Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA MIJINA BA LAFIYA?

INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA MIJINA BA LAFIYA?


                            Tambaya:

Salaam, Dr macece mijinta ba yada lafiyan aure tsawon lokachi, sai ya zamana tana yawan releasing ba sai tayi wani dogon tunani na sha'awaba, ya matsayin ibadarta yake ?

                                Amsa:

To gaskiya abin yake daidai shi ne: ya nemi magani, in kuma bai samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga cikin manufofin aure, katange ma'aurata daga fadawa haramun, kamar yadda shararren hadisinnan ya tabbatar.

Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar da saukin sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba, saboda iyayenki za su iya wajabtawa mijin neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya rabuwa, Allah ya azurta kowa dağa falalarsa.

Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa ki cikin hadari, mata nawa ne suka zama mazinata ta hanyar wannan sababin?
Ya wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita, tun da ya fita ne ta hanyar jin dadi.

ALLAH NE MAFI SANI

Dr. Jamilu Zarewa.

12/6/1437

22/3/2016

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren

MIFTAHUL ILMI

a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

JINI YANA ZUBO MINI, BAYAN CIKINA YA KAI WATA HUDU?

JINI YANA ZUBO MINI, BAYAN CIKINA YA KAI WATA HUDU?

                           Tambaya:

Assalamu Alaikum Dr dan Allah inada tambaya akan matar da keda ciki yakai wata hudu sai jini ya rinka xubar mata daga baya kuma sai ya dauke bayan kwana guda ko biyu yakan iya dawowa ko bayan wasu awoye shin ya hukuncin sallar ta? xata jinkirta sallah sai jinin ya dauke ko xata rika yin wanka duk sanda ya dauke tayi rankon sallolin baya ne. 
Nagode

                                Amsa:

To 'yar'uwa mutukar cikin ya kai wata hudu kuma jinin da yake fita yana hade da ciwon haihuwa, to ya zama jinin biki, kuma zai hana sallah, amma Idan babu ciwon haihuwa to mutukar ya zo da sifar jinin haila (baki ko karni) to zai zama haila, tun da a zance mafi inganci mai ciki tana iya yin haila.
 
In ya fita daga wadannan biyun zai zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah ba, in har jinin kusa-kusa yake fita, za ki iya jinkirta salloli, sai ya dan tsagaita, sai ki rama sallaolin da aka yi su kina da tsarki, saboda addinin musulunci addini ne mai sauki, babu kunci da damuwa a cikinsa, kamar yadda aya ta karshe a suratu Al-hajj ta yi bayanin haka.

Allah ne mafi Sani. 

Dr. Jamilu Zarewa

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren 📖MIFTAHUL ILMI📖 (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI_ a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

Wai akwai Hadisin da yasoke Hadisin da yace idan dayanku zaiyi layyah idan watan zullhijah yafita kada yayi aski da yanke farce ko kumba da cire gashi a jikinsa har sai ya yanka dabbar sa?

Asssalamu Alaikum
.
.
Tambaya ta 2,630
=
Wai akwai Hadisin da yasoke Hadisin da yace idan dayanku zaiyi layyah idan watan zullhijah yafita kada yayi aski da yanke farce ko kumba da cire gashi a jikinsa har sai ya yanka dabbar sa
Saboda naji wani malami yace wai.akwai Hadisi daga sayida Aisha dayake cewa Annabi
s a w yana tura Hadaya daga madina Zuwa makkah.batare dayaje aikin Hajji ba kuma baya haramtawa kansa aski da sauransu
=
=
Amsa
=
=
_Toh dafari dai shi wannan mutuminda yake wannan maganar ba malami bane, anadai cemasa malami yana amsawa, kuma ina kyautata zaton wannan maganar shugabannin mu'utazalawan zamaninnan sune suke fadarta, wadanda su dama sun shahara wajen musu da inkarin hadisan Annabi (s.a.w) suna cewa akaishi bola, to wannan maganar cewa ansoke haramcin aski da yanke farce ga me shirin layya to maganarsuce kuma qarya sukeyi ba,a sokesuba.

            Kudena ganin girman rawaninsu kuna jin damuwa dan munce qarya sukayi, domin babu shakka duk mutuminda zaice maka wannan haramcin an sokeshi to maqaryacine shi ko wanene.

       Amma idan kanaso kagane qaryarshi afili to katambayeshi, dan Allah me rawani, dan be halasta kakirashi malam ba, sekace masa yau dai shekaru fiyeda dubu daya da dari hudu ake wannan musulincin, kace to meyasa kakaf malamanda akayi a wadannan shekarun tundaga kan sahabbai har zuwa kan malamanmu nayau basu gane cewa ansoke  wannan hukuncinba sai shine ayau yasan abunda basu saniba???

        To sekace mishi yariqe wannan sabuwar fahimtar tashi kukuma sekubi wadancan ayarin na sahabbai da tabi'ai da sauran malaman Allah suda basuce an sokeba, shikuma seka biya dashi tacikin suratun nisa'i ayata 115, inda Allah ta'ala yake cewa:

Wanda yasa6awa manzon Allah bayan hujja ta bayyana gareshi, sekuma yabi hanyarda bata muminaiba, to zamu barshi da abunda ya janyoma kanshi, makomarshi kuma wutar jahannama yana me wanzuwa acikinta.

    ```Allah ta'ala ya tsaremu```
=
=
Allah yasa mudace
.
.
DAGA ZAUREN
.
KITABU WAS SUNNAH
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*

Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika

Share:

COMEDIANS GA NAKU

COMEDIANS GA NAKU

          TAMBAYA

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu

Malam don Allah menene hukunci wandanda suke Kirkirar labarin karya wai don su bama mutane dariya?

               AMSA

    Wa alaikumus salam warahmatullah.

Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace :

( AZABA TA TABBATA GA WANDA ZAI BADA WANI LABARI SAI YAYI KARYA DOMIN YADARIYANTAR DA JAMA'A DASHI, AZABA TA TABBATA AGARESHI, SANNAN AZABA TA TABBATA AGARESHI).

Tirmizi yaruwaitoshi acikin كتاب الزهد (kitabus zuhudi) babi na 10, abinda
yazo gameda Wanda zai furuta wata kalma domin yasa mutane dariyata dubi: Hadisi na 2315.

a dubi: Abu dawud:4990.

a dubi:Sahihul jam'i:7136.

daga:
Bahazu bin Hakim daga Babansa daga kakansa (رضي الله عنهما)

⚫Kamar masu karatun Ruwan bagaja
⚫Iliya Dan Mai karfi novels ,
⚫da masu rubutawayda
⚫ masu karantawa da
⚫ masu yi da baki duk sun shiga cikin wannan hadisin.

Allah ya kare mu da karya ko wace iri ce.

والله تعالى أعلم
〰〰〰〰〰〰〰〰〰〰〰

SHAFI'U SHEHU MINNA

(08033410797)

daga zauren:

ISLAMIC GROUP

Share:

Idan mace da mijinta sukaye wasanni sosai amma basu jima'i ba kuma sperm bai zuban mata ba amma shi yafitar shin Zatayi wankane koko à a?

Asssalamu Alaikum
.
.
Tambaya ta 2,629
=
Idan mace da mijinta sukaye wasanni sosai amma basu jima'i kuma sperm bai zuban mata ba amma shi yafitar shin Zatayi wankane koko à a
=
=
Amsa
=
=
Toh wannan bazatayi wankaba, saboda wanka yana wajabane saboda fitar maniyyi, kokuma saduwa koda maniyin be fita ba, amma bawai mujarradin mu'amala kawai se ace tayi wankaba, shinedai zeyi wanka dole amma itakam bazatayi wanka ba
=
=
Allah yasa mudace
.
.
DAGA ZAUREN
.
KITABU WAS SUNNAH
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*

Watsaps
08036222795

Share:

Wai da gaskene shuwagabannin Saudi ba suso ayi hawan Arafa ranar Jumua? Wai saboda tarihi ya nuna a lokacin zaa Karbe milki a hannunsu?

Tambaya:

Assalamu Alaikum Malam.  Wai da gaskene shuwagabannin Saudi ba suso ayi hawan Arafa ranar Jumua? Wai saboda tarihi ya nuna a lokacin zaa Karbe milki a hannunsu?

Wa alaikumus salamu warahmatullah.

Wannan maganar karyace tareda izgili ga addini, Allah yakare mana imaninmu.

1. Annabi Sallallahu alaihi wasallam, yayi arfa ne ahjjatul wada'i shekara ta tara bayan hijira hajjin karshe arayuwarsa.

Ansamo daga Umar Umar Dan Khaddab Allah kara masa yarda, lallai wani mutun daga cikin yahudawa yace: ya Amirul Muminina, akwai wata aya acikin littafinku da ace cikinmu ne jama'ar yahudawa ta sauka da munriki wannan yinin idi duk shekara inta zagayo, sai yace: wace aya ce? Sai yace: (ALYAUMA AKMALTU LAKUM DINAKUM, WA ATMAMTU ALAIKUM NI IMATIY WARADITU LAKUMUL ISLAMA DINA). Umar yace: Hakika munsan wannan yinin, da wurinda tasauka ga Annabi Sallallahu alaihi wasallam, yana tsaye ne afilin arfa ranar jumu'ah. Imamul Buhari yaruwaitoshi acikin kitabul Imani na Sahihul Bukhariy, babin karuwar imani da tawayarsa, babina na: 33. Hadisi na: 45.

Darasin da zamu dauka awannan hadisin yana da yawa kadan daga ciki:

A. Annabi yayi arfar Hajjatul wada'i ranar Jumu'ah ne, saboda haka babu wani tarihi da ya nuna za'a kwace mulki daga hannunsu amusulunce.

B. duk abinda yacika zai taragewa ne ahankali, harda Imani.

C. Yahudawa sunsan gaskiyar musulunci hassada kawai ke hanasu bi.

D. Yahudawa larabawan bidi'a ne.


E. Sahabbai basu bidi'ah.

F. Ba arena bidi'a komai karancinta.

G. Wamnan ayar bayanta ba wani hukunci da aka sake saukarwa bayanta na ibada, sai dai na tauhidi da akida, ayar da aka saukar karshe gabaki daya akur'ani ayar dake bakara: 281.

H. Ba'ayarda ayi wani biki ko idi ko hutun shekara Ashekara ace duk in shekara ta kewayo ayi sai biyu kawai, Idin layya dana azumi. Lokacin da Annabi Sallallahu alaihi wasallam yazo madina yasamesu suna wasa duk shekara aranaku biyu sai yace: (HAKIKA ALLAH YA CANZA MUKU SU DA WASU YINI BIYU DA SUKA FISU ALHERI, YININ SALLAR LAYYA DA TA AZUMI ).

Abu dawud:1134.

Saboda haka babu:
X'mas day, Maulidi day, da children day, da Birth day, da independence day, Democracy day,  da workers day, da Teacher day, da Hijab day, day, day, day,... duk babu su amusulunci.

I. Ashekarar 2006. Dani akayi arfa, kuma aranar Juma'ah akayita, kuma ba'asamu hajjinda yatara dan mutun kafinsa irinsa ba,  kuma ba wanda aka kwacewa mulki kuma ba wanda yamutu cikin sarakunan, balle ma wannan shekarar akafi saukin mutuwa a aikin hajji.

J. Idan Arfa ta kama ranar Jumu'ah, to duk kasashen larabawa dake kewayen makkah, zakaga sunyi cincirindo sunzo aikin hajji hadda shuwaganni.

K. Sai dai hadisin da yace: wai arfa ranar  Jumu'ah dai dai take da Arfa arba'in 40, bai ingantaba.

Allah yabamu ikon fahimtar addininmu.

Wallahu ta ala a alam.

Shafi'u Shehu Minna.

Daga Islamic Group.

Share:

Suratul Bayyina Da Fassarar ta

Suratul Bayyina Da Fassarar ta


Sura ta 98 @yoyinta 8 an saukar da ita a Madina

```بسم الله الرحمن الرحيم

١.لم يكن الذين كفرو من اهل الكتب و المشركين منفكين حتى تاتيهم البينة.

1⃣.  Wadanda suka kafirta na daga Ahlul kitabi da mushirikai basu kasance suna sabani ba har saida gaskiya tazo masu.

٢.رسول من الله يتلوا صحفا مطهرة.

2⃣.  Manzo yazo masu daga Allah ya karanta masu takardu masu tsarki.

٣.فيها كتب قيمة.

3⃣. A ciki akwai Littatafai masu inganci.

٤.وما تفرق الذين اوتو الكتب الا من بعد ما جاءتهم البينة.

4⃣.Ahlul kitabi Basu Samu Rabuwar kai ba har saida hujjah ta zo masu.

٥.وما امروا الا ليعبدوا الله مخلصين له الدين حنفاء و يقيموا الصلوة ويؤتوا الزكوة، وذالك دين القيمة.

5⃣.Bamu umurceku ba saidan ku bauwata @llah kuma masu tsarkake addini a gareshi kuna karkata daga addinin karya, Ku tsaida sallah Ku bada zakkah,wannan shine addini mai karfi.

٦.ان الذين كفروا من اهل الكتب والمشركين فى نار جهنم خلد ين فيها، اولؤك هم شرالبرية.

6⃣.Lalle wadanda suka kafirta daga wadanda aka baiwa littafi (yahudu da nasara) da mushirikai suna cikin wutar jahannama suna masu dawwma,Wadannan sune mafi sharrin Alkarya.

٧.ان الذين ءامنوا و عملوا الصلحت اولؤك هم خير البرية.

7⃣.Lalle wadanda sukayi imani kuma suka aikata aiki na gari,Wadannan sune mafi Alkhairi Alkarya.

٨.جزاؤهم عند ربهم جنت عدن تجرى من تحتها الانهر خلدين فيها ابد، رضى الله ورضواعنه، ذالك لمن خشى ربه.

8⃣.Sakamakon su yana ga Ubangijinsu Ya tanada musu Aljanna wace koramu ke gudana a cikinta har abada, Ya arda dasu sums sun arda dashi, Waccan shine Sakamakon musu jin tsoron Allah. ```+2347039135966

Share:

ZA MU IYA HADA SALLOLI SABODA DOKAR TA-BACI?

ZA MU IYA HADA SALLOLI SABODA DOKAR TA-BACI?

                          

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Dan Allah muna neman fatawar ku game da halin da muke ciki a garin GEIDAM na jihar YOBE. Wato yau fiye da watanni hudu kenan muna cikin dokar tabaci a garin GEIDAM na jihar YOBE,kuma dokar karfe 7:00pm ne. To wasu malamai suna bada fatawar cewa ahada sallar magariba da Isha, wasu kuma suna bada fatawar cewa kowa yayi sallar isha a gida, wasu kuma suna bada fatawar cewa ayi sallar magariba sannan Idan lokacin sallar isha yayi sai afito domin yin sallar (duk da hadarin dake cikin karya dokar). To don Allah ku amsa mana domin anfanin al'umar musulmi.

                               Amsa:

Wa'alaikum assalam, A fahimtata mağanar wadanda suka ce a jira sai lokaci ya yi tafi inganci, akan wadanda suka ce a hada sallolin, saboda malamai sun yi itifaki cewa Sallah ba ta ingantuwa kafin lokacinta, in ba a wuraren da sharia ta togace ba, amma sun yı sabani game da wajabcin sallar jam'i inda malakiyya suka tafi akan cewa: sunna ce, a wajan Shafi'iyya kuma Fardhu kifaya ce, idan wasu dağa cikin musulamai suka yi sun daukewa ragowar, duk abin da malamai suka yi ittifaki ana gabatar da shi akan abin suka yi sabani, dön haka ba za'a yi sallah kafin lokacinta ba, saboda a riski jam'i, tun da an yi sabani akan wajabcinta.

Bai halatta mutum ya jefa kansa cikin hallaka ba, don kawai ya riski sallar jam'i, saboda hakkokin Allah an gina su ne akan rangwame, wannan yasa mutum zai iya fadan kalmar kafirci idan aka takura maşa, don ya kubutar da kansa, kamar yadda kissar Ammar bn Yasir da aya ta: 106 a suratul Nahal suka tabbatar da haka, dön haka yın sallarku a gida shi ne daidai, ba fitarku ba wacce za ta iya sanyawa a harbe ku.

A Zance mafi inganci sallar jam'i wajibi ce, saboda karfin dalilan da HANABILA suka kafa hujja da su, saidai abin da ya tabbata a ilimin Usulul Fiqh shi ne: Sharadi ya fi wajibi karfi, sababi kuma an fi kula da shi fiye da sharadi, lokutan sallah sabuba ne da sharia ta rataya wajabcin salloli akan şu, dön haka za'a gabatar da su akan wajibai, in ba wurin da Allah da manzonsa suka togace ba.

Dr. Jamilu Zarewa

14/03/2016

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI📖 (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

AIKIN DA ZAKAYI KA SAMI LADAN WANDA YAYI HAJJI DA UMRA

AIKIN DA ZAKAYI KA SAMI LADAN WANDA YAYI HAJJI DA UMRA

       

  TAMBAYA

Assalamu alaikum
Wani aikine nutum zaiyi Allah yabashi ladan haji da umara

           
AMSA

Wa alaikumus salamu warahmatullah.

Suna da yawa, kadan daga ciki:

1. Annabi(صلى الله عليه وسلم) yace: ( WANDA YA SALLACI ASUBA ACIKIN JAM'I[jama'a], SANNAN YAZAUNA AWURIN YANA ANBATON ALLAH HAR RANA TA FUTO, SANNAN YASALLACI RAKA'A BIYU[na nafila] TA KASANCE AGAREAHI TAMKAR HAJJI DA UMRAH),

Anas yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)    CIKAKKU).
wato Hajji da Umra
Sunanut Tirmiziy: 586.


2. Annabi Sallallahu  yace: ( DUK WANDA YAFITA DAGA GIDANSA DA ALWALLA ZUWA GA SALLAR FARILLAH[jama'a], TO LADARSA KAMAR LADAR MAI MAHARRAMA DA HAJJI).
Sunanu Abi dawud: 558

3. ( WANDA YAFI DAGA GIDANSA ZAIJE SALLAR WALHA[duha], BA ABINDA YAFITAR DASHI SAI ITA, LADARSA KAMAR LADAR MAI UMRA NE).

a duba:Sunanu Abi dawud:558.


Daga Abu Umamah Allah yakara masa yarda.

4. Annabi (صلى الله عليه وسلم)yace: ( SALLAH ACIKIN MASALLACIN KUBA,  TAMKAR UMRA CE).

a duba:Sunanu Ibnu Majah:1411.

a duba:Tirmiziy:324.

5. Dabtaniy yaruwaito acikin Al ausad Annabi (صلى الله عليه وسلم) have:

( IDAN MACE NA GIRKI, TANA KAI KOMO TSAKANIN DAKINTA DA MADAFI[kiching , domin dauko gishiri mai dadai sauransu], TO ANA BATA LADAR SAFA DA MARWA NE).

6. Ana cewa: Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: ( IDAN MACE TAYI KWALLIYA TA KWANTA KAN GADON MIJINTA TANA JIRAN DAWOWARSA, TO TANA DA LADAR HAJJI DA UMRA).

Karin bayani

❗1. Zuwa masallaci jam'i na jawo ladar aikin hajji.

❗2. Zuwa masallaci sallar walha na kawo ladar Umrah.

❗3. Zama bayan sallar asuba ana zikir na sunnah ba atashiba, ba ayi magana ba, ba'ayi bacci ba, ba ayi tusa ba, har rana tafito ,kuma akayi sallar hantsi raka'a biyu, na sa a Samu ladar Hajji da Umrah ga baki daya.

