Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

Fassarar Wakar Tu Mila De

Fassarar Wakar Tu Milade

Sunan Waka: Tu Milade

Sunan Fim: All Is Well

Shekarar Fita: 2015

Hada Sauti: Himesh Reshammiya

Rubuta Waka: Mayur Puri

Sunan Kamfani: T-Series

Mawaki: Ankit Tiwari

Mai Fassara: Haiman Khan Raees 

Ooo Oooo...

* Bekasi Hai, Bebasi Hai, Beqaraar Hai Aarzoo

Akwai Rashin samun taimako, akwai Tilastawa, kuma Muradai na sun Gaza Hutawa 

* Rabba Mere Tu… Rabba Mere Tu…

Ya Ubangiji na! 

* Zara Sa Tu Aasra De

Ka Agaza Min 

* Zara Sukoon Tu Dila De

Ka bani Sukuni 

* Meri Duaa Ko Tere Karam Se

 Addu'a ta da girman zatin ka 

* Mere Khuda Ab Tu Mila De

Ka hadasu ya ubangiji na (Amsa min Addu'a ta/ka biya min bukata ta)

* Tu Milade…

Ka hada su 

Ooo Oooo...

* Dard Bhi De, Par Dawa De

Ka hadani da cuta, amma ka bani maganin ma 

* Arzyion Ko Honsla De

Ka Bani Kwarin Guiwa akan Addu'a ta 

* Meri Duaa Ko Tere Karam Se

 Addu'a ta da girman zatin ka 

* Mere Khuda Ab Tu Mila De

Ka hadasu ya ubangiji na (Amsa min Addu'a ta/ka biya min bukata ta)

* Tu Milade…

Ka hada su 

Ooo Oooo...

* Aashiyaana, Har Thikana, Mera Tanha

Masauki na, da duk inda na zauna yanzu cike yake da kadaici. 

* Raahaton Ka, Mil Saka Na, Ek Lamha

Na kasa zaune na kasa tsaye 

* Tanhaayi Parchhai Hoke Aayi Mere Roobarooo

Kadaici ya zamo inuwa ta kuma gashi ya tare ni gaba da gaba. 

* Rabba Mere Tu… Rabba Mere Tu…

Ya ubangiji na!! Ya ubangiji Na!! 

* Soona Jo Dil Hai Phir Basa De

Ka Maida Zuciya ta wacce take cike da kadaici ta zamo wuri wanda ya Cancanci zama 

* Jeene Ki Ab To Koi Wajah De

Ka bani dalilin ci gaba da rayuwa

* Meri Duaa Ko Tere Karam Se

 Addu'a ta da girman zatin ka 

* Mere Khuda Ab Tu Mila De

Ka hadasu ya ubangiji na (Amsa min Addu'a ta/ka biya min bukata ta)

* Tu Milade…

Ka hada su 

Ooo Oooo...

* Boond Bhar Ki, Pyaas Meri, Tu Hai Dariya

Kishirwa na bai wuce na digo ba, Yayinda Kai Kuma Tamkar Kogi ne 

* Mera Hissa, Hoga Kitna, Ek Katra

Rabo na a cikin bai wuce cikin cokali ba 

* Meri Aahein Teri Raahein Takti Hain Aur Kya Kahoon

Na zuba ido ne kawai Inga Yadda zaka yi, To me zan ce? 

* Rabba Mere Tu… Rabba Mere Tu…

Ya ubangiji na! Ya ubangiji na!! 

* Mujhko Bana De Ya Mita De

Ko dai Ka cika min bukatata ko kuma ka kawar dani kawai 

* Banda Tera Hoon Tu Faisla De

Ni bawan ka ne, kuma na yarda da duk Kaddarar da ka Jarabce ni da ita. 

* Meri Duaa Ko Tere Karam Se

 Addu'a ta da girman zatin ka 

* Mere Khuda Ab Tu Mila De

Ka hadasu ya ubangiji na (Amsa min Addu'a ta/ka biya min bukata ta)

* Tu Milade…

Ka hada su 

Ooo Oooo...


Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Infohaiman999@gmail.com 

Share:

SHARHIN FIM DIN DON

*SHARHIN FINA FINAI* 

Directed by Farhan Akhtar
Produced by Gauri Khan Ritesh Sidhwani
Farhan Akhtar

Jaruman cikin film din 

Shah Rukh Khan
Priyanka Chopra
Arjun Rampal
Boman Irani
Isha Koppikar
Om Puri

an saki film din 20 October 2006 


Kasuwancin miyagun ƙwayoyi da aka kafa a Kuala Lumpur yana bunkasa. An tura tawagar mataimakin kwamishinan 'yan sandaa De Silva (Boman Irani) zuwa birnin don magance aikin Singhania (Rajesh Khattar) sannan kuma ya kama manajan sa"Don" (Shah Rukh Khan). Singhania da Vardhan , wanda ba a san inda ba yake ba. Bayan Ramesh (Diwakar Pundir), ɗaya daga cikin abokan hulɗa na Don, ya yanke shawarar barin ƙungiyar, Don ya kashe shi. Daga baya, matar da Ramesh zai aura Kamini (Kareena Kapoor) ta yanke shawarar taimaka wa 'yan sanda, amma an kashe ta.
 Shirye-shirye don ɗaukar wa dan uwansta da budurwar sa fansa, Roma (Priyanka Chopra) ta shiga ƙungiyar Don. Don ya ji rauni lokacinda yake ƙoƙarin tserewa daga 'yan sanda har ya shiga coma. De Silva ya sami mai kama Don mai suna Vijay (Shah Rukh Khan) kuma ya roƙe shi ya shiga aikinsa don 'yan sanda su saku damar kusantar Singhania. Vijay ya yarda da lokacin da De Silva ya yi alkawalin ya saka Deepu (Tanay Chheda), wani yaro Vijay ya ke kula dashi, a makaranta a Kuala Lumpur.

 Ana haka, Jasjit (Arjun Rampal), mahaifin Deepu, wanda aka saki ne daga kurkuku, ya shirya kashe De Silva don ɗaukar fansar mutuwar matarsa An kwantar da Vijay a asibiti, inda Dr Ashok Gilwani yayi masa tabu irin na Don. Lokacin da Don ya mutu ba da daɗewa ba, wasa ya fara. Vijay, kamar Don, ya shiga ƙungiyar ta Kuala Lumpur. De Silva ya nemi Vijay daya nemo mashi wani casset wanda ke dauke da cikakkun bayanai game da kungiyar Lokacin da Vijay ya same shi, Roma tayi ƙoƙarin kashe shi, amma De Silva ya gaya mata game da shirinsa, kuma ta yarda ta taimake shi.

