cikin teku kafin nayi wani yunkuri dani dashi mun lume izuwa karkashin tekun
ba zato ba tsammani kuma sai naga munci gaba da tafiya a karkashin ruwa tamkar akan doron kasa muke ba a ruwa ba nan ne fa na dada cika da mamaki ainun.
Haka dai dokin nawa yayi ta tafiya dani a karkashin teku har tsawon sa a biyar kawai sai naga ya juyo da baya cikin tsananin gudu fiye da na farko tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya nan da nan muka iso bakin gabar tekun muka fito waje fitarmu keda wuya ..Sai dokin ya tsugunna kasa ya kama kumallo nan take ya amayar da wata irin bakar ciyawa duk wannan abu da ya faru hannu na na rike da wannan sanda ta hannuna shi kuwa takalmin nan dake kafata bai bar jikina ba kwatsam sai naga wani danguntun Aljani ya bayyana a gabana wanda baifi na kifeshi da kwando ba.
Aljanin yayi sujjada a gareni yace an gaisheka ya wakilin adalin sarki ka kwantar da hankalin ka ka sani cewa indai kana tare da wannan sanda ta hannunka da kuma wannan takalmi na kafarka babu wani tsautsayi da zai sameka
.
Koda naji wannan batu sai na cika da mamaki nace kai kuma waye yaya akayi kasan wannan al amari?
Koda jin wannan tambaya sai aljanin ya bushe da dariya yace ni sunana MAKANUL URUD kuma na kasance mai tsaron wanda duk yake tare da wannan sanda da takalmin in baka mance ba asalin wadannan abubuwa biyu na mahaifin matarka ne wato Abu hakim a wajansa ta gajesu
.
Labarin wadannan sanda da wannan takalmi mai tsawon gaske ne koda zamu kwana bakwai a nan ba zan iya gama jawabi ba ina sanar dakai cewa makiyanka ne suka ciyar da wannan doki naka wata ciyawar sihiri don ya haukace yaje ya hallakar da kai lokacin da ya afka dakai cikin tekunne na biyoku cini na aza dokin a kaina naci gaba da tafiya daku kuma na dinga zuko iskar numfashi daga can saman tekun ina feso muku kuna shaka.
Hm kaji Aikin sihiri .
Wannan shine iyakar bayanin da zan iya yi maka a yanzu sai kuma idan ka sake ganina a karo na biyu koda gama fadin haka sai aljanin ya bace bat bacewarsa keda wuya sai na tashi dokina tsaye na haye kansa na taho nan fada.
Nima yanzu da wannan kalami nake muku sallama don haka na sallami kowa ya tafi izuwa gida a sanar da sauran jama a wadanda basu san hallarataba cewa ina nan a raye ban mutu ba
nan take fada ta watse jama a suka tafi izuwa gidajensu suna masu farin ciki 
Al amarinsu waziri Akiyanu kuwa batun bakin ciki a cikin zuciyoyinsu ba sai an fada ba domin yadda sukaga rana haka suka ga dare a wannan rana
kashe gari da sassafe sukayi shiri su takwas suka tafi izuwa wani kauye da ake kira BAHUS a sirrance don ziyarar wani maketacin boka wanda ake kira da SHUBURUL UZAB
.
boka shuburul uzab ya shahara a cikin yankin kasar misra harma ana ganin cewa in banda boka HADIMUL ASUR babu wand aya fishi ilimin tsafi
da rana tsaka su waziri suka isa gidan boka shuburul uzab inda suka iske shi tsaye a kofar gidansa ya kura musu idanu yana mamaki koda suka matso daf dashi sai ya dubesu ya tuntsure da dariya yace..
Lale marhaban da manyan baki wadanda na dade ina jiran zuwansu a irin wannan rana........
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama su waziri Akiyanu suka sauko daga kan dawakansu cikin sanyin jiki gaba dayansu suka risina suka kwashi gaisuwa sannan waziri ya dubi boka shuburul uzab cikin nutsuwa yace.
Yakai wannan boka mai daraja kai kuwa menene dalilin da yasa kace ka dade kana jiran zuwanmu gareka?
Idan har kana son mu ziyarceka me yasa tuntuni baka aika mana muzo ba?
Zan Cigaba Insha Allah

Share:

Popular Posts

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive

Recent Posts

Unordered List

 • Lorem ipsum dolor sit amet, consectetuer adipiscing elit.
 • Aliquam tincidunt mauris eu risus.
 • Vestibulum auctor dapibus neque.

Sample Text

Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipisicing elit, sed do eiusmod tempor incididunt ut labore et dolore magna aliqua.

Ut enim ad minim veniam, quis nostrud exercitation test link ullamco laboris nisi ut aliquip ex ea commodo consequat.

Pages

Theme Support

Need our help to upload or customize this blogger template? Contact me with details about the theme customization you need.