❗4. Mata masu daukar yar aiki tana yi musu abinci suna yin hasarar Safa da Marwa.

❗5. Kwalliya asa turare ajira mai gida akan gado yana sa asamu hajji da umrah.

❗6. Maziyarta madina suyi kokarin sallah a masallacin kuba, inkun kara sati daya.A madina  sai kukoma, domin Annabi duk mako yake zuwa, amma ba dole sai kayi alwallah daga gida ba.

❗7. Mata marasa aure, ansha dasu, anyi masu fintinkau, Allah sarkin.

〰〰〰〰〰〰〰〰〰〰〰

AMSAWA

SHAFI'U SHEHU MINNA

(08033410797)

daga zauren:

ISLAMIC GROUP 1 & 2

Share:

YAUSHE NE AZUMIN ASHURA DA TASU'A 1439/2017???!!!

YAUSHE NE AZUMIN ASHURA DA TASU'A 1439/2017???!!!

Assalamu alaikum, Duba da yanda ake yawan tambaya dangane da yaushe ne ranar azumin Ashura da Tasu'a na wannan shekara, ya sanya muka ga ya dace mu sanar da mutane cewa a bisa Sanarwa da masana wannan fanni suka yi kuma mai Alfarma Sarkin Musulmi ya sanar shi ne: Ashura da Tasu'a za su kasance ce ne ranar Asabar da Lahadi wato 30/09/2017 da 01/10/2017, in sha Allahu Ta'ala.

Kuma kamar yadda aka sani sunna ce ta Ma'aiki, sallallahu 'alaihi wa sallama, azumtar wannan rana.

Allah Ta'ala Ya sa mu dace.

✍🏼Dan uwanku a Musulunci:
Umar Shehu Zaria_
27/09/2017.

Daga: ZAUREN FIQHUS SUNNAH

Share:

NA JONA SALLATA DA TA MAMU BAYAN AN GAMA SALLAR JAM'I, SHIN TA INGANTA?

NA JONA SALLATA DA TA MAMU BAYAN AN GAMA
SALLAR JAM'I, SHIN TA INGANTA?

Tambaya:​

Assalamu alaikum malam. Shin ya halatta abi wanda bai samu cikakken jam'i
ba sallah? Misali, na zo masallaci na taradda jam'i na sallar
asr saura raka'a 2, da aka idar na mike tsaye don karasa raka'a
2 da ta ragemin, sai ga makararre ya sake hada jam'i da ni.
Shin wannan jam'in na 2 ya halatta? Idan ya halatta, tare da
hujjoji.

Amsa​

Wa alaikum assalam.To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar
zuwa zantuka guda biyu:

1. Malaman Hanafiyya da Malikiyya, sun tafi akan haramcin
hakan, saboda ba'a samu magabata suna yi ba, sannan kuma
shi masabuki ba liman ba ne, Annabi S.A.W kuma ya yi umarni
da bin liman ne kawai, sannan hakan zai iya jawowa sallah ta
ki karewa, tun da wanda ya bi masabuki, shi ma in ya gama
yana ramako wani zai iya zuwa ya bi shi, don haka sai ya
haramta . Duba Fathul-kadeer 1\277 da kuma Mawahibul-jalil
4\489.

2. Malaman Shafi'iyya da kuma Hanabila a mafi ingancin
zancensu, sun tafi akan halaccin hakan, saboda hadisin Ibnu
Abbas lokacin da ya ga Annabi yana sallah da daddare sai ya
bi shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba
ta:666, A wannan hadisin za mu fahimci cewa ya halatta
mutum ya zama liman a tsakiyar sallah, ko da kuwa bai yi
niyyar hakan ba tun daga farko, tun da Annabi S.A.W bai hana
Ibnu Abbas ba lokacin da ya bi shi, tare da cewa ba su fara da
shi ba, sannan kuma duk lokacin da masabuki ya rabu da
liman to yana daukar hukuncin mai sallah shi kadai ne, don
haka sai ya halatta a bi shi.
Duba Nihayatul-muhtajj 2\233 da kuma Insaf 2\36.

Zancen da ya fi inganci shi ne zance na biyu saboda abin da ya
gabata da kuma hadisan da suke nuna falalar sallar jam'i.

Allah ne mafi sani.

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
07/12/2014

Share:

MENENE AKA HANA WANDA YAKE SAN YIN LAYYA YA AIKATA?

MENENE AKA HANA WANDA YAKE SAN YIN LAYYA YA AIKATA?

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

AMSA:

Idan Watan zul-hijjah ya kama, haramunne akan Namiji ko mace da ya kesan yin layya, ya yanke farcensa ko sumarsa.

Saboda hadisin da Muslim ya ruwaito (1977) daka Ummu Salama Allah yaqara mata yarda daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Idan Kuka ga Watan zul-hijja, kuma dayanku yana san Yin layya, ya kame  daka yanke farcensa ko Aske gashinsa)

Imamun Nawawi Rahimahullahu yace: Malamai Sunyi Sabani akan wanda watan zul-hijjah ya kama yana san yin layya.

Sa'eed da Ibnu Musayyib da Rabi'ah da Ahmad da Ishaq da Dauda da Wasu MalamanvSahafi'iyyah sukace: Haramunne mutum yacire komai na gashinsa, da farcensa, harsai yayi layya, shafi'i yace: Makaruhine karhanci na Kamala, ba Haramun bane.

Sharhin Muslim.

Mace ya Halatta ta Tsefe gashin kanta, ta Wankeshi, Saidai kada ta Tajeshi, Abunda ya zuba na gashinta yayin tsefewa da Wankewa Baya cutarwa akan layyarta.

Fatawa bin Baaz (18/47).

Ya Halatta Wanda yake da Niyyar layya ya gyara tufafinsa ko yasa turare ko yin jima'i.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai

WhatsApp Group

2348123432272

Share:

SHIN YA HALATTA YIWA WANDA YA MUTU LAYYA?

SHIN YA HALATTA YIWA WANDA YA MUTU LAYYA?

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

AMSA:

Asali layya an shar'anta ta ga wanda yake rayayye, Kamar yanda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam da Shabbansa suka kasance sunaiwa kansu da iyalansu layya, abunda wasu suke dauka na kebance layya ga wanda ya mutu bashi da Asali.

Yiwa Wadanda ya Mutu layya kashi uku ne:-

Nafarko: Yiwa mamaci layya amma yabi cikin rayayyu, mislai, Ka niyyaci layya ga kanka da iyalanka, rayayyu da Matattu.

Wannan ya halatta, asalin Wannan shine layyar Annabi Sallallahu Alaihi wasallam da iyalan gidansa daka cikinsu akwai wadanda suka mutu

Na Biyu: Yiwa mamaci Layya saboda yabar wasiyyar Ayi masa, za'ai masa don zartar da wasiyyar sa, ( Wannan dolene) saidai idan mutum yakasa, Saboda fadin Allah madaukakin Sarki ( Duk Wanda ya canja Abunda mamaci yai wasici dashi na Alkhairi, zunubin yana kan wanda ya canja wasiyyar, Lallai Allah mai jine mai ganine)

Na Uku: Yiwa mamaci layya dan kyautatawa, kamar yiwa iyaye layyah, Wannan ya halatta.

Malaman Hanabila Sukace: ladan zai isa garesu kuma zasu Amfana dashi, qiyasi akan yi musu sadaka.

Saidai Bama ganin kebance yiwa mamaci layya yana daka cikin Sunnah.

Domin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam bai yiwa kowa layya daka cikin wadanda suka mutu ba a kebance, baiyiwa Ammunsa Hamza layya ba, wanda yana cikin manyan Makusantansa.

Baiyiwa 'ya'yansa wadanda suka mutu a rayuwarsaba, baiyiwa Matarsa khadija ba, tana daka cikin matan da yafi so, kuma ba'a ruwaito daka Sahabbansa ba.

Yana daka cikin Kus-kure abunda wasu suke aikatawa, yiwa mamaci layya farkon shekarar da ya mutu, suna kiranta da layyar rami) suna qudurce babu wanda ya halatta yai tarayya dashi acikin ladanta, ko suyiwa mamatansu layya saboda wasiyyarsu, amma basa yiwa kansu da iyalansu layya,

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai

WhatsApp Group

2348123432272

Share:

WADANNE SHEKARUNE SUKE WAJIBI A KULA DASU YAYIN LAYYA?

WADANNE SHEKARUNE SUKE WAJIBI A KULA DASU YAYIN LAYYA?

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

AMSA:

Malamai sun hadu akan akwai wasu shekaru da shari'a ta iyakance wajan layya, bai halatta yin layya da dabbar data gaza daka suba.

Duk wanda ya yanka dabbar data gaza da shekarun layyarsa bata yiba.

An ruwaito hadisai dasuke nuni akan haka, Duba Al-majmu'u na Nawawi

Bukhari ya ruwaito (5556) da muslim (1961) daka bara'u bin Azib, yace wani dan'uwansa da'ake cewa abu burda ya tambayi manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, yayi layya da akuyar da bata cika shekara guda ba? Annabi yace: jeka kayi layya da ita,  Amma daka kai babu wanda ya halatta yayi da akuyar da batakai shekara daya ba,

Musilm ya ruwaito hadisi (1963) daka jabir Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( kada ku yanka dabbar layya sai wacce ta cika shekara, saidai idan kunsamu kanku cikin qunci saiku yanka wacce bata kai shekaraba daka cikin tumaki,

Nawawi acikin Sharhin Muslim yace: Malamai Sukace: "Musannah" itace wacce ta tafi shekara ta biyu daka kowanne dangin dabbobin ni'ima raqumi ko saniya, awaki da tumaki zuwa sama, Wannan bayanine qarara akan bai halatta yanka wacce bata shekaraba inba Daka dangin tumaki ba, a kowanne hali.

Alhafiz acikin Talkees (4/285) yace:

Zahirin hadisin ya nuna baya halatta yanka tunkiya ko rago wanda bai shekara ba, sai idan baka da halin siyan wanda yacika shekara ya tafi ta biyu, ijma'i abisa sabani, wajibine ayi tawilinsa, ya dauki abunda yafi falala, qaddarawarsa shine, Kada ku yanka dabba sai wacce ta cika shekara guda.

Haka Nawawi yace: acikin sharhin Muslim, da Aunul Ma'abuud.

Yazo acikin Mausu'ah fiqhiyyah (5/83) wajan Anbaton Sharadin layya.

Dabba ta kai shekarun layya, ta zama "saniyyah" raqumi ko saniya ko akuya (jaz'ah) ko wacce take sama da ita daka tumaki, bai halatta yin layya da dabbar da batakai "saniyyah" ba, Sai cikin tumaki, ko abunda bai kai jaz'ah cikin tumaki ba....

Wannan Sharadin An hadu akansa tsakanin malamai Saidai sunyi sabani akan fassarar Saniyyah da Jaz'ah

Kamar yanda ibnu Abdul barri ya fada acikin tarteebul Tamheed (10/267)

Kamar yanda nawawi yace: acikin Al-majmu'u (8/366).

Jaz'ah a dangin tumaki, itace wacce ta cika wata shida awajan ```Hanafiyyah da Hanabila, a wajan Malikiyyah da shafi'iyyah itace: Wacce ta cika shekara.

Al-Musinnah: Daka akuyoyi itace: Wacce ta cika shekara daya,a wajan Malikiyyah da Hanafiyyah da Hanabila, Awajan shafi'iyya kua itace: wacce ta cika shekara biyu```

Musinnah daka Shanu: Itace wacce ta cika (shekara biyu) awajan Hanafiyyah da Shafi'iyya da Hanabila, Awajan malikiyyah itace: Wacce ta cika shekara uku.

Musinnah cikin Raquma itace: Wacce ta cika shekara biyar, awajan Hanafiyyah da Malikiyyah da Shafi'iyyaj da Hanabila.

Duba:- Bada'i'il Sana'i'i (5/70) da Baharul ra'iq (8/202) da Attaaju wal-ikleel (4/363) da Sharhin Muktasarul khaleel (3/34) da Maj-mu'u (8/365) da Al-Mugny (13/368).

Yazo afatawa lajnatul da'imah (11/377), Sukace:.

Dalilai na Shari'a Sun nuna ya halatta yin layya da, ( Tunkiya ko ragon da ya kai wata shida) akuya ko taure wacce ta cika shekara guda, Saniya ( Wacce ta cika shekara biyu) raqumi wanda ya cika (shekara biyar) Abunda yake qasa da Wadannan baya halatta ayi hadaya ko layya dashi, domin Dalilai na Qur'ani da Sunnah sahinsu yana fassara sashi.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai

WhatsApp Group

2348123432272

Share:

SHIN YA HALATTA HADA LAYYA DA AQIQA?

SHIN YA HALATTA HADA LAYYA DA AQIQA?

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

AMSA:

Idan layya da aqiqa suka hadu, kanaso kaiwa danka yanka ranar idin babbar Sallah, ko aranakun gyaran nama, shin layya ta wadatar maka da yin aqiqa?.

Malamai Sunyi Zantuka guda biyu akan wannan Matsalar.

Nafarko, layya bata iyuwa ahadata da aqiqa, wannan shine mazhabar malikiyyah da shafi'iyyah da ruwaya daka imamu Ahmad.

Hujjarsu itace: ko wanne daya daka cikinsu karan kansa yake ci, tsakanin layya da aqiqa,

Daya bata wadatarwa akan daya, kowanne cikinsu yana da Sababinsa, sababin kowanne ya saba dana dayan, daya bata tsayuwa da daya.

Kamar yankan tamattu'i da yankan fidya.

Haitamy rahimahullahu acikin Sharhin Minhaaj (9/371) yace:  Idan mutum ya niyyaci yankan aqiqa da layya da dabba daya bata wadatar akan dayar ba, wannan shine zahiri, domin kowanne acikinsu sunnace mai zaman kanta.

Zance Na biyu: Layya tana wadatarwa akan aqiqa,  ruwaya daka Imamu Ahmad itace mazhabar Ah-naaf, haka hasanul basary da Muhammad bin Sireen da Qatada Allah yajiqansu da rahama Sukace

Hujjarsu itace: Dukkansu manufar yinsu shine samun kusanci zuwa ga Allah da yanka, daya tana shiga cikin daya, kamar yanda tahiyatul Masjida take shiga cikin Sallar farillah ga Wanda ya shiga masallaci.

Al-Musannaf na Ibnu Abiy shaiba (5/534).

Hasanul Basary yace: idan kaiwa yaro layya ta isar masa akan aqiqarsa..

Kamar yanda Shishaam da Ibnu sireen sukace

Qatada yace: Layya bata wadatarwa akan aqiqa, harsai anyi masa aqiqarsa.

Buhty acikin sharhin muntahal iradaa (1/617) yace: idan lokacin aqiqa yai dai-dai da lokacin layya, idan akai aqiqa ta wadatar akan layya, idan akai layya ya wadatar akan aqiqa..

Kamar juma'a ce tayi dai-dai da ranar idi, idan kai wanka daya ya isar akan dayan, haka wanda yai yanka saboda tamattu'i ranar Sallah, ya isar masa akan layyah.

