Skip to main content

HARAMCIN TABA MACE KODA AN BIYA SADAKI, HAR SAI AN DAURA AURE :

HARAMCIN TABA MACE KODA AN BIYA SADAKI, HAR SAI AN DAURA AURE :

TAMBAYA
********************
Assalamu Alaikum, dafatan Malam yayi Sallah lafiya. Allah kuma yasaka da Alkhairi akan ilmantar da Al'umma da kakeyi. Malam inada tambaya ne menene hukuncin sadaki a Musulunci? Shin ya halarta ga mutumin da yabiya sadakin mace da yayi mu'amala da ita na auratayya ba tare da an daura aure? Nagode.

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Shi Sadaqi 'daya ne kawai daga Sharuddan aure. Ba'a daura aure fache sai an ambaceshi ko kwatankwacinsa.

Amma bayar da sadaqi ka'dai ba wai yana nufin shikenan aure ya dauru ba. Koda anyi baiko, ai baiko amatsayin yarjejeniya yake. Amma ba wai auren bane.

Mace bata halatta ga namiji har sai na zauna an daura musu aure. Amma ayanzu tunda ba'a daura muku aure ba, sunanku "SAURAYI DA BUDURWA". ba wai Ma'aurata ba.

Kuma idan wata Mu'amala ta shiga Tsakaninku, sunan wannan abun "ZINA". Kuma laifin yana nan akanku, ga kuma zubewar Qimarku awajen Allah.

Ya kamata 'Yan Mata ku rika maida hankalinku, yanzu haka akwai samarin da suka mayar da kaiwa sadaqi ya zama Ticket dinsu na yin zina. Ta wannan hanyar Sun lalata rayuwar yara Mata da yawa.

Bai halatta ba, kuma bai kamata ki amince ma saurayi ya ta'ba koda farcen yatsanki ba. Koda rana daya ce ta rage kafin 'daurin aurenku, kuma komai yawan Miliyoyin kudin da yakai gidanku.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU (09/09/2017 18/12/1438).

Comments