Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

ZAN IYA BAWA ARNE GIDAN HAYA?

ZAN IYA BAWA ARNE GIDAN HAYA ?

Tambaya

Assalamu Alaikum
Don Allah yahalatta a gina gida abawa kiristan haya?

Amsa

Wa alaikum assalam

ya halatta mana, tun da Annabi S.A.W. yayi mu'amala da Yahudawa kuma ya mutu silkensa na yaki yana wajan  Bayahude saboda Sha'ir din da ya amsa kamar yadda ya zo a hadisi ingantacce

Akwai gonakin Annabi S.A.W. da na sahabbai a wajan Yahudawan Khaibar inda suke aiki a cikinsu suke bawa musulmai rabin abin da ya fito na amfani kamar yadda ya tabbata a Sahihu Al-bukhari

In har an san zai yi barna ko sabon Allah a cikin gidan bai halatta a ba shi hayarsa ba, Allah  madaukakin sarki yana cewa: "Kada ku rika taimakekeniya wajan aikata sabo" Suratu Al'ma'idah aya ta: 2.

A cikin Suratu Al-mumtahanah Allah ya yi bayani cewa: Ana iya kyautatawa kafirai a kuma yi musu adalci mutukar ba sa yakar musulmai, hakan sai ya nuna halaccin ba su haya

Allah ne mafi sani

Dr, Jamilu Zarewa

15/12/2017

Gà dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH sai ya yi saving wannan number +2348122248585 sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatsApp.Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.

Share:

Love Letter

LOVE LETTER

        READ THIS AND APPRECIATE
                  MY LOVE TO YOU
I Love You. I know you will be shocked, but you mean so much to me. I try to get close to you but you seem to be looking elsewhere. The more I give you my attention, you think about someone else. My heart pains when I call and no one answers. I try to give myself to you but you seem not to be ready. Pls let me love you. Its me Allah. Everyday you open your inbox to read messages from your friends but how many times do you open  your Quran to read message from Allah? Please read this to  the end. My name is Allah. You hardly have time for me. I love you and always bless you. I am always with you.  I need you to spend 30 mins of your time with Me today. Don't pray. Just praise. Today I want this message across the world before midnight. Will you help ? Please do not cut it and I'll help you with something that you are in need of. Just dare Me! A blessing is coming your way. Pls Drop everything & pass it on. Tomorrow will be the Best Day of your Life. Don't break this chain. Send this to 14 friends in 10mins. The Clock Starts Now!

Share:

Qur'an

📖 Qur'ani na da harrufa 323,015
.
📖 Qur'ani na da Juzi'i 30
.
📖 Qur'ani na da Hizbi 60
.
📖 Qur'ani na da rubu'i 240
.
📖 Qur'ani na da ushuri 480
.
📖 Surorin Makkah 85
.
📖 Surorin Madinah 29
.
📖 Surarin da suka fara da 'Alhamdu' guda 5
.
📖 Surorin da suka fara da Tasbihi guda 6
.
📖 Surorin da suka fara da harrufa guda 19
.
📖 Guraren Sujjada a Qur'ani guda 15
.
📖 Farkon wanda ya fara bayyana karatun Qur'ani cikin Sahabbai a Makkah shi ne Abdullahi bn Mas'ud
.
📖 Kalma mafi tsayi a cikin Qur'ani ita ce 'Fa'asqainaakumuhu' ta na da harrufa 11 a rubutun ta na larabci.
.
📖 Qira'ar da tafi shahara wajen karatun Qur'ani ita ce ruwayar Hafs daga Aasim. Hafs ya bar duniya a shekara ta 180 H, Asim kuma 127H
.
📖 Tsuntsaye da aka ambaci sunayen su a Qur'ani;
*Alba'ubh
*As Salwa
*Al Guraab
*Al Jarad
*An Nahl
*Al Hudhuda
*Az Zubab
.
📖 Sahabin da aka ambaci sunan sa a Qur'ani Zaidu bn Thabit a cikin Suratu Ahzab
.
📖 Rabe-raben Qur'ani ; akwai Surori masu suna;
*As Saba'ud Diwaal- sune Bakara, Aali Imran, Nisa'i, Ma'ida, A'araf, An'am, Yunus. Su 7 ne, su suka fi tsayi.
*Akwai Almi'aini; daga bayan Yunus zuwa Surorin da suka kai ayoyi 100 ko kusa da haka
*Almathani
*Almufassal su ne kananan surori daga 'Qaaf' ko 'Hujrat'
.
📖 Surah mafi girma ita ce Suratu Fatiha
.
📖 Aya mafi girma ita ce Ayatul Kursiyyu
.
📖 Shugaban masu Tafsirin Qur'ani shi ne Imamud Dabariy
.
📖 Annabin da aka fi ambaton sunan sa a Qur'ani shi ne Annabi Musa (s.a.w) sau 136
.
📖 Sura ta karshen sauka cikin Qur'ani ita ce suratun Nasr (Iza ja'a)
.
📖 Aya ta karshen sauka a Qur'ani ita ce aya ta 281 a cikin Bakara (Wattaquu yauman) a magana mafi inganci
.
📖 Surorin da aka ambace su da sunan dabbobi;
*Baqara-Saniya
*Namli-Qudan Zuma
*Ankabut-Gizo Gizo
*Nahli-Turuwa
*Fiyl-Giwa
.
📖Surorin da aka ambace su da sunayen Annabawa;
*Suratu Yusuf
*Suratu Hud
*Suratu Ibrahim
*Suratu Muhammad
*Suratu Nuh
*Suratu Yunus
.
📖Surorin da aka ambace su da sunayen su taurari;
*Suratut Najm
*Suratul Qamar
*Suratud Dariq
*Suratush Shams
*Suratul Buruj
.
📖Surorin da aka ambace su da sunayen lokuta;
*Suratul Fajr
*Suratul Laili
*Suratud Dhuha
*Suratul Asr
.
📖Dabbobin da aka ambace su cikin Qur'ani;
*Baqara Saniya
*Ba'ubha Kwarkwata
*Zubaab Quda
*Namli Tururuwa
*Hudhuda tsuntsu
*Naaqah Raquma
*Khail Doki
*Bighaal Alfadari
*Himar Jaki
*Qusuurah Zaki
*Jaraad Fari
*Zi'b Kerkeci
*Kalb Kare
*Guraab Hankaka
*Fiyl Giwa
*Ankabuut Gizo Gizo
*Nahl Zuma
*Su'ban
*Ibil Rakumi
.
📖 Sunayen Mala'iku da ya zo cikin Qur'ani;
*Jibril
*Miika'iil
*Maalik
*Haruut
*Maarut
.
📖Daular da aka ambace ta cikin Qur'ani ita ce daular Rumawa-Ruum
.
📖 Qabilar da aka ambace ta a cikin Qur'ani ita ce qabilar Quraishawa-Quraish
.
📖Littattafan Tafsiri da suka fi shahara;
*Tafsirud Dabari
*Tafsiru Ibn Katheer
*Tafsiru Ruhul Ma'ani-Aluusiy
*Tafsirul Qurdabi
*Tafsiru Mafaatihul Gaib
.
📖Gurare 4 sunan Mai Gidan mu ya zo a cikin Qur'ani;
*Aali Imran aya ta 144
*Ahzab aya ta 40
*Muhammad aya ta 2
*Fathi aya ta 29.
.
Daga littafin
ماذا تعرف عن القرآن والنبي
Please don't forget to share, this is worth sharing.

Share:

MAGANGANUN MALAMAI GAMEDA HUKUNCIN TURA SAKONNIN HAPPY JUMU'AT

MAGANGANUN MALAMAI GAME DA HUKUNCIN TURA SAKONNIN

HAPPY JUMU'A;

JUMU'A MUBARAK;

JUMU'AH KAREEM;
da sauransu

A haqiqanin gaskiya wannan bashi da asali daga Magabata, kamar yadda manyan malamai suka bada fatawowi akai kamar haka:

-An tambayi Sheikh Fauzan Fauzan:

Menene hukuncin Musulmi yacema dan'uwansa Musulmi Jumu'a Mubarak a kowacce Jumu'a, ta hanyar turawa a waya da sauransu?

Sai yace:

"هذا لا أصل له، وهو بدعة، ولا يجوز التهنئة بيوم الجمعة، هذا لم يرد فيه شيئ، وليس من عمل السلف، فهو مبتدَع، والمبتدعة يستغلون الآن الجوالات والإنترنتات -على ما يذكرون-؛ ويستعملونها لترويج البدع؛ بهذه الطريقة."

Ma'ana:
Wannan baida asali kuma yin hakan bidi'ah ne, ba'a yadda mutum yarinka taya mutane murna ba, domin ba'a samo wani nassi akan haka ba, kuma bashi daga cikin aikin magabata wato. Wannan fararren abune, sannan kuma yan bidi'a suna yada wannan acikin wayoyi da internet, kuma suna anfani dashi domin yada bidi'a ta wannan hanyar.

-Shi kuma,  Sheikh Ahmad bin Yahya Annajmi (Rahimahullah) cewa yayi Kamar haka:

Yawaita kalmar JUMU'AH MUBARAK Shin haka ya hallata?

Sai yace:

"لم نعرف هذا عن السَّلف."

Ma'ana:
Bamusan wannan daga magabata ba.

