Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

SIMILARITIES BETWEEN THEM

Similarities between them.

Do you belong to their group? Ask yourself.

The Prophet (Peace be upon him) said: *You would tread the same path as was trodden by those before you inch by inch and step by step so much so that if they had entered into the hole of a lizard, you would follow them in this also. The companions (May Allah be please with them all) asked, Yaa RasooluLlah, do you mean Jews and Christians (by your word) "those before you?" He said: who else? (Saheeh Muslim)*

Is it true we are following their footsteps?

*Christian:* Sunday services without proof
*Muslim:* Asalatul Sunday without adilat

*Christian:* Vigil without proof
*Muslim:* Tahajjud alakojo without mutaba'ah

*Christian:* Congress night no evidence
*Muslim:* Lailatul Qadr without following the good examples

*Christian:* Jesus (Alayh Salaam)'s birthday (Christmas)
*Muslim:* Prophet Muhammad (Sala Allahu Alayh Wa Salaam)'s birthday (maulid nabiy)

*Christian:* New Year celebration
*Muslim:* Hijrah celebration/awareness

*Christian:* Musical instruments
*Muslim:* Bandiri and dhikr oloyi

*Christian:* Wake keeping/final burial + menu menu
*Muslim:* Firdau prayer + menu menu

Are we acting like them or not?

Hope you remember you are not under any obligation to follow anyone when he is against the Qur'an and Sunnah but compelled to follow the Prophet strictly because he doesn't say what pleases him except what Allah inspired him to say.

Yaa Ikhwan, ignore all innovations (bid'ah) because they lead to misguidance and misguidance leads to hell. No one prays for that.

Don't act like the Jews who bring and twist adilat (proofs) to suit themselves nor act like the Christians who don't have proofs but engage themselves in worship.

Remember you shall be call to account over all you did on earth even if it is as small as an atom.

*#TakeHeed

As Salaamu 'Alaikum Wa RahmatuLlah Wa Barakaatuh

Share:

MIJINA BAYA SON HAIHUWA KO YA HALATTA NA HANA MISHI KAINA?

*_MIJINA BA YA SON HAIHUWA, KO YANA HALATTA NA HANA SHI KAINA???_*

                                *Tambaya*
Assalamu alaikum.  Malam ina da matsala  tsakanina da mijina, baya son haihuwa ko saduwa muka yi  saidai  ya zubar  a waje,  Ga shi  kuma  yarinyar mu  daya, ita  ma  bai damu  da  ita  ba,  ina  da laifi  In na  hana  shi  kaina  ??

                                     *Amsa*
Wa'alaikum assalam To 'yar'uwa yana da kyau ki Sani cewa ya Halatta a samu tazara a tsakanin iyali, abin da musulunci  ya hana shi ne kin haihuwa kwata-kwata,  saboda babbar manufar aure shi ne hayayyafa, don a samu wadanda za su bautawa Allah.

Zubar da maniyyi a wajan Farji ya halatta saboda hadisin Jabir wanda yake cewa "Mun kasance muna yin azalo (zubar da maniyyi a waje yayin saduwa) a lokacin da Qur'ani yake sauka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4911.

Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: Bai halatta mace ta hana mijinta kanta ba saboda hujjar yana *AZALO,* tun da Alqur'ani bai haramta ba.

Saduwa rukuni ne babba a aure, Wannan yasa Annabi S.A.W ya ce: (Mace ta amsa kiran mijinta ko da tana kan kaskon tuya  ya kira ta, sannan la'ana ta tabbata ga  wacce mijinta ya yi fushi da ita, saboda ya  neme ta ba ta ba shi hadin-kai ba.

Kula da abin da mutum ya haifa wajibi  ne, ciyar da su kuma sadaka ne, Wannan yasa za ki dinga yiwa mijinki nasiha cikin  ladabi don ya fahimci gaskiya.

Allah ne mafi sani

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

Share:

SIFFOFIN JININ HAILA

*_INA SO NA SAN SIFFOFIN JININ HAILA?_* *Tambaya:* Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Don tambaya gare ni Kan wani ruwa ke fitomin amma kuma ba jini bane .INA ganinsa kasa kasa .babu wari ko qarni tare dashi .INA ganinsa idan nayi Azumi ko nayi aiki sosai .se marata tayi ciwo .shine yake fitomin. Yaya Azumi na da sallah ta take shin zan cigaba da yansu ? .sannan yana fitomin wajan qarfe 3 na rana ne . *Amsa:* Wa'alaikum assalam, mutukar ba jini bane, kuma ba baki ba ne, ba shi da karni, to ba zai hana sallah da azumi ba, zai yi kyau ki je wajan likita don ya duba lafiyarki, saboda abin da kika gani zai zama ba jinin haila ba ne, tun da ya rasa daya daga cikin siffofinsa. Allah ne mafi sani 7 Ramadan, 1437H (12/06/2016). Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Share:

INA SON KARIN BAYANI AKAN 'YAN TABLIG

*INA SON KARIN BAYANI AKAN 'YAN TABLIG ? ? ?* *Tambaya:* Assalamu alaikum . Da fatan Malam yana lafiya . Dan Allah ina son bayani akan tabligh da mutanen pakistan suka assasa kuma suke yawon da awa suna kiran mutane su fita da'awa na wasu kwanaki ko watanni. Mijina ya shiga kuma zai tafi kwana 40 amma ni hankali na ya ki kwanciya da hakan . Jazakallah . Ina binku ne a whatsapp. *Amsa:* Wa alaikum assalamu.To 'yar'uwa 'yan tablig wasu jama'a ne wadanda suka sanya da'awa i zuwa ga Allah babban aikinsu, kuma mutane ne masu gudun duniya, in sun je gari da'awa ba sa sauka wajan kowa, saidai şu shiga masallaci, suna dagewa sosai wajan da'awa duk alhamis a wasu kasashen, Muhammed Yûsuf Al-kandahlawy Ba'indiye wanda ya mutu a shekara ta:1364 bayan hijira shi ne ya kafata. Saidai akwai kura-kurai da yawa a tafiyarsu, daga cikin akwai : *1.* Karancin ilimi, ba şu damu şu yi ilimi mai zurfi ba, ko dan yaya şu ka Samu sai şu tsunduma çıkın da'awa. *2.* Ba şu damu da hana aikata mummuna ba, şuna karfafa da'awarsu ne wajan umarni da ayyukan da Allah ya ke so. *3.* Suna da karancin ilimin tauhidi, sun fi damuwa da bayanin falalolin ayyuka *4.* Suna kafa hujja da hadithai raunana da na karya. *5.* Wasu daga cikinsu suna sakaci da hakkokin iyalansu, saboda shagalarsu da da'awa. *6.* Sukan aibanta malaman da ba sa cikinsu, da rashin damuwa da Şakacı da da'awa. *7.*Karancin iliminsu yana jawo musu fadawa kura-kurai wajan fassara Al'qur'ani. In har kin san mijinki yana da karancin ilimi zai fi kyau ki sanya a tsawatar masa, game da bin su don kar ya fito kafin ya nuna, duk wanda ya zamar da kansa malami kafin ya isa, barnarsa za ta fi gyaransa yawa. Allah ne mafi sani *Amsawa* *DR. JAMILU YUSUF ZAREWA* 5/3/2016
Share:

INA RUBUTAWA DALIBAI WAEC MENENE MATSAYINA?

*INA RUBUTAWA DALIBAI WAEC, MENENE MATSAYINA ?* *Tambaya Assalamu alaikum mallam shin ya matsayi na ya ke ? Ina taimakawa wadanda suka dade da gama makarantar sakandare wajen rubuta waec neco etc, kasancewar ba za su iya ba, ko kuma wadanda ba su samu backgorund mai kyau ba a sakandarensu, to shin mallam hakan da matsala? *Amsa Wa alaikum assalam To malam rubutawa wani jarrabawa zai shiga cikin algus din da Allah ya haramta, domin za'a baiwa wani aikin da wani ya yi, ba tare da lalura ba, Annabi s.a.w. yana cewa a cikin hadisin Muslim mai lamba ta : 279, "Duk wanda ya yi mana algus to ba ya cikinmu" Rubutawa wani jarrabawa yana da illoli masu dimbin yawa, daga ciki : zai sanya a samu malaman da ba su cancanta ba, sannan zai jawo a cutar da al'umma, domin yanzu idan ka rubutawa wanda yake a fannin liktanci jarrabawa, ka ga zai iya zuwa ya bada magani ko ya yi tiyata ba bisa ka'ida ba. Sannan lalurar da mutane suke kafa hujja da ita ta cewa : dalibai da yawa ba za su shiga jami'o'i ba, in ba'a taimaka musu ta wannan hanyar ba, ba zai iya zama hujja ba a shari'ance, domin za su iya ware wasu watanni su yi karatun mutukar sun yarda da bukatar su ta shiga jami'ar, ga shi kuma barnar da take cikin rubuta musu jarrabawar ta fi maslahar shigarsu jami'a girma, saboda haka sai abin ya zama ya haramta, domin idan kana so ka gane abu haramun ne ko halal, to ka kalli barna da maslahar da take ciki, in maslaha ta fi yawa to ya zama halal, in kuma barna ta fi yawa to ya zama haram, kasancewar za'a iya samun malaman da ba su cancanta ba, yana nuna girman barnar da take ciki, ga kuma kasancewarsa dangwashe da algus din da Allah ya haramta, ga shi kuma zai jawo mutane su zama kasalallu masu ci da gumin wasu. Allah ne ma fi sani. *Amsawa* *DR JAMILU YUSUF ZAREWA* 26/10/2014
Share:

INA DA LAIFI IDAN MIJINA YA NEME NI NAKI YARDA SABODA BAYA BANI HAKKINA

*INA DA LAIFI IDAN MIJINA YA NEME NI NAKI YARDA DON BAYA BANI HAKKINA* *TAMBAYA* Assalamu alaikum. Malam nice mijina baya kuladani,Baya bani hakkin da Allah yace yabini. Idan yanemeni naki yarda,inada laifi ???? Wassalamu alaikum Wa'alaykumussalam *AMSA* Eh kina da laifi, don shari'a batace ki hana shi hakkin sa ba,don ya tauye miki naki hakkin, dole ne ki bashi na shi hakkin,sannan ki roki Allah akan naki hakkin, tare da bin dukkan wata hanyar da shari'a ta yadda don ganin kin samu. Wallahu A'alam *_Malam Nuraddeen Muhammad Mujaheed_*
Share:

An AYA A DAY 2

*IN THE NAME OF ALLAH, THE MOST BENEFICENT, THE MOST MERCIFUL*. 29 RABIUL THANI 1439. TUESDAY, 16 JANUARY 2018. *AN AYAH A DAY HELPS YOU UNDERSTAND ISLAM, INCREASES YOUR FAITH, PROTECTS YOU AGAINST EVIL & BRINGS YOU NEAR ALLAH*. *AYAH*. 7. And remember Allah's Favour to you & His Covenant with which He bound you when you said, "We hear & we obey. And fear Allah. Verily, Allah is All-Knower of that which is in (the secrets of your) breasts. 8. O you who believe! Stand out firmly for Allah as just witnesses & let not the enmity & hatred of others make you avoid justice. Be just: that is nearer to piety & fear Allah. Verily, Allah is Well-Acquainted with what you do. *QURAN CHAPTER 5 vs 7-8*. *HADITH* Abdullah Bin Amr: (May Allah be pleased with him) narrated that Rasuulilah (Sallallaho Allaihe Wasalam) said, "Convey my teachings to the people even if it were a single sentence, and tell others the stories of Bani Israel (which have been taught to you), for it is not sinful to do so. And whoever tells a lie on me intentionally, will surely take his place in the Hell fire. *SAHIH BUKHARI, VOL. 56: HADITH NO 4.667* *BROTHERS & SISTERS, WE LEARN FROM THE ABOVE HADITH THAT IT IS A GREAT SIN TO TELL A LIE ABOUT MUHAMMED (PEACE BE ON HIM), WHOEVER DOES SO WILL SURELY BE PLACED IN THE HELL FIRE*. *NEVER SPREAD MESSAGES/SOO CALLED HADITH CLAIMING TO BE FROM THE PROPHET UNTILL YOU HAVE FULL EVIDENCE TO SUPPORT IT ELSE STAY AWAY FROM IT TO PROTECT YOURSELF FROM SPREADING LIES & THE HELLFIRE* *LET US PERFORM OUR 5 DAILY SALLAT ON TIME & IN JAMAT, PAY OUR ZAKAT & REPAY OUR RAMADAN DEBT AS WE GRADUALLY APPROACH RAMADAN & ALSO MAKE DUA FOR OUR LATE DAD & MUM & ALL DECEASED*.
Share:

AN AYA A DAY!

AN AYAH A DAY HELPS YOU UNDERSTAND ISLAM, INCREASES YOUR FAITH, PROTECTS YOU AGAINST EVIL & BRINGS YOU NEAR ALLAH *AYAH*. 148. For every nation there is a direction to which they face (in their prayers). So hasten towards all that is good. Wheresoever you may be, Allah will bring you together (on the Day of Resurrection). Truly, Allah is Able to do all things. *QURAN CHAPTER 2 vs 148*. *HADITH* Masruq: (May Allah be pleased with her) narrated that, Aisha (May Allah be pleased with her) said that a Jewish came to her & mentioned the punishment in the grave, saying to her. 'May Allah protect you from the punishment of the grave. She then asked Allah's Apostle about the punishment of the grave. Rasuulilah (Sallallaho Allaihe Wasalam) said, 'Yes, there is punishment in the grave. She then added, after that I never saw Allah's Apostle but seeking refuge with Allah from the punishment in the grave in every prayer he prayed. *SAHIH BUKHARI, VOL. 23: HADITH NO 2.455* *PLS LET US PERFORM OUR 5 DAILY SALLAT ON TIME & IN JAMAT, PAY OUR ZAKAT & REPAY OUR RAMADAN DEBT AS WE GRADUALLY APPROACH RAMADAN & ALSO MAKE DUA FOR OUR LATE DAD & MUM & ALL DECEASED*.
Share:

HUKUNCIN YIN DILKA

*HUKUNCIN YIN DILKA* *Tambaya* Mace ta ba da jikinta ga mata 'yan uwanta don a yi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din nan wai haramun ne? Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta? In haramun ne kenan daga ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata 'yar uwarta mace ta gani ba? Jazakallahu khairaljazaaa. Amsa : To 'yar'uwa malamai sun yi sabani game da tsaraicin mace ga 'yar uwarta Musulma, akwai wadanda suka tafi akan cewa : bai halatta 'yar uwarta mace ta ga wani abu a jikinta ba, sai abin da ya saba bayyana a tsakanin mata, idan suna zaune isu-isu, kamar kafa da hannu da fuska da wuya da makamacin haka. Sai dai abin da mafi yawan malaman fiqhu suka tafi akai shi ne : al'aurar mace ga 'yar'uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya zuwa gwiwa, kamar yadda al'aurar maza take a tsakaninsu. Don haka bai hallata ta bari wata mace ta kalli sama da wannan wurin da aka iyakance ba, amma idan kafira ce matar to malamai sun yi bayani cewa ba za ta kalli wani abu ba, sai abin da ya saba bayyana, don haka sai a kula lokacin da za a je dilka wajen wacce ba musulma ba, don kada garin neman gira a rasa ido . Sannan a bisa wannan bayanin da kika yi, dilkar da kika siffanta za ta zama ba ta halatta ba, tun da za a ga abin da shari'a ba ta hallatata a gani ba. Allah ne mafi sani *Dr Jamil Zarewa* 24/10/2014
Share:

HUKUNCIN YIN ASIRIN MALLAKAR MIJI

HUKUNCIN YIN ASIRIN MALLAKAR MIJI : TAMBAYA TA 2437 ****************** Assalamu Alaikum malam barka da safia. malam ina cikin wani yanayi shine nace bari in nemi shawara gurin ka. Malam ina Shan wiya agidan aurena. Mujina ya kasance baya ganin darajata da kimata. ba so ko daya. Duk maganar da ta fito bakinsa sai ya fada min duk zafinta. Wulakanci kala kala. shekara Tara ina zaman hakuri darajar aure da darajar iyayena. Malam abin kamar an farraka mu. Duk Inda na samu addu'a don zaman lafia da soyayya yinta nake. Malam har da addu'o'in karya sihiri nayi sau dayawa. Mal shine aka ban shawara da in yanke faratuna  in kona in hada da jinin haila in bashi yaci zai daidaita. shine nace bari in tambaya shin ya dace inyi hakan. na gode Allah ya saka.in bukatar reply AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Baiwar Allah ki sani cewa zamanki agidan Mijinki zaman ibadah ne. Kuma ita ibadah ga mimini alkhairi ne. Kuma ba lallai ne dole sai komai ya tafi kamar yadda kike so ba. Dole sai kinyi hakuri da duk halin da kika tsinci kanki. Shi hakuri abu ne mai lada sosai kuma Mumini yana samun Qarin lada da daukakar darajoji ta, dalilin hakurinsa akan halin da ya tsinci kansa. Allah Madaukakin Sarki yace : "KAYI HAKURI SABODA HUKUNCI UBANGIJINKA.. ". Wata Mata takai Qarar mijinta wajen Manzon Allah (saww) akan halinsa. Sai Manzon Allah (saww) yace mata "KI DUBA, MIJIN NAN NAKI SHINE WUTARKI KUMA SHINE ALJANNARKI (WATO IDAN KINYI HAKURI DASHI KINYI MASA BIYAYYA ZAKI SAMU ALJANNAH. IDAN KUMA KIKA SA'BA MASA ZAKI SHIGA WUTA). Ki sani cewa Mijinki duk taurin kansa da wulakancinsa bai kai Fir'auna ba. Amma ga Matar Fir'auna nan ta shiga Aljannah saboda dalilin hakurinta da kuma Qardin imaninta. Kada ki biye ma Qawaye da 'Yan uwa Mata masu baki miyagun shawarwari. Hakika zasu sanyaki cikin ramin shirka ne da tsafe-tsafe irin na kafirci. Farce da kuma jinin haila duk Qazanta ne. Yadda kika san ke kanki ba zaki iya ci ba, to bai halatta ki sanya ma mijinki cikin abincinsa ba. Kuma bayan zaluncin dake cikkn yin hakan ga kuma Shirka ne da champe-champe. Kuma Allah ya hana. Kiji tsoron Allah ki tsaya bisa abinda yake na halal. Wato addu'a da kuma neman mafita awajen Allah. Tare da Qaurace ma bin miyagun shawarwari irin na bokanci. Ki duba amsar tambaya ta 1952 acikin jerin fatawoyin Zauren Fiqhu zaki ga mun rubuta halastattun hanyoyin da ake bi domin karya sihirin raba tsakanin ma'aurata. Kuma bayan shi ma mun sha yin rubuce-rubucen ayoyin karya sihiri. Ki binciko ta google ko facebook zaki samesu. Allah ya shiryi Mijinki ya ganar dashi gaskiya, Ya ha'da zuciyoyinku ku zauna lafiya ameen. WALLAHU A'ALAM. DAGA ZAUREN FIQHU (12-05-1439 29-01-2018).
Share:

HUKUNCIN KALLON KWALLON KAFA

*HUKUNCIN WASAN KWALLON KAFA!!!* *Tambaya:* Assalamu alaikum Malam ina tambaya ne akan kwallon qafa, akwai wanda yake neman aurena sana'arsa kenan, da ita yake ci yake sha yake komai, so malam ina kokonto akan wannar sana'ar tasa, kada ya kasance sai anyi auren inji cewa ba halal bane, tunda ana biyansa idan sukayi wasa, to shine malam ko a taqaice a sanar dani wani abu akai, saboda musan makamar mu, nagode. *Amsa:* Wa alaikum assalam To 'yar'uwa ına rokon Allah ya baki miji nagari, malamai suna kasa kwallo gıda uku: *1.* Kwallon da ake yi saboda motsa jiki, kamar mutum biyu su hadu, su yi ball don su tsinka jinin jikinsu, wannan kam ta halatta mutukar ba ta kautar daga ambaton Allah ba, ko kuma sallah idan lokacinta ya shiga. *2.* Kwallon da kungiyoyi biyu ko sama da haka za su hada kudi su sayı kofi wanda a karshe kungiya daya za ta dauka, wannan kam bai halatta ba, saboda daidai yake da CACA, kuma yana sabbaba gaba da kiyayya a tsakanin 'yan kwallo. *3.* Idan ya zama wani ne daban zai sanya Kofin, shi ma malamai sun ce haramun ne saboda asali musabaka da wasan tsere haramun ne, in ba abin da dalili na shari'a ya halatta ba, irin wannan kwallon kuma ba ta cikin abin da aka togace, sannan akwai barna mai yawa a cikinta, domin zai yi wuya a tashi irin wannan Kwallon wani bai ji ciwo ko ya karye ba, ga kuma haushi da kulewa da yake samun wanda aka kayar, wasu lokutan har da doke-doke tsakanin kungiyoyin guda biyu. Idan ya zama mijin da za ki aura yana yın nau'i na biyu ko na uku, to ya wajaba ki yi masa nasiha idan kuma yaki ji, to auransa akwai hadari saboda zai ciyar dake da haramun. Don neman karin bayani duba: - Fataawaa Al-lajna Adda'imah 3/238, - Fataawaa Muhammad bn Ibrahim 8/116. Allah ne mafi Sani. *Amsawa* *DR. JAMILU YUSUF ZAREWA* 12/11/2015.
Share:

HUKUNCIN MATAR DA TAYI AURE A CIKIN AURE

HUKUNCIN MATAR DA TA YI AURE A CIKIN AURE ASSALAMU ALAIKUM Game da tambayarka da ka yi akan matar da ta yi sabon-aure, ba tare da mijinta ya sake ta ba. Bayan bincike da tambayar malamai, na isa i zuwa ga hukunci kamar haka : 1. Abin da ta yi mummuna ne a shari'ar musulunci saboda ta yi aure cikin aure. 2. Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a matsayin mazinaciya take, saboda haka duk kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta zina ne. 3. Yaran da su ka Haifa da mijnta na biyu, 'ya'yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba a baya. 4. Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har yanzu ita matarsa ce saidai idan ya sake ta. 5. Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba tare da sake daura aure ba, saidai dole sai bayan ta tuba, domin ita a matsayin mazinaciyya take, kuma Allah ya hana auren mazinaciya. 6. Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari saboda girman zunubin da ta aikata. 7. Zai yi kyau su je wajan Alkali wanda ya san shari'a, domin ya yi musu hukunci. ALLAH YA KIYAYE MU DAGA IRIN WANNAN AIKA-AIKAR. Jamilu Zarewa 21/12/2012
Share:

HUKUNCIN LADANCI A SALLAH

HUKUNCIN LADANCI A SALLAH ? Tambaya : Assalamu alaikum Malam Meye hukuncin ladanci a sallah haram ne ko in akayi ba laifi ? Amsa: Wa alaikum assalam To dan'uwa mutukar liman yana daga murya, to yin ladanci bidi'a ne kamar yadda wasu malaman suka fada. Amma idan liman yana da lalura ko rashin lafiya ko kuma masallacin yana da girma ta yadda dukkan mamu ba za su ji muryarsa ba, to ya halatta, saboda a lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi rashin lafiya, sayyidina Abubakar ya kasance yana daga murya da kabbara saboda ba'a jin na Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito Allah ne mafi sani . Amsawa DR. JAMILU YUSUF ZAREWA 9/1/2014
Share:

HUKUNCIN KARI KO RAGI A CIKIN AL'ADA

HUKUNCIN KARI KO RAGI A CIKIN AL'ADA. Tambaya ASSALAMU ALAIKUM, da fatan mallam yana cikin koshi lfy,. dan ALLAH mal ina da tambaya, ni ce nake jinin haila kwana 5 na saba yi to amma wannan karan kwana 9 yayi min, bayan na yi wanka da kwana 3 sai kuma wani brown din abu tare da jini kadan yake fito min wanda har yanzu bai dena ba shi ne nake tambaya akan hukuncin wannan rikitaccen lamarin nawa. Nagode Amsa To malama ana iya samun ragi ko kari a jinin haila, don haka karin ba zai cutar ba, saboda shi ma haila ne, mutukar bai wuce iyaka ba, ta yadda zai zama jinin istihala, amma brown din da kike gani to mutukar bayan kin kammala haila ya zo, to ba ya cikinta, ba zai hana azumi ba da sallah, domin shi ne ake kira kudra, ita kuma kudra, idan ta zo bayan jinin haila, to ba ta cikinsa, kamar yadda hadisin Ummu Addiyya ya yi nuni, inda take cewa: "Mun kasance ba ma kirga kudra da sufra bayan tsarki a cikin haila. Bukhari 1\426 Allah ne mafi Sani Amsawa:✍🏻 Dr. Jamilu Yusif Zarewa. MARKAZUS SUNNAH
Share:

HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUNYI TSADA

*HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA ?* *Tambaya Assalamu alaikum.malam wata tambaya nake da ita Dr. Wai shin meye gasiyar hukuncin wanda ya sayi kaya a lokacin da suke araha ya boye da niyyar in sunyi tsada ya fito da su ya sayar dan ya sami riba mai yawa? Allah shi dada budi amin *Amsa Walaikum assalam To dan'uwa ya zo a hadisi cewa : "Ba wanda yake boye kaya sai mai zunubi" Tirmizi ya rawaito shi a : 3\567, kuma ya kyautata shi, saidai malamai sun yi sabani akan irin kayan da ya haramta a boye da wadanda ba su haramta ba : 1. Akwai wadanda suka tafi cewa : duk wani abu da mutane suke bukatarsa to bai halatta mutum ya siya ya ajjiye ba, da nufin sai yayi tsada ya fito da shi, don haka har tufafi da magunguna bai halatta a boye su ba, saidai idan ya siya ne da nufin ya yi amfani da su nan gaba. Ko kuma iyalansa, Wannan shi ne maganar Abu-Yusuf babban almajirin Abu-hanifa, kamar yadda yazo a littafin : Daurul-kiyam wal'aklak fil-islam shafi na : 295. Sannan ita ce maganar Malik a Mudawwanah kamar yadda ya zo a : 4\291. 2. Akwai malaman da suka tafi cewa ya halatta a boye abin da yake ba abinci ba ne da mutane za su ci su rayu, kamar barkono, zabibi, mai, da sauransu, saboda yawanci mutane suna cutuwa ne idan aka boye abinci. An rawaito wannan daga Abdullahi dan Mubarak da Sa'id dan Musayyib kamar yadda Tirmizi ya ambata a Sunan dinsa 3\567 sannan ita ce maganar Shafi'iyya da Hanbaliyya , kamar yadda ya zo a Raudatu Addalibiina 3\411 da kuma Almugni 4\154 Wasu malaman suna rinjayar da maganar farko, amma idan ba siyan abin ya yi ba, ya mallake shi ne ta wata hanya, ko kuma ya noma sai ya boye har ya yi tsada sannan ya siyar, to wannan bai haramta ba, ko da kuwa abinci ne, har wasu malaman ma sun hakaito ijma'in malamai akan halaccin haka, kamar yadda ya zo a Jami'ussagir shafi na : 481 Allah ne mafi sani *Amsawa* *DR. JAMILU YUSUF ZAREWA* 15/8/2014
Share:

HUKUNCE-HUKUNCEN MAI TAKABA

*HUKUNCE-HUKUNCEN MAI TAKABA* *Tambaya:* Assalamu alaikum wa rahmatullaah. gafarta Malam pls ayi mana bayani koda a takaice ne dangane da hukunce - hukuncen takaba... Na shiga wajen mahaifiya dazu, take cewa in tambaya mata Malamai tanadin shari'a akan wannan al'amari. Nagode *Amsa:* Wa alaikum assalam To dan'uwa ina rokon Allah ya jikan mahafinku, akwai hukunce-hukunce da suka shafi takaba, ga muhimmai daga ciki: *1.* Mai takaba za ta zauna a gidan mijinta ba za ta fita ba, har sai ta gama iddarta, wacce take wata hudu da kwana goma, kamar yadda aya ta: 234 a suratul Bakara take nuni zuwa hakan . *2.* Ba za ta saka kaya masu kyau ba, don haka za ta guji ado, kamar yadda hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304, ya yi bayanin hakan. *3.* Shari'a ta hana mai takaba ta sanya turare, kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 5343, ya tabbatar da hakan, *4.* Malamai suna cewa mai takaba ba za ta sanya tozali ba , kamar yadda hadisin Nasa'i mai lamba ta: 3565 ya bayyana hakan. *5.* An hana mai takaba yin lalle, kamar yadda hanin ya zo a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304. *6.* Idan wata bukata ta kama za ta iya fita daga gida, ko da rana ne ko da dare. *7.* Za ta iya yin Magana da mazan da ba muharramanta ba, idan bukatar hakan ta kama, saidai ta guji, sanyaya murya, kamar yadda aya ta 32 a suratul-ahzab ta hana sanyaya murya ga wadanda ba muharramai ba. *8.* Babu wani launi na kaya na musamman da aka shar'anta mata ta sanya, don haka, duk kayan da ba kwalliya a jikinsu ya halatta ta sanya su . *9.* Za ta iya yin wanka da sabulun da yake ba mai kanshi ba . *10.* Za ta iya zama ta yi hira da makusantanta, har ma za ta iya bude gashin kanta, idan su duka muharramanta ne . *11.* Bai halatta wani ya nemi auranta ba, har sai ta gama idda, saidai za'a iya yin jirwaye mai kama da wanka, kamar yadda aya ta 235 ta yi nuni zuwa hakan. *12.* Idan mai takaba tana da ciki, to iddarta ita ce: haife abin da take dauke da shi, kamar yadda hadisin Subai'a mai lamba ta: 5014 a Sahihul Bukhari ya tabbatar da hakan. Allah ne mafi sani. 27\3\2015 Amsawa: Dr Jamilu zarewa. Gabatarwa: Abu-Unaisa. Masu son kasancewa Damu ta shafin mu na Facebook Sai su bi ta wannan Rariya dake kasa 👇🏿👇🏿👇🏿 https://mobile.facebook.com/Darus-sunnah-Foundation-263121204166444/ Ga duk mai sha'awar shiga wannan zaure na Darussunnah zai aika da sunan sa da jahar sa ta wadannan lambobi: +2347035888158, +2348139789030. -Ta WhatsApp din zaka Tura ba ta SMS ba, -Idan ka Tura a Lamba Guda daya To Kada Ka Tura Izuwa ga Daya Lambar.
Share:

WALIMAR SAUKAR AL QUR'ANI

*_WALIMAR SAUKAR AL-QUR'ANI !!_*

                                 *Tambaya*
Slm. malam ko akwai nassi da yake nuni akan halarcin yin walimar saukar alqur,ani.??

                                     *Amsa*
To dan'uwa malamai suna cewa : Yin walimar saukar Alqur'ani ta kasu kashi biyu:

1. Wanda ya sauke Alquir'ani ya yi walima saboda godiya ga Allah, wannan kam ya halatta, saboda nassoshin da suka zo wadanda suke kwadaitarwa akan godewa Allah akan ni'imominsa.

2. Yin walimar saboda riya cewa ibada ce mai zaman kanta, wannan kam bidi'a ne tun da ba'a samu Annabi ﷺ da sahabbansa sun yi ba, don haka yana da kyau wanda ya yi walima ya bayyanawa mutane cewa ya yi ne don godewa Allah, ba wai don kasancewar hakan ibada ce mai zaman kanta ba.

Amma abin da aka rawaito cewa: Umar R.A ya yanka rakumi bayan ya gama haddace & kiyaye suratul-bakara, to wasu malaman hadisin sun raunana shi kamar Ibnu-kathir A Musnadul-farouk 2\571, saboda a cikin sanadinsa akwai Abu-bilal Al-ashhary, wanda Dara-kudni ya  raunana.

Allah ne mafi sani

Don neman Karin bayani duba fatawaa Allajna Adda'imah 2\488.

29/1/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

NAMIJI ZAI IYA YIN KUNSHI?

*_NAMIJI ZAI IYA YIN KUNSHI !!!_*

                              *Tambaya?*
Assalamu alaykum Warahmatullahi, Da fatan malam yana lafiya, Malam ya halatta namiji yayi kunshi?

                                   *Amsa:*

Wa'alaikum assalam, Ya halatta namiji ya yi kunshi a gemunsa da kansa, da launin da yake ba baki ba, kamar yadda Annabi ﷺ ya yi umarni a yiwa Abu-Khuhafa mahaifin sayyadi Abubakar R.A lokacin da ya musulunta ranar bude Makka a hadisin Ibnu Hibban mai lamba: 5472 Wanda Shuaibu Al'ar'na'u'd ya inganta.

Ya wajaba namiji ya nisanci duk wani kunshi da zai zama kamanceceniya da mata, saboda Allah ya la'anci namijin da yake kamanceceniya da mata kamar yadda ya tabbata a hadisin Tirmizi mai lamba ta: 2784.

 Yana daga cikin ka'diojin da ya kamata a sani cewa: Kamanceceniya da mata yana iya banbanta daga wuri zuwa wuri, yana sabawa daga al'ada zuwa wata.

Allah ne mafi sani

15/11/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

KO KASAN AL QUR'ANI ZAIYI CETON MA'ABOTANSHI RANAR KIYAMA?

*_KO KASAN ALQUR'ANI ZAIYI CETON MA'ABOTANSHI RANAR ALQIYAMA?_*
.
.
.
"An karbo daga Abu Umaamah Albaahiliy yace: Naji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yana cewa: " Ku karanta Alqur'ani don zai zo ranar alqiyama yana mai ceton ma'abotanshi."
(Muslim)

Wanda ya ajiye tilawa yayi maza ya dawo ya cigaba da tilawarshi ba dare ba rana.
Wanda bashi da tsari na tilawa arana toh ya dage yayi kuma ya kiyayeshi.

Ka tashi cikin dare mutane na barci kayi ibada to lallai hakan akwoi riban gaske.
Cikin shagulgulanka ka warema Alqur'ani lokacinsa.

Kina nan kin duqufa karatun littafan hausa, da kallace kallacen finafinai, anyi magana kince wai ba abin yi kana zaune shiru! ki kiyayi kanki da bata lokaci a aikin banza!

Abin mamaki wani sai ya zauna yaita cewa wai duk ya gaji bashi da abunyi? Yana nan jin wake wake da kallace kallace, zantuka marasa amfani! shin a ina ka aje Qur'aninka? ka manta zikirine? ko har ka gama tanadin guzurinka ne?

Kar ka kuskura ka bar Qur'ani duk rintsi don cikin yawan tilawar qur'ani tare da tadabburin ma'anoninsa, kiyayeshi ba dare ba rana, aiki dashi, yanada wani dadi da natsuwa dake mantar dakai dukkan wahalhalun rayuwa, damuwa، dagulewan al'amura, baqin ciki da sauransu.

♡Ga kuma tarin Laada ko wane harafi daya lada goma. zaka iya qirga yawan ladan? Kaga yanda Ubangiji keso ma bayinsa rahamarsa sai wanda yaqi.
Shaikhul Islam bnTaimiyyah Allah ya masa rahama yace: Banga wani abu da yake gyara hankali da ruhi, kuma yake kiyaye jiki, sannan yake qunshe da farinciki fiye da lizimtar kallon littafin Allah.

'Yan uwa mu yi kokarin ribatan lokutanmu ga ababen da zasu amfanemu.

Allah ya datar damu.

Rubutawa:- Umar Surajo Abu khadeejah
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

HUKUNCIN SHUGABA BAYA HALATTA HARAM

*_HUKUNCIN SHUGABA BA YA HALATTA HARAM !!!_*

                                *Tambaya:*
Assalamu alaikum malam ga tambayata. mutum ne ya ya kasanche yana son yayi karatu, amma kuma bashi da ishesh shen kudi, sai yaji gashi ana tallafawa wanda suka riga suka fara karatun, dan akara musu karfin guiwa wajen himma da kwazo. wato (shucorlarship) sai ya kasance shi kuma yana da hanya wanda zai iya samun wannan kudi na (scolarship in) duk da dai bai fara karatum ba,kuma asali, ana bawa wanda suka soma ne.Toh mallam ya hallatta ya karba har indai karatun zai fara da wannan kudi. amma kuma kudin, ba na jaharsa bane, na wata jaha ce da ban, amma yana da wata hanya da zai iya samun wannan kudi .toh! YAHALLATTA YACI KOKO A'A MALAM?

                                    *Amsa*
Wa'alaikum assalam, To abin da zan iya cewa shi ne: ya ji tsoron Allah, ya bi ka'ida wajan amsar kudin, kada ya amshi kudin da a kundin tsarin mulki ko dokar shariar musulunci ba'a bawa irinsa. In har aka ba shi kudin da ba'a bawa irinsa, saboda yana da hanya ko kafa a wurin to ya ci haramun, yana dağa cikin ka'idojin musulunci : حكم القاضي لا يحل حراما ولا يحرم حلالا don haka ko da shugaba ya halatta maka kudin hukuma wanda baka cancance su ba, ba zai zama halal a wajan Allah ba, wannan sai ya wajabta yın taka-tsantsan.

Allah ne mafi Sani.

28\1\2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

RUBUTACCIYAR TAMBAYAR SHEIKH JAFAR MAHMUD ADAM

*_RUBUCACCIYAR TAMBAYAR SHEIK JAFAR MAHMUD ADAM RAHIMAHULLAH_*

                               *Tambaya*
Assalamu Alaikum, Malam shin menene matsayin Auren Dole, idan aka yiwa yarinya in taqi auren matuqa tace ita bazata yarda ba, shin taqi biyayya ne ga iyayenta, ko kuma shin ta sabawa Allah da Manzonsa?

                                    *Amsa*
Wa'alaikumus Salamu Warahamatullah Wabrakatuhu.

To wannan bata sabawa Allah(SWA) kuma bata sabawa Manzon Allah ba, idan aka miki auren dole bakyaso kikace bazaki yarda ba, ba wanda kika sabawa, yanzu iyayenki basu da 'yanci da zasu miki auren dole, Manzon Allah ﷺ ya hanasu, yanzu sune suka sabawa manzon Allah da sukayi miki auren dole, ya kamata iyaye susan wannan, wai shin ma, menene kukeso da auren dole, wai shin so kuke 'yarku taje ta dawo-taje ta dawo, ku dai so kuke ta zauna, abin da iyaye bakwa ganewa idan yarinyaku taqi mutun, wallahi ko mutun shi AMIRUL MUMMININA ne shi, in Mace bata sonsa bazata taba masa da'a ba, dalili kuwa shine;

Hakan tafaru da Manzon Allah ﷺ, ya auri wata mata, bayan ya aureta, yasa aka kaita wani gidan gona, bayan an kaita ya shiga inda take tana zaune yace baza kizo ba, sai tacewa manzon Allah, a'a sai dai kai kazo nan gun, sai manzan Allah ya matsa kusa da ita, ya daga hannusa zai dora akanta sai tace masa "A'UZU BILLAHI MINKA" sai manzon Allah yariqe hannusa, bai dora hannunsa a kanta ba, sai yace mata kin nemi tsari ga wanda ake neman tsari gashi, shike nan tashi kitafi gidanku, shike nan sai manzon Allah ya saketa.

Hadisi nagaba, an sami wata yarinya: Iyayanta da suka aurar da 'yarsu atilas wanda taje ta fadawa manzon Allah ﷺ sai ya bata zabi in kinga dama ki zauna, in kinga dama akashe auren, sai tacewa Manzon Allah ﷺ zanyi haquri na zauna, dama nazo ne inma wannan tambayar kafadi amsar, dan iyaye susan basu da ikon tilassawa 'yarsu auren wanda bataso, hadisine ingaccece

Hadisin Mugid da Barira, Barira baiwace ta Nana Aisha, tana da mijinta mai suna Mugid, sai auren su ya mutu, mugid yana matuqar son  barira, barira tana matuqar kin mugid, idan yana zaune ta wuce idonsa akanta har sai ya daina ganinta,, har Manzon Allah ﷺ yake cewa Abdullahi Bn Abbas, baka mamakin inda Mugid yakeson Barira, ita kuma tana matukar kinsa, Abdullahi Bn Abbas yace wallahi nakula, Manzon Allah da kansa daya tausaya masa yaje gidan barira, manzon Allah yana da ikon da zaice tazo gidansa, amma da kansa ya tashi yaje inda take yace barira abin daya kawoni wajanki na zo ne danmu tattauna akan aurenki da mugid, sai ta sunkuyar da kanta tayi shuru, sai tacewa manzon Allah Umarni kake bani ko kuma kana bani shawara ne, manzon Allah yace a'a shawara nake baki, sai tace to bana sonshi. Ma'ana inda umarni yake bata dole ne, tabi umarnin manzon Allah, amma tunda shawarace tace bazan aureshi ba, haka aka hakura, Yadda manzon Allah yaji tausayin mugid da sai ya matsawa barira sai ta aure shi, tunda Manzon Allah ﷺ hakin da yake da shi akanka, akaina, yafi hakin da iyayenmu suke dashi akanmu.

           Dan haka iyaye akiyaye da yiwa 'yaya auren dole, duk wanda yarinya bata sonsa, ya takura mata  ya aureta wannan baisan mai yake ba gaskiya, Anan zamu dakata, sai kuma fitowa ta gaba

Rubutawa:- Sani Muhammad Olan (Diyayi)
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

KARFE NAWA LOKACIN SALLAR AZUHUR KE FITA

*_KARFE NAWA LOKACIN SALLAR  AZUHUR KE FITA?_*

                                *Tambaya*
Assalm mallm da Allah karfe nawa lokacin sallan Azahar ke fita ?.

                                    *Amsa:*
Wa'alaikum assalam, zababben lokacin Azahar (Muktari) yana fita ne idan tsawon kowanne Abu ya yi daidai da shi. Lokacin masu uzuri (Dharury) na sallar azahar yana karewa idan rana ta fadi.

Shari'a ba ta rataya lokutan sallah da karfe nawa ba, ta rataya su ne da álamomin yanayi kamar yadda aya ta: 78 a Suratul Isra'i ta tabbatar da haka.

Wannan ya sa babu Wata sallah da za'a iya sanya lokacin shigarta ko fitarta na din-din da agogon da muke amfani da shi a yanzu, saboda karfe da mintuna suna iya sabawa da yanayi dağa wani watan zuwa wani, misali wani lokacin rana ta kan fadi bayan karfe biyar, wasu lokutan kuwa sai bayan karfe bakwai, wannan yasa fahimtar shigar lokutan sallah da fitarsu ta hanyar alamomin da sharia ta sanya yake da muhimmanci.

Allah ne mafi sani.

25/01/2016.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

HIKIMOMIN DA AZUMI YA KUNSA

*_HIKIMOMIN DA AZUMI YA KUNSA_*

                                 *Tambaya:*
Assalamu alaikum Don Allah malam a taimaka min da bayani game da sababin da yasa ake yin azumi??

                                     *Amsa:*
Wa'alaikum assalam Azumi ginshiki ne, daga cikin turakun musulunci, wadanda addinin musulunci, ba zai cika ba sai da su, Allah da manzonsa sun yi umarni da shi, saboda wasu muhimman manufofi, ga wasu daga ciki:

*1.* Samun tsoron Allah, saboda mai azumi yana barin abin da yake so saboda Allah, hakan zai sa, ya kara samun tsoron Allah.

*2.* Samun kariya daga Shaidan, saboda azumi yana takure hanyoyin Shaidan, wannan ya sa zunubai suke karanci a Ramadan.

*3.* Tuna talakawa da wahalar da suke ciki, saboda duk lokacin da mai kudi ya dandana yunwa zai tuna halin da talakawa suke ciki.

*4.* Sabawa rai wajen barin abin da take so, da kuma hakuri akan abin da take sha'awa.

*5.* Kankare zunubai da kuma samun daukakar daraja, saboda azumi yana gyara zuciya, da kuma rai.

*6.* Samun lafiyar jiki, saboda azumi yana kariya daga cututtuka masu yawa, kamar yadda likitoci suka tabbatar da hakan.

*7.* Ta hanyar azumi mutum zai saba da yin aikin don Allah, saboda azumi sirri ne tsakanin Allah da bawansa.

Allah ne mafi sani

29/1/2013

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

HUKUNCIN YIN HUDUBA GA YARON DA AKA HAIFA

*_HUKUNCIN YIN HUDUBA GA YARON DA AKA HAIFA_*

                             *Tanbaya*
Assalamu alaikum malam
DAN ALLAH INA NEMAN KARIN BAYANI AKAN HUDUBAR SUNA DA YADDA AKE YI.

                                  *Amsa*
Wa'alaikum assalamu Game da kiran sallah da ikama a kunnen yaron da aka haifa wannan bai inganta ba, saboda hadisin kiran sallah Tirmizi ya rawaito shi da sanadi mai rauni, Baihaki kuma ya rawaito shi a Shu'abul-imani sai dai a sanadinsa akwai maruwaita guda biyu wadanda ake tuhumar su da karya, amma hadisin da ya zo akan yin ikama kuwa, to malamai sun ce hadisi ne na karya.

*SAI DAI YA TABBATA A SUNNAH ANA TAUNA DABINO A SAWA YARO  A BAKI.*

Allah ne mafi sani.

31/12/2013

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

AZUMIN KWANA UKU A WATAN RAJAB

*_AZUMIN KWANA UKU A WATAN RAJAB!!!_*

                              *Tambaya*
Assalamu alaikum inayiwa malan fatan alkhairi, tambayata iyace :- Azumi uku na tsakiyar wata wanda ake kira " Ayyaamul beed " na watan Rajab
To ya hallata a muslunci?.

                                  *Amsa*
Wa alaikum assalam, Ya tabbata a cikin hadisin Tirmizi mai lamba ta: 761: Annabi ﷺ ya cewa Abu-zarrin idan za ka yi azumi, to ka azumci ranar sha uku da ranar sha hudu da sha biyar daga kowanne wata, watan Rajab Daya ne dağa cikin watannin musulunci za'a iya azumin da ya tabbata a ragowar watanni a cikinsa, saidai kawai watan bai kebanta da Wata falala ba.

Allah ne mafi sani.

21\4\2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

HUKUNCIN WANDA YA AURI MACE SABODA KYANTA

*_HUKUNCIN WANDA YA AURI MACE  SABODA KYANTA??_*

                              *Tambaya*
Malam : Akwai wani hadisi da yake Magana kan cewa kowa ya auri mace kawai dan kyanta Allah zai hana masa jindadin kyan, ko dan kudinta kawai Allah zai hana masa jin dadin kudin,.... shin kuwa hadisin akwai shi kuma ya inganta?

                                 *Amsa*
Ga Yadda Hadisin yake: Duk Wanda ya Auri Mace saboda kudinta, Allah zai kara masa Talauci, duk Wanda ya Auri Mace saboda kyawunta Allah zai kara masa muni.

Saidai a cikin hadisin akwai Abdussalam bn Abdulkuddus wanda yake rawaito hadisan karya, don haka hadisin bai inganta ba, kuma ba za'a kafa hujja da shi ba.

Allah ne mafi sani

26/1/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

NA KARBI KYAUTA DAGA KARUWA KO YA HALATTA NA AMFANA DA ITA?

*_NA KARBI KYAUTA DAGA KARUWA, KO YA HALATTA NA AMFANA DA ITA?_*

                              *Tambaya*
Assalam,malam akwai hujjar da ta kore kar6ar kyauta daga karuwa ?

                                    *Amsa*
Wa'alaikum salam, Tabbas Annabi ﷺ ya haramta cin kudin karuwa, wanda ta samu ta hanyar karuwanci, kamar yadda hakan ya zo a hadisi mai lamba: 1567, wanda Muslim ya rawaito.

Saidai malamai suna cewa: Duk wanda ya zama a cikin dukiyarsa akwai halal da haram, to idan ya maka kyauta za ka iya amsa, mutukar ba ka tabbatar daga haram ya dauko ya baka ba, saboda Annabi ﷺ ya yi mu'amala da yahudawa kuma a cikin dukiyarsu akwai halal da haram, har ma ya mutu silkensa na yaki yana jingene a wajansu.

Don neman Karin bayan duba Al-muhallah na Ibnu Hazm 6/184.

Allah ne mafi sani

26/1/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

TAURIN BASHIN MAWADACI ZALUNCI NE

*_TAURIN BASHIN MAWADACI ZALUNCI NE!!!_*

                               *Tambaya:*
Assalamu alaikum, akramakallahu tambaya ta akan bashi ne, akramakallah ya muslunci ya tsara akan wadannan ka ke bi bashi amma sun hanaka kuma suna da kudin. Wace azaba Allah ya tanadarwa wadan da basa biyan bashi. nagode daga

                                  *Amsa:*
Wa'alaikum assalam To dan'uwa taurin bashi mawadaci zalunci ne yana halatta mutuncinsa da yi masa ukuba kamar yadda hadisin da Imamu Ahmad ya rawaito a Musnad a lamba ta:17945, kuma Ibnu Hajar ya kyautata ya tabbabtar da hakan.

Duk wanda ya karbi bashin mutum da niyyar zai mayar masa, Allah zai taimaka masa wajan mayarwa.

Ya halatta ka kai wanda kake bi bashi kotu, don ta amsar maka hakkinka, mutukar ka tabbatar yana da shi amma ya hana ka, saboda hadisin da ya gabata.
In har aka tabbatar da cewa rashin kudi ne ya hana shi biya, ya wajaba a jira har ya samu, kamar yadda aya ta :280  a suratul Bakara take nuni zuwa hakan.

Biyan bashi akan lokaci yana da mutukar muhimmanci, saboda wanke tukunya don gobe yana saukake girki.

Allah ne mafi sani.

27\1\2016.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

HUKUNCIN YIN KIRAN SALLAH BA TARE DA TSARKI BA

*_HUKUNCIN YIN KIRAN SALLAH BA TARE DA TSARKI BA!!!_*

                                *Tambaya*
Assalamu Alaikum, malam ko ya halatta mutumin da yake da janaba ya kira sallah ??

                                   *Amsa*
To dan'uwa wasu daga cikin malamai suna cewa tsarki ba sharadi ba ne yayin kiran sallah, saboda babu wani nassi ingantacce wanda ya nuna hakan, don haka ya halatta ga mai janaba, da mai karamin kari su yi kiran sallah, saidai abin da ya fi shi ne yin cikakken tsarki kafin kiran sallah, saboda fadin Annabi ﷺ "Ina kin na ambaci Allah alhali ba ni da tsarki", kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 16, kuma Albani ya inganta shi a Sahihu-sunani Abi-dawud 1\16.

Don neman Karin bayani duba: Fathul-bary 3\113 da Majmu'u fataawaa wa makaalatin mutanawwi'a 10\338.

27/1/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

FIVE PILLARS OF ISLAM ACCORDING TO THE BIBLE

FIVE PILLARS OF ISLAM ACCORDING TO THE BIBLE: 1. Shahada(mark 12:29) 2. Salat(matthew 26:39) 3. Zakat(Hebrew 10:24) 4. Fasting(Matthew 4:1-1) 5. Hajj(Psalm 84:5-6) ALBAYAAN MUSLIMS PREACHERS ASSOCIATION THE TRUTH FROM THE BIBLE ABLUTION IN THE BIBLE Leviticus. 19:27 Leviticus. 21:5 Jeremiah. 9:25 1 chronicles. 19:5 Exodus. 30:17 Exodus. 40:30 John. 13:4 HOW TO DRESS IN THE BIBLE Exodus. 28:1 WOMEN SHOULDN'T SPEAK IN CHURCH Ezekiel. 13:17 Corinthians. 14:34-38 Tito. 2:3 1 Timothy. 2:11 Revelation. 2:19 1 timothy. 2:8 HOW TO WORSHIP IN THE BIBLE Genesis. 17:1 Psalm. 95: 6 Ezekiel. 43:3 Kings. 18:39 Psalm. 5:7 Numbers. 20:6 Nehemiah. 8:6 Matthew. 26:36 Matthew. 17:1 Revelation. 7:9 IS WINE/PORK ALLOWED Leviticus. 11:7 Deuteronomy. 14:8 Isaiah. 65:3 Proverbs. 31:3 Isaiah. 4:11 Amos. 6:5-7 Habakkuk. 2:15 Leviticus. 10:8 Isaiah. 66:17 PROPHECY OF MOHAMMED IN THE BIBLE Genesis. 49:10 Genesis. 16:7-14 Deuteronomy. 18:18 Deuteronomy. 34:10 Jeremiah. 34:18 Isaiah. 21:13 Isaiah. 19:19 Daniel. 7:13 Mathew. 21:33-43 Galatians. 4:21 John. 1:19-22 John. 14:30 John. 16:7-14 Act. 7:37 John. 14:15 Revelation. 7:9-12 Revelation. 19:10-16 SHARIAH IN THE BIBLE Deuteronomy. 6:1 Deuteronomy. 13:-1-11 Deuteronomy. 22:13-22 Deuteronomy. 21:18-21 Deuteronomy. 22:25 Mathew. 15:3 Joshua. 1:18 Hebrews. 10:28 Leviticus. 20:9-16 Leviticus. 20:27 According to the Islamic doctrine, Muslims should believe in all the prophets sent by Allah almighty among the prophet are Adam, Noah, Jacob, Moses, Jesus, Mohammed and lives (Quran 3:84) Any person or group or pastor interested in discussion or any debate concerning these should contact this number or address below. TYPED BY. Faisal Mohammed Suleiman LOCATION:Asenua behind unity oil filling station or Fowade back of noble dream bank off momponteng. Road Every:Monday From:5:30am TO 6:00am Albayaan Muslims preachers At Alpha radio 104.9 MOBILE NUMBER. +233242886567/+233574226741 or +233278384156 share it to save someone's life Asalamualiakum warahmatullahi wabarakaatuh
Share:

Qur'an Maganar Allaah Ce

ALKUR'ANI MAGANAR ALLAH CE KUMA WAHAYIN SHI: 1. Ba a siffanta Alkur'ani Mai girma da cewa: Shi halitta ce, ko kuwa shi mai halitta ne ba, a'a abin da ake cewa game da shi shi ne: Alkur'ani Mai girma magana ce ta Allah, kuma wahayi ne naSa, wannan shi ne mazhabar Magabata; Imam Malik da waninsa. 2. Imam Husain Al-Bagwiy ya ce cikin littafinsa Sharhus Sunnah 1/186:- ((وقد مضى سلف هذه الأمة وعلماء السنة على ان القرءان كلام الله ووحيه ليس بخالق ولا مخلوق، والقول بخلق القرءان ضلالة وبدعة لم يتكلم بها احد في عهد الصحابة والتابعين رحمهم الله)). Ma'ana: ((Magabatan wannan Al'ummah tare da Malaman Sunnah sun tafi a kan cewa: Alkur'ani Maganar Allah ce kuma wahayin Shi, sam ba mai halitta ba ne ba kuma wanda a ka halitta shi ba ne. Maganar cewa Alkur'ani halitta ce bata ce, kuma bidi'ah, babu mutum daya a zamanin Sahabbai da Tabi'ai Allah Ya yi musu rahama da ya taba hurta wannan maganar)). 3. Imamul Baihaqiy ya ruwaito cikin Sunan Athari na 21,415 daga Yahya Bin Khalaf Al-Muqri ya ce:- ((كنت عند مالك بن أنس، فجاءه رجل فقال: ما تقول فيمن يقول: القرءان مخلوق؟ فقال: زنديق كافر فاقتلوه)). Ma'ana: ((Na kasance a gurin (Imam) Malik Dan Anas, sai wani mutum ya zo ya ce: Me kake cewa game da mutumin da yake cewa: Alkur'ani halitta ce? Sai (ya amsa) ya ce: Zindiki ne kafuri ku kashe shi)). 4. Imamuz Zahbiy ya ce a cikin littafin "Mukhtasarul Uluwwi Lil Aliyyil Gaffar" shafi na 75: Maimuun Bin Yahya Al-Bakriy ya ce:- ((قال مالك: من قال القرءان مخلوق يستتاب فان تاب وإلا ضربت عنقه)). Ma'ana: ((Malik ya ce: Duk wanda ya ce Alkur'ani halitta ce, to a neme shi da ya tuba, in ya tuba shi ke nan, in kuma bai tuba ba sai a sare wuyansa)). Allah muke roko da Ya tausaya mana Ya tsare mu daga fadawa cikin bidi'o'in Mu'utazilawa, da ma sauran bidi'o'in. Ameen.
Share:

1+1

We live in a world where 2 + 2 = 5, Just as 1 + 1 +1 = 1 If you are confused 😕, Who is god? Jesus Is Jesus the son of Mary? Yes Who created Mary? God. Who is God? Jesus Jesus is the begotten son. Yes Who is his father? God. Who is God? Jesus. Jesus is a servant of God? Yes Who is God? Jesus. Jesus died on the cross? Yes Who resurrected him? God. Who is God? Jesus Jesus is a messenger? Yes Who sent him? God. Who is God? Jesus. Did Jesus worship while on earth? Yes Whom did he worship? God. Who is God? Jesus. Did God have a beginning? No.... Then who was born on 25 DEC?Jesus. Who is God? Jesus. Where's God? In heaven How many are there in heaven?Only one God. Where's Jesus? He is sitted on the right hand of his father. Who is God? Jesus. Then how many are they in heaven? Only one God Then how many seats? One Where's Jesus? Seated next to God. Then how are they seated? On one chair Its only understood by those with the holy spirit. Who is God? Jesus. Ha haha what a confusion. So beautiful to be a Muslim, Allah (SWT) have mercy on us all and grant us His straight path for us not to go astray FIVE PILLARS OF ISLAM ACCORDING TO THE BIBLE: 1. Shahada(mark 12:29) 2. Salat(matthew 26:39) 3. Zakat(Hebrew 10:24) 4. Fasting(Matthew 4:1-1) 5. Hajj(Psalm 84:5-6) ALBAYAAN MUSLIMS PREACHERS ASSOCIATION THE TRUTH FROM THE BIBLE ABLUTION IN THE BIBLE Leviticus. 19:27 Leviticus. 21:5 Jeremiah. 9:25 1 chronicles. 19:5 Exodus. 30:17 Exodus. 40:30 John. 13:4 HOW TO DRESS IN THE BIBLE Exodus. 28:1 WOMEN SHOULDN'T SPEAK IN CHURCH Ezekiel. 13:17 Corinthians. 14:34-38 Tito. 2:3 1 Timothy. 2:11 Revelation. 2:19 1 timothy. 2:8 HOW TO WORSHIP IN THE BIBLE Genesis. 17:1 Psalm. 95: 6 Ezekiel. 43:3 Kings. 18:39 Psalm. 5:7 Numbers. 20:6 Nehemiah. 8:6 Matthew. 26:36 Matthew. 17:1 Revelation. 7:9 IS WINE/PORK ALLOWED Leviticus. 11:7 Deuteronomy. 14:8 Isaiah. 65:3 Proverbs. 31:3 Isaiah. 4:11 Amos. 6:5-7 Habakkuk. 2:15 Leviticus. 10:8 Isaiah. 66:17 PROPHECY OF MOHAMMED IN THE BIBLE Genesis. 49:10 Genesis. 16:7-14 Deuteronomy. 18:18 Deuteronomy. 34:10 Jeremiah. 34:18 Isaiah. 21:13 Isaiah. 19:19 Daniel. 7:13 Mathew. 21:33-43 Galatians. 4:21 John. 1:19-22 John. 14:30 John. 16:7-14 Act. 7:37 John. 14:15 Revelation. 7:9-12 Revelation. 19:10-16 SHARIAH IN THE BIBLE Deuteronomy. 6:1 Deuteronomy. 13:-1-11 Deuteronomy. 22:13-22 Deuteronomy. 21:18-21 Deuteronomy. 22:25 Mathew. 15:3 Joshua. 1:18 Hebrews. 10:28 Leviticus. 20:9-16 Leviticus. 20:27 According to the Islamic doctrine, Muslims should believe in all the prophets sent by Allah almighty among the prophet are Adam, Noah, Jacob, Moses, Jesus, Mohammed and lives (Quran 3:84)
Share:

YAYA YA KAMATA NAYI DA RIBAR BANKIN DA NA AMSA

*YA YA KAMATA NAYI DA RIBAR BANKIN DA NA AMSA ?* *Tambaya* Assalamu alaikum malam Menene ra'ayin malaman Sunna akan kudin da banki suke karawa mutane a cikin Saving account? Ya yakamata ayi amfani dasu? Allah ya karemu daga aikata kuskure. *Amsa* Wa alaikum assalam Farko dai ya haramta ga musulmi ya bude accout din da za'a dinga saka masa kudin ruwa a ciki, saboda Allah ya haramta cin riba ya kuma yi shirin yaki da Wanda bai daina ci ba à cikin aya ta 275 a Suratul Bakara da ayoyin da suka zo bayanta. Annabi SAW ya la'anci mai cin riba da wanda ya rubutata da wanda aka wakilta da wanda ya yi shaida akanta. Kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi ingantacce. Idan mutum ya amshi Interest din Banki to ya wajaba ya tuba ga Allah da niyyar ba zai sake amsa ba, tun da Allah ya Hana. A zance mafi inganci zai iya amfani da kudin wajan yin aikin da zai amfani jama'a kamar gina Asibitoci ko kwatar da ruwa zai wuce ko kuma hanyoyin da mutane za su bi su wala, saidai ba shi da ladan wannan aikin da ya yi, saboda ba dukiyarsa ba ce. wannan ita ce maganar manyan malaman musulunci na wannan zamanin kamar Sheik Ibnu Bazz da sauransu. Allah ne mafi sani *amsawa* *DR. JAMILU YUSUF ZAREWA* 27/07/2017
Share:

YAWAITA SALATI GA MANZON ALLAAH A DAREN JUMA'A DA YININ JUMA'A

YAWAITA SALATI GA MANZON ALLAH ﷺ A DAREN JUMA'A DA YININ JUMA'A Yana daga cikin falalar Daren juma'a da yinin juma'a,Manzon Allah ﷺ ya umarnin mu yawaita yi masa salati a wannan lokuta,saboda Hadisin Anas bn Malik رضي الله عنه yana cewa:Manzon Allah ﷺ yace: (Ku yawaita yi mini. Salati a ranar juma'a da daren Juma'a,duk wanda yayi min salati guda daya,Allah zai yi masa salati guda goma) @صحيح الجامع DAGA CIKIN FALALA SALATI GA MANZON ALLAH ﷺ Wanda yayi Manzon Allah satai guda daya Allah zai yi masa salati guda goma @حسنه الألباني - الصحيحة 1407] Mafi kusanci da chanchanta ga Manzon Allah ﷺ a ranar alqiyama,sune masu yawaita yi masa salati @حسن لغيره - صحيح الترغيب1668 Manzon Allah ﷺ yana cewa,ku yawaita yi min salati, domin Allah ya wakilta wani Mala'ika na musamman a wajan Qabarina,babu wanda zaiyi min salati face wannan mala'ikan yace dani, wane dan wane yayi mata salati yanzu @حسنه الألباني الصحيحة 1530 Manzon Allah ﷺ wani mai zuwa ya zo min daga wajan Ubangijina,sai yace; Duk wanda yayi maka salati daga guda daya daga cikin al'ummarka,Allah zai rubuta masa kyakkyawan aiki guda goma,Kuma a kankare masa laifuka guda goma,kuma a daukaka Darajarsa sau goma,kuma a maida masa salatin shima ayi masa @صححه الألباني - صحيح الجامع | 57 ] Ku yawaita yi min salati ku jajirce cikin yawaita addu'a,kuma kuriqa cewa (اللهم صلِّ على محمد وعلى آل محمد، وبارك على محمد وآل محمد كما باركت على إبراهيم وآل إبراهيم إنك حميد مجيد) @صححه الألباني - صحيح الجامع | 3783 ] Wanda yayi salati guda daya,Allah zai yi masa salati goma @صححه الألباني - صحيح الجامع |6358] Babu wanda zaiyiwa Manzon Allah ﷺ Sallama,face Allah ya mayarmin da ruhina har sai na mayar masa da sallama @حسنه الألباني - صحيح أبي داود | 2041] Allah ne mafi sani Allah bamu ikon cika Umarnin Manzon Allah ﷺ da yawaita salati a gareshi.
Share:

YAWO BABU DANKWALI A TSAKAR GIDA

YAWO BABU DAN-KWALI A TSAKAR GIDA ? Tambaya: Assalamu alaikum,Allah gafarta malam shin zan iya yawo acikim gida ba dan kwali? Amsa: Mace zata iya yawo babu Dan kwali idan tana tsakanin 'yan uwanta mata musulmai saboda al'aurar mace ga 'yar uwarta mace musulma tana kasancewa ne tsakanin guiwa zuwa cibiya, mutukar akwai mazan da ba muharramai ba to bai halatta ta bude kanta ba, saboda dukkan mace Al'ura ce in ban da fuska da tafukan hannu. Allah ne mafi sani. Dr. Jamilu Zarewa 24/1/2016
Share:

ZAN AURI MA'AIKACIN BANKI AMMA INA TSORON CIN HARAM

ZAN AURI MA'AIKACIN BANKI, AMMA INA TSORON CIN HARAM ? Tambaya: Assalamu Alaikum, Dr. Akwai wata kanwata da wani ma'aikacin banki yake so ya aura, ta bangaren mu'amalarsa za mu ce Alhamdulillah, to shi ne take neman menene halarcin auransa a shari'a? Saboda tana tsoron kar ya rika ciyar da ita da dukiyar haramun. Amsa : To dan'uwa Annabi s.a.w. yana cewa : "Allah ya la'anci mai cin riba da mai rubutata, da wadanda suka yi shaida akan haka" Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1598. Hadisin da ya gabata yana nuna haramcin aiki a bankunan da suke mu'amala da riba, saboda ma'aikacin banki zai rubuta ko kuma ya shaida, ko ya taimaka wajan tsayuwar harokokin banki, kamar mai gadi, da dan aike . . Duba fatawaa Allajanah adda'imah 15\41, da Fataawaa Islamiyya na Ibnu-uthaimin 2\401. Idan ya zama abin da ma'aikacin banki yake amsa haramun ne, kuma ba shi da wata sana'a sai wannan, akwai hadari a auransa, saboda zai ciyar da matarsa da haramun Malamai suna cewa duk mutumin da yake samun kudi ta hanyoyin halal da haram, idan ya maka kyauta za ka iya amsa, saboda Annabi s.a.w. ya yi mu'amala da yahudawa, kuma a dukiyarsu akwai halal da haram, amma in ba shi da wata sana'a sai ta hanyar haram to ba za ka iya cin dukiyarsa ba. Wasu malaman sun halatta aikin banki a bankuna masu kudin ruwa da niyyar kawo gyara, idan niyyar mutum ta tsarkaka. Allah ne mafi sani . Jamilu Zarewa 10\4\2015
Share:

ZAN IYA RARRABA KAFFARAR RANTSUWA

*ZAN IYA RARRABA KAFFARAR RANTSUWA ?* *Tambaya* Assalamu alaikum, Dr. don Allah a amsa mana wannan tambayar. Ya halatta in raba kaffarar azumin rantsuwa? *Amsa* Wa alaikum assalam, ya halatta a rarraba azumin kaffarar rantsuwa, saboda aya ta: 89 a suratul Ma’ida da ta yi bayanin kaffarar rantsuwa ba ta kayyade azumi ukun da jerantawa ba, wannan yasa da yawa daga malamai suka tafi akan halaccin rarraba azumin. Ba’a yin azumi uku a kaffarar rantsuwa sai ga wanda ya kasa ciyar da miskinai goma ko tufatar da su, kamar yadda ayar ta yi bayani dalla-dalla akan haka. Allah ne mafi sani *Dr, Jamilu Zarewa* 1/01/2017
Share:

ZAN IYA WANKAN JANABA BA TARE DA ALWALA BA

*ZAN IYA WANKAN JANABA, BA TARE DA ALWALA BA ?* *Tambaya:* Assalamu alaikum. Tambayata Anan shine:. Menene hukuncin yin wankan janaba batare da yin alwala ba? *Amsa:* Wa alaikum assalam Ya halatta ayı wankan janaba ba tare da alwala ba, kamar yadda ya zo a hadisin Ummu-salama, Saboda Annabi S,A.W. ya siffanta mata wankan janaba da cewa: "Ya ishe ki, ki zuba ruwa sau uku akan kı sannan ki zuba ruwa a duka jikinki, in kika yi haka, kin tsarkaka" kamar yadda Abu-dawud ya rawaito, kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lam bat a: 251. A cikin wannan hadisin babu alwala, wannan sai ya nuna wankan ya yi da waccar sifar da kika tambaya. Saidai sifar da ta zo da alwala a hadisin Nana A'isha ita ce mafi cika, kamar yadda malamai suka bayyana. Allah ne mafi sani. *Amsawa*✍🏻 *DR. JAMILU YUSUF ZAREWA* 6\3\2016
Share:

Today's Reminder

عَنْ اِبْنِ مَسْعُودٍ ‏- رضى الله عنه ‏- قَالَ: قَالَ رَسُولُ اَللَّهِ ‏- صلى الله عليه وسلم ‏-{ لَا يَحِلُّ دَمُ اِمْرِئٍ مُسْلِمٍ; يَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اَللَّهُ, وَأَنِّي رَسُولُ اَللَّهِ, إِلَّا بِإِحْدَى ثَلَاثٍ: اَلثَّيِّبُ اَلزَّانِي, وَالنَّفْسُ بِالنَّفْسِ, وَالتَّارِكُ لِدِينِهِ; اَلْمُفَارِقُ لِلْجَمَاعَةِ } مُتَّفَقٌ عَلَيْهِ 1‏ .‏ lbn Mas’ud (RAA) narrated that The Messenger of Allah (ﷺ) said: “The blood of a Muslim who testifies that none has the right to be worshipped but Allah and that I am His Messenger, cannot be shed lawfully, except in three cases: a married person who committed adultery, in Qisas (retaliation) for murder (life for life) and the apostate from Islam who abandons the Muslim Jama’ah (community).” Agreed upon. Bulugh al-Maram (Crimes (Qisas or Retaliation)) English reference : Book 9, Hadith 1199 Arabic reference : Book 9, Hadith 1169
Share:

Today's Verse

وَإِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلَائِكَةِ إِنِّي جَاعِلٌ فِي الْأَرْضِ خَلِيفَةً ۖ قَالُوا أَتَجْعَلُ فِيهَا مَن يُفْسِدُ فِيهَا وَيَسْفِكُ الدِّمَاءَ وَنَحْنُ نُسَبِّحُ بِحَمْدِكَ وَنُقَدِّسُ لَكَ ۖ قَالَ إِنِّي أَعْلَمُ مَا لَا تَعْلَمُونَ [Al-Baqara : 30] (2:30) Just *36 recall the time when your Lord said to the angels *37 , "I am going to appoint a vicegerent *38 on the Earth." They humbly enquired, "Are you going to appoint such a one as will cause disorder and shed blood on the Earth? *39 We are already engaged in hymning Your praise, and hallowing Your name". *40 *36). Thus far man has been summoned to serve and obey God on the grounds that God is his creator and sustainer, that in His grasp lies man's life and death, that He alone is the Lord Who rules over the entire universe in which he lives. In view of this, the only attitude which can be deemed appropriate for man is one of service and subjection to God. The same idea is presented in the following section, but supported on slightly different grounds In this connection the Qur'an defines precisely the true nature of man and his correct position in the universe. It also enlightens us to a period of man's past which is otherwise inaccessible. What the Qur'an tells us here, with its practical consequences, is of far greater value than knowledge derived by unearthing bones and pottery