Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

MUNA BIYAWA KANMU BUQATA NIDA SAURAYINA TA HANYAR FIRA AWAYA

MUNA BIYAWA KANMU BUQATA NIDA SAURAYINA TA HANYAR FIRA AWAYA

        DAGA ZAUREN
HISNUL-MUSLIM

           TAMBAYA

Assalamualaikum
Malam nice da saurayina To Malam ya kasance Muna biyawa Junan mu bukata Ta hanyar Waya
   Mal menene hukuncin haka amusulunci?

            AMSA

To baiwar Allah wannan haramunne babu kyau
Ita zina dama kala kala ce malamai suka rarrabeta
      Akwai zinar ido wato kakalli tsiraici harkaji dadi akwai zinar baki wato kuyi magana ta sha'awa dankuji dadi akwai zinar hannu wato masoya suringa taba junansu ayita wasanni har aji dadi
      Akwai zinar farji wato kwanciya da mace asadu da juna wato babbar zina kenan

To yar uwa duk wannan abubuwan dana ambata  dukkansu sunansu Zina
    Illa iyaka kawai wata tafi wata amma duk wacca kikeyi aciki to sunanki wacca takeyin zina saidai kituba kikoma ga Allah
Kuma saurayin naki dama ba auranki zaiyiba
       Idanma auranki zakyi to zaki auri wanda mutuncinku  yazube tundaga waje
Allah shine masani

JUNAIDU BALA ABDULLAHI
Abu salma

Masu buqatan shiga Wannan Zaure na hisnul Muslim   suyiwa daya daga cikin wadannan  number  magana ta whatsApp+2348065523065
+2348162067271
    Domin Neman Karin bayani akan wata fatawa sai Ku kira wannan numbar↓
+2347065588557
سبانك اللهم وبحمدك، اشهد ان لا اله الا انت استغفرك واتوب اليك، 
Kuna iya samun mu ta  facebook ta wannan link indanke Qasa
https://mobile.facebook.com/Hisnul-Muslim-667684316700356/?fref=none

Share:

TAYI AURE DA CIKIN SHEGE

TA YI AURE DA CIKIN-SHEGE??

Tambaya:

Assalamu alaikum. Malam Wata tayi cikin shege da wani mutum,sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri ya aureta.
Yanzu sunyi Auren,yaya hukuncin Auren a Shari'a yake???

Amsa

Wa alaykum assalamu Zina sabon Allah ne da kuma yada fasadi a bayan qasa. Aure kuwa sunnar Manzon Allah ne, da samar da zuriya mai albarka. Kuma an kwadaitar da mu yin sa. Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar da ita sai ta yi jini wanda ake kira Istibra’i, kafin a daura mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure. Kuma idan har an daura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za a raba wannan auren ko da sun haifi `ya`ya, domin suna ganin an daura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana daura aure a cikin idda. Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce ne kuma rusasshe.
Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi`i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i kafin ta yi aure, amma idan har an daura auren ba ta yi istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma suka qara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka daura mata aure, to, auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa ya ce: mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu- dawud : 1847.
Don neman karin bayani duba : AL-MUDAWWANNAH aL-KUBRAH 2\173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79.

A fahimtata, fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin ayi auren, saboda fita daga sabanin malamai abin só ne, sannan kuma za'a kaucewa fadawa hadari, amma idan an riga an yi auren to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci tsakanin zina da aure, saidai ya wajaba şu nisanci saduwa, kafin ta haihu Saboda hadisin da ya gabata.

Allah ne mafi sani.

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
27/02/2016

Share:

MENENE YAFI WUTAN JAHANNANMA BALA'I DA MASIFA?

MENENE YAFI WUTAN JAHANNANMA
BALA'I DA MASIFA?

*****************************
Sahabban Manzon Allah (saw) sunyi masa
tambaya, sukace ya manzon Allah (saw)
menene yafi wutar  Jahannama masifa da
azaba?
Sai Manzon Allah (saw) yace;
Fushin Allah shine yafi wutar Jahannama masifa da
balbalin bala'i.

Ya Rasulillahi! Mene yake sawa
Allah yayi fushi da mutuM?