 Vijay ya bawa De Silva disc. A lokacin da De Silva ya kashe Singhania, 'yan sanda suka zo suka kama Vijay. An kashe De Silva a cikin harbe-harbe, Vijay yana cikin hadari saboda De Silva shine kadai mutumin da zai iya tabbatar da cewa shi ba ainihin Don ba ne. Bayan an gano ainihin shi waye, abokan Don suka juyawa Vijay baya kungiyar ta shiga yakin. Vijay ya tsere kuma da Roma don dawo da diski kuma ya tabbatar da rashin laifinsa

Ana haka, Jasjit ya shiga gidan De Silva don jira shi kuma ya sami disc.An kirasa a waya ana cewa idan yana so ya ga ɗansa, zai zamla dole ya kawo disc ga mutanen da ke riƙe da Deepu. Lokacin da ya hadu da su, ya fahimci cewa De Silva yana da rai kuma shi ne Vardhan, wanda ke amfani da Vijay don ya kusaci abokin gabar sa. Bayan haka, Jasjit ya shiga gwagwarmaya tare da Vijay amma Deepu ya katse shi, ya gaya masa game da Vijay, wanda ya kasance mai kula da shi a lokacin da Jasjit baya nan. Jasjit ya haɗa kai da Vijay da Roma kuma ya ba da labarin game da ainihin waye Vardhan. Sun zo da shiri. Jasjit ya shirya taro tare da Vardhan, amma uku sun sanar da hakan Interpol.

A cikin gwagwarmaya, Vijay yana gab da kashe Vardhan , amma inspector Malik (Om Puri) ya katse shi, wanda ya roke shida bar Vardhan, wanda aka kama shi daga baya. An saki Vijay, kuma Roma ta fada wa Vijay tana sonshi lokacin da za a kai shi asibiti. Bayan da Vijay ya kira Roma da "Junglee Billi" ("Wildcat") amma motar asibiti ta wuce dashi, Roma ta gane cewa shine ainihin Don saboda shi ke kiranta da wannan sunan kuma ta fadawa Malik. An bayyana cewa ainihin Don yana da rai, kuma nuna cewa shine Vijay a duk lokacin. Lokacin da yake a asibiti, Don ya samu sauki daga raunin da ya samu, kuma ya ji maganar Vardhan / De Silva da Vijay. Bayan aikin Vijay, Don ya tashi daga ɗaki lokacin da Vardhan da Dr Ashok ba su nan kuma sun tafi ɗakin da Vijay ke kwance. Ya sauya wuri da Vijay kuma ya cire wa Vijay na'urar da take taimaka masa yayi numfashi,wanda ya sa shi ya mutu. An kuma bayyana cewa disc din da Don ya ba 'yan sanda na karya ne. A halin yanzu, tare da Vardhan da Singhania an cire su daga hanyarsa, Don ya zama mai kula da dukkanin harkokin miyagun ƙwayoyi na Asia. Don ya sake haɗawa da Anita (Isha Koppikar) a filin jirgin sama kuma ya ce rabin maganarsa da ya ke yi, "Don Ko Pakadna Mushkil Hi Nahi" .....

By @munnir the special one👑

Share:

Fassarar Wakar Jeena Jeena

Fassarar Wakar Jeena Jeena

Sunan Waka: Jeena Jeena

Sunan Fim: Badlapur

Shekarar Fita: 2015

Sauti: Sachin-Jigar

Rubutawa: Dinesh Vijan Da Priya Saraiya

Kamfani: T-Series

Mawaki: Atif Aslam 

Mai Fassara: Haiman Khan Raees 

Hmm Mmm... Hmm Mmm… Hmm Mmm… Hmm Mmm… (x2)

* Dehleez Pe Mere Dil Ki, Jo Rakhe Hain Tune Kadam

Yayinda Kika Iso Bakin Kofar Zuciya Ta 

* Tere Naam Pe Meri Zindagi, Likh Di Mere Humdum

Na Sadaukar Da Rayuwa ta wa Sunan Ki 

* Haan Seekha Maine Jeena Jeena Kaise Jeena

Na Koyi Yadda Zan Rayu 

* Haan Seekha Maine Jeena Mere Humdum

Na Koyi Yadda Zan Rayu, Masoyiya ta 

* Na Seekha Kabhi Jeena Jeena Kaise Jeena

A Da ban taba Koyon yaya Zan Rayu ba 

* Na Seekha Jeena Tere Bina Humdum

Ban Taba Koyon Yadda zan Rayu ba tare da ke ba Masoyiya ta

* Dehleez Pe Mere Dil Ki, Jo Rakhe Hain Tune Kadam

Yayinda Kika Iso Bakin Kofar Zuciya Ta 

* Tere Naam Pe Meri Zindagi, Likh Di Mere Humdum

Na Sadaukar Da Rayuwa ta wa Sunan Ki 

* Haan Seekha Maine Jeena Jeena Kaise Jeena

Na Koyi Yadda Zan Rayu 

* Haan Seekha Maine Jeena Mere Humdum

Na Koyi Yadda Zan Rayu, Masoyiya ta 

* Na Seekha Kabhi Jeena Jeena Kaise Jeena

A Da ban taba Koyon yaya Zan Rayu ba 

* Na Seekha Jeena Tere Bina Humdum

Ban Taba Koyon Yadda zan Rayu ba tare da ke ba Masoyiya ta


Hmm Mmm... Hmm Mmm… Hmm Mmm… Hmm Mmm…

* Sacchi Si Hain Yeh Taareefein, Dil Se Jo Maine Kari Hain… (x2)

Wadannan Yabo Ne Na gaskiya nake miki daga Zuciya Ta (x2) 

* Jo Tu Mila To Saji Hai, Duniya Meri Humdum

Yayinda Na Sameki, Sai Duniya ta Ta Qawatu Matuka 

* O Aasmaan Mila Zameen Ko Meri

Duniya Ta Ta Cika Burin Ta 

* Aadhe Aadhe Poore Hain Hum

Dukkan Mu Ba a cike muke ba, Yanzu da muka Hadu Ne muka zama DAYA 

* Tere Naam Pe Meri Zindagi, Likh Di Mere Humdum

* Tere Naam Pe Meri Zindagi, Likh Di Mere Humdum

Na Sadaukar Da Rayuwa ta wa Sunan Ki 

* Haan Seekha Maine Jeena Jeena Kaise Jeena

Na Koyi Yadda Zan Rayu 

* Haan Seekha Maine Jeena Mere Humdum

Na Koyi Yadda Zan Rayu, Masoyiya ta 

* Na Seekha Kabhi Jeena Jeena Kaise Jeena

A Da ban taba Koyon yaya Zan Rayu ba 

* Na Seekha Jeena Tere Bina Humdum

Ban Taba Koyon Yadda zan Rayu ba tare da ke ba Masoyiya ta


Hmm Mmm... Hmm Mmm… Hmm Mmm… Hmm Mmm… (x2)


©
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Haimanraees@gmail.com

Masu satar fasaha ta kare muku 

Share:

ZAN IYA SAWA A MALLAKE MIN MIJINA BA DON NA CUTAR DA SHI BA

ZAN IYASAWA A MALLAKE MIJI NA! BADAN NA CUTAR DASHI BA??
:
Daga zauren
KHULAFA'UR-RASHIIDUN
:
Assalama Alaikum warahamatullah

malam ya halasta mata tamalake mijinta?

inhar zamansu badadi, domin tasamu hankalinshi yakomo gareta. amma bada niyar cutarwaba.
:
                          *****
:
Wa'alaikumussalam Warahamatullahi wabarkatuhu

A,a Qur'ani da sunnah basu koyar da hakaba, zuwa wajen masu bada irin wannan maganin yana janyo asaran sallan kwana 40, koma yayi sanadin futar damutum daga Musulunci gabadaya !!
:
Mallaka miji anayine ta hanyoyin kyautatawa da bin umarnin ALLAH

Amma idan zama ya gagara, se aje atattarasu ahada waliyanta danashi, ko wakilansu, masu hankali adedeta Auren
:
Amma kan zuwa wajen boka haramun ne!!!!!