Kamar yanda yazo acikin kashshaful Qina'i (3/30).

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai

. WhatsApp Group

2348123432272

Share:

Sallar Juma'a Ranar Idi

`Assalamu alaikum
Malam yaya hukuncin sallar jumu'a ranar idi? Shin ta wajaba ko kuma bata wajaba ba?```

AM'S A:

*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ.

Idan mutum yayi sallar idi tareda liman, toh jumu'at bata wajaba ba, yanada zabi guda biyu, idan yaga dama ya sallace ta idan kuma yaga dama yabarta sai yayi sallar azahar. Saboda hadisai sun inganta.

ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ: ‏ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻋﻴﺪﺍﻥ ﻓﻲ ﻳﻮﻣﻜﻢ ﻫﺬﺍ ﻓﻤﻦ ﺷﺎﺀ ﺃﺟﺰﺃﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ، ﻭﺇﻧﺎ ﻣﺠﻤﻌﻮﻥ ﺇﻥ ﺷﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ. ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ، ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺒﻮﺻﻴﺮﻱ: ﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ ﻭﺭﺟﺎﻟﻪ ﺛﻘﺎﺕ.

Daga Ibnn Abbas Allah ka kara musu yarda cewa lalle Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) yace: sallar idi biyu sun hadu wannan rana/yini naku (sallar idi da sallar jumu'at kenan), Wanda yaso (idi) ta isar masa jumu'a, Amma mu zamu hadasu (idi da jumu'a kenan) inshaa Allah.

(Ibn Majah ya ruwaito shi.).

(Albuwaisriy yace isnaadinsa ingantacce ne kuma maruwaitansa amintattu ne).

عن ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﻗﺎﻝ: ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻋﻴﺪﺍﻥ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺼﻠﻰ ﺑﺎﻟﻨﺎﺱ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: ‏ﻣﻦ ﺷﺎﺀ ﺃﻥ ﻳﺄﺗﻲ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻓﻠﻴﺄﺗﻬﺎ، ﻭﻣﻦ ﺷﺎﺀ ﺃﻥ ﻳﺘﺨﻠﻒ ﻓﻠﻴﺘﺨﻠﻒ. ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ﻭﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ.

Daga Ibn Umar Allah ka yarda dasu yace: Eidi biyu (jumu'a da Eidi) sun hadu a zamanin Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) sai ya jagoranci mutane sallah (sallar idi) sannan yace Wanda yakeson zuwa jumu'a toh yaje (yayi jumu'arsa), Wanda yakeso ya bazaiyi (jumu'a) ba, toh kar yayi jumu'a din.

(Ibn Majah da Dabaraani suka ruwaito shi).

والله أعلم،

********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

Tambayoyin Musulunci

            Whatsapp Group

Share:

IDAN UBA BAI YIWA DANSA AKIKA BA RANAR BAKWAI, MENENE MAFITA ?

IDAN UBA BAI YIWA DANSA AKIKA BA RANAR BAKWAI, MENENE MAFITA ?

Tamabaya

Assalamu alaikum.
yaa shaikh (dr.) mutun ne Allah ta'ala ya bashi karuwa ta (haihuwa) bai samu hali yin yanka ba, har sai bayan wata hudu tukunna Allah ya hore mashi, shin yankannan tana kanshi ko ta fadi???

Amsa

Wa alaikum assalam,

Ya tabbata a cikin hadisin Tirmizi cewa ana yiwa abin da aka Haifa Akika ranar 7/wata.
Wasu  malaman daga cikin Sahabai da wadanda suka zo bayansu sun yi karin bayani cewa: in ba'a samu damar yi ba ranar bakwai ana iya  yi ranar 14 ko kuma  ranar 21.

Duk wanda bai samu damar yiwa dansa Akika  ba a  kwanakin da aka ambata a sama,  to babu wani kayyadajjen lokaci, zai iya  yi duk lokacin da ya samu dama.

AKIKA hakki ne akan Uba zai yi kyau ya yiwa dansa a lokacin da Annabi S. a. w  ya ambata, in kuma ba shi da dama, ya yi masa da zarar Damar ta samu.
Allah ne mafi sani

Don neman karin bayani duba: Daka'iku Ulin Nuha 1/615.

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

26/08/2017

Daga

ZAUREN FIQHUS SUNNAH

Share:

Hukuncin Yin AMFANI DA MOTAR OFFICE A HARKOKIN KASHIN-KAI

AMFANI DA MOTAR OFFICE A HARKOKIN KASHIN-KAI ?


Tambaya

Assalama alaikum Malam ya halatta mutum ya zuba mai a motar ma'aikatar da yake aiki, ya kai matarsa unguwa, ko ya je harkokinsa na yau da kullum, a ciki ?

Amsa:

Wa alaikum assalam

To dan'uwa kwamitin fatawa na din-din na Saudiyya ya bada fatawa cewa: Bai halatta mutum ya yi amfani da motar gwamnati wajan harkokinsa na yau da kullum ba, tun da ba dan haka aka tanaje ta b\a, kamar yadda ya zo a fatawa mai lamba ta: 16594.

Sheik Ibnu Uthaimin yana cewa: "Ko da shugabanka na office ya halatta maka, bai halatta ba, tun da b a huruminsa ba ne, ba kuma mallakinsa ba ne, kamar yadda ya zo a: Lika'u babil maftuh: 238.

Yana daga cikin siffofin muminai kiyaye amanar da aka damka a hannunsu, kamar yadda aya ta: 8 a suratul Muminuna ta tabbatar da hakan.

An rawaito cewa Khalifa Umar dan Abdul'aziz ba ya amfani da fitilar gwamnati a harkokinsa na kashin-kai, ko da kuwa bako ya yi bai zai yi hira da shi da fitilar gwamnati ba, in har ba matsalolin da suka shafi jama'a za su tattauna ba, wannan sai ya nuna taka-tsantsan da dukiyar office yana daga cikin tsentseni.

Duk wanda ya wadatu Allah zai wadatar da shi, wanda ya kame Allah zai kamar da shi, Wadatar zuci taska ce da ba ta karewa.

Allah ne mafi Sani.

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

25\2\2016

Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH

Share:

HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA

HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA

Tambaya :

Assalamu alaikum. Malam  wata tambaya nake da ita Dr. Wai shin meye gasiyar hukuncin wanda ya sayi kaya a lokacin da suke araha ya boye da niyyar in sunyi tsada ya fito da su ya sayar dan ya sami riba mai yawa? Allah shi dada budi amin

Amsa :

Walaikum assalam To dan'uwa ya zo a hadisi cewa : "Ba wanda yake boye kaya sai mai zunubi"  Tirmizi  ya rawaito shi a : 3\567, kuma ya kyautata shi, saidai  malamai sun yi sabani akan irin kayan da ya haramta a boye da wadanda ba su haramta ba :

1. Akwai wadanda suka tafi cewa : duk wani abu da mutane suke bukatarsa to bai halatta mutum ya siya ya ajjiye ba,  da nufin sai yayi tsada ya fito da shi, don haka har tufafi da magunguna bai halatta a boye su ba, saidai idan ya siya ne da nufin ya yi amfani da su  nan gaba. Ko kuma iyalansa, Wannan shi ne maganar Abu-Yusuf babban almajirin Abu-hanifa, kamar yadda yazo a littafin : Daurul-kiyam wal'aklak fil-islam shafi na : 295. Sannan ita ce maganar Malik a Mudawwanah kamar yadda ya zo a : 4\291.