Ga kadan daga cikinsnu.
1.Kashe Musulmi mumini da gan-gan.
2. Wulakanta iyaye.
3. Barin tsaraici awaje.
4. Yawan sabon Allah, ko kuma tuban muzuru.
5. Kin yin Sallah akan lokacinta Da dai sauransu.
Yaa ubangiji ka karemu daga aika duk wani abun da zai sa kayi fushi damu.

AMIN SUMMA AMIN

Dan Allah kuyi sharing

Share:

BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI

BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI

Tambaya:


Mal. menene bambanci tsakanin nifakul amali da i'itikaadi ?

Amsa:


To malam : Nifaqul i'itikadi (wanda ake kudurcewa a zuciya) shi ne boye kafurci da kuma bayyana musulunci, kamar yadda wasu mutane suka yi a zamanin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, duk wanda ya siffantu da wannan to ba musulmi ba ne.

Amma nifakul-amali (aiki) kuwa to shi ne wanda ya zo a cikin hadisin abdullahi dan amr inda annabi s.a.w. yake cewa : "Dabi'u guda hudu duk wanda suka kasance tare da shi, to ya zama cikakken munafiki, wanda kuma yake da daya daga cikinsu to yana da dabi'ar munafukai har sai ya barta : idan ya yi zance ya yi karya, idan aka amince masa ya ci amana, idan ya yi alkawari ya yi yaudara, idan ya yi husuma sai ya yi fajirci". Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : (34) da Muslim a hadisi mai lamba ta : (106).

Don haka in mutum ya siffantu da daya daga cikin wadannan dabi'u guda hudu, to bai fita daga musulunci ba, saidai yana da tawayar imani.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa

16/11/2014

Daga: ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Share:

TANA AZUMI MIJINTA YA SUMBACE TA

TANA AZUMI SAI MIJINTA YA SUMBACETA?
 
Tambaya

Malam macece tayi kitso alhalin tana azumi sai mijinta yaga kitson ya basa sha'awa saiya sumbacesa ita kuma take sha'awa tazo mata harta jika pant dinta

Amsa

Wa akaikumus salamTo yar uwa da farko dai anyi wasa da azumi kwarai da gaske kuma ba daidai bane kina azumi ki bari mijinki ya sumbaceki ta yadda har zaki fitar da wani abu dazai bata miki azumi' wannan akwai ganganci a ciki.

Amma shi azumin nafila dama mai shi yanada yan'cin ya karyashi koya cigaba Annabi S.A.W ya fada cikin hadisi sahihi mai azumin nafila shine sarkin kansa idan yaga dama ya karya manzon Allah s.a.w. ya bada wannan damar.

Malamai suna cewa fitar maziyyi idan har maziyyine ya fita karamar sha'awa kenan zance mafi inganci baya karya azumi amma idan maniyyi ne ya fita to azumi ya karye shikenan idan na nafila ne bakida lada idan kuma farilla ne akwai kaffara akansu bisa kaulin malamai amma wasu malaman sukace sai anyi jama'i kaffara take wajabta idan nafilane shikenan idan kuma na farillah ne saiki rama guda daya wannan shine zance mafi inganci.

Allah shine mafi sani.

amsawa
DR. ABDALLAH GADON KAYA
Share:

Friday Messages 005

.. ..Ya Allah never let our hearts be disturbed by the trials of life. Open the doors of your Mercy to us, ease our ways, accept our worship, bless our end, comfort our graves, forgive our sins & forgive our parents and make our final resting place be aljanatul Firdaus. Ameen! Juma'at Mubarak!!...
Share:

BACCIN BAYAN SALLAR ASUBA

BACCIN BAYAN SALLAR ASUBA!!

                            Tambaya

Assalamu alaikum, malam INA da wata
tambaya shin menene hukuncin yin bacci
bayan sallar asuba? Allah ya taimaki malam!

                            Amsa

To malam babu wani hadisi mai inganci wanda ya hana bacci bayan sallar asuba, sai dai bayan sallar asuba lokaci ne mai albarka,wannan yasa Annabi S.A.W idan ya yi sallar asuba baya tashi daga wurin sallar sai rana ta fito, haka ma sahabbansa Allah ya yarda da su, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamaba ta : 670. 

Kuma Annabi S.A.W yana cewa : "Allah ka sanyawa al'umata albarka a cikin jijjifinta" Tirmizi a hadisi mai lamba ta : 1212, kuma ya kyautata shi.