Wallahu a,alam
========================
*```Date* ```[25-04-1439]Hj {12-01-2018}
_Masu buqatan Group suyima Auwal Abu ja'afar magana ta whatsApp_
*[+2347035269582]* ko DAN MAMA +2349033206238
           *```Kuna iya samun mu ta facebook*```
https://mobile.facebook.com/khulafaurrashidun/?
((سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أشْهَدُ أنْ لَا إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ، أسْتَغْفِرُكَ وأَتُوبُ إِلَيْكَ))
〰〰〰〰〰〰〰〰✔
Aji Tsoron ALLAH kada achanja mana komai! In anga kuskure asanar damu !
Share:

Fassarar Wakar Saware

Fassarar Wakar Saware

Sunan Waka: Saware

Sunan Fim: Phantom
  
Shekarar Fita: 2015
     
Hada Sauti: Pritam

Rubuta Waka: Amitabh Bhattacharya

Sunan Kamfani: T-Series

Sunan Mawaki: Arijit Singh

Mai Fassara: Haiman Khan Raees 
  
* Pehle Kyun Na Mile Hum, Tanha Hi Kyun Jale Hum

Me yasa tun tuni bamu hadu ba? Me yasa zukatan mu ke kuna da kadaici? 

* Milke Muqammal Hue Hain, Ya They Tanha Bhale Hum

Shin mun hadu ne har mun zama daya, ko kuwa gara mu kasance cikin kadaici? 

* Saware... (x3)

Ya Ke Abar So na (x3) 

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda kike fatar Faruwar sa da wanda nake fatar Faruwar sa duk basu faru ba 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ba Zata iya kaiwa ga gaci ba 

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda kike fatar Faruwar sa da wanda nake fatar Faruwar sa duk basu faru ba 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ba Zata iya kaiwa ga gaci ba 

Sun Bairiya Saware… (x2)

Ki Saurara Yake Muguwar Abar So 

* Pal Pal Ginke Guzara Maano Karza Utaara

Na karar da Lokutan rayuwa ta ina mai kirga su tamkar bashin da ake bi na 

* Tum Se Munaasib Hua Hai Phir Se Jeena Humaara
   
A tare da ke ne na samu dalilin yin rayuwa 

* Saware... (x3)

Ya Ke Abar So na (x3) 

Hmm... 

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda kike fatar Faruwar sa da wanda nake fatar Faruwar sa duk basu faru ba 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ba Zata iya kaiwa ga gaci ba 

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda kike fatar Faruwar sa da wanda nake fatar Faruwar sa duk basu faru ba 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ba Zata iya kaiwa ga gaci ba 

Sun Bairiya Saware… (x2)

Ki Saurara Yake Muguwar Abar So * Dhalti Raat Ka Ik Musaafir Subah Alvida Keh Chala

Matafiyin asubanci yana bankwana da Safiya 
  
* Jeete Jeete Raah Ho Saka Na Marke Haq Ada Kar Chala

Lokacin da yake raye, ya kasa zama hanyar da mutane zasu iya Bi don yin tasu tafiyar, amma a yayin mutuwar sa, sai ga aikin ya kammala. 

O... 

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda kike fatar Faruwar sa da wanda nake fatar Faruwar sa duk basu faru ba 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ba Zata iya kaiwa ga gaci ba 

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda kike fatar Faruwar sa da wanda nake fatar Faruwar sa duk basu faru ba 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ba Zata iya kaiwa ga gaci ba 

Sun Bairiya Saware… (x2)

Ki Saurara Yake Muguwar Abar So


Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Infohaiman999@gmail.com 

Share:

Friday Messages 080

O Allah, do not call me to account for what they say and forgive me for what they have no knowledge of and make me better than they imagine,Happy Jummu'ah.
Share:

DAILY QURANIC VERSE

☀ DAILY QURANIC VERSE 🌙📚➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖

Allah Azzawajal Said In His Glorious Book 📖👇🏽


And when My slaves ask you (O Muhammad SAW) concerning Me, then (answer them), I am indeed near (to them by My Knowledge). I respond to the invocations of the supplicant when he calls on Me (without any mediator or [Quran chapter : 2: Verse 186]
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦

Share:

FASSARAR WAKAR BAATEIN YE KABHI NA

Fassarar Wakar Baatein Ye Kabhi Na

Sunan Waka: Baatein Ye Kabhi Na (Male)

Sunan Fim: Khamoshiyan

Shekarar Fita: 2015

Sauti: Jeet Gannguli

Rubutawa: Sayeed Quadri

Kamfani: Sony Music Entertainment India Pvt. Ltd.

Mawaki: Arijit Singh

Mai Fassara: Haiman Khan Raees

* Baatein Ye Kabhi Na Tu Bhoolna

Kada ki taba Mantawa da cewa

* Koi Tere Khaatir Hai Jee Raha

Wani na rayuwa ne kawai saboda ke

* Jaaye Tu Kahin Bhi Ye Sochna

Ko ina zaki je, ki tuna da hakan

* Koi Tere Khaatir Hai Jee Raha

Wani na rayuwa ne kawai saboda ke.

* Tu Jahaan Jaaye Mehfooz Ho… (x2)

A duk Inda kike, Ina Miki Fatar Aminci. (x2)

* Dil Mera Maange Bas Ye Dua

Addu'ar Da Zuciya ta ke Yi kenan

* Baatein Ye Kabhi Na Tu Bhoolna

Kada ki taba Mantawa da cewa

* Koi Tere Khaatir Hai Jee Raha

Wani na rayuwa ne kawai saboda ke

* Jaaye Tu Kahin Bhi Ye Sochna

Ko ina zaki je, ki tuna da hakan

* Koi Tere Khaatir Hai Jee Raha

Wani na rayuwa ne kawai saboda ke.

* Humdard Hai, Humdum Bhi Hai

Tamkar  Kyakkyawar Abokiyar alaka

*Tu Saath Hai Toh Zindagi

Haka rayuwa take Idan kina tare da ni

* Tu Jo Kabhi, Door Rahe

A duk lokacin da kika yi nesa da ni

* Ye Humse Ho Jaaye Ajnabi

Rayuwar sai ta zamo Bakuwa a gare ni

* Tujhse Mohabbat Karte Hain Jo… (x2)

Irin son da nake miki... (x2)

* Kaise Karein Hum Usko Bayaan

Ta yaya zan iya bayyana shi?

* Baatein Ye Kabhi Na Tu Bhoolna

Kada ki taba Mantawa da cewa

* Koi Tere Khaatir Hai Jee Raha

Wani na rayuwa ne kawai saboda ke

* Jaaye Tu Kahin Bhi Ye Sochna

Ko ina zaki je, ki tuna da hakan

* Koi Tere Khaatir Hai Jee Raha

Wani na rayuwa ne kawai saboda ke.

* Jaagi Bhi Hai, Royi Bhi Hai

Suna tsayawa cur, kuma suna yin kuka

* Aankhein Ye Raaton Mein Mere

Wadannan Idanuwan nawa, tsawon dare

* Kyun Har Ghadi Milke Tujhe

Duk da Kasancewa na tare da ke

* Lagti Rahe Bas Teri Kami

Me yasa nake jin Kewarki

* Hum Toh Na Samjhe Tum Hi Kaho… (x2)

Na kasa fahimtar meye hakan, ki fada min (x2)

* Kyun Tumko Paake Tumse Juda

Har bayan na same ki, duk da haka ina nesa da ke

* Baatein Ye Kabhi Na Tu Bhoolna

Kada ki taba Mantawa da cewa

* Koi Tere Khaatir Hai Jee Raha

Wani na rayuwa ne kawai saboda ke

* Jaaye Tu Kahin Bhi Ye Sochna

Ko ina zaki je, ki tuna da hakan

* Koi Tere Khaatir Hai Jee Raha

Wani na rayuwa ne kawai saboda ke.

* Tu Jahaan Jaaye Mehfooz Ho… (x2)

A duk Inda kike, Ina Miki Fatar Aminci. (x2)


Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Infohaiman999@gmail.com

Share:

Verse Of The day

“And certainly, We shall TEST you with something of FEAR, HUNGER, LOSS of HEALTH, LIVES and FRUITS, but give glad TIDINGS to As-Saabiroon (the PATIENT).

Who, when afflicted with calamity, say: ‘Truly, to ALLAAH ﷻ we belong and truly, to Him we shall return.’

They are those on whom are the Salawaat (i.e. who are blessed and will be forgiven) from their Lord, and (they are those who) receive His Mercy, and it is they who are the guided ones”

[AL-BAQARAH 2:155-157] 

Share:

Fassarar Wakar Teri Khushboo

Fassarar Wakar Teri Khushboo

Sunan Waka: Teri Khushboo (Male Version)

Sunan Fim: MR. X

Shekarar Fita: 2015

Sauti: Jeet Gangulli

Rubutawa: Rashmi Singh

Kamfani: Sony Music

Mawaki: Arijit Singh

Mai Fassara: Haiman Khan Raees

* Teri Khushboo Aur Teri Saansein…

Kamshin ki da Numfashin ki

* Katra Katra Sab Bhulayenge…

(Da) Duk wani abu da ya Shafe ki zan manta shi a hankali a hankali

* Silvatein Jo Tumne Chhodi Hain…

Duk wata damuwa da kika tafi kika bari

* Dheere Dheere Sab Mitayenge…
Da sannu Sannu Zasu bace daga cikin tunani na

* Kaatne Ko Itni Lambi Umr Aage Hai…

Akwai Ragowar rayuwa mai tsawo a gaba da zata zo ta wuce

* Jaane Kiske Peeche Tu Bewajah Bhaage Hai…

Babu wanda yasan Me Kike Da bukata, Ya Zuciya ta

* Aankh Nam Hoti Hai Hone Do…

Idan Idanuwa Zasu Jike nema da hawaye, to su Jike din

* Honth Lekin Muskurayenge…

Labba zasu yi Murmushi

* Uski Raaton Se Subah Apni…

Daga dararen ta ne Safiyoyi na suke Samuwa

* Rafta Rafta Kheench Laayenge…

Da Sannu Sannu Zan Janye

* Aisa Koi Dil Nahi, Jo Kabhi Toota Nahi

Babu wata Zuciya da bata taba Karyewa ba

* Kaanch Se Ummeed Kya Rakhna...

Menene na tunanin wai gilashi ba zai fashe ba?

* Aisa Koi Dil Nahi, Jo Kabhi Toota Nahi

Babu wata Zuciya da bata taba Karyewa ba

* Kaanch Se Ummeed Kya Rakhna...

Menene na tunanin wai gilashi ba zai fashe ba?

* Kaatne Ko Itni Lambi Umr Aage Hai…

Akwai Ragowar rayuwa mai tsawo a gaba da zata zo ta wuce

* Jaane Kiske Peeche Tu Bewajah Bhaage Hai…

Babu wanda yasan Me Kike Da bukata, Ya Zuciya ta

* Aankh Nam Hoti Hai Hone Do…

Idan Idanuwa Zasu Jike nema da hawaye, to su Jike din

* Honth Lekin Muskurayenge…

Labba zasu yi Murmushi

* Uski Raaton Se Subah Apni…

Daga dararen ta ne Safiyoyi na suke Samuwa

* Rafta Rafta Kheench Laayenge…

Da Sannu Sannu Zan Janye

* Chal Nayi Shuruaat Kar, Bhool Ke Jo Ho Gaya

Bari mu fara daga farko bayan mun manta da duk abinda ya faru ya wuce

* Haath Pe Yun Haath Kya Rakhna…

Me zai sa mutum ya tsaya a waje daya?

Ho…

* Chal Nayi Shuruaat Kar, Bhool Ke Jo Ho Gaya

Bari mu fara daga farko bayan mun manta da duk abinda ya faru ya wuce

* Haath Pe Yun Haath Kya Rakhna…

Me zai sa mutum ya tsaya a waje daya?

* Kaatne Ko Itni Lambi Umr Aage Hai…

Akwai Ragowar rayuwa mai tsawo a gaba da zata zo ta wuce

* Jaane Kiske Peeche Tu Bewajah Bhaage Hai…

Babu wanda yasan Me Kike Da bukata, Ya Zuciya ta

* Teri Khushboo Aur Teri Saansein…

Kamshin ki da Numfashin ki

* Katra Katra Sab Bhulayenge…

(Da) Duk wani abu da ya Shafe ki zan manta shi a hankali a hankali

* Silvatein Jo Tumne Chhodi Hain…

Duk wata damuwa da kika tafi kika bari

* Dheere Dheere Sab Mitayenge…
Da sannu Sannu Zasu bace daga cikin tunani na

©
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Infohaiman999@gmail.com

Masu satar fasaha ta kare muku

Share:

FASSARAR WAKAR SANAM RE

Fassarar Wakar Sanam Re

Sunan Waka: Sanam Re

Sunan Fim: Sanam Re

Shekarar Fita: 2016

Hada Sauti: Mithoon

Rubuta Waka: Mithoon

Sunan Kamfani: T-Series

Mawaka: Mithoon da Arijit Singh

Ho Oo Oo...

* Bheegi Bheegi Sadkon Pe Main, Tera Intezaar Karun

In Jiranki a tsakanin Jikakkun Layuka

* Dheere Dheere Dil Ki Zameen Ko, Tere Hi Naam Karun

A hankali a hankali ina ta baki Filayen Zuciya ta

* Khudko Main Yun Kho Doon, Ke Phir Na Kabhi Paoon

Ina so in rasa kaina a garin yin hakan ta yadda ba zan taba samuwa ba.

* Haule Haule Zindagi Ko, Ab Tere Hawaale Karun

Da sannu Sannu dai ina ta mika rayuwa ta izuwa gare ki

* Sanam Re, Sanam Re, Tu Mera Sanam Hua Re (x2)

Ya Masoyiyata, Kin zama Abar Kaunata

* Karam Re, Karam Re, Tera Mujh Pe Karam Hua Re…

Wannan duk saboda Karamcin Ki ne a gare ni

* Sanam Re, Sanam Re, Tu Mera Sanam Hua Re (x2)

Ya Masoyiyata, Kin zama Abar Kaunata

Ho Oo Oo...

* Tere Qareeb Jo Hone Laga Hoon, Toh Toote Saare Bharam Re

A Yayinda nake kara kusantuwa dake, duk tunane Tunane na sai suka fara bayyana

* Sanam Re, Sanam Re, Tu Mera Sanam Hua Re (x2)

Ya Masoyiyata, Kin zama Abar Kaunata

Ho Oo Oo...
 
* Baadalon Ki Tarah Hi Toh, Tune Mujh Pe Saaya Kiya Hai

Kamar giza gizai haka kika zamo Inuwa a gare ni

* Baarishon Ki Tarah Hi Toh, Tune Khushiyon Se Bhigaaya Hai

Kamar ruwan sama, haka kika Jike ni da Farinciki

* Aandhiyon Ki Tarah Hi Toh, Tune Hosh Ko Udaaya Hai

Kamar Iska haka kika tafi da tunani na

* Mera Muqaddar Sanwara Hai Yun, Naya Savera Jo Laaya Hai Tu

Kin sabunta Kaddara ta, ta hanyar samar da sabuwar safiya a rayuwa ta

* Tere Sang Hi Bitaane Hain Mujhko, Mere Saare Janam Re

Da ke kawai nake son na Kare Rayuwa ta tare.

* Sanam Re, Sanam Re, Tu Mera Sanam Hua Re (x2)

Ya Masoyiyata, Kin zama Abar Kaunata

* Sanam Re… Sanam Re…

Ya Masoyiya ta! Ya Masoyiyata!!

* Karam Re, Karam Re, Tera Mujh Pe Karam Hua Re…

Wannan duk saboda Karamcin Ki ne a gare ni

* Karam Re… Karam Re…

Karamcin Ki ne! Karamcin ki ne

* Sanam Re, Sanam Re, Tu Mera Sanam Hua Re

Ya Masoyiyata, Kin zama Abar Kaunata

Ho Oo Oo...

* Mere Sanam Re Mera Hua Re

Abar sona ta zama tawa

* Tera Karam Re Mujh Pe Hua Yeh

Wannan Karamcin ki ne a gare ni

* Mere Sanam Re Mera Hua Re

Abar sona ta zama tawa

* Tera Karam Re Mujh Pe Hua Yeh

Wannan Karamcin ki ne a gare ni

Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Infohaiman999@gmail.com

Share:

THE QUR'AN

_*The Qur'an*_

*1.* In a beautiful Hadith, Rasulullah (Sallallahu Alaihi Wasallam) said: _"When a man dies and his relatives are busy in funeral, there stands an extremely handsome man by his head. When the dead body is shrouded, that man gets in-between the shroud and the chest of the deceased. When after the burial, the people return home, 2 angels, namely, Munkar and Nakeer (being names of two special Angels), come in the grave and try to separate this handsome man from the dead man, so that they may be able to interrogate the dead man in privacy about his faith. But the handsome man will say, 'He is my companion, he is my friend. I will not leave him alone. If you are appointed for interrogation, do your job. I cannot leave him until I get him admitted into Paradise'. Thereafter he turns to his dead companion and says, 'I am the Qur'an, which you used to read, sometimes in a loud voice and sometimes in a low voice. Do not worry. After the interrogation by Munkar and Naker, you will have no grief.' When the interrogation is over, the handsome man arranges for the dead, from Al-Mala'ul A'laa (the Angels in Heaven), silk bedding filled with musk."_

*2.* Rasulullah (SAW) said:  _"On the Day of Judgement, before Allah, no other Intercessor will have a greater status than the Qur'an, neither a Prophet nor an angel."_

*3.* Please keep forwarding this 'Hadith' to all... because Rasulullah (SAW) said: _'Pass on knowledge from me even if it is only one verse'. May Allah bestow this favour on all of us. AMIN._

_*May Allah accept our efforts, forgive us and have mercy on us. Ameen*_

🔚

Share:

FASSARAR WAKAR AARAHA HOON PALATKE

Fassarar Wakar Aaraha hoon palatke

Sunan Waka : Aa raha hoon palat ke

Sunan Fim: Don 2

Mawaki: Shah Rukh Khan

Mai Fassara: Haiman Khan Raees

Mere dushman samajh rahe the main

Ab kabhi laut ke na aaunga

Ek gumnaami ka samundar hai

Uss mein hi jaa ke doob jaunga

Abhi baaki meri kahani hai

Saari duniya ko jo sunaani hai

Mujhe phechano, dekho main hun kaun

Aa raha hoon palat ke

Main hoon Don..

Makiya na Suna Tunanin Cewa Ba Zan Taba Dawowa ba

Wai Akwai Wani Boyayyen Kogi Da Naje Na Fada

Amma A labari na da Saura Fa

Wanda Duniya ya Kamata taji Shi

Ku Gane ni... Ku Kalli Wanene Ni

Ina Nan Dawowa

Nine, Don

Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Infohaiman999@gmail.com

Share:

FASSARAR WAKAR BANDE HAIN HUM USKE


Fassarar Wakar Bande Hain Hum Uske

Sunan Waka: Bande Hain Hum Uske

Sunan Fim: Dhoom 3

Shekarar Fita: 2013

Sauti: Pritam

Rubutawa: Sameer Anjaan

Kamfani: YRF Music

Mawaka: Shivam Mahadevan Da Anish Sharma

Mai Fassara: Haiman Khan Raees

* Aasmaan Ki Chhat Pe, Hai Apni Duniya

Duniyar mu tana Saman rufin Sararin samaniya Ne

* Khilkhilati Jisme, Hai Apni Khushiyan

A Can ne Farincikin Mu Ke Yin Fure

* Chand Ki Chhalni Liye, Taare Chunte Hain Hum

A Matatar wata ne, Muke Zabar Taurari

* Jaaduyi Hai Ye Jahaan, Hai Nahi Koi Gham

Wannan Duniyar Tsafaffiya Ce, Babu Bakin ciki a cikin ta

* Bande Hain Hum Uske, Humpe Kiska Zor

Mu Bayin Allaah Ne, Waye Ya Isa ya ja da mu?

* Ummedon Ke Sooraj, Nikle Chaaron Ore

Muna shan hantsi a Karkashin Dubunnan hasken ranakun Rabo

* Iraadein Hain Fauladi, Himmati Har Kadam

Da Qaqqarfan Quduri, Da Nagartaccen Qwazo

* Apne Haathon Kismat Likhne, Aaj Chale Hain Hum...

Mun Sa Damba Yau Domin Mu Rubuta Qaddarar Mu...

* Aasmaan Ki Chhat Pe, Hai Apni Duniya

Duniyar mu tana Saman rufin Sararin samaniya Ne

* Khilkhilati Jisme, Hai Apni Khushiyan

A Can ne Farincikin Mu Ke Yin Fure

* Chand Ki Chhalni Liye, Taare Chunte Hain Hum

A Matatar wata ne, Muke Zabar Taurari

* Jaaduyi Hai Ye Jahaan, Hai Nahi Koi Gham

Wannan Duniyar Tsafaffiya Ce, Babu Bakin ciki a cikin ta

* Bande Hain Hum Uske, Humpe Kiska Zor

Mu Bayin Allaah Ne, Waye Ya Isa ya ja da mu?

* Ummedon Ke Sooraj, Nikle Chaaron Ore

Muna shan hantsi a Karkashin Dubunnan hasken ranakun Rabo

* Iraadein Hain Fauladi, Himmati Har Kadam

Da Qaqqarfan Quduri, Da Nagartaccen Qwazo

* Apne Haathon Kismat Likhne, Aaj Chale Hain Hum...

Mun Sa Damba Yau Domin Mu Rubuta Qaddarar Mu...

Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Infohaiman999@gmail.com


Share:

YA TURA WANI GIDAN BOKA BAI SANI BA

*_YA TURA WANI GIDAN BOKA BAI SANI BA?_*

                               *Tambaya*
Assalamu Alaikum
Dr, nine wani ya faka a motor dinshi sai ya tambaye ne shin na san gidan wani mutumi sai nayi mishi kwatance sai daga baya na tuna gidan boka zai je, meye hukuncin wanda ya yi hakan?

Allah ya sakawa malan da gidan aljannah fiddausi

                                 *Amsa*
Wa'alaikum assalam, Mutukar ba da saninsa ba ya nuna masa, Allah ba zai kama shi da laifin hakan ba, saboda Allah ya yiwa al'umar Annabi Muhammad S.A.W afuwa cikin abin da suka aikata da kuskure ko mantuwa kamar yadda ayar karshe a suratul Bakara ta tabbatar da hakan.

Allah ne mafi sani

11/10/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

YAYA YA KAMATA INYI DA RIBAR BANKIN DA NA AMSA?

*_YA YA KAMATA NAYI DA RIBAR BANKIN DA NA AMSA?_* 

                              *Tambaya*
Assalamu alaikum malam Menene ra'ayin malaman Sunna akan kudin da banki suke karawa mutane a cikin Saving account? Ya yakamata ayi amfani dasu? Allah ya karemu daga aikata kuskure.

                                *Amsa*
Wa'alaikum assalam Farko dai ya haramta ga musulmi ya bude account din da za'a dinga saka masa kudin ruwa a ciki, saboda Allah ya haramta cin riba ya kuma yi shirin yaki da Wanda bai daina ci ba à cikin aya ta 275 a Suratul Bakara da ayoyin da suka zo bayanta. 

Annabi S.A.W ya la'anci mai cin riba da wanda ya rubutata da wanda aka wakilta da wanda ya yi shaida akanta. Kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi ingantacce. 

Idan mutum ya amshi Interest din Banki to ya wajaba ya tuba ga Allah da niyyar ba zai sake amsa ba, tun da Allah ya Hana. 

A zance mafi inganci zai iya amfani da kudin wajan yin aikin da zai amfani jama'a kamar gina Asibitoci ko kwatar da ruwa zai wuce ko kuma hanyoyin da mutane za su bi su wala, saidai ba shi da ladan wannan aikin da ya yi, saboda ba dukiyarsa ba ce.

Wannan ita ce maganar manyan malaman musulunci na wannan zamanin kamar Sheik Ibnu Bazz da sauransu. 

Allah ne mafi sani.

27/07/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

ZAN IYA AURAN JIKAR YAYATA?

*_ZAN IYA AURAN JIKAR YAYATA?_*

                            *Tambaya*
Assalamu Alaikum, Allah yasa Malam yana cikin koshin lafiya. Malam Ina neman a warware mun wata matsala ne, Akwai aure tsakanina da jikar yayata? Wato dani da kakar yarinyan mahaifinmu daya.

                                *Amsa*
Wa'alaikum assalam, Babu aure a tsakaninku mutukar mahaifiyarku daya da kakarta, saboda aya ta (23) a suratun Nisa'i ta haramta auran 'yar 'yar'uwa wacce kuke uwa daya ko uba daya ko kuma shakikai.

'Yar 'yar'uwa a wannan ayar ta hada da Jikarta da jikar jikarta har zuwa can kasa kamar yadda malaman Fiqhu su ka yi karin bayani.

Don neman karin bayani duba babun NIKAH a Fiqhul Muyassar da tafsiran malamai ga aya ta (23) a Suratun Nisa'i.

Allah ne mafi Sani.

19/08/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

TA HAIHU KAFIN TA CIKA WATA BAKWAI DA AURE

*_TA HAIHU KAFIN TA CIKA WATA BAKWAI DA AURE_*

                             *Tambaya*
Assalamu Alaikum. Malam yarinya ne aka aurar da ita batayi wata bakwai ba 7 ta haihu cikakkiyar yarinya yar wata tara (9) to malam meye hukuncin auren kuma ya hallaccin jaririyar a musulunci?

                                 *Amsa*
Wa'alaikum salam, In har an San tanada ciki aka yi auran wannan hukuncinsa a fili yake, kuma auran bai inganta ba  a zance mafi inganci, amma in haihuwa ta yi bayan wata bakwai, kuma ba'a santa da ciki ba to dansa ne, saboda ayar suratu Lukman da tá suratul Ahkafi sun nuna cewa ana iya haife ciki a watanni shida.
Auran dá  aka yi dá cikin shege ba tare da an sani ba  ya inganta, saidai ba  zá'à danganta cikin zuwa mijin ba, tunda ba shi ya yi ba.

In har ya san tana da ciki bayan sun yi aure bai halatta ya take  ta ba har saí ta haihu, saboda fadin Annabi S.A.W "Duk wanda ya yi imani dá Allah da ranar Lahira to kar ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" kamar yadda Abu-dawud ya rawaito.
In ta haihu za su iya cigaba dá mu'amalarsu ta aure, musamman in bai sani ba saí dá aka daura.

Allah ne mafi sani.

07/08/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

WACCE JINI YA DAUKE MATA AMMA TAKI YIN TSARKI

_*Tambaya:*_

Assalamu alaikum,
Mallam dan Allah tambaya nake wai wacce jinin haila  ya dauke mata taqi yin wanka har tsawon kwana daya ko biyu,menene hukuncinta shin zata rama sallolin kwanakinne ko yaya zatayi,ngd.

_*Amsa:*_

Wa'alaikumussalamu Warahmatullah.

_Ya zama wajibi akanta ta rama sallolin da ta bari daga lokacin da Jinin ya dauke. Sannan ta yi ta istigfari don neman yafiya daga Ubangiji domin ta aikata babban saɓo._

_Saboda faɗin Annabi (ﷺ): *“Idan hailarki ta zo to ki bar sallah, Idan ta kare sai ki yi wanka, ki yi sallah."* bukhary ya ruwaito shi._

Wallahu a'alamu.

_*✍🏾Ayyoub Mouser Geewerh.*_
_*📞08166650256.*_

Daga zauren:

_*🕌Islamic Post.*_

_Ga masu bukatar kasancewa tareda mu a zauren mu na WhatsApp, sai su turo da cikakken sunan su zuwa Wannan number, 08166650256, a WhatsApp._

Share:

ADDU'AR NEMAN BIYAN BUKATA

_*TAMBAYA.*_

Assalamu alaikum.. Dan Allah Malam. Wani adduane Mutun zaiyi idan yana rokan Allah yabashi wani abu?

_*AMSA:*_

_Wa'alaikumussalamu Warahmatullah._

_Yana da kyau me addu'a Ya kaskantar da kansa ga Ubangiji, sannan ya cire kokonton amsar addu'ar a zuciyarsa._

_An karbo hadisi daga Buraidata (r.a) ya ce: *manzon Allah (ﷺ)* ya ji wani mutum yana cewa: *Allahumma inni as'aluka bi anni ash-hadu annaKa antallahu Laa ilaaha illa anta, al-ahadus samadu, alladzi lam yalid wa lam yulad wa lam yakun lahu kufwan ahad,* sai manzon Allah (ﷺ) ya ce: *“Lallai ka yi roƙo da sunan da Idan aka yi roƙo da shi ana bayarwa, kuma idan aka yi addu'a da shi ana amsawa".* mutane hudu suka ruwaito shi, Ibn Hibban ya inganta shi._

_Wannan hadisin na nuna mana kenan ana saurin amsa addu'ar Wanda ya yi amfani da wadannan 👆🏾sunayen kenan._

_Saboda haka 'yar uwa Idan za ki yi addu'a, sai ki fara ambaton wadancan sunayen, sannan sai addu'ar ta biyo baya._

Wallahu A'alamu.

_*✍🏾Ayyoub Mouser Geewerh.*_
_*📞08166650256*_

_*🕌Islamic Post.*_

_Ga masu bukatar kasancewa tareda mu a zauren mu na WhatsApp, sai su turo da cikakken sunan su zuwa Wannan number, 08166650256, a WhatsApp._

Share:

WAJABCIN YIN WANKA BAYAN FITAR MANIYYI

_*Wajibcin Yin Wanka Bayan Fitar Maniyyi.*_

_*Tambaya:*_

Assalamu Alaikum warahmatullah

Dan Allah malam inna Neman karin ilimine akan Matan da ta wetting kanta tana bukatan tayi wankan starki ko kuwa basai tayiba?

_Wa'alaikumussalamu Warahmatullah Wabaratuhu._

_Ƴar uwa wajibi ne ga mutum Musulmi namiji ko mace ya yi wanka yayin da *Maniyyi* ya fita daga jikinsa ta hanyar jindadi ko a cikin barci._

_Domin *Allah (ﷻ)* Ya ce:_

_*”....وَإِن كُنتُم جُنُبًا فَاطَّهَّرُوا....“*_

_Ma'ana: *“Idan kun kasance kuna da janaba to ku yi tsarki (wanka)”*   (Alma’ida : 6)._

_Kuma *manzon Allah (ﷺ)* ya faɗi ga Aliyu cewa: *“Idan ka fitar da ruwa (Maniyyi) to ka yi wanka”* [Abu Dawud ne ya rawaito shi]._

_Sannan kuma an karbo hadisi daga Abi Sa'idul khudry (r.a) ya ce: *manzon Allah (ﷺ)* ya ce: *“Wanka yana kasancewa saboda fitar Maniyyi”.* Muslim ya ruwaito shi, amma asalinsa a cikin Ɓukhary ne._

_Saboda haka ƴar uwa duk wadda ta yi *wetting* ɗin kanta, to wajibi ne akanta ta ti wanka._

_Allah Ya bamu ilimi mai amfani👏🏽._

_Amsawa: *Ayyoub Mouser Geewerh.*_
_*08166650256.*_

_Daga Zauren:_

_*🧕Islamic Post Women.*_

_Ga masu bukatar kasancewa tareda mu a zauren mu na WhatsApp, sai su turo da cikakken sunan su zuwa Wannan number, 08166650256, a WhatsApp._

Share:

YA NEMI AURE A CIKIN IDDA

*_YA NEMI AURE A CIKIN IDDA ?_*

*_Tambaya_*

Assalamu Alaikum, Malam tambaya ne nakeso a taimaka a amsa mun akan sha’anin aure.

Malam mace ne tana zaune da mijinta sae ya kasance zaman sun babu dadi, kullum a cikin matsaloli iri-iri har ya kai ga takoma gidan iyayenta. Iyayenta sun matsa mata se da ta tilasta mijinta ya saketa, saboda suna da wani manufa akan idon ya saketa tsohon saurayinta
se ya aureta. 

Bayan ta matsawa mijinta akan lalle ya saketa se mijin nata ya amince akan zai kawo mata takardan sakin. Mallam a ranan da sukayi zai kawo mata takardan sakin, kawai sae ta samu tsohon saurayinta akan ta naso da
zaran ta gama idda se ya aureta. Mallam menene hukuncin wannan auren idon tagama idda ya aureta?

Na taba ji ance duk wanda ya nemi mace tana idda babu aure a tsakanin su har abada, Mallam don Allah ka taimaka mana da Karin bayani ?.

*_Amsa_*

Wa alaikum assalam,

in mutum ya nemi mace tana idda ya aikata haramun, kamar yadda aya ta: (235) a suratul Bakara ta tabbatar da hakan,saidai in an yi auran bayan ta gama idda auran ya inganta, amma an aikata zunubin nema. Malikiyya suna haramta mace ga mutum har abada in ya aure
ta cikin idda, ba in ya neme ta ba.

Allah ne mafi sani.

27/12/2016
Rubutawa: Abu - Manar.
Gabatarwa: Abu-Unaisa.

Ga duk mai sha'awar shiga wannan zaure na Darussunnah zai aika da sunan sa da jahar sa ta wadannan lambobi:

+2347035888158,
+2348099586379,
+2348139789030.

-Ta WhatsApp din zaka Tura ba ta SMS ba,
-Idan ka Tura a Lamba Guda daya To Kada Ka Tura Izuwa ga Daya Lambar,

Kai dai kawai Ka Jira Bayan Ka tura.

Share:

MUNA ZUBAR DA CIKI DA MIJINA IDAN LIKITA YA GAYA MANA YARON DA ZAMU HAIFA SIKILA NE

*_MUNA ZUBAR DA CIKI NI DA MIJINA IDAN LIKITA YA GAYA MANA YARON DA ZAMU HAIFA SKILA NE:_*

                              *Tambaya:*
Slm mallam ni AS ce mijinama ma desame genotype muke dashi yarana biyu babban AA karamar AS duk sanda na sami chiki muna zuwa a duba mana genotype din babyn dake chikin likitochi suka tabbatar da SS ne sai musa a chire amma bai kaiwa 4months muke chirewa mallam meye hukunchin yin hakan

                                   *Amsa:*
Wa'alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakaatuhu, To 'yar'uwa Malamai sun yi ijma'i akan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba.

Amma sun yi sabani game da zubar da ciki kafin ya kai watanni hudu, wasu sun haramta, wasu kuma sun halatta wasu sun karhanta.

Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin da bai kai wata hudu ba, idan akwai lalura, zubar da cikin Scler ba dole ya zama lalura ba, tun da ana iya haihuwarsa ya rayu, ya bautawa Allah ya amfani al'uma, don haka barin cikin shi ne ya fi, saidai idan kuka zubar kafin ya cika wata hudu saboda matsalar da kuke tunanin yaron zai iya fuskanta a rayuwarsa ba za'a ce kun yi laifi ba, tun da bai zama mutum ba, kuma ba za'a tashe shi ranar alkiyama ba.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

WANDA YA SAKI MATARSA CIKIN MAYE BATA SAKU BA

*_WANDA YA SAKI MATARSA A CIKIN MAYE, BA TA SAKU BA!!_*

                             *Tambaya*
Assalamu alaikum malam, tambaya ce dani. Mijina ne yasake ni sau biyu, sai yasha abin maye yace na zo nasameshi, nii kuma banzoba saboda bana son abin da yakesha na maye, shine yace idan banzoba a bakin aure na. Shin yaya auren mu? Allah ya saka da alheri. 

