Skip to main content

YA NEMI AURE A CIKIN IDDA

*_YA NEMI AURE A CIKIN IDDA ?_*

*_Tambaya_*

Assalamu Alaikum, Malam tambaya ne nakeso a taimaka a amsa mun akan sha’anin aure.

Malam mace ne tana zaune da mijinta sae ya kasance zaman sun babu dadi, kullum a cikin matsaloli iri-iri har ya kai ga takoma gidan iyayenta. Iyayenta sun matsa mata se da ta tilasta mijinta ya saketa, saboda suna da wani manufa akan idon ya saketa tsohon saurayinta
se ya aureta. 

Bayan ta matsawa mijinta akan lalle ya saketa se mijin nata ya amince akan zai kawo mata takardan sakin. Mallam a ranan da sukayi zai kawo mata takardan sakin, kawai sae ta samu tsohon saurayinta akan ta naso da
zaran ta gama idda se ya aureta. Mallam menene hukuncin wannan auren idon tagama idda ya aureta?

Na taba ji ance duk wanda ya nemi mace tana idda babu aure a tsakanin su har abada, Mallam don Allah ka taimaka mana da Karin bayani ?.

*_Amsa_*

Wa alaikum assalam,

in mutum ya nemi mace tana idda ya aikata haramun, kamar yadda aya ta: (235) a suratul Bakara ta tabbatar da hakan,saidai in an yi auran bayan ta gama idda auran ya inganta, amma an aikata zunubin nema. Malikiyya suna haramta mace ga mutum har abada in ya aure
ta cikin idda, ba in ya neme ta ba.

Allah ne mafi sani.

27/12/2016
Rubutawa: Abu - Manar.
Gabatarwa: Abu-Unaisa.

Ga duk mai sha'awar shiga wannan zaure na Darussunnah zai aika da sunan sa da jahar sa ta wadannan lambobi:

+2347035888158,
+2348099586379,
+2348139789030.

-Ta WhatsApp din zaka Tura ba ta SMS ba,
-Idan ka Tura a Lamba Guda daya To Kada Ka Tura Izuwa ga Daya Lambar,

Kai dai kawai Ka Jira Bayan Ka tura.

Comments