Wannan yake nuna cewa lokaci ne mai
albarka, wanda bai dace da bacci ba,
wannan ya sa ko da rundunar yaki Annabi S.A.W yake so ya aika, yakan aikata ne a
farkon yini saboda albarkar lokacin.

Wasu daga cikin magabata, sun karhanta
yin baccin bayan sallar asuba, Urwatu dan Zubair yana cewa : "Idan aka ce min wane yana baccin safe na kan guje shi' kamar yadda Ibnu Abi-shaiba ya ambata a
Musannaf dinsa 5\222.

Ya kamata ka shagala da neman ilimi ko
kosuwanci a irin wannan lokacin.

Allah ne mafi sani. 

Dr. Jamilu  Zarewa.

DAGA ZAUREN
نساء اهل الجنة
رجال اهل الجنة
DOMIN SHIGA WANNAN GROUP  08029399000 ko 08143979048

Share:

Friday Messages 004

: بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَاةِ مِن يَوْمِ الْجُمُعَةِ فَاسْعَوْا إِلَىٰ ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُون
Haza yaumul akbar; yaumul shukur, yaumul salama! Alhamdulillahi ala ni'matil Islam. May Allah shower His endless blessings upon U & Ur family. (Ameen)
       Juma'@ Mubarak!!
Share:

Friday Messages 003

"O Allah, don't let us turn away from You, no mater how many trials and difficulties You test us with. Let the difficulties make us stronger in faith and more closer to You, Oh Allah! Respond to our prayers, forgive our parents, guide our children and heal our sickness, have mercy on our death, defeat our enemies, guide our loved ones and grant us Jannatul Firdaus. Juma@ Mubarak.
Share:

Friday Messages 002

Haza Yaumul Akbar Yaumul Shukur Yaumul salama! Alhamdulillahi ala Ni'matil Islam. May Allah shower His endless blessings upon you & your family. Jum'at Mubarak
Share:

Friday Messages 002

Faith-Wealth-Health-Peace-Joy-Happiness-Freedom-Forgiveness-& Paradise these are all my wishes for you today & forever Juma'at mubarak

Share:

HUKUNCIN DAURA LAYA DA GURU

HUKUNCIN DAURA LAYA  DA GURU !!!!

14 -01 -1439
04 -10 -2017

      Tambaya
Assalam Alaikum.

Malam, menene hukuncin amfani da LAYA KO GURU a musulunci?

Allah yasa mu dace.
        Amsa

Wa alaikum assalam.
To dan'uwa Layu da guru sun kasu kashi biyu:
1. Layun da aka yi su da Sakandami ko Hatimi ko sunayan aljanu ko wani abu na daban wanda ba Qur'ani ba, wannnan malamai sun cimma daidaito game da haramcinsu kamar yadda ya zo a Fataawaa Allajna Adda'imah 2/212 saboda fadin Annabi S.A.W. (LAYU da kuma abin da ake daurawa mace don miji ya sota shirka ne) kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (3883) kuma Albani ya inganta shi, sannan da hadisin da Imamu Ahmad ya rawaito mai lamba ta: (16969), inda Annabi S.A.W. yake cewa: (Wanda ya rataya laya to ya yi shirka, shima wannnan hadisin Albani ya inganta shi a Silsila Sahiha.
Hadisan da suka gabata suna nuna haramcin daura Laya saboda Manzon tsira ya kira ta da shirka, shirka kuma tana fitar da mutum daga musulunci.

2. LAYUN da aka yi su daga Alqur'ani ko hadisai ingantattu, wadannan na'u'i malamai sun yi sabani akansu:

A. Sun halatta saboda sun kunshi sunan Allah da kuma karatun alqur'ani wanda sifar Allah ce, wanda ya dogara da su ya dogara ga Allah, wannan ita ce maganar Amru bn Al-ass da Aisha da wasu daga cikin magabata.

B. Ba su halatta ba saboda Ba'a samu Annabi S.A.W. ya yi ba, da hakan shari'a ne da angan shi ya yi ko da sau daya(1) ne a rayuwarshi, sannan rataya layun da suke dauke da Alqur'ani zai jawo a wulakanta su tun da za'a shiga wurare marasa tsarki da su lokacin biyan bukata, kiyaye hakan kuma yana da kamar wuya.
Zance mafi inganci shi ne haramcin amfani da Layun da suke daga Alqur'ani saboda dukkan alkairi yana cikin biyayya ga manzon Allah S.A.W, sannan shari'ar musulunci ta halatta mana addu'o'i da yawa na neman kariya wadanda suka wadatar da mu daga layu.

Allah shine mafi sani.

Don neman karin bayani duba: Taisirul Azizil Hamid shafi na : (136) da kuma Ma'arijul Kabul 2/510

Amsawa
Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Abibiyemu  ashafin facebook
www.facebook.com/Islamicsunnah

kota WhatsApp a zauren Islamic sunnah+2348065575014

Ko adireshin email
(saboawaisu01@gmail.com)

Share:

Friday Message 001

As no roof can stand without supports, may the power of Almighty ALLAH that lifted the sky above the earth without a single pillar lift you up and grant you all your heart desires in this life and that of the hereafter. Ameen. Jummuah Mubarak.

Share:

WANDA AKA YIWA KYAUTA BAI AMSA BA, HAR YA MUTU, SHIN ZAI SHIGA RABON MAGADA?

WANDA AKA YIWA KYAUTA BAI AMSA BA, HAR YA MUTU, SHIN ZAI SHIGA RABON MAGADA?

                            Tambaya

Assalamu alaikum. Dan Allah Ga wata tambaya ta gaggawa. Wata baiwar Allah ta sayi kaya da niyyar baiwa 'yar uwarta, amma kafin ta bata sai 'yar uwar ta rasu. Shin wannan sayayya ta shiga cikin kayan gado? Na gode.

                                Amsa

To dan'uwa ba zai shiga rabon magada ba, saboda kyauta ba ta tabbata sai an amsa, Wannan ya sa lokacin da sayyadina Abubakar ya yiwa 'yarsa Aisha kyauta ba ta amsa ba, Har mutuwa ta zo masa ya soke kyautar, ya mayar da ita dukiyar magada. Kamar yadda Malik ya rawaito a Muwada'i a hadisi mai lamba ta: 717.

Wannan ita ce maganar mafi yawancin malamai.

Don neman Karin bayani duba : Al'umm na Shafi'I 4\64, da Bada'iussana'i'i 6\8.

Dr. Jamilu Zarewa

13\4\2015

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.

Share:

MALAM MENENE HUKUNCIN WANDA YAKALLI BLUE FILM (BF) DA RANA YANA AZUMI HAR YA FITAR DA MANIYYI KUMA BAIYI WANKABA HAR SALLOLIN AZAHAR DA LA'ASAR SUKA WUCESHI???

MALAM MENENE HUKUNCIN WANDA YAKALLI BLUE FILM (BF) DA RANA YANA AZUMI HAR YA FITAR DA MANIYYI KUMA BAIYI WANKABA HAR SALLOLIN AZAHAR DA LA'ASAR SUKA WUCESHI???

                           Tambaya

Malam minene hukuncin wanda ya kalli Blue Film (BF) da rana yana Azumi har ya fitar da Maniyyi kuma baiyi wanka ba har Sallolin Azahar da La'asar suka wuce shi???

Domin naji kace wanda yayi mafarki da rana yafitar da maniyyi azuminsa yananan.‎ Shima wannan kenen a zuminsa yananan?

                              Amsa

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN. Lallai wannan kayi babbar ta6argaza. Bakada azumi sannan sai kayi kaffarar guda sittin (60) duk da wanda kakarya zakayi (61) kenan babu hutu.
Domin wannan ba uxury bane a wajen Ubangiji gangancine kayi. Koda mai matar aure ta sunnah an haramta masa ya sadu da ita da rana acikin watan azumi, sai yayi kaffara.
.
.
.
Balantana kai daka tafka sa6on Allah kana kallon kafirai maqiya Annabi Muhammad (S.A.W) suna tafka Masha'a har kafitar da maniyyi, sannan kake taqama da wanda yayi mafarki da rana.
.
.
.
                  HUJJA ANAN ITACE:

Duk wanda yake bacci baisan a inda yakeba, hankalinsa baya tare dashi, sannan koda wani abu zai sameshi acikin baccin nasa bashida ikon kare kansa kamar yadda zai iya a zahiri.

Kamar yadda yazo a hadisai cewa: An dauke alqalamin rubutun zunubi akan mutum uku (3).
1. Qaramin yaro.
2. Mahaukaci.
3. Maiyin bacci har saiya farka.
Wadannan mutanen dukansu hankalinsu baya tare dasu.

Amma banda wanda yasha giya yafita daga hayyacinsa, domin wannan shine yajawa kansa. Saboda haka zaka rama azumi guda (61) bayan sallah.
.
.
.
.
Sannan inajan kunnen matasa maza da mata suguji yin (Chatting) a cikin watan azumi saboda gudun afkawa fitina irin wannan.

Allah ka shiryi matasanmu maza da mata ka aurar dasu ga ma'aurata nagari.

Rubutawa:- Ãbûbäkår Êkâ.

______________________________________

» Zauren SHEIKH JAFAR MAHMUD ADAM

Share:

SHIN ZAN IYA TSARKI DA RUWAN ZAMZAM?

SHIN ZAN IYA YIN TSARKI DA RUWAN ZAMZAM?

                         Tambaya:

Malam wani ya tambaye ni, shin zai iya yin tsarki da ruwan zamzam, saboda ya ji an ce yana kara karfin mazakuta, to gaskiya malam ban sani ba, shi ne na ce bari na tambayi Fukaha'u ?

                              Amsa:

To dan'uwa ruwan zamzam ruwa ne mai albarka, kamar yadda ya zo a hadisi cewa : Waraka ne ga cututtuka, Suyudi ya kyautata shi a Jami'ussagir, duba Faidhu Alkadeer 3/489.

Saidai duk da haka ya halatta ayi tsarki da shi a zance mafi inganci , saboda ba'a samu dalilin da ya hana hakan ba, ga shi kuma daga cikin ka'idojin malamai duk abin da ba'a samu nassin hani akansa ba a cikin mu'amalolin mutane, to ya halatta.

Sannan sahabbai sun yi tsarki da ruwan da ya bubbugo daga hannun Annabi S.A.W, ruwan zamzam kuma ba zai fi wannan ruwan daraja ba.

Don neman Karin bayani duba: Hashiyatu Ibnu-abiidin 1\180 da kuma Insaf 1\27.

Allah ne mafi sani

Amsawa: Dr Jamilu Yusuf Zarewa.
Gabatarwa: Abu-Unaisa.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.

Share:

Menene hukuncin Azumin wanda yayi mafarki da rana har Maniyyi yafito masa??

Tambaya ta (338)
:
Menene hukuncin Azumin wanda yayi mafarki da rana har Maniyyi yafito masa??
:
Amsa:
:
Dangane da hukuncin Fitar Maniyyi ga wanda yake azumi mafi yawan Malamai cikinsu harda Mazhabobin nan guda huɗu wato:
:
_*→(1)---Malikiyya
_*→(2)---Shafi'iyya
_*→(3)---Hanafiyya
_*→(4)---Hanabila
:
_Dukkansu suntafine akan cewa fitar da Maniyyi da gangan ta hanyar da ba jima'i ba yana lalata azumi, danhaka idan Mai-Azumi yayi Istimna'i, ko ya rungumi Matarsa, ko yayi wasa da'ita, hartakai ga yafitar da Maniyyi to azuminsa ya lalace, danhaka Malamai sukace dukkan Mutumin da yasan cewa Sha'awarsa tana da ƙarfin da indai zaiyi wasa da Matarsa Maniyyi zaifito masa to haramunne agareshi yayi hakan da'ita, idan kuwa yayi har Maniyyi yafita to wajibine sai yarama wannan azumin, amma idan yakasance Maniyyin yafitane ta hanyar mafarki kokuma tunani ko kallon Mace batare da yayi wasa da'itaba, mafi yawan Malamai sukace azuminsa bai lalace ba saidai wajibine yayi wankan janaba, amma Mazhabin MALIKIYYA sukace koda mafarki yayi dolene sai yarama wannan azumin,_
:
_Danhaka Malamai sunyi Saɓani dangane da yanayin ramuwar azumin da Mutum zaiyi, Mafi yawan Malamai suntafine akancewa zai rama azumi guda ɗayane kawai batare da yayi wata Kaffara ba, domin Nassin yin Kaffara yazone akan wanda yayi Jima'i da Matarsa da rana, Saidai Mazhabin MALIKIYYA suntafine akancewa idan Mutum yayi Mafarki har yafitar da Maniyyi to azuminsa ya lalace kuma dolene sai ya rama batare da kaffaraba, amma idan wasa yayi da Mace ya rungumeta ko ya Shafata ko yayi Istimna'i har yafitar da Maniyyi, to wajibine sai yayi ramuwa tare da Kaffara, domin sunyi Ƙiyasine akan hukuncin wanda yayi Jima'i da Matarsa da gangan da rana,
:
_Amma. Mazhabin ZAHIRIYYA suntafine akan cewa wanda yafitar da Maniyyi da gangan ta dukkan wata hanyar da ba Jima'i yayi da Matarsa ba* sukace azuminsa yana nan bai lalace ba, domin babu wata Hujja afili Ƙarara daga cikin Al-Ƙur'ani ko Hadisi datace azuminsa ya lalace, to amma Saidai maganar Malaman da sukace azuminsa ya lalace tafi Ƙarfi,
:
_Amma maganar da tafi inganci wacce mafi yawan Malamai sukafi rinjayar da'ita shine, fitar Maniyyi ta hanyar mafarki baya karya azumi, domin Ɗan-Adam bashi da wani iko na ya'iya hana kansa yin mafarki alokacin da yake barci ba, hakanan magana mafi inganci fitar Maniyyi ta hanyar tunani ko kallo shima bayar karya azumi, amma duk dahaka ba'ace Mutum yarika sanya irin wannan tunanin acikin Zuciyarsa ba, amma fitar Maniyyi dagangan tahanyar wasa tsakanin Ma'aurata, ko tahanyar Istimna'i, wannan kam yana lalata azumi, kuma za'ayi ramuwane kaɗai batare da Kaffaraba, amma idan Mutum yayi jima'i da Matarsa da gangan da rana, tofa koda baikawo Maniyyiba ramuwa da Kaffara sunhau kansa:_
:
(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)
:
ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:
:
Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:
                
:
*"المغني لإبن قدامة"
:
*الشرح الممتع" (6/234)
:
*"المجموع للنووي" (6/349)
"""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
             Daga Zauren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
             AMSAWA
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє"
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/

Share:

Meye hukuncin mutane biyu su kwana a bargo daya.??

Assalamu alaikum

Meye hukuncin mutane biyu su kwana a bargo daya.??

AMSA


وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،

Amsar wannan tambaya tana a karkashin wannan hadisi na Abdullai ibn Amr ibn al-Aas (radiyallahu anhu).

```عن ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺍﻟﻌﺎﺹ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ: ﻣُﺮُﻭﺍ ﺃَﻭْﻟَﺎﺩَﻛُﻢْ ﺑِﺎﻟﺼَّﻠَﺎﺓِ ﻭَﻫُﻢْ ﺃَﺑْﻨَﺎﺀُ ﺳَﺒْﻊِ ﺳِﻨِﻴﻦَ ﻭَﺍﺿْﺮِﺑُﻮﻫُﻢْ ﻋَﻠَﻴْﻬَﺎ ﻭَﻫُﻢْ ﺃَﺑْﻨَﺎﺀُ ﻋَﺸْﺮٍ ﻭَﻓَﺮِّﻗُﻮﺍ ﺑَﻴْﻨَﻬُﻢْ ﻓِﻲ ﺍﻟْﻤَﻀَﺎﺟِﻊِ.```
_(ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ‏(495) ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ "ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ"

An karbo daga Abdullai ibn Amr ibn al-Aas (radiyallahu anhu) yace; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) yace; Ku umarci 'ya'yanku da suyi sallah idan sunkai shekara bakwai. Kuma Ku dakesu Idan sunkai shekara goma (basa yin sallah), kuma ku rarraba su a makwancinsu (a raba musu shinfida idan sun kai shekara goma)._
(Abu Dawuda,  495). Albani ya inganta shi a Sahih Abi Dawuda.

```ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﻮﻭﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ:
ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺃﻥ ﻳﻀﺎﺟﻊ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻭﻻ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻭﺍﺣﺪ ﻓﻲ ﺟﺎﻧﺐ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺮﺍﺵ ، ﻭﺇﺫﺍ ﺑﻠﻎ ﺍﻟﺼﺒﻲ ﺃﻭ ﺍﻟﺼﺒﻴﺔ ﻋﺸﺮ ﺳﻨﻴﻦ ﻭﺟﺐ ﺍﻟﺘﻔﺮﻳﻖ ﺑﻴﻨﻪ ﻭﺑﻴﻦ ﺃﻣﻪ ﻭﺃﺑﻴﻪ ﻭﺃﺧﺘﻪ ﻭﺃﺧﻴﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﻀﺠﻊ.```
_*"ﺭﻭﺿﺔ ﺍﻟﻄﺎﻟﺒﻴﻦ ‏(7/28)"*_

Imam Nawawi (rahimahullah) yace:
Baya halatta ga namiji ya kwanta tareda namiji (a shimfida guda), ko kuma mace ta kwanta tareda mace (a shimfida guda), koda dayansu yana a gefe daya na shimfidar. Idan yaro ko yarinya suka kai shekara goma, ya zama wajibi a raba yaron (a shimfida) tsakaninsa da tsakanin Mamarsa, Babansa, yar uwarsa (kanwa ko yayarsa), da dan uwansa a wajen barci. (Dole ne ya rika kwana a shifidarsa shikadai).
Rawdatul taalibeen, 7/28).

Saboda haka bai halatta mutum biyu su kwana a shimfida guda idan shekarunsu sun kai goma (10).

* Namiji bazai kwanta shimfida daya da wani namiji ba.

* Namiji bazai kwana da wata mace wacce ba matarsa ba a shimfida daya. Wannan haramun ne.

* Mace bazata kwana da wata mace ba a shimfida daya.

* Mace bazata kwana a shimfida daya da wani namiji wanda ba mijinta ba.

والله أعلم،

**********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

Tambayoyin Musulunci
            Whatsapp Group

Share:

Miye hukunci Wanda yaje fira sai yaji gabansa yajike shi wankan janaba wajaba agareshi ko wankewa zaiyi

HUKUNCIN MAI ZUWA ZANCE WANDON SHI YA JIKE!!!

                             Tambaya

Miye hukunci Wanda yaje fira sai yaji gabansa yajike shi wankan janaba wajaba agareshi ko wankewa zaiyi

ASSALAMU ALAIKUM

                                 Amsa

Wa'alaiku mussalam, Matukar hirar ce ta saka shi jin dadi har ya fitar da abin da abin da ya ke sawa a yi wanka, wajibine ya yi wanka.

                                Nasiha

Bai dace har mutum ya je yana hirar da zata rika wajabta masa wanka ba.

Akwai dokoki wadanda idan aka kiyaye su hakan bazata faruba.
1- Shigar da mace zata fito wajen saurayi.
2- Kalaman da za suyi.
3- Samun fuska a wajen mace da saurayi ya ke samu.
4- Idan zatazo zance tazo da muharramanta.
5- Idan za'ayi Hirar ayita a sarari, ba'a lungu ba ko kwararo.
Da sauran abubuwa makamantansu.

ALLAH YA SHIRYA MU AMEEN

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

Miye hukunci Wanda yaje fira sai yaji gabansa yajike shi wankan janaba wajaba agareshi ko wankewa zaiyi ?

HUKUNCIN MAI ZUWA ZANCE WANDON SHI YA JIKE!!!


                             Tambaya

Miye hukunci Wanda yaje fira sai yaji gabansa yajike shi wankan janaba wajaba agareshi ko wankewa zaiyi

ASSALAMU ALAIKUM

                                 Amsa

Wa'alaiku mussalam, Matukar hirar ce ta saka shi jin dadi har ya fitar da abin da abin da ya ke sawa a yi wanka, wajibine ya yi wanka.

                                Nasiha

Bai dace har mutum ya je yana hirar da zata rika wajabta masa wanka ba.

Akwai dokoki wadanda idan aka kiyaye su hakan bazata faruba.
1- Shigar da mace zata fito wajen saurayi.
2- Kalaman da za suyi.
3- Samun fuska a wajen mace da saurayi ya ke samu.
4- Idan zatazo zance tazo da muharramanta.
5- Idan za'ayi Hirar ayita a sarari, ba'a lungu ba ko kwararo.
Da sauran abubuwa makamantansu.

ALLAH YA SHIRYA MU AMEEN

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

malam menene hukuncin bin kurma wanda ba ya ji sallah?

LIMANCIN KURMA!!!

                         Tambaya

Assalamu alaikum, malam menene hukuncin bin kurma wanda ba ya ji sallah?