                                  *Amsa*
Wa'alaikum assalam, Malamai sun yi sabani game da aukuwar sakin wanda yake cikin maye:

1. Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa idan ya saki matarsa, tabbas sakin ya auku, saboda shan giya sabon Allah ne, kuma shi ya jawowa kansa, don haka ba za'a yi masa uzuri ba, wannan ita ce maganar Abu-hanifa da Malik da Shafii a daya daga cikin zantukansa.

2. Sakinsa bai auku ba, saboda lokacin da Ma'iz ya zo ya tabbatarwa Annabi S.A.W ya yi zina saida ya tambaye shi ko ka sha giya ne, kamar yadda Baihaki ya rawaito a Sunanul-kubrah, hakan sai ya nuna mashayin giya ba'a amsar maganarsa. 

Sannan an rawaito daga sayyadina Usman da Ibnu Abbas cewa: sakin mashayin giya ba ya aukuwa, kuma ba'a san wanda ya Saba musu ba a cikin Sahabbai.

Wannan ita ce maganar Imamu Ahmad da Zahiriyya da Ibnu Taimiyya.
Babban Muftin Saudiyya na waccan lokacin Sheik Abdulaziz bn Bazz da wasu Malaman suna rinjayar da magana ta biyu saboda mashayin giya bai san abin da yake fada ba, hakan sai ya sa ya yi kama da Mahaukaci wanda Alkalami ya saraya daga kan shi, kai har sallah ma an hana mashayin giya ya yi saboda ba ya cikin hayyacinsa, kamar yadda aya ta (43) a Suratu Annisa'i ta tabbatar da hakan.

Allah ne mafi sani.

Don neman karin bayani duba: Al-Mugni 7/289 da kuma Sharhul Munti'i 10/233

9/08/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

NAWA NE ZAKKAR MILIYAN DAYA?

*_NAWA NE ZAKKAR MILIYAN DAYA_*

                               *Tambaya*
Assalamu Alaikum

Tambaya daga jahar Taraba Suna so Dr ya amsa musu a wannan zaure mai albarka.

Wata ce take da Miliyan daya tana so tafir da zakka nawa ne ya kamata ta fitar dashi?

Allah ya tsare mana Dr ya yi mashi sakamako da gidan aljannah fiddaus.

                                 *Amsa*
Wa'alaikum assalam, Idan ta mallaki miliyan daya (1,00000), kuma su ka yi shekara daya a wajanta, to za ta fitar da dubu ashirin da biyar (25,000), wato daya cikin arba'in din abin da ya mallaka.

Allah ne mafi sani.

10/10/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

MENENE TAFARKIN QUR'AN DA HADITH?

*_MENENE TA'ARFIN QUR'ANI DA HADITH_*

*👈 القرآن لغة:* مصدر قرأ بمعني قرأ وهو الجمع والضم.

*👈 القرآن اصطلاحا :* هو كلام الله المنزل علي نبيه محمد (صلى الله عليه وسلم)المعجز بلفظه،المتعبد بتلاوته المنقول إلينا بالتواتر ،المكتوب بين دفتي المصحف، من أول سورة الفاتحة الي آخر سورة الناس.

*👈 الحديث النبوي* أو السنة النبوية عند أهل السنة والجماعة هو ما ورد عن النبي محمد صلى الله عليه وسلم من قول أو فعل أو تقرير أو صفة خـَلقية أو صفة خُلقية أو سيرة سواء قبل البعثة (اَي بدء الوحي والنبوة ) او بعده.

*MA'ANA: 👇👇👇*

*👉Al Qurani :* shine zancen Ubangiji wanda ya sauka ga Annabi Muhammad (SAW), mai mu'ujizar fada, tilawarsa ibadace, wanda jama'a masu yawa na daga sahabbai da tabi'ai suka ruwaito shi Izuwa  garemu, rubutacce a mushaf, daga farkon suratul Fatiha izuwa karshen suratun Naas.

*👉 Hadisi:* shine abinda ya samu daga Annabi (SAW) na daga magana, ko aiki, ko wani yayi abin a gabansa bai hanaba sai ma karfafa abin yayi, ko siffa ta halayya, ko siffa ta halitta , ko wani labari daga gareshi, sawa'un alokacin da Aka saukar masa da Annabta ko bayan lokacin.

✍ Rubutawa:- *Malama Ummu Hamdan wa Hameed*
Gabatarwa:- *Dalibin malama*

Share:

MIJIN DA YA SADU DA MATARSA KAFIN TAYI WANKAN HAILA

*_MIJINA YA SADU DA NI, KAFIN NA YI WANKAN HAILA?_*

                            *Tambaya?*
Assalamu alaykum, malam inada tambaya, malam mi ar hukuncin mace taqare haila batayi wanka ba mijin ta ya sadu da ita?

                                *Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Maganar mafi yawan malamai shi ne: ta jira sai ta yi wanka kafin su sadu, kamar yadda suka fahimta a aya ta 222 a suratul Bakara, amma Abu-hanifa yana ganin halaccin haka, saboda ya fahimci tsarki a ayar da yankewar jinin haila kawai.

Riko da mazhabar farko shi ne ya fi saboda Allah ya kira haila da cuta.

Babu wata kaffara ga wanda ya sadu da matarsa kafin ta yi wanka bayan yankewar jinin haila.

Allah ne mafi sani:

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.*_MENENE TA'ARFIN QUR'ANI DA HADITH_*

*👈 القرآن لغة:* مصدر قرأ بمعني قرأ وهو الجمع والضم.

*👈 القرآن اصطلاحا :* هو كلام الله المنزل علي نبيه محمد (صلى الله عليه وسلم)المعجز بلفظه،المتعبد بتلاوته المنقول إلينا بالتواتر ،المكتوب بين دفتي المصحف، من أول سورة الفاتحة الي آخر سورة الناس.

*👈 الحديث النبوي* أو السنة النبوية عند أهل السنة والجماعة هو ما ورد عن النبي محمد صلى الله عليه وسلم من قول أو فعل أو تقرير أو صفة خـَلقية أو صفة خُلقية أو سيرة سواء قبل البعثة (اَي بدء الوحي والنبوة ) او بعده.

*MA'ANA: 👇👇👇*

*👉Al Qurani :* shine zancen Ubangiji wanda ya sauka ga Annabi Muhammad (SAW), mai mu'ujizar fada, tilawarsa ibadace, wanda jama'a masu yawa na daga sahabbai da tabi'ai suka ruwaito shi Izuwa  garemu, rubutacce a mushaf, daga farkon suratul Fatiha izuwa karshen suratun Naas.

*👉 Hadisi:* shine abinda ya samu daga Annabi (SAW) na daga magana, ko aiki, ko wani yayi abin a gabansa bai hanaba sai ma karfafa abin yayi, ko siffa ta halayya, ko siffa ta halitta , ko wani labari daga gareshi, sawa'un alokacin da Aka saukar masa da Annabta ko bayan lokacin.

✍ Rubutawa:- *Malama Ummu Hamdan wa Hameed*
Gabatarwa:- *Dalibin malama*

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form