Skip to main content

INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA MIJINA BA LAFIYA?

INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA MIJINA BA LAFIYA?


                            Tambaya:

Salaam, Dr macece mijinta ba yada lafiyan aure tsawon lokachi, sai ya zamana tana yawan releasing ba sai tayi wani dogon tunani na sha'awaba, ya matsayin ibadarta yake ?

                                Amsa:

To gaskiya abin yake daidai shi ne: ya nemi magani, in kuma bai samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga cikin manufofin aure, katange ma'aurata daga fadawa haramun, kamar yadda shararren hadisinnan ya tabbatar.

Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar da saukin sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba, saboda iyayenki za su iya wajabtawa mijin neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya rabuwa, Allah ya azurta kowa dağa falalarsa.

Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa ki cikin hadari, mata nawa ne suka zama mazinata ta hanyar wannan sababin?
Ya wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita, tun da ya fita ne ta hanyar jin dadi.

ALLAH NE MAFI SANI

Dr. Jamilu Zarewa.

12/6/1437

22/3/2016

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren

MIFTAHUL ILMI

a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Comments