ADDU'AR NEMAN BIYAN BUKATA

_*TAMBAYA.*_

Assalamu alaikum.. Dan Allah Malam. Wani adduane Mutun zaiyi idan yana rokan Allah yabashi wani abu?

_*AMSA:*_

_Wa'alaikumussalamu Warahmatullah._

_Yana da kyau me addu'a Ya kaskantar da kansa ga Ubangiji, sannan ya cire kokonton amsar addu'ar a zuciyarsa._

_An karbo hadisi daga Buraidata (r.a) ya ce: *manzon Allah (ﷺ)* ya ji wani mutum yana cewa: *Allahumma inni as'aluka bi anni ash-hadu annaKa antallahu Laa ilaaha illa anta, al-ahadus samadu, alladzi lam yalid wa lam yulad wa lam yakun lahu kufwan ahad,* sai manzon Allah (ﷺ) ya ce: *“Lallai ka yi roƙo da sunan da Idan aka yi roƙo da shi ana bayarwa, kuma idan aka yi addu'a da shi ana amsawa".* mutane hudu suka ruwaito shi, Ibn Hibban ya inganta shi._

_Wannan hadisin na nuna mana kenan ana saurin amsa addu'ar Wanda ya yi amfani da wadannan 👆🏾sunayen kenan._

_Saboda haka 'yar uwa Idan za ki yi addu'a, sai ki fara ambaton wadancan sunayen, sannan sai addu'ar ta biyo baya._

Wallahu A'alamu.

_*✍🏾Ayyoub Mouser Geewerh.*_
_*📞08166650256*_

_*🕌Islamic Post.*_

_Ga masu bukatar kasancewa tareda mu a zauren mu na WhatsApp, sai su turo da cikakken sunan su zuwa Wannan number, 08166650256, a WhatsApp._

Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive