Thursday, 15 February 2018

WACCE JINI YA DAUKE MATA AMMA TAKI YIN TSARKI

_*Tambaya:*_

Assalamu alaikum,
Mallam dan Allah tambaya nake wai wacce jinin haila  ya dauke mata taqi yin wanka har tsawon kwana daya ko biyu,menene hukuncinta shin zata rama sallolin kwanakinne ko yaya zatayi,ngd.

_*Amsa:*_

Wa'alaikumussalamu Warahmatullah.

_Ya zama wajibi akanta ta rama sallolin da ta bari daga lokacin da Jinin ya dauke. Sannan ta yi ta istigfari don neman yafiya daga Ubangiji domin ta aikata babban saɓo._

_Saboda faɗin Annabi (ﷺ): *“Idan hailarki ta zo to ki bar sallah, Idan ta kare sai ki yi wanka, ki yi sallah."* bukhary ya ruwaito shi._

Wallahu a'alamu.

_*✍🏾Ayyoub Mouser Geewerh.*_
_*📞08166650256.*_

Daga zauren:

_*🕌Islamic Post.*_

_Ga masu bukatar kasancewa tareda mu a zauren mu na WhatsApp, sai su turo da cikakken sunan su zuwa Wannan number, 08166650256, a WhatsApp._


EmoticonEmoticon