Skip to main content

INA RAGE GIRMAN BUHU SABODA SAMUN RIBA?

INA RAGE GIRMAN BUHU SABODA SAMUN RIBA?

08 -12 -1438
30 -08 -2017

        Tambaya

Assalamu Alaykum hayyakallahu ya sheik Dan Allah INA Neman sanin halaccin wannan business din , shinkafa idan an shigo da ita daga Niger ko kwatano bata da riba, to idan an kawo ta kafin akai ta kasuwa ana cire kwano daya a kowane buhu sai mutum ya tada buhunhuna to wannan ita CE ribar sa, yin hakan ya halatta ko yana cikin tauye mudu? Allah ya dawo da DR lafiya

            Amsa

Wa alaikum assalam, Haramcin wannan a fili yake, tun da ALMUNDAHANA ne da kuma Algus, saboda duk wanda zai saya, zai saya ne a matsayin cikakken buhu daga Niger ko kwatano.

Annabi S.A.W. yana cewa a cikin hadisin da Muslim ya rawaito “Duk wanda ya yi mana Algus ba ya cikinmu”.

Ayoyin farko na Suratul Mudaffifina Sun yi bayanin azabar da Allah ya tanadarwa Masu tauye mudu .
Wanda ya kiyaye dokokin Allah zai kiyaye shi, wanda ya saba masa zai hadu da shi a madakata.
Babu wata wadata da Allah zai yiwa mutum fiye da hakuri da Kuma wadatar zuci.
Allah ya hallakar da Al’umar Annabi Shu'aibu saboda tauye mudu kamar yadda kissoshinsu suka zo a Suratul A’ARAF da suratu HUD da SHU’ARA’I haka nan Ankabuti.

Allah shine mafi sani
Dr, Jamilu Zarewa

Abibiyemu a adireshin facebook

www.facebook.com/Islamicsunnah

Kota WhatsApp a zauren Islamic sunnah +2348065575014

Ko adireshin email
(saboawaisu01@gmail.com)

Comments