2. Akwai malaman da suka tafi cewa ya halatta a boye abin da yake ba abinci ba ne da mutane za su ci su rayu, kamar barkono, zabibi, mai, da sauransu, saboda yawanci mutane suna cutuwa ne idan aka boye abinci. An rawaito wannan daga  Abdullahi dan Mubarak da Sa'id dan Musayyib kamar yadda Tirmizi ya ambata a Sunan dinsa  3\567   sannan ita ce maganar Shafi'iyya  da Hanbaliyya , kamar yadda ya zo a
Raudatu Addalibiina 3\411 da kuma Almugni 4\154

Wasu malaman suna rinjayar da maganar farko, amma idan ba siyan abin ya yi ba, ya mallake shi ne ta wata hanya, ko kuma ya noma sai ya boye har ya yi tsada sannan ya siyar, to wannan bai haramta ba, ko da kuwa abinci ne, har wasu malaman ma  sun hakaito ijma'in malamai akan halaccin haka, kamar yadda ya zo a Jami'ussagir  shafi na : 481

Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Share:

NA SHA NONON MATATA,YAYA AURANMU?

NA SHA NONON MATATA,YAYA AURANMU?


Tambaya :

Don Allah malam ya matsayin mutumin da ya sha nonon matarsa,  ya aurensu  yake ?

Amsa :
 
To dan'uwa Allah madaukakin sarki ya halatta maka jin dadi da dukkkan bangarorin jikin matarka, in ban da dubura ko kuma saduwa da ita lokacin da take haila,don haka ya halatta ka tsotsi nononta mutukar babu ruwa a ciki,amma idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi sabani akan halaccin hakan zuwa  maganganu guda biyu : 

1.Ya halatta, saboda kasancewar nonon da yake haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru biyu,  saboda fadin Annabi s.a.w. "Shayarwar da take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha saboda yunwa" , Bukhari lamba ta : 5102, 

 ma'ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba zai yi tasiri ba wajan haramta aure,  wannan ita ce maganar mafi yawan malamai .

2. Bai halatta ya sha ba, saboda ko da yaushe mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi s.aw. ya  umarci matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim, don ta haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha nono to zai yi tasiri wajan haramcin aure .

Zancen da ya fi karfi shi ne ya halatta miji ya sha nonon matarsa, saidai rashin shan shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin malamai yana da kyau.

 Don neman Karin bayani duba : Bidayatul-mujtahid 2\67

Allah ne mafi sani

Amsawa:

Dr Jamilu Yusuf Zarewa.

ZAUREN DARUL-ISLAM

Share:

Malam wai da gaskene cewar, kowa sai ya dandana wutar lahira, banda Annabi Muhammad (S.A.W.)?

MALAM MINENE GASKIYAR WANNAN MAGANAR?


                            Tambaya:

Malam wai da gaskene cewar, kowa sai ya dandana wutar lahira, banda Annabi Muhammad (S.A.W.)?

(Daga Dahiru Adam).                                Amsa


DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.

A’a cewa akayi "WADDUHA" ba cewa akayi "MUTHEEQUHA" ba.

Watau kowa sai yabi takan wuta sannan ya wuce. Domin Siradi, akan wuta aka dorashi, mutanen da aka yiwa hisabi zuwa Aljanna sai sunbi takan Siradin.

Wanda yake a kan wuta.
Shine (acikin Alkur'ani) akace: "WA-IN-MINKUM-ILLA WARIDUHA KAN-ALARABBUKA HATMAN MAQDIYYA".

"وَإِن مِّنكُمْ إِلَّا وَارِدُهَا كَانَ عَلَىٰ رَبِّكَ حَتْمًا مَّقْضِيًّا".
Suratul Maryam.

Amma kuma jin zafinta (wutar) sai wanda Allah ya nufa da yaji zafin nata, sannan yaji zafin. Allah ka tseratar damu daga azabar wuta.

WALLAHU A'ALAM.


Rubutawa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren

📖MIFTAHUL ILMI📖

(WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

Na Sadu Da Tsohuwar Budurwa Ta Alhalin Tana da Aure

TAMBAYA
========

Assalamu alaikum.

Malam fatan anyi sallah lfy.
Malam bansan da wace fuska zan fada maka irin halinda nake cikiba.
Malam agaskiya nayi qoqarin yin kyakkyawan aiki amma ta hanya mummuna,Malam anyima budurwata auren dole ga tsoho Wanda ya girmi kakanta,ta sanadiyyar haka ta kamuda ciwon zuciya da hawan jini mai tsanani, yanzu haka sunfi shekara bata taba bari ya kusancetaba,tabi duk irin matakan daya kamata tabi akan ya saketa,amma yaqi.saboda yasan inanan ina jiranta saboda wallahi Malam muna matuqar qaunar junanmu,Wanda yakai matsayin bazamu iya rayuwaba idan bama tare.daga qarshe ta yanke shawarar mu sadu da juna,wata qila idan yaganta da ciki kuma yasan ba nashi bane,dole zai saketa.daga nan sai muyi aurenmu.kuma malam Allah cikin ikonsa sau daya kawai abin ya faru,kuma shima bawai wani wadataccen yanayiba,amma yanzu haka kwana 13 kenan ya kamata ace taga al'adarta amma bata ganiba,Wanda hakan na nuna kamar ta samu ciki.
Wallahi Malam kuma yanzu bansan yanda zanyiba.meye matsayinmu Malam Dan Allah👏

AMSA
=====

Matsayinki kun kasa hakuri da ikon Allah, kunyi  gaban kanku, sabida haka Kuje Ku tubarwa Allah.

Amma kunyi ba daidai ba.
  Sannan Jan hankali ga maza, ya kamata mace koda ta gwal ce, idan har bata sonka ka hakura ka barta ga Wanda take so. Duk da cewar akwai kaddarar idan Allah yasa akwai Aure a tsakaninku sai ka aureta, amma da ka fahimci akwai Matsala sai ka gaggauta ka hakura da ita. koda bayan ka aureta ne.
Sannan maganar ciki da kuka yi, sai dai ka jira kuma kaga yadda Allah zaiyi, domin nima wallahi bansan yadda zance maka ba.

  Amma Ku jira kuga yadda Allah zaiyi, idan Allah yasa yaga wannan cikin ya saketa, shikenan sai kuyi aurenku bayan ta gama idda. Amma ka kwana da saninka, dole ne sai kunje gaban Shari'a, amma daga baya dole kotu shi zata baiwa wannan Dan, sabida wata ka'ida ta malikiyya da sukace SHI DA NA MAI SHIMFIDA NE.

Kenan duk Lokacin da aka sami irin wannan matsalar, dole ne kotu zata baiwa wannan Dan, sabida a kare martabar wannan Yaron.

  Babu wata hujja da zai baiwa kotu da zai nuna wannan Dan ba nasa bane, har sai idan itace tayiwa kotu bayani gamsashshe cewar wannan Dan ba nasa bane.


  Anan kuma sai kotu tayi muku hukunci kai da ita.

  Wani Lokacin kuma iyaye suna cin kudin mutum, a haka zasu takurawa yarsu sai ta zauna dashi sabida bazasu iya biyansa kudin da suka kwakwala a wurinsa ba.

  Wannan ma ya kamata iyaye Ku kiyaye, ba daidai bane, Ku zaku zauna Lafiya, amma kuma yayanku Ku tada musu hankali.

Allah shine masani.

ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share:

BANA IYA BACCI IDAN NA KWANTA DA TSAGIN DAMA NA

BANA IYA BACCI IDAN NA KWANTA DA TSAGIN DAMA NA


                            Tambaya:

Assalamu alaikum, mutum ne baya iya bacci duk lokacin da ya kwanta da daddare da tsagin shi na dama, amma da ya juya bangaren hagu cikin yan mintina sai yayi bacci.
Ina mafita.

                                Amsa:
Wa'alaikumus-salam wa Rahmatullah, wannan matsalar alamu sun gwada cewa shaidanu sun taka babbar rawa wajen faruwar haka, don haka mafita ita kulawa da zikirinda Annabi alaihis-salam ya koyar yayi bacci zai taimaka matuka, haka nan da sauran zikirai da shari'a ta tabbatar tsari ne ga dan adam.

Allah ne mafi sani.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

HARAMCIN TABA MACE KODA AN BIYA SADAKI, HAR SAI AN DAURA AURE :

HARAMCIN TABA MACE KODA AN BIYA SADAKI, HAR SAI AN DAURA AURE :

TAMBAYA
********************
Assalamu Alaikum, dafatan Malam yayi Sallah lafiya. Allah kuma yasaka da Alkhairi akan ilmantar da Al'umma da kakeyi. Malam inada tambaya ne menene hukuncin sadaki a Musulunci? Shin ya halarta ga mutumin da yabiya sadakin mace da yayi mu'amala da ita na auratayya ba tare da an daura aure? Nagode.

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Shi Sadaqi 'daya ne kawai daga Sharuddan aure. Ba'a daura aure fache sai an ambaceshi ko kwatankwacinsa.

Amma bayar da sadaqi ka'dai ba wai yana nufin shikenan aure ya dauru ba. Koda anyi baiko, ai baiko amatsayin yarjejeniya yake. Amma ba wai auren bane.

Mace bata halatta ga namiji har sai na zauna an daura musu aure. Amma ayanzu tunda ba'a daura muku aure ba, sunanku "SAURAYI DA BUDURWA". ba wai Ma'aurata ba.

Kuma idan wata Mu'amala ta shiga Tsakaninku, sunan wannan abun "ZINA". Kuma laifin yana nan akanku, ga kuma zubewar Qimarku awajen Allah.

Ya kamata 'Yan Mata ku rika maida hankalinku, yanzu haka akwai samarin da suka mayar da kaiwa sadaqi ya zama Ticket dinsu na yin zina. Ta wannan hanyar Sun lalata rayuwar yara Mata da yawa.

Bai halatta ba, kuma bai kamata ki amince ma saurayi ya ta'ba koda farcen yatsanki ba. Koda rana daya ce ta rage kafin 'daurin aurenku, kuma komai yawan Miliyoyin kudin da yakai gidanku.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU (09/09/2017 18/12/1438).

Share:

MIJINA YANA SADUWA DA NI RANAR GIRKIN KISHIYATA

                           Tambaya

Asslmu alaikum
Mun kasance mu biyu awajen mijinmu.
Sai ya kasance yar uwata bata iya gamsar dashi, to ko ranar girkinta yakan shigo ya tara dani da rana ko da daddare.

Tambaya anan shi ne malam shi hakan ya halasta?

Kuma idan na mishi magana yadaina zuwa baya ji ba gidan mu daya ba.
Dan Allah hukuncin hakan da mafita.

                              Amsa:

Wa'alaikum assalam, Ya wajaba ya nemi izininta, tun da hakkinta ne, in har ta sarayar ya halatta ya sadu da ke a ranar kwananki da kwananta.
Saboda lokacin da Nana Saudah ta tsufa ta ji tsoron kada Annabi S.A.W ya sake ta, ta dauki kwananta ta bawa Nana A'isha, kamar yadda Bukhari ya rawaito. 

Bayan haka Annabi S.A.W yana yin kwana dai-dai a dakunan matansa guda bakwai, ita kuma Nana Aisha yana mata kwana biyu, Saudat kuwa ba ya kwana da ita, saboda ta sarayar da hakkınta.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu zarewa.

4/7/1437
12/4/2016

DAGA ZAUREN

نساء اهل الجنة
رجال اهل الجنة

DOMIN SHIGA WANNAN GROUP  08029399000 ko 08143979048

Share:

INA RAGE GIRMAN BUHU SABODA SAMUN RIBA?

INA RAGE GIRMAN BUHU SABODA SAMUN RIBA?

08 -12 -1438
30 -08 -2017

        Tambaya

Assalamu Alaykum hayyakallahu ya sheik Dan Allah INA Neman sanin halaccin wannan business din , shinkafa idan an shigo da ita daga Niger ko kwatano bata da riba, to idan an kawo ta kafin akai ta kasuwa ana cire kwano daya a kowane buhu sai mutum ya tada buhunhuna to wannan ita CE ribar sa, yin hakan ya halatta ko yana cikin tauye mudu? Allah ya dawo da DR lafiya

            Amsa

Wa alaikum assalam, Haramcin wannan a fili yake, tun da ALMUNDAHANA ne da kuma Algus, saboda duk wanda zai saya, zai saya ne a matsayin cikakken buhu daga Niger ko kwatano.

Annabi S.A.W. yana cewa a cikin hadisin da Muslim ya rawaito “Duk wanda ya yi mana Algus ba ya cikinmu”.

Ayoyin farko na Suratul Mudaffifina Sun yi bayanin azabar da Allah ya tanadarwa Masu tauye mudu .
Wanda ya kiyaye dokokin Allah zai kiyaye shi, wanda ya saba masa zai hadu da shi a madakata.
Babu wata wadata da Allah zai yiwa mutum fiye da hakuri da Kuma wadatar zuci.
Allah ya hallakar da Al’umar Annabi Shu'aibu saboda tauye mudu kamar yadda kissoshinsu suka zo a Suratul A’ARAF da suratu HUD da SHU’ARA’I haka nan Ankabuti.

Allah shine mafi sani
Dr, Jamilu Zarewa

Abibiyemu a adireshin facebook

www.facebook.com/Islamicsunnah

Kota WhatsApp a zauren Islamic sunnah +2348065575014

Ko adireshin email
(saboawaisu01@gmail.com)

Share:

YAUSHE AKE FARA KARBARBARIN BAYAN SALLOLIN AYYAMUT TASHREEQ?

YAUSHE AKE FARA KARBARBARIN BAYAN SALLOLIN AYYAMUT TASHREEQ?

Ana fara karbarbarin bayan sallan farilla ne da bayan asubahi na ranar Arafa har zuwa sallan la'asar na karshen ayyamut Tashreeq, wato ranar goma sha uku (13) ga wata.

Duk lokacin da mutum ya idar da sallan farilla, ya yi istighfari sau uku kuma ya ce: "Allahumma antas salaam wa minkas salaam tabaarakta Yaa dhal-Jalaalu Wal ikraam". Sai mutum ya fara kabbarbari.

A duba Majmuu' Fataawa Ibn Baaz 17/13 da as-Sharhul Mumti' na Ibn Uthaimeen 5/220, Allah Ta'ala Ya yi musu rahama baki daya.

✍🏼Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
31/08/2017.

Daga: *MINBARIN SUNNAH*

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form