-Haka kuma an tambayi Sheikh Abdulmuhsin Al-Abbad Kamar haka:

السؤال: -بناء على أن يوم الجمعة يوم عيد- هل يجوز التهنئة فيه كأن يقال: "جمعة مباركة" أو "جمعة متقبلة"؟

Ma'ana:
Idan muka dauki Jumu'a ranar idice,  shin ya hallata murinka taya juna murna aranar, Kamar mutum yace JUMA'A MUBARAK, ko kuma JUMA'A MUQABBALAH?.

Sai yace:

والله- ما نعلم شيئا يدل على هذا، أما بالنسبة لعيد الفطر، والعيدين فقد جاء عن الصحابة أنه كان إذا لقي بعضهم بعضا قال: "تقبل الله منا ومنكم" أو "تقبل الله طاعتكم").

Ma'ana:
Wallahi bamusan wani abu dake nuni akan hakan ba,
Amma Kamar idil fitr da kuma iduna guda biyu, haqiqa yazo daga sahabbai cewa idan dayansu yahadu da daya yana cemasa ALLAH YA KARBA MANA KUMA YA KARBA MUKU, Kokuma ALLAH YA KARBI BIYAYYARKU.

-Haka an tambayi Sheikh Abdul'aziz bin Abdullah Âl Sheikh cewa: Menene hukuncin fadin JUMA'A MUBARAK?

Sai yace:

ما لها أصل، يبثون في الجوال يوم الجمعة: "جمعة مباركة"، هي الجمعة مباركة بلا شك، وأن الله تعالى خصنا به، وقد أضل عنه اليهود والنصارى، لكن التهنئة به كل جمعة ما أعلم له أصلا.

Baida asali, suna turawa awaya ranar Jumu'a, JUMA'A MUBARAK
Ko shakka babu cewa ita ranar mai albarkace kuma Allah ya kebance mana ita, kuma an batar da Nasara da Yahudu daga gareta, to saidai taya murna acikinta bansan yanada asaliba.

-An tambayi sheikh bin Baaz Allah yajikansa: yayi dogon bayani dakuma tsoratarwa akan bid'a, akarshe dai yake cewa:

Idan mutum yana cewa dan uwansa wani lokacin batare da ya dawwama akantaba kuma bai yarda da cewa an samota anassi ba, kawai dai ta hanyar addu'a, to ina kwadayin hakan bazai zamo laifi ba. 

Amma barinta yafi domin kar ta zama Kamar sunnar data tabbata.

Yan'uwa! Wajibine mu nisanci bid'a ko yaya take.

Domin Manzon Allah ya tsoratar damu akan bid'a, kamar yadda yazo acikin hadisai da dama, daga ciki akwai irin hadisin da Bukhari ya fitar kamar haka:

عن النبي -صلى الله عليه وسلم- أنه قال: من عمل عملا ليس عليه أمرنا فهو رد. رواه مسلم والبخاري معلقا، وفي لفظ لهما:
من أحدث في أمرنا هذا ما ليس منه فهو رد.

Don Allah muji tsoron Allah mu kiyaye.

Allah yasa mudace.

Sabon tsari

*Ahmad El-Maude Zaria*

Daga kafarku mai Albarka
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Daarus-sahaabah Network Zaria, kaduna state, Nigeria.
+2347036108733

Share:

MIJINA BAYA BIYAMIN BUKATA, MENENE SHAWARA

MIJINA BA YA BIYA MIN BUKATA, MENENE SHAWARA ?

Tambaya

Assalamun alaikum, Malam mace ce mijinta ba ya iya biya mata bukata saboda raunin mazakutarsa, kuma ashe abin da ya raba shi da uwar gidansa kenan.

Kasancewar ba ya biya mata bukata ta shiga cikin halin damuwa, sannan ta yanke shawarar cewa: in ya kira ta shimfidarsa ta daina zuwa, to malam ta yi laifi game da wannan shawarar da ta yanke ?

Amsa
Wa alaikum assalam,

A shawarata  kamata yayi a kira magabatansu su xauna su tattauna a gano yadda xa'a warware matsalar.

Idan har ya tabbata ba cikakken namiji ba ne to xa'a bashi shekara daya ya nemo magani.

Idan ya warke shikenan, in bai warke ba kuma xa ta iya fadawa cikin haram idan taci gaba da xama dashi, to ya halarta a raba auran, kamar yadda aka raba da uwar gidan.

Yana daga cikin manyan manufofin aure: ma'aurata guda biyu su katange junansu daga haram, in har aka rasa wannan to akwai matsala a xamantakewar aure.

Allah ne mafi sani.

*Dr, Jamilu Zarewa*

22/11/2017

Ga dukkan mai son shiga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH* sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.

Share:

Hukuncin Wanda Yayi Sallah Da JANABA

```Assalamu alaikum```
```Malam ga tambayata kamar haka, mutun ne ya tashi da janaba da safe yana tashi sai yayi sallah asuba kuma yaci gaba da sallah har tsawon wannan ranar sai washe gari sai yatuna jiya baiyi wankan janaba ba shin yazaiyi wajen rama sallolin jiya Allah yasa mudace.```

_*AMSA:*_
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،

Wanda yayi sallah batareda Tsarki ba, ya wajaba agareshi yayi Tsarki sannan ya sake sallarsa abisa ittifaqin malamai koda a bisa mantuwa yayi.

*Imamun Nawawi* yace: Musulmai sun hadu akan haramcin yin sallah da hadasi, kuma sun hadu akan cewa bãta inganta ta kowane irin yanayi, sawa'un yana sane ko baya sane ko acikin mantuwa ne. Idan yayi sallar da janaba ne bai Saniba ko kuma a mantuwa to babu zunubi akansa. Amma idan yayi sallar yana sane cewa yanada janaba kuma yasan haramun ne yin sallah da janaba, to ya aikata zunubi mai girma.

والله أعلم،

***********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_

Share:

Nijeriya Ta Mutun Uku Ce

Najeriya ta mutum uku ce inji Malam Aminu Kano :

1. SHASHASHA,
2. BARAWO
3. MAHAUKACI

Bahaushe  = Shashasha, kulum nasa yake so ya mutu yagaje shi, in zaka rataye dan uwansa shi zai baka igiya.
Bayerabe  = barawo.
in kaji yayi shuru to yana cutar ka, in yace a yi misaya to naka yafi,
IBO = Mahaukaci.
yafi kowa morar kasar kuma baya iya zama a yanki sa, sai ana wasu amma kulum a raba kasa.
- Malam Aminu Kano 34 years

Share:

Golden Reminder

GOLDEN REMINDER

"And remind, for indeed, the reminder benefits the believers."  [Adh-Dhariyat 51:55]. 

✍🏼  Leave peacefully with people, because someday you will need them to accompany your corpse to the grave. 

✍🏼  Strive to perform Salat on time, for someday it will be your only true friend in the grave.

✍🏼  Endeavour to be obedient and dutiful to your parents, for you will become a parent someday if death did not overtake you. 

✍🏼  Embrace the act of forgiving people, so long as you also offend Allaah. 

✍🏼  Worship Allaah as if you are seeing Him, because He is seeing you. 

✍🏼  Recite the Qur’an often, for it will intercede on your behalf the Day of Qiyamah (Judgement). 

✍🏼 seize the slightest opportunity to do good, for you may not have the opportunity again. 

✍🏼  Make effort to rebroadcast this message, for it will count on your Scale of Deeds someday.

_May Allaah make our end better than our beginning.

Share:

Ya Halasta Rokon Addu'a?

TAMBAYA
=========
👇
Assalamu alaikum shin yahalasta inroki yan uwana musulmi sutayani da addu a gawata bukatata ta alheri

AMSA
=====
👇
Kwarai kuwa.
Musamman ma mutanen kirki, ya tabbata wani lokaci manzon Allah saw yace da dayyadina UMAR lokacin da zaije aikin Hajji, YA DAN UWANMU KARKA MANTA DAMU CIKIN ADDU'O'INKA.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

TAMBAYA DA AMSA

*Tambaya Da Amsa*
.
.
*DAGA DALUBAN ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
.
.
21-3-1439
10-12-2017
.
.
_1---------------Wanene Waliyyi???_
=
_Amsa---------------Waliyi shine wanda yayi imani da Allah kuma yakejin tsoron Allah sannan kuma yanabin sunnar Annabi (s.a.w) wannan shine waliyi****_
=
=
_2-----------------Shin dole ne waliyi sai yasamu karama????_
=
_Amsa----------Aa ba dole bane sai waliyi yazama yanada karama akwai waliyyai dayawa wadanda basuda karama sai karamar imani****_
=
=
_3---------------Wanene mafi daraja da falala acikin waliyyan Allah???_
=
_Amsa-------------Shine Sayyidina Abubakar Siddeq******_
=
=
_4-------------Wanene yafi daraja da falala tsakanin Annabawa dakuma waliyyai???_
=
_Amsa-------------Annabi guda daya yafi waliyyan duniya dukkansu****_
=
=
_5----------------Su wanene Ahalus sunnah wal jama'a???_
=
_Amsa-------------Sune wadanda suke akan irin abinda Annabi (s.a.w) da sahabbansa suka rayu akansa basu canza ba****_
=
=
_6---------------Menene yasa ake cemusu Ahalus sunnah???_
=
_Amsa---------------Saboda riqonsu da sunnah ta Annabi (s.a.w)*****_
=
=
_7----------------Shin a dalilin wanene aka saukarda aya ta 94 cikin suratun Nisa'i???_
  =
_Amsa--------------An saukarda itane Dalilin Usamah dan Zaidu****_
=
=
_8----------------Wanene mutuminda Annabi (s.a.w) yace yajiyo sautinsa yana rera karatun Alqur'ani agidan Aljannah???_
=
_Amsa------------Shine Haritha Dan Nu'uman (RA)****_
=
=
_9--------------Wanene yayi limancin sallar gawar Annabi Muhammad (s.a.w)???_
=
_Amsa----------Ba'abar wani mutum daya yayi masa limanciba shiga aka dingayi mutane goma goma suyi masa sallah su fito wadansu su shiga****_
=
=
_10-------------Wanene yayiwa sayyidatuna Khadija sallar gawa bayan rasuwarta??_
=
_Amsa----------------Ba'ayi mata sallah ba saboda lokacinda tarasu ba'a shar'anta sallar gawa ba*****_
=
=
_11------------- Shin hadisai guda nawane acikin littafin Sahihul Bukhari harda wadanda aka maimaita???_
=
_Amsa------------ Akwai Hadisai guda 7,257, idan aka cire wadanda aka maimata kuma sunzama  guda 4000*****_
=
=
_12----------- Hadisai guda nawane acikin littafin Sahihu Muslim harda wadanda aka maimaita???_
=
_Amsa------------- Guda 12,000, idan aka cire wadanda aka maimaita kuma shima dai guda 4000 ne*****_
.
.
Allah yasakama kowa da alkhairi,
.
.
.
*DAGA DALUBAN ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan
hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ , ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ
ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila
ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika

Share:

ZAN IYA AURAN ME CIWON LIMONIYA?

TAMBAYA
========
👇
SLM mlm barka da warhaka, mlm Dan allah nine ina da budurwa da muke soyayya inason xan aureta sai kai naji lbr wai tana da ciwon lamoniya 2n tana yarinya shin mlm idan nafasa auranta nayi yaudarane ko nayi daidai?

AMSA
======
👇
Ae limonia bata daga cikin jinyar da zaisa ka dena auren mace Sabida ita. Domin ba daukarta akeyi ba, haka ba kamar sikila bace, wadda ko yaushe kana kan hanyar asibiti da wuraren magani ba, limonia sai in ta taso, haka kuma da ansha magani ana warkewa, Sabida ina da wanda yake da limonia amma daga baya wanke kwata-kwata yanzu bashi da ita, ya warke.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Barka Da Safiya

​.....BARKA DA SAFIYA.....​

       ​Allah Yasanya Wannan Rana Tazama Samun Gafara Ga Dukkan Mai Zunubi Daga Cikinmu​, ​Ya Shirya Dukkan Wani Mai Sabo Daga Cikinmu, Ya Allah Ya Warakar Da Dukkan Marasa Lafiya Daga Cikinmu.​
    ​Ya Allah Kayi Rahama Ga Dukkan  Magabatanmu.​ ​Ya Allah Kai Mai​ ​Ikone Akan Dukkan Komai  *Allah Kasa Ranar Mutuwarmu Itace Ranar Farin Cikinmu. Allah Yasa Ranar Shiga Kabarinmu Shine Ranar Hutunmu. Allah Yasa Ranar Hisabi Shine Ranar Arzikinmu. Allah ya Sa mudace. Amin Ya Rabbi.​

Share:

YAWAITA SALATI GA ANNABI RANAR JUMA'A

⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖

YAWAITA SALATI GA ANNABI S.A.W ARANAR JUMA'A
➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
Annabi s.a.w* yana cewa: (Yana cikin mafificiyar Ranakunku Ranar Juma'a, dan haka ku yawaita yin Salati agareni acikinta, domin ana bujuromin da salatinku gareni)
@Saheehu Abu Dauda.

Annabi S.A.W  yace: (Duk wanda yayi salati a gareni, Allah zaiyi masa salati Guda Goma).
@Saheehul Jami'i

KADAN DAGA CIKIN FALALAR SALATI GA ANNABI S.A.W
➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
1-Wanda yayiwa Manzon Allah s.a.w Salati ya cikasa Umarnin Allah ne dayiwa dukkan masu imani.

2-Kuma yayi koyi cikin Abinda Allah da Mala'ikunsa sukeyi ga *Annabi s.a.w

3-Wanda yayi Salati guda ga Annabi s.a.w Allah zaiyi masa Huda Goma.

4-Za'a Rubuta masa Lada Guda Goma kuma a kankare masa zunubai guda goma.

5-Za'a Daukaka darajarsa sau goma.

6-Allah yana Amsa Adduar da akayi tare da Salatin Annabi s.a.w Acikinta.

7-Yana samun Ceton Annabi s.a.w ga mai Yawaita salati ga Annabi s.a.w.

8-Hanyace ta samun gafarar Allah.

_9-Hanyace ta Samun kariya da tsaron Allah ga mai yawaita salati ga Annabi s.a.w.

10-Manzon Allah s.a.w yana mayar da Salati ga dukkan wanda yayi masa Salatin.

11-Yin salati ga Manzon Allah s.a.w a wajan Zama yana sanyawa Mutum Rashin Asara a Ranar Alkiyama.

12-Hanyace ta magance Talauci.

13-Mai yawaita salati ga Annabi s.a.w duk lokacin da aka amabaci Sunansa, mai wannan halin baya cikin Marowata. kuma ya ku6uta daga Adduar dauwama cikin Azaba ga dukkan wanda aka ambaci sunansa baiyi masa salati ba.

14-Samun kusanci ga Annabi s.a.w a Ranar Alkiyama.

15-Annabi s.a.w yana sanin duk wanda yayi masa Salati.

16-Samun Rayuwa Mai Dadi.

ﺍﻟﻠﻬُﻢَّ ﺻَﻞِّ ﻋَﻠﻰ ﻣُـﺤﻤَّﺪٍ ﻭﻋﻠَﻰ ﺁﻝِ ﻣُـﺤﻤَّﺪٍ، ﻛَﻤَـﺎ ﺻَﻠَّﻴﺖَ ﻋَﻠَﻰ ﺇﺑْﺮَﺍﻫِﻴْﻢَ ﻭﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﺇﺑﺮﺍﻫِﻴْﻢَ، ﺇﻧَّﻚَ ﺣَﻤﻴﺪٌ ﻣَﺠﻴﺪٌ، ﺍﻟﻠﻬُﻢَّ ﺑَﺎﺭِﻙْ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﺤﻤَّﺪٍ ﻭﻋَﻠﻰ ﺁﻝِ ﻣُﺤﻤَّﺪٍ، ﻛﻤَﺎ ﺑَﺎﺭَﻛْﺖَ ﻋَﻠَﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫِﻴْﻢَ ﻭﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﺇﺑْﺮﺍﻫﻴﻢَ، ﺇﻧَّﻚ ﺣَﻤِﻴْﺪٌ ﻣَﺠِﻴْﺪ .

✍🏼Mustapha Musa

Share:

Today's Reminder

SECOND REMINDER. Thursday. FIX YOUR WORLD BY PLACING ALLAH, HIS MESSENGER AND THE QUR'AN IN THE RIGHT PLACE IN YOUR HEART. BismilLah

An Imam was struggling to prepare his Friday sermon and didn't want to be disturbed by his five year old daughter, so he removed a map of the world from his study, tore it into pieces and gave it to her to assemble with the promise that he would answer all her questions and play with her when she was done. He knew she would never be able to fix it.

To his amazement, in less than five minutes, she returned to him in his study with the map in perfect shape, every continent and every country in its place. The surprised father asked, ''Honey, you don't know anything about geography, so how did you fix the world so easily and quickly? The five year old girl smiled sweetly and replied, ''The picture of of THE HOLY QU'R' AN and the inscription LA ILLAHA ILLALLAHA MUHAMMADU ROSULULLAH was at back of the map and I knew that if ALLAH, His MESSENGER and QUR'AN are put in the right place, the whole world would be in perfect shape'.

That was just the right inspiration he needed for his sermon. He thanked his daughter and prepared a powerful sermon on the subject: "Fix Your World By Placing ALLAH, His MESSENGER and the QUR'AN in the Right Place in your heart ".
To whoever is reading this message, just place ALLAH, His MESSENGER and QUR'AN in the rightful place and your life will be in order.
I hope you understand this just like I do. Share and spread it to the world, let them know that THEIR WORLD CAN NOT BE COMPLETELY FIXED WITHOUT ALLAH, HIS MESSENGER AND THE QUR'AN.
MAY ALLAH BLESS US ALL AND KEEP GUIDING US ALL. AAMEEN.

Share:

ZAN CIRE HAKORIN MAKKAH SABODA KAUCEWA LAM'A A ALWALA TA?

ZAN CIRE HAKORIN MAKKA SABODA KAUCEWA LAM'A A ALWALATA?

                              *Tambaya:*
Mlm da gaske ne da ake cewa hakorin Makka lam'a ne? saboda ruwan alwala ba ya taba ainihin hakorin mutum?

                                 *Amsa:*
To malam a zance mafi inganci, bai zama dole ruwan kurkure Baki sai ya game dukkan hakora ba, saboda abin da ake nufi da kurkure baki shi ne zagaya ruwa a baki a fito da shi, don haka hakorin Makka ba zai kawo lam'a ba, amma kuma wasu malaman suna ganin kurkure baki ba zai cika ba sai ruwan ya game, don haka barin sanya hakorin Makka Shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin malamai abin so ne.

Ya wajaba ga maza su guji sanya hakorin zinare, saboda Allah ya haramta zinare ga mazan al'umar Annabi Muhd S.A.W kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta a Sunan dinsa a hadisi mai lamba ta: 1720.

Don neman karin bayani duba Alminhaj sharhin Müslim na Nawawy 3/105.

Allah ne mafi Sani.

12/11/2015

Asamwa:- Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

Today's Reminder

*🗓Rabi'ul-Awwal 24, 1439🗓*
*🗓December 13, 2017🗓*
*Yawm Al-Arba'aa*
*Wednesday*

All Praise is due to ALLAAH, The Forgiver and Concealer of Faults, The Guide to Repentance, The ONE who Responds to duas

Salaat, Salaam and Salutations Upon The Best of Creation, Our Beloved Nabi صلّى اللّـه عليه و سلّم

*O OUR MOST COMPASSIONATE اللّـه*, we ask YOU for guidance, piety, virtuousness and affluence, guard us with Islam all the time, and protect us from the malicious acts of the enemy and the envious

*O OUR CHERISHER*, YOU control all the hearts so make our belief in Islam steadfast, give us strength to overcome our weaknesses and be our guardian

*O THE MOST MERCIFUL اللّـه*, release our captives, heal our fractures, and give us the patience to face difficult times and win against our enemies

*O OUR MOST GIVING اللّـه*, save us from disease, agony, and ill-fate. Let us live a happy and healthy life, and enjoin upon us the same abode of martyrs and the neighbourhood of the Prophets

*O OUR MOST BELOVED اللّـه*, help us to always constantly and diligently remember,praise and worship YOU well

*O OUR BELOVED اللّـه*, let us love Imaan, and let us hate disbelief, blasphemy and disobedience, and make us among those who are guided by YOU

*O OUR اللّـه*, protect us from disbelievers, bless us with Imaan, forgive our sins, reward us with Jannah, keep us steadfast on Siraatul Mustaqeem and accept this dua of ours   آمِيْن يَارَبَّ الْعَالَمِينْ

صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ

Subhaanarabika Rabbil Izzati Amma Yassifoon Wassalaamun Alal Mursaleen Walhumdulillahir Rabbil Aalameen

*Reminder read the following dua 3 times after Fajr Salaah إن شاء الله*

سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ:
عَدَدَ خَلْقِهِ،
وَرِضَا نَفْسِهِ،
وَزِنَةَ عَرْشِهِ
وَمِدَادَ كَلِمَاتِهِ

Subhan-ALLAAHI wa bihamdihi, `adada khalqihi, wa rida nafsihi, wa zinatah `arshihi, wa midada kalimatihi

ALLAAH, is free from imperfection & I begin with HIS praise, as many times as the number of HIS creatures, in accordance with HIS Good Pleasure, equal to the weight of HIS Throne & equal to the ink that may be used in recording the words [for HIS Praise] *(Muslim)*

*BELIEVER REMINDS https://goo.gl/M7c3sc ON WHATSAPP*

Share:

Hukuncin Sallar Janaza Da Taimama

TAMBAYA
========
👇
Assalamu alaikum
Allah ya jikan mallam!
shin ya halatta sallar janaza da taimama, ko kuma wajibi ne sai da alwala?

AMSA
======
👇
SAYYIDISSABIQ a cikin littafin FIQHUSSUNNA yace, ita taimama chanji ce ta alwala, kuma duk abinda yake karya alwala, shine yake karya taimama, Sabida haka, idan Dalilin yin taimama ya hau kan mutun, to zaiyi taimama ne, sai yayi sallarsa a haka.
Kenan tinda ana yin sallar Farillah da taimama, kaga sallar janaza itace ma tafi chanchanta.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Menene Hukunci Na?

TAMBAYA
=========
👇
Assalamu alaikum malam fatan alheri inada tambaya
Wanda nasanine zaiyi aure sai family matan sunatambaya na akansa.
Thus yataba aure 2 months kawai sukayi da matan suka rabu sanadiyan baida lafiya.
Sunji yayi aure baijima ba yasaki matan shine suke tambayata dalilin rabuwan shi damatansa.
Idan nafadi masu nayi laifi ko inna boye nayi laifi? Yazanyi. Nagode

AMSA
======

Idan yarda da amincewa tasa akazo wurinka bincike, dole ne ka fito ka fadi gaskiya, koda kuwa wannana gaskiyar taka itace silar da zaisa ya dena aurenta.
Amma kuma bai halatta ba, ba'a tambayeka ba ka tare mutum Kayi masa zance akan matar da zai aura ba.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Hukuncin Fitsarin Yara

TAMBAYA
=========

Assalamu Alaikum mlm tmbyn anan shine naji anacewa Idan yaro karami Wanda baayayesaba yayiwa mutun fitsari zai iya yayyafa amma idan nace ce sai an zuba ruwa anmatse mlm ina gaskiar lamarin.

AMSA
=====
👇
Ya tabbata daga manzon Allah saw, idan ka duba nan kusa cikin littafin bulugul maram zaka sami hadisai ruwaya guda biyu.
Na farko, an kawowa manzon Allah saw karamin yaro, sai yayi masa fitsari, sai manzon Allah saw ya yayyafa ruwa a wurin wannan fitsarin.
  Ruwaya ta Biyu kuma, an kawowa manzon Allah saw wata Karamar yarinya, sai tayi masa fitsari, sai manzon Allah saw ya wanke wurin da ruwa.
  Da wannan ne, Malamai sukace, Sabida ika mace fitsarin ta yafi yawa, Akan na namiji.
  wasu sukace, Sabida ita mace tana jinin haila koda bayan ta girma, shi kuma jinin haila, Allah ya ambata da sunan kazanta.

Allah shine masani


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Tambayoyi Uku

TAMBAYA
========

Assalamu alaikum,

Mallam ina da tambayoyi  kamar haka:

1)Naji wani malami yace :Ãdam saw wannan da muka fito daga yayansa shine na karshe Kafinsa anyi wasu Ãlãm -Ãlam bila adadin.

2)Qudubai Allah kadai yasan adadinsu daga cikinsu akwai Wanda Allah yabada tasarrufin kula da iskar da bayi suke shãka wasu tasarrufin abin da bayi suke ci wasu ruwan da ake shã dasauran aiyuka na rayuwar bayi.

3) Sannan mallam me Mallam Sharia sukace game da "AUTÃDU, NUJBA'U da kuma QUDBA'U shin mutanene, ko Aljanu ko shaidanu ko kuma malaiku?  Don naji wani malami yace sunayin magana da Allah.

Dafatan Mallam yana cikin koshin lfy.

AMSA
======

1. Gaskiya ba haka bane.
Allah ya halicci mala'iku kafin ya halicci duk wani mutum.
Farkon wanda Allah ya fara halitta daga cikin mutane shine Annabi Adamu.
Wannan shine maganar da ta dace da doron Alqur'ani mai girma da Kuma sunnar manzon Allah saw.
  Sannan akwai hadisin ceto, Wanda Anas Dan malam ya rawaito daga manzon Allah saw, inamul Bukhari da Muslim suka fitar dashi, manzon Allah saw yace, Bayi zasuje wurin Annabi Adamu, suce dashi, KAINE WANDA ALLAH YA FARA HALATTA A DORON DUNIYAR NAN, KUMA KAINE WANDA ALLAH YA HALITTA DA HANNUNSA, MUNA SON KA ROKA MANA ALLAH KOWA YASAN MATSAYINSA.
  kaga kenan wani ma yazo yace Maka akwai wasu halittar Alam a doron kasa kafin zuwan Annabi Adamu, Wannan ba haka bane. ISRA'ILIYYAT ne kawai.
 
2. Wannan ba haka bane gaskiya.

3. Wannna kuma ban sani ba, sai dai a tambayi manyan Malamai.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Shin hakan Yayi?

TAMBAYA
=========
👇
Kamar kai ne kazo wurina sayen atampha,a wuri NA babu irin wadda kake so.sai NA baka kudi nace kaje ka sawo da kanka ba zan samu zuwa kasuwa ba,amma NA CE idan zaka biya kudin sai ka Dora min riba.ya cinikin ya ke?

AMSA
=====

Wannan cinikin bai halatta ba gaskiya.
  Dole idan da akwai a wurinka ka siyar masa, idan kuma babu ka tura shi inda zai samu, yaje ya gani ya zaba da kansa. Amma babu lefi ka rakashi Kayi masa ciniki Dan kar a cuceshi, sai ya dauki kudin da kansa ya biya, anan kuma ganin damarsa ne ya baka wani abu ko yayi Maka godiya ko yayi Maka Addu'ah ta fatan Alkairi.
  Ko kuma Kuyi yarjajjeniya dashi akan zai baka wani abu idan ka kaishi inda Ake siyarwa.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Macen da aka sawa rana

TAMBAYA
=========
👇
Assalamuaaikum
mlm tambayata itace👉
Wacce nasiha zaka yiwa samari da 'yan matan da akasa musu ranar aure
Dan yanxu malam abun ya tabarbare
Sai kaga muce ansamata rana ammah bata daina tara samariba
Dan Allah malam ka taimaka kayi wannan nasihar kamar yadda kasaba (wato yin amfani da ayoyin AlQur'ani da in gantattun hadisai)na gode Allah ya sakawa mlm da gidan aljannah amin summa amin

AMSA
======
👇
  To maganar gaskiya, manzon Allah saw yace, baya halatta wani ya nemi aure akan auren Dan uwansa, har sai ya dena ko yayi masa izini cewar yaje ya nemeta shi ya fasa aurenta.
  Sabida haka kenan, baya halatta ga mace tana da wanda akayi alkawari tsakanin iyaye, harma anje ga maganar sa musu rana, bai kamata tana sauraron wani ba wanda ba shi ba.
  Duk matar da kaga ansa mata rana da wani kuma tana sauraron wani daban, to koda ta ka aureta kana da tabbacin zata iya sauraron wani daban.
   Sannan ya kamata mata su sani cewar dole mutum daya fa zaki aura ba biyu ba ko sama da haka, kenan menene na batawa kanki lokaci kina sauraron wani daban? idan wanda aka sanya miki rana ne bakya sonshi, sai kiyiwa iyayenki bayani a farde maganar auren.
  Sannan wasu matan kwadayi ne ke kaisu ga haka, wato wani saurayin yana bata kudi, shi kuma wanda zai aureta tsakani da Allah, baya bata kudin da wannan na banza din yake bata. Tinda yasan yana bata kudi ne Dan bukatar kansa, ba Dan Allah ba.
  Sannan wata tana kula wani ne, Sabida yana taba jikinta tana jin dadi, shi kuma wanda zai aureta Sabida yasan tsakani da Allah yake sonta, idan ya bata rayuwarta a waje ma yasan aikin banza ne. Kenan wanna ma yana abinda yake kawowa zakaga mace tana kula wannan wanda yake sanya mata nishadi a duk lokacin da taso.
  Wasu kuma zugace irin ta kawaye, sai su kaiki Su baroki, Sabida kin sami wanda zaku Rufawa junanku asiri, Su kuma basason hakan, Sabida Su basu samu ba, kinga kenan idan baki fahimta ba sai su rabaki da zahiri ke kuma sai ki kama gaibu, nan gaba kuma ki zama abar tausayi.
 
  Shawara ta ga MAZA, duk wanda aka sanya masa rana da wata kuma take sauraron wani daban, sai ya rabu da ita yaje ya nemi wata, Sabida babu mutunci a ciki, koda ka aureta ma Akwai matsala, domin Ni kaina na fahimci so ake a sami wanda ya fika ne kuma ba'a samu ba.
  Kenan koda ta aureka zatana ganin kamar alfarma tayi Maka da ta aureka.
 
Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Ina tsarin Iyali

TAMBAYA
=========
👇
Assalamu alaikum malan Allah yasa wannan taimako da kakeyi ya zama sadakatul jariya.Ameen
Tambayata itace ina tsarin iyali nida mijina munada yara maza 2 daya 5yrs karamin kowa 2 da rabi, to nagaji dashan magani hakanan kuma Alhamdulillah yaranmu sunyi wayo inason in daina shikuma yace ba yanzu ba kuma mahaifiyata takan kirani ta bani shawara indaina planning hakan yanzune lokacin 'kurciyata da zan haihu tacemin wayanda suke dogon jinkiri harsu manyanta sukan samu matsaloli wurin haihuwa kamar CS da sauransu, nikuma ina tsoron indaina planning asamu ciki ya juyamin baya domin ko malaria nake yanzu zai damu yana cewa Allah yasa ba kwashe2 nayiba. Don Allah malan minene shawararka a gareni.
Na gode.

AMSA
======
👇
To dake dashi duk kuna naku tsarin, Allah kuma yana yimuku nasa.
  Sabida haka bazaku haihu ba sai Allah ya kaddara muku ita, sannan bazaku hana haihuwar Dan da Allah ya kaddara zaku haifeshi ba.
  Maganar tsarin iyali kuma, nasan haka Allah ya kaddara yayan da zaku haifa kenan. Domin da Ace zakuke ta haihuwa, tunanin Kuyi wani family planning ma bazai zo zuciyarki da ta mijinki ba.
  Maganar kwashe-kwashen ciki da yake cewa kinayi, to waye yake kwasa miki inba shi ba.
  Maganar gaskiya akwai jahilci a cikin wannan tsarin da yake yi a gidansa na rashin son haihuwa.
  Manzon Allah saw yace, Ku auri mata masu haihuwa, zanyi alfahari daku a ranar Alkiyama.
  Sannan wani ya taba zuwa wurin manzon Allah saw yace  zan auri wata mata, sai dai bata haihuwa, sai manzon Allah saw yace dashi, Rabu da ita, kaje ka auri mai haihuwa.
  Sannan kuma idan Allah ya karbe yayan da ya Baku nan gaba yaya zakuyi?
  Maganar magani kuma ya kamata ki rage, Sabida nan gaba kar ya baki matsala, kina neman shawarar likitoci akan hakan.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Me Ya kamata Inyi?

TAMBAYA
========
👇
Malam dan Allah inaso kaban shawara inada manema guda 2 daya yanada mata saiyana fadamin sabanin da sukeyi da matarsa yanacewabayajin dadin zama da ita
2 shikuma Malam yana da saurin zuciya abunda yakai yayi zuciya da wanda baikaba duk zaiyi maizuciya

AMSA
=====
👇
To dukansu basu chanchanci ki aurensu ba.
Amma dai a bisa larura yanzu da Mazan aure suke wahala, Dalilin rashin kudi da tsadar rayuwa da ake ciki, sai ki duba wanda zuciyarki tasan zata iya hakuri dashi, tinda shi wannan mai gaya miki sirrun gidansa, akwai matsala, Sabida mutum maras surru ko zance kukeyi, idan ka ganshi to ka dena, domin da yaji abinda kika fadi, ko da zarar yaji abin da kika aikata gaba zaiyi da maganarka.
  shi kuma mai yawan zuciya da fushi bashi da dadin sha'ani, komi fushi, bazaki ji dadin zama dashi ba.
Amma dai Ni a tunani na, ki auri mai saurin fushin, Sabida wannan halitta ne, kuma zakike bashi hakuri idan baki da girman kai.
  Amma dai ki duba kiga wanda kikasan zaki iya maleji dashi a cikin Su.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Wanda Aljana ta Aura

TAMBAYA
=========
👇
Assalamu alaikum, Allah shi gafata Malam tambaya ta itace. Mutum ne yayi aure amma yana da jinnul ashiq a jikin sa, sai aljanar tasa ya saki matar daban daban har sau uku. Sai daga baya aka je  gun rukuya aka tabbatar yana da aljana itace ma take sa shi wannan saki har sau uku. To Malam menene matsayin wannan shika a musulunci? Zai iya mayar da matar sa ko kuwa sai ta aura?

AMSA
======
👇
Da yawa daga cikin irin rabuwar aurenmu, matsala ce irin ta aljani, idan suka auri namiji, basa barinsa da mace, haka idan suka auri mace basa barinta da namiji, sai sunga sun cire musu Jin dadin auren ko kuma sun raba wannan auren, kamar yadda Allah yake cewa, DAN SU RABA TSAKANIN MACE DA MIJINTA ".
maganar saki kuma ta saku.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Yaya Zaiyi

TAMBAYA
=========
👇
Assalamu alaikum gafatta mlm akwai wani abokina ada yataso da iskancisa yasha yin alfasha iri iri to yanzu Allah ya shiryeshi muna tareda shi danshima yanzu haka yayi nisa da sosai cikin karatun addini danshima yanzu harna koyarwa yara qanana tareda da wa'azi to shine mutan gari suke cewa malamin nakuma da dan iskane,shiine yanzu koda yaga wasu suna aikata lefi yanajin tsoran hanasu domin sai su inkaimai akan wani abu dayai acan baya,malam me wannan abokin nawa yakamata yayi gashi ya tufa,amma mutane sunai masa gori,hakan yasa wani lokacin ma yake tsoran yiwa mutane wa'azi wace shawara zaka iya bashi?

AMSA
======
👇
Dole zaici gaba da yimusu wa'azi mana.
  Bakaga sayyadina umar ba, lokacin da ya musulunta, duk inda yasan yana zuwa majalisin Su na kafirai, saida yaje yayi musu wa'azi, yace mu kam mun gane gaskiya. Babu abun bautawa da gaskiya sai Allah.

Saboda haka ba ruwansa da wanda zai gaya masa ba daidai ba.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Ina Neman cikakken Bayani

TAMBAYA
========
👇
Tambayana shine malam   I malam rakaan biyu na karshen sallah nafila ba ayi mata karatu bayan fatiha 2 malam Don Allah inason Amin cikakken bayani akan sujudu kabli da baadi kuma idan akayi me ake karantawa a ciki

AMSA
=====
👇
Sujuda kabli itace, sujuda guda biyu bayan an Gama tashiya kafin ayi sallama ake yinta, zaka kai goshinka sau biyu kamar yadda Kakeyi a sallar ka.
  Sujuda ba'adi kuma ana yinta ne bayan anyi sallama, itama ana kai gashi kasa sau biyu ne kamar yadda Kayi a kowacce raka'a.
  Tasbihin da akeyi a sujuda, itama haka zakayi.
  Ana yin sujudu kabli ne idan An rage wani abu a cikin sallah.
  Haka ana yin sujuda ba'adi ne idan an kara wani abu a cikin sallah.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Riya

TAMBAYA
=========
👇
Assalamu alikum mallam Allah ya Kara karfin imani ameen tambayata itace shin idan mutum yana aikin alkairi sai yakeji zuciyar tana raya masa kamar yanayi ko kuma kamar yanayin  riya toh Allah zai bashi zunubi abisa haka?. Allah ya taimaka.