                            Amsa

Wa alaikum assalam To dan'uwa limancin kurma bai inganta ba, harma wasu malaman sun hakaito ijma'i akan haka, saboda kurma ba zai iya tsayar da wasu daga cikin rukunan sallah ba, kamar kabbarar harama da karatun fatiha da sallama, don haka binsa sallah zai jawo sallar wadanda suke binsa ta zama ba ta cika ba.

Saidai wasu malaman sun tafi akan cewa, ya halatta ya yiwa kurame irinsa limanci.
Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba : Sharhul-kabir na Abdurrahman dan khudaamah 2\38.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa

15\2\2015

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI  a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

Shin Mace zata rama sallar Maghrib da Isha'i idon Jini ya dauke mata kafin hudowar alfijir,?

Tambaya

Assalamu alaikum

Shin Mace zata rama sallar Maghrib da Isha'i idon Jini ya dauke mata kafin hudowar alfijir,?

Ko idon ya dauke mata kafin faduwar Rana zatayi sallar Azahar da La'asar?

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻜﻴﻢ ﺍﻟﻌﻠﻴﻢ .

Amsa:

Idan mai haila taitsarki bayan shigar lokacin sallar isha'i wajibine tayi sallar isha'i din domin tariski lokacinta, haka zatayi sallar magariba domin ana hadasu yayinda aka samu uzuri.
Hakanan idan tai tsarki bayan shigar lokacin la'asar zatayi sallar la'asar da azahar, wannan shine abunda wasu daka cikin shabban Annabi sallallahu Alahi wasallam sukai fatawa dashi, shine kuma abunda jamhurdin malamai sukai fatawa dashi.
Amma idan tai tsarki bayan sallar asuba, ko sallar azhar, ko sallar magariba baztai wata sallah ba sai guda daya kawai, itace sallar datai tsarki acikin lokacinta, ( Asuba ko azahar ko magariba) domin wadannan sallolin ba'a hadasu dawani abu dayake kafinsu.
Ibnu qudama rahimahullah acikin Almugni ( 1/238) yace: Idan mai haila tai tsarki kafin rana tafadi zatai sallar azahar da la'asar,
idan tai tsarki kafin hudowar alfijir zatai sallar magariba da isha'i, anruwaito wannan daka Abdurrahman bin Auuf, da Abdullahi dan Abbas, da dawus, da Mujahid, da Annaka'i, da zuhuri, da rabi'ah, da malik, da lais, da shafi'i, da ishaq, da Abissauri.

Imamu Ahmad yace: gaba dayan tabi'ai sunyi fatawa da wannan maganar sai hasanul basari shi kadai yace: abunda ya wajaba agareta shine sallar datai tsarki acikin lokacinta kawai, itace fatawar sauri dalibansa, domin lokacin sallar farko yafita lokacin tanada uzuri, saboda haka bata wajaba akantaba.
An ruwaito daka malik cewa idan tariski lokacin sallah tabiyu gwar-gwadon yanda zata iyayin raka'a biyar lokaci baifitaba, sallar farko tawajaba agareta, domin gwar-gwadon lokacin raka'a daya shine lokacin sallar farko ahalin uzuri, tawajaba akanta da riskarsa, kamar yanda zata risketa afarkon lokacinta.

Asram da ibnu munzir sun ruwaito daka Abdurrahman bin Auuf da Abdullahi dan Abbas sunce: Idan mai haila tai tsarki kafin hudwar alfijir da gwar-gwadon lokacinda zata iya raka'a daya , zatai magariba da isha'i, idan tai tsarki kafin faduwar rana zatai azahar da la'asar gaba daya, domin lokacin sallah tabiyu shine lokacin tafarko ahalin uzuri, idan mai uzuri yariskeshi wajabcinta yakamashi, kamar yanda wajabcin ta biyu yahaushi.
Wasu malaman kuma sukace: babu abunda zata rama sai sallar data riski lokacinta kawai, amma wacce lokacinta yawuce bazata rama taba, shaik usaimin rahimahullah yarinjayar da wannan maganar takarshe.

Abunda yafi shine aiki da fatawar jamhur din malamai, zatai sallah biyu ahade, bazata rama dukkan sallolin wuni ba, idan kuma tarama iya wacce tariski lokacinta Ana fatan babu komai akanta.

Wallahu A'alam

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form