Friday, 22 September 2017

Na Sadu Da Tsohuwar Budurwa Ta Alhalin Tana da Aure

TAMBAYA
========

Assalamu alaikum.

Malam fatan anyi sallah lfy.
Malam bansan da wace fuska zan fada maka irin halinda nake cikiba.
Malam agaskiya nayi qoqarin yin kyakkyawan aiki amma ta hanya mummuna,Malam anyima budurwata auren dole ga tsoho Wanda ya girmi kakanta,ta sanadiyyar haka ta kamuda ciwon zuciya da hawan jini mai tsanani, yanzu haka sunfi shekara bata taba bari ya kusancetaba,tabi duk irin matakan daya kamata tabi akan ya saketa,amma yaqi.saboda yasan inanan ina jiranta saboda wallahi Malam muna matuqar qaunar junanmu,Wanda yakai matsayin bazamu iya rayuwaba idan bama tare.daga qarshe ta yanke shawarar mu sadu da juna,wata qila idan yaganta da ciki kuma yasan ba nashi bane,dole zai saketa.daga nan sai muyi aurenmu.kuma malam Allah cikin ikonsa sau daya kawai abin ya faru,kuma shima bawai wani wadataccen yanayiba,amma yanzu haka kwana 13 kenan ya kamata ace taga al'adarta amma bata ganiba,Wanda hakan na nuna kamar ta samu ciki.
Wallahi Malam kuma yanzu bansan yanda zanyiba.meye matsayinmu Malam Dan Allah👏

AMSA
=====

Matsayinki kun kasa hakuri da ikon Allah, kunyi  gaban kanku, sabida haka Kuje Ku tubarwa Allah.

Amma kunyi ba daidai ba.
  Sannan Jan hankali ga maza, ya kamata mace koda ta gwal ce, idan har bata sonka ka hakura ka barta ga Wanda take so. Duk da cewar akwai kaddarar idan Allah yasa akwai Aure a tsakaninku sai ka aureta, amma da ka fahimci akwai Matsala sai ka gaggauta ka hakura da ita. koda bayan ka aureta ne.
Sannan maganar ciki da kuka yi, sai dai ka jira kuma kaga yadda Allah zaiyi, domin nima wallahi bansan yadda zance maka ba.

  Amma Ku jira kuga yadda Allah zaiyi, idan Allah yasa yaga wannan cikin ya saketa, shikenan sai kuyi aurenku bayan ta gama idda. Amma ka kwana da saninka, dole ne sai kunje gaban Shari'a, amma daga baya dole kotu shi zata baiwa wannan Dan, sabida wata ka'ida ta malikiyya da sukace SHI DA NA MAI SHIMFIDA NE.

Kenan duk Lokacin da aka sami irin wannan matsalar, dole ne kotu zata baiwa wannan Dan, sabida a kare martabar wannan Yaron.

  Babu wata hujja da zai baiwa kotu da zai nuna wannan Dan ba nasa bane, har sai idan itace tayiwa kotu bayani gamsashshe cewar wannan Dan ba nasa bane.


  Anan kuma sai kotu tayi muku hukunci kai da ita.

  Wani Lokacin kuma iyaye suna cin kudin mutum, a haka zasu takurawa yarsu sai ta zauna dashi sabida bazasu iya biyansa kudin da suka kwakwala a wurinsa ba.

  Wannan ma ya kamata iyaye Ku kiyaye, ba daidai bane, Ku zaku zauna Lafiya, amma kuma yayanku Ku tada musu hankali.

Allah shine masani.

ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876


EmoticonEmoticon