AMSA
======
👇
Da alama riya din yake yi, tinda har zuciyarsa tana raya masa hakan.
  Allah kuma yana amfani da zuciyar mutum ne.
 
Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

Mutumin Da Yayi Mafarki

TAMBAYA
=========
👇
Assalamu alaikum mlan Allah yakarama ikhlasi amee rambayata itace shin menene hukun mutumin dayayi mafarki dadaddare to da asuba tayi sai yaje yayi sallah batareda yayi wankaba kuma bai canxa kayaba ko kuma da yayi wankan sai yaje yayi sallah dakayan bai cireba harma sallar axahar taxo kuma yaje yayi dakayan ajikinsa

AMSA
=====
👇
Wannan rashin wankan da baiyi ba har yaje yayi sallah a haka shine babban kuskure, sai dai ko inda wata larura ce da tasa baiyi wankan ba, Anan kenan zaiyi taimama, Sabida larurar da take tare dashi ta rashin ruwa ko tsananin sanyi ko kuma idan akwai wani rauni jikinsa wanda idan ya zuba ruwa za'a iya bashi matsala.
  Maganar kayan da yake jikinsa, bai wanke ba yaje yayi sallah dashi, babu wani abu.
Sabida akwai malaman da suke da hujjoji masu Karfi akan cewar maniyyi ba najasa bane.
  Hijjarsu ta farko, Bukhari da Muslim sun rawaito hadisi daga sahibatul kissa Ummuna Aisha Allah ya kara mata yarda tace, ina kankare maniyyi daga tufafin manzon Allah saw, sai yaje yayi sallah da wannan tufafin.
  Da wannan ne Malamai sukace maniyyi ba najasa bane, Sabida dole duk yadda aka kai da kankarewa sai an sami saura a wurin.
  Sannan kuma sukace, idan da maniyyi najasa ne, to mutum ma zai iya zama najasa kenan, tinda asalinsa kenan.
  Sannan bazai yiwuba, namiji yake zubawa matarsa najasa a jikinta ba.
 
Magana ta karshe, idan maniyyi ya bushe za'a kankareshi da farce, Wannan shine yafi chanchanta da Ace wankewa akayi, Sabida waccan ruwayar da ummuna aisha ta rawaito mana.
  Idan kuma yana danye ne bai bushe ba, za'a wanke shi.
Sabida hadisi da ummuna aisha Allah ya kara mata yarda tace  ina wanke maniyyi daga tufafin manzon Allah saw sai yaje yayi sallah, alhalin ana ganin sawun wurin da na wanke daga tufafin nasa.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

MENENE HUKUNCIN JININ DA YAKE ZUWA SANADIYAR ALLURAR FAMILY PLANNING?

TAMBAYA
========
👇
Asalamu Alaikum  Allah yakarawa mallam basira
Mallam maiye wukuncin jinin dayake zuwa sanadin allural family flaning?

AMSA
======

Bashi da wani hukunci, Sabida haka baya hana sallah da azumi da dawafi da sauran ibada.
Sabida Jini ne na cuta.
FATIMATU BINTU ABI HUBAISHIN tazo wurin manzon Allah saw tace tana fama da jini baya daukewa, Shin zan dena yin sallah kenan? sai manzon Allah saw yace da ita, Wannan jinin cuta ne. Zakike dena sallah ne kawai a kwanakin da jikinki yake zuwa miki. Wato a iya kwanakin hailarki.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

WANE ABUBAKAR DIN NE?

TAMBAYA
=========

Assalamu Alaikum.. Allah ya taimaki malam tambaya ce dani kamar haka.. Acikin jerin sunayen matan sayyidina umar r. a akwai Mai suna Ummu khulsum bint Abubakary. To tambayar anan itace : Shin wane Abubakar din ne?  Sayyidina Abubakar ko kuma wani Abubakar ne daban? 
Tambaya ta biyu itace.. Akwai wani hadisi da manzon Allah s a w ya bamu labarin wani mutum da yace wa 'ya'yan sa idan ya mutu su qona shi sannan su dauki tokar rabi su zuba a cikin teku rabi kuma su sheqe don kada ya hadu da ubangiji saboda yace idan har ya hadu da ubangiji to zai yi masa azaba.. Har daga qarshe manzon Allah s a w yace Allah zai tayar dashi ya tambaye shi dalilin haka, har Allah s w t yace to ya gafarta masa.. Kuma hadisin ya nuna bai ta'ba aikin alkhairi ba.. To tambaya ta anan itace shin aikin alkhairin da aka ce bai ta'ba yi ba shin har da Sallah ko kuwa?

AMSA
=====

Ban san umar ya taba auren yar gidan sayyadina Abubakar ba, haka nayi ta bincike cikin littattafan tarihi ko zan sami wannan bayanin, amma ban samu ba gaskiya.
   Abinda nake dashi, anan shine, idan ka duba littafin ANNASABU WAL MASAHARATI BAINA AHLUL BAITI WASSAHABA " shafi na 328.  Matan da sayyadina umar ya aura sune,
1. ZAINAB BINTU MAZ'UM, yar uwar usman ibn maz'um.
2. UMMU KULSUM BINTU JARUL ALKUZA'IYYA.
3. UMMU HAKEEM BINTUL HARIS ALMAKZUUMA.
4. JAMEELA BINTU SABIT wadda yar Uwa ce ga AASIM IBN SABIT.
5. ATIQAH BINTU ZAID.
6. UMMU KULSUM BINTU ALIYU BIN ABI DALIB.
  Wadannan suna matan sayyadina umar Dan khaddab.
  Sabida haka, kenan sayyadina Umar sirukine ga SAYYADINA ALIYU IBN ABI DALIB, Gashi kuma yan Shi'a suna zagin sayyadina Umar siruki ga sayyadina Aliyu.

  'Yayansa kuma sun hada da.
1. Ruqayya
2. Hafsat matar manzon Allah saw.
3. Fatima, wadda mata ce ga Abdurraahman ibn zaid.
4. Zainab, wadda itama mata ce ga Abdurraahman ibn mu'utamad.
5. Abdullahi, Wanda shine na biyu daga cikin wadanda sukafi kowa rawaito hadisin manzon Allah saw. Daga abi huraira sai shi.

  Kissar wannan bawan Allah da ka kawo, tana cikin sahihul Bukhari, kitabu Ahaadisul Anbiya da Kuma kitabuttauheed, haka Muslim ma ya kawota cikin sahihun sa a kitabuttauheed, sannan Doktor mustapha Murad ya kawo wannan Kissar a cikin littafin KULUQUL MU'UMIN shafi na 95.
  Kamar yadda ruwayar ta nuna, Wannan mutumin bai taba aikata duk wani nau'in Alkairi ba a rayuwarsa. Domin haka. Manzon Allah saw ya Nassanta, kuma manzon Allah saw cewa yayi, anyi wani mutum kafin zuwan wannan al'ummar, kaga kenan ba ma a wannan zamanin aka yishi ba.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876SECOND REMINDER. Thursday. FIX YOUR WORLD BY PLACING ALLAH, HIS MESSENGER AND THE QUR'AN IN THE RIGHT PLACE IN YOUR HEART. BismilLah

An Imam was struggling to prepare his Friday sermon and didn't want to be disturbed by his five year old daughter, so he removed a map of the world from his study, tore it into pieces and gave it to her to assemble with the promise that he would answer all her questions and play with her when she was done. He knew she would never be able to fix it.

To his amazement, in less than five minutes, she returned to him in his study with the map in perfect shape, every continent and every country in its place. The surprised father asked, ''Honey, you don't know anything about geography, so how did you fix the world so easily and quickly? The five year old girl smiled sweetly and replied, ''The picture of of THE HOLY QU'R' AN and the inscription LA ILLAHA ILLALLAHA MUHAMMADU ROSULULLAH was at back of the map and I knew that if ALLAH, His MESSENGER and QUR'AN are put in the right place, the whole world would be in perfect shape'.

That was just the right inspiration he needed for his sermon. He thanked his daughter and prepared a powerful sermon on the subject: "Fix Your World By Placing ALLAH, His MESSENGER and the QUR'AN in the Right Place in your heart ".
To whoever is reading this message, just place ALLAH, His MESSENGER and QUR'AN in the rightful place and your life will be in order.
I hope you understand this just like I do. Share and spread it to the world, let them know that THEIR WORLD CAN NOT BE COMPLETELY FIXED WITHOUT ALLAH, HIS MESSENGER AND THE QUR'AN.
MAY ALLAH BLESS US ALL AND KEEP GUIDING US ALL. AAMEEN.

Share:

MASU BADA MAGANIN MATA SUKAN BADA KAZA KAZA ACI, AMMA WAI KAR A TAUNA KASHI

MASU BADA MAGANIN MATA SUKAN BADA KAZA AHADA ACI, AMMA WAI KAR ATAUNA QASHI

DAGA ZAUREN

📕 *HISNUL MUSLIM*📕

   *TAMBAYA*
Assalamu alaikum, malam dangane da maganin mata dasuke sha NA Karin ni'ima naji wani anacewa su dafa kaza suci naman amma kada suci kashin wai suyi rami surufe kashin to yamatsayin hakan dakuma yanka Kazan, Allah gafarta malam?

