Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Tambaya Ta 004 Siradi Da Wuta

*_MALAM MINENE GASKIYAR WANNAN MAGANAR?_*


                            *Tambaya:*
Malam wai da gaskene cewar, kowa sai ya dandana wutar lahira, banda Annabi Muhammad (S.A.W.)?
(Daga Dahiru Adam).                                *Amsa*‎
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
A’a cewa akayi "WADDUHA" ba cewa akayi "MUTHEEQUHA" ba.

Watau kowa sai yabi takan wuta sannan ya wuce. Domin Siradi, akan wuta aka dorashi, mutanen da aka yiwa hisabi zuwa Aljanna sai sunbi takan Siradin.

Wanda yake a kan wuta.
Shine (acikin Alkur'ani) akace: "WA-IN-MINKUM-ILLA WARIDUHA KAN-ALARABBUKA HATMAN MAQDIYYA".

"وَإِن مِّنكُمْ إِلَّا وَارِدُهَا كَانَ عَلَىٰ رَبِّكَ حَتْمًا مَّقْضِيًّا".
Suratul Maryam.

Amma kuma jin zafinta (wutar) sai wanda Allah ya nufa da yaji zafin nata, sannan yaji zafin. Allah ka tseratar damu daga azabar wuta.

_WALLAHU A'ALAM._

Rubutawa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑_*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.

Share:

Tambaya Ta 003

*HUKUNCIN MACE TA YI TAFIYA BA TARE DA MUHARRAMI BA*

Fatawar Mata fitowa ta 1

*TAMBAYA:*
Mene ne hukuncin mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba?.

*AMSA:*
An hana mace ta yi tafiya face tare da Muharrami wanda zai tsare ta kuma ya kare ta daga barnan mabarnata da fasikancin fasikai.

Hakika hadisai ingantattu sun zo wanda suke hana mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba, daga cikin su:

An rawaito daga Abdullahi Dan Umar, Radhiyallahu Anhu, ya ce: Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_Kada mace ta yi tafiya na kwanaki uku face tare da ita akwai Muharrami_*.

Sannan an karbo daga Ibn Sa'id, Radhiyallahu Anhu, Lallai Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, Ya hana mace ta yi tafiya yini biyu ko darare biyu face tare da mijinta ko Muharraminta.

Kuma an karbo daga Abi Hurairah, Radhiyallahu Anhu, daga Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_Ba Ya halatta ga mace ta yi tafiya na jini da dare face tare da ita akwai Muharraminta_* Bukhari da Muslim ne suka riwaito.

Amsawa: *_Sheikh Saleh al-Fauzan, Rahimahullah_*

A duba littafin فتاوى المرأة المسلمة shafi na 863.

✍🏼 Tattarawa:
*_Mal Umar Shehu Zaria_*

Share:

Tambaya Ta 002 Wa Ya Dace Yayiwa Mace Wankan Gawa?

*WAYE YA DACE YA YI MA MACE WANKAN GAWA?*

Fatawowin Mata fitowa ta 2

*TAMBAYA:*
Waye ya dace ya yi ma mace wanka idan ta mutu?, kuma shin ya halatta Mace kafira wanda ba Musulma ba ta yi mace Musulma wanka idan ta rasu?. Sannan da shigar da ita Kabari sharadi ne dole sai Makusantanta, ko kuwa kowane Musulmi zai iya shigar da ita kabari?. Akwai wasu mutane shin ya halatta a bar su, su shigar da mace kabarinta?.

*AMSA:*
Musantan mace su ne za su yi mata wanka kuma za a yi la'akari da wanda suka fi kusanci daga cikin wanda za su iya kyautata wankan. Kuma ya halatta a wakilta kowace mace wanda za ta iya kyautata wanke ta, koda kuwa ba makusanciyarta ba ce. Haka nan ya halatta miji ya wanke matan shi, ita ta wanke shi.

Dangane da Mace kafira ta wanke Musulma, wannan bai halatta ba, domin wanke mamaci ibada ce, kuma Ibadan wanda ba Musulmi ba, bata inganta.

Dangane da shigar da mace kabarinta, ya halatta wani daga cikin Musulmi ya shigar da ita koda ba makusancinta ba ne, matukar zai kyautata haka.

Amsawa: Al-Lajnatu al-Daa'imah Lil iftaa'i.

A duba littafin فتاوى المرأة المسلمة shafi na 441.

✍🏼 Tattarawa:
*_Umar Shehu Zaria_*

Share:

Suratul Zil Zila

*☘☘Suratul Zilzila Da Fassararta☘☘*

```🌹بسم الله الرحمن الرحيم🌹

١.اذا زلزلت الارض زلزالها.

1⃣.Idan aka girgiza kasa girgizawa.

٢.واخرجت الارض اثقالها.

2⃣.Kuma Kasa ta fitar da kayanta masu nauyi.

٣.وقال الاءنسن مالها.

3⃣.Sai Mutum yace miye ya sameta???.

٤.يؤمذ تحدث اخبارها.

4⃣.A Ranar zata bada Labarinta.

٥.بان ربك اوحى لها.

5⃣ .Saboda Ubangijinka yayi mata Wahayi.

٦.يومذ يصدر الناس اشتاتا ليرو اعلمهم.

6⃣.A ranar Mutane zasu fito daban-daban domin a Nuna masu Aiyikansu.

٧.فمن يعمل مثقل ذرة خيرا يراه.

7⃣.Toh Duk Wanda ya aikata wani aiki na Alkhairi kwatankwacin kwayar zarra zai ganshi.

٨.و من يعلم مثقل ذرة شرا يراه.

8⃣.Haka ma duk Wanda ya aikata aiki na sharri kwatankwacin kwayar zarra zai ganshi.```

*🌷Rubutawa🌷*

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

+2347039135966

Share:

Tambaya Ta 001 Hukuncin Saukewa Mamaci Alqur'ani Bayan Ya Mutu

*_HUNKUNCIN SAUKEWA MAMACI ALQUR'ANI BAYAN YA MUTU_*

                           *Tambaya:*
Assalamu alaikum Wai Malam Meye Hukuncin Saukewa Mamaci Al-qur'ani?

                                *Amsa*
Wa'alaikum assalam. To malamai sun yi sabani akan wannan mas'ala zuwa maganganu guda uku :

*1*. Bai halatta ba, saboda ba'a samu wani nassi da yake nuni zuwa haka ba, kuma ita ibada ba'a  yinta sai da nassi na musamman, sannan  kuma mutum ba shi da wani abu sai aikinsa, kamar yadda aya ta 39 da take cikin suratu Najm, take nuni zuwa haka, tun da ba'a samu ba, yin hakan zai zama bidi'a, wannan ita ce maganar farko ta Shafi'i.

*2*. Ya  halatta ayi, saboda hadisan da suke nuna cewa mamacin yana iya amfana da abin da mai rai zai masa, kamar hadisan da suka yi umarni da yi masa sallah da nema masa gafara bayan ya mutu, da  yi masa sadaka, wannan shi ne maganar mafi yawan malamai, har wasu marubuta ma sun hakaito ijma'i akan haka, saboda mutane sun jima suna yi kuma malamai ba su yi musu inkari ba.

*3*. Akwai wadanda suka tafi akan cewa : idan dansa na cikinsa ya yi masa, to ladan zai same shi, amma wanda ba dansa ba, ba zai yi masa ba, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi" Dan mutum yana daga cikin aikinsa" Abudawud ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi a sahihu sunani-abi-dawud hadisi mai lamba ta: 2528.

Saidai wasu malaman, suna rinjayar da magana ta uku, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : "Idan dan'adam ya rasu ayyukansa sukan yanke sai dayan abubuwa guda uku : sadaka mai gudana, ko ilimin da ake amfana da shi, ko da nagari da yake masa addu'a"  kamar yadda Tirmizi ya rawaito shi kuma ya inganta shi a hadisi mai lamba ta :1376.
    
Wadancan hadisan kuwa da masu Magana ta biyu suka kafa hujja da su, to za'a yi amfani da su ne a iya inda suka zo, amma ba za'a yi kiyasin karatun qur'ani akan su ba.

Don neman Karin bayani : duba majmu'ul fataawa :24\366 da Nailul Audaar 4\112 da Ahakamul jana'iz shafi na: 171.

Allah shine mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa.

23/04/2017

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

WaΖ™ar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waΖ™e ak...

Contact form