            *AMSA*
Wa'alaikumussalam Warahmatullahi Wabarakatuh Wannan kuma karya ne da kuma sabo da salon tsafi babu wani maganin musulunci da akayi masa sharadi irin wannan don haka wannan maganin ko waye yake bayar dashi bai halatta a kar6a ba domin shirka zata iya shiga ciki Allah ya tsare mu, Allah ne mafi sani.

HUSSAINI HARUNA IBN TAIMIYYA*
Abu nabeelah

Masu buqatan shiga Wannan Zaure na hisnul Muslim   suyiwa daya daga cikin wadannan  number  magana ta whatsApp

+2348065523065
+2349039510396

    Domin Neman Karin bayani akan wata fatawa sai Ku kira wannan numbar↓
*+2347065588557*
  ((سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أشْهَدُ أنْ لَا إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ، أسْتَغْفِرُكَ وأَتُوبُ إِلَيْكَ))
====================√
❌Banaka bane kada ka chanja komai, kaji tsoron ALLAH ❌
Kuna iya samun mu ta  facebook ta wannan link indanke Qasa
https://mobile.facebook.com/Hisnul-Muslim-667684316700356/?fref=none

Share:

Taskar Hikima

TASKAR HIKIMAR

Idan farce yayi tsawo shi muke yankewa ba yatsan ba.Haka ne idan mukayi sabani, kawar dashi ya kamata muyi ta hanyar sulhu bata hanyar yanke alaka dake tsakani ba, muyi afuwa ga juna yan uwa domin dukkaninmu masu kuskurene Allah yayi mana afuwa baki daya.

Gabatarwa: Abu-Unaisa

Masu son kasancewa Damu ta shafin mu na Facebook sai su bi ta wannan Rariyar dake kasa🏿

https://mobile.facebook.com/Darus-sunnah-Foundation-263121204166444/

Ga duk mai sha'awar shiga wannan zaure na Darussunnah a whatspp zai aika da sunan sa da jahar sa ta wadannan lambobi:

+2347035888158,
+2348139789030.

-Ta WhatsApp din zaka Tura ba ta SMS ba,
-Idan ka Tura a Lamba Guda daya To Kada Ka Tura Izuwa ga Daya Lambar.

Share:

Friday Messages 079

O' Allah! Light every path we follow, give us wisdom, guide every step we take, bless every decision we make. O Allah! Enrich us with patience, strengthen our Iman, Grant us contentment, peace of mind and restore lasting tranquility to our land. O'Allah! Grant us authority & join us with the righteous. Grant us a reputation of honor among later generations & count us among the dwellers of Jannah, Ameen Ya Rabbi. Juma'at Mubarak!
Share:

Friday Messages 778

May Allah distance Us from shame and failure, destroy every evil plan against Us and our loved ones, protect Us from known & unknown enemies May Allah (SWT) support us & our family with His Love, Kindness, Mercy, Blessings & Forgiveness... May you continue to enjoy Allah's Rahmah, Ni'imah & protection till yaumul Qiyamah. (Ameen) Jumu'at Mubarak
Share:

Friday Messages 778

May Allah distance Us from shame and failure, destroy every evil plan against Us and our loved ones, protect Us from known & unknown enemies May Allah (SWT) support us & our family with His Love, Kindness, Mercy, Blessings & Forgiveness... May you continue to enjoy Allah's Rahmah, Ni'imah & protection till yaumul Qiyamah. (Ameen) Jumu'at Mubarak
Share:

Friday Messages 077

A true believer is he who is constantly conscious about death,prays for his parents,family & wishes others well.May Allah count us amongst them.MORNG $ JUM@ KRM

Share:

Friday Messages 076

A successful life is built upon consistent prayers, humility, sacrifices, patience and forgiveness, may our prayers and all our good deeds be accepted by Allah, may he turn our burdens into blessings, disappointments into favours, misfortunes into fortunes and grant us complete guidance today and always. Ameen, Juma'at mubaraq.

Share:

HUKUNCIN TSARE YARA A GIDA IN YAMMA TAYI

SHIN DA GASKENE  ANNABI (S.A.W) YA BADA UMARNI ATSARE YARA IDAN MAGRIBA TA GABATO?

DAGA ZAUREN
📕 HISNUL-MUSLIM 📕

       TAMBAYA

Assalamu alaikum, Dan Allah miye matsayin maganan da ake cewa in magrib ya gabato a daga jarirai/kananan yara.idan suna kwance, wai sai bayan isha a kwantar da su. Shin a addinance ne ko dai al'ada ne

         AMSA

Wa'alaikumussalam Warahmatullahi Wabarakatuh Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace idan maghriba ta gabato to ku kama kananan yaran ku, kuma ku tsare su.... Domin a lokacin shaidanu suke yin wasannin su... Don haka musulunci ne ya koyar da hakan idan ma yaran suka nuna rashin ji a wannan lokaci to ya halatta adan bigesu da bulala, zuwa wani lokaci Kuma sai a rabu dasu, Allah yasa mudace

HUSSAINI HARUNA IBN TAIMIYYA
Abu nabeelah

Masu buqatan shiga Wannan Zaure na hisnul Muslim   suyiwa daya daga cikin wadannan  number  magana ta whatsApp
+2348065523065
+2349039510396
    Domin Neman Karin bayani akan wata fatawa sai Ku kira wannan numbar↓
+2347065588557
سبانك اللهم وبحمدك، اشهد ان لا اله الا انت استغفرك واتوب اليك، 
Kuna iya samun mu ta  facebook ta wannan link indanke Qasa
https://mobile.facebook.com/Hisnul-Muslim-667684316700356/?fref=none

Share:

Today's Reminder

Verse of the day
:And do not treat people with arrogance, nor walk proudly on earth, Allah does not love the arrogant showoffs.[Q:chafter 31: verse 18]

Hadith of the day
:On authority of Sufyan bin Abdullah, may Allah be pleased with him said: I said "Oh the messenger of Allah, tell me something about Islam which I can ask of one but you. He said, "say : I believe in Allah and thereafter up upright.

Quote of the day
:A Qur'an in hand is worth two on the shelf.

         Forward as received.    

       Jumu,at Kareem to all Muslim ummah.

Share:

ZAN IYA SADUWA DA MAI HAILA, IDAN NA SA CONDOM?

ZAN IYA  SADUWA DA MAI HAILA, IDAN NA SANYA CONDOM ?
    

Tambaya

Assalamu Alaikum. Malam Allah ya karama daukaka da imani. Ga tambayata: Shin mutum zai iya saduwa da matarsa idan tana Haila matukar yasa Condom?

                           
Amsa
Wa'alaikum assalam.

To dan'uwa bai halatta ka sadu da mai haila ba ko da kuwa ka sanya Condum, saboda Allah ya haramta saduwa da mai haila, kuma ya kira jinin haila a aya ta 222 a suratul. Bakara da cuta, sannan ya rataya halaccin saduwa da mace mai haila da abubuwa biyu wato: yankewar jini da kuma yın wanka.                                                      
Ba namiji ne kadai haila take iya cutarwa ba, idan ana saduwa da mace mai haila mahaifarta za ta takure sai jini ya barke mata, wannan sai yake nuna cewa: ba za'a sadu da mace mai haila ba ko da an sa Condum .
          
Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa
 
28/11/2015

Ga dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH Sai ya yi saving wannan number+2348122348585 sannan ya tura da sunnasa da adireshinsa ta what'sApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.

Share:

CIKAKKEN BAYANI GAMEDA ZIKIRI BAYAN KIRAN SALLA

CIKAKKEN BAYANI GAMEDA ZIKIRI BAYAN KIRAN SALLA

      TAMBAYA

Assalam malam Dan inason amini cikeken bayanin abin da mutun Zeke fada a yayin kiran sallah da kuma bayan Angama
Ma'ana addua'o in

      AMSA

Wa alaikumus salamu warahmatullah.

❗1). A. Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace :( IDAN KUKAJI KIRAN SALLAH, TO KUFADI DAI DAI DA ABINDA MAI KIRAN SALLAR YAKE FADA).
👉🏿 Buhari: 611.
👉🏿 Muslim:383.
Daga Abu Sa'id Alkhuduriy Allah yakara masa yarda.
❗  B. A Hadisin Umar Allah yakara masa yarda. Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: ( IDAN LADAN YACE: ALLAHU AKBARUL LAHU AKBAR, SAI DAYANKU YACE: ALLAHU AKBARUL LAHU AKBAR, SANNAN YACE:: ASH HADU ALLA ILAHA ILLLAH, SHIMA YACE: ASH HADU ALLA ILAHA ILLALLAH, SANNAN YACE: ASH HADU ANNA MUHAMMADAR RASUULULLAH, SAI SHIMA YACE:  ASH HADU ANNA MUHAMMADAR RASUULULLAH, SANNAN YACE: HAYYA ALAS SALAH, SAI YACE: LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH, SANNAN YACE: HAYYA ALAL FALAH, SAI YACE: LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH, SANNAN YACE: ALLAHU AKBARUL LAHU AKBAR, SAI SHIMA YACE: ALLAHU AKBARUL LAHU AKBARULLAHU AKBAR, SANNAN YACE: LA ILA ILLALLAH, SHIMA YACE: LA ILAHA ILLALLAH DAG ZUCIYARSA, TO YA SHIGA ALJANNAH).
👉🏿 Muslim: 385.
👉🏿Abu dawud: 523.
❗2). A. Bayan kiran sallar sai ayi wadannan addu'o'in:
Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali Muhammadin kama sallaita ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima innaka hamidun majid. Allahumma barik ala muhammadin wa ali muhammadin kama barakta ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima Innak hamidun majid
Inkayi wannan Annabi yace: ( Allah zaiyi maka goma.
👉🏿Muslim: 384.📒
👉🏿 Abudawud: 523.📕
👉🏿 Tirmiziy: 3695.📗
Dan Amru Allah yakara masa yarda.
⚡B. Wa ana ash hadu alla ilaha illallah, wahdahu la sharika lah, wa ash hadu anna Muhammadan abdahu warasulah, raditu billahi rabban wabil islami dinan, wabi Muhammadin rasulan. Annabi yace:( DUK WANDA YAFADI HAKA BAYAN YAJI KIRAN SALLAH, ANGAFARTA MASA ABINDA YAGABATA NA DAGA ZUNUBBANSA).
👉🏿 Muslim: 386. 📒
👉🏿Abu dawud: 525.📕
👉🏿 Tirmiziy:21📗.
Daga Sa'ad Bunu Abi Wakkas Allah yakara masa yarda
❗C. Allahumma rabba hazihid da'awatit tammah, wassalatil ka'imah ati Muhammadanil wasilata walfadilah, wab as'hu maka'man mahmudanil lazi wa adtah.
Annabi yace: ( DUK WANDA YAFADI HAKAN BAYAN KIRAN SALLAH, CETONA YA HALATTA AGARESHI RANAR KIYOMA).
👉🏿Buhari: 614📚.
👉🏿Abu dawud:529.📙
👉🏿 Tirmiziy: 211📒.
Daga Jabir Allah yakara masa yarda.
❗D. Sai kayi addu'ar bukatarka ta duniya da lahira
Annabi Sallallahu alaihi wasallam_ yace: (ADDU'A TSAKANIN KIRAN SALLAH DA IKAMA, KARKABBACE).
👉🏿 Abu dawud: 521.📕
👉🏿 Tirmiziy: 212📗.
👉🏿 Ibnu khuzaimah: 425📚.
Daga Anas Allah takara masa yarda.

Karin bayani:
✔1. Wajen hayya alassalah da falah( حي على الصلاة/ حي على الفلاح
, La haula zakace,  sau duka hudun.
✔2. Karshen Ash hadu alla ilaha illallah, ba acewa wahdahu la sharika kalah, sai ankamma kiran sallar za'ayi, munkawo addu'ar.
✔3. Za'abi ladan kalma kalma.
✔4. Ko sau nawa kaji kiran sallar zakayi mai mai abinda yake fada, koda masallatai nawane.
✔5. Ikama ma zaka maimaitata kamar yadda yake akiran sallah. Amagana mafi inganci.
✔6. Idan ladan yace: Ash hadu, sai kace: wa ana, ya wadatar.
👉🏿Buhari: 914. 📙
✔7. Ba'ayin addu'a bayan tada Iqamah.

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
والله تعالى أعلم
〰〰〰〰〰〰〰〰〰〰〰
✏ _AMSAWA_:🖊
SHAFI'U SHEHU MINNA
(☎ *08033410797) 
daga zauren:
ISLAMIC GROUP 1 & 2_🌙
👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼

Share:

Friday Messages 075

GAISUWAR JUMA'AH!

     Hudubar farko a duniya

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace a hudubar sa ta farko a birnin Madina; "Ku yada sallama a tsakanin ku, Ku ciyar da abinci, Kuyi zumunci sannan Ku tashi cikin dare kuyi sallah lokacin mutane suna bacci.
Idan kukayi haka zaku shiga aljannah"
     Ya Allah Ka bamu ikon aikata wadan nan ibadun, amin.

              Barkan mu da
                   Juma'ah!

Share:

Friday Messages 074

Alhamdulillah!!! Jannatil firdaus, Jannatil ma'awa, Jannatil Na'im, Jannatil Adni, Jannatil Aliya, Jannatil Darul-khuldi, Jannatil Darul-salam. These seven (7) categories of PARADISE are designed by Allah 2 reward believers on d last day. May Allah (SWT) grant us an  estate in d highest class in JANNATUL FIRDAUS AMEEN!!! Jumm@ mubaraq

Share:

Friday Messages 073

Oh Allah! Include us  Among the Beneficiaries of this Great Day, "Friday". Save our Souls from the flame of Hellfire, Grant us Access to the Shade's of Your throne on the Day of  Judgement,  Blot out our sins before our death, Ease our tasks and Grant us Jannatul Firdausi. Ameen.

Share:

GARIN DAN WAKE DA TUBANI

Mata: Kai Sumul❗😘😘
Miji : Wayyo Dadi❗❗😱😱
Mata: Ahhhhhh Lagwada ❗❗❗😋😋
Miji : Uhm Santi❗❗❗😇😇

Laure: 🙊🙊🙊🙊Wai me kuke yi ne haka kamar wasu Kananan yara👬👬 ke da Mijin naki💑❓
Mata: Hmmm bari kawai Laure in ana Sallah Ba a Magana😷😷
Laure: A'a don Allah ki Fadamin mana 'Yar uwa👏🏻👏🏻
Miji: Wato wani irin Dan Wake🍲 🍲ne Mai Shegen Dadi wanda ban taba cin irin sa ba.
Laure: 😳😳 Ah Dan Wake🍲🍲 kuma❓❓
Mata: 😀😀 Eh kwarai kuwa, sai dai ba irin wanda kika saba ci bane, domin shi wannan an yi shi ne da ♻GARIN DAN WAKE DA TUBANI♻❗❗❗
Laure: Garin Dan Wake Da Tubani kuma🤔🤔Menene shi❓❓❓❓
Mata: Ai wani Sabon Garin🍚🍚 Dan Wake🍲🍲 da aka hada shi da Alkama🌾 Rogo🍠 Wake🌿 Gujjiya🍀 da Kuma Kuka🌴
Laure: 😃😃😃Ah Kice Abu Goma da Ashirin kenan. To Amma ya ake amfani da shi??
Mata: Ai abin ba wuya, Kwaba🍧 shi zaki yi da ruwan kanwa, Sannan ki Mulmula🌕🌕🌕 shi dai dai yadda kike so, Sannan ki Tsumbula Shi a cikin Tafasashen🍵🍵🍵 ruwa, Bayan kaman Mintuna Ashirin2⃣0⃣ sai ki sauke ki Zuba a ruwan sanyi. Shikenan sai Suburbuda❗❗😋😋
Laure: Ah Kice Sauki ya samu kenan, babu ruwana da 'Yan Nike-Nike. To Amma Nawa ake Siyar da shi, kin san abubuwan yanzu sai a hankali 😴😴😴
Mata: Hakane Laure! To amma kada Gaban ki ya fadi domin ba wani tsada gare shi ba, Ana Saida Kilo daya ne akan  Naira 250 Kacal, ga Masu Sari kuma ana Sarar Musu da Shi ne akan Naira 225 su kuma su bi ribar Naira 25 akan Kowane Kilo. Ga Masu Son Rabin Kilo Kuma Naira 125 Kacal, ga masu Sari kuma ana Sarar musu da shi ne akan Naira 115 su Kuma sai subi ribar Naira Goma a Kowane Rabin Kilo.
Laure: HEHEHE Kice Shagali kenan kuda a Gefen gyambo. Yanzu a ina zan iya samun wannan garin dan Waken ❓❓❓
Miji: kina iya Ziyarta ofishin su da ke Kurna Asabe B Dala L.G Kano.
Laure: To Yanzu in Wasu Kuma suna so daga wasu Jahohin ya zasu yi kenan ❓❓❓
Mata: Hahaa ai nan ma akwai wani Tsarin d aka Bullo da shi don biyan Bukatun masu bukata, ga duk mai so sai ya tuntubi wadannan lambobin 08110298305, 08185819176.
Laure: Ah to lallai nima bari in je in nemi Nawa don yau nima mu Rakashe💃💃💃  da Mai gida ❗❗❗
Miji: Ai Gwamma dai Kam, muma bari mu ci gaba da Caskadewa 👫👫👫👫❗❗❗❗😀😀😀

To ku kuma me Kuke jira ❓❓❓kowa yayi Maza ya nemi nashi

Ga masu son yin talla da mu
08185819176
09077652718
Haimanraees@gmail.com

© @HaimanRaees

Share:

Friday Messages 072

Assalamu Alaikum

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace a hudubar sa ta farko a birnin Madina; "Ku yada sallama a tsakanin ku, Ku ciyar da abinci, Kuyi zumunci sannan Ku tashi cikin dare kuyi sallah lokacin mutane suke bacci.
Idan kukayi haka zaku shiga aljannah"
     Ya Allah Ka bamu ikon aikata wadan nan ibadun, amin.

              Barkan mu da
                   Juma'ah!

Share:

Friday Messages 071

السلام عليكم ورحمة الله وبركاته.....
Oh Allah! We have nothing except what You grant. We own nothing except by Your permission and We know nothing except by Your leave. Grant us the best of possessions and knowledge that will lead us to paradise. Ameen thumma Ameen ya Allah.

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

WaΖ™ar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waΖ™e ak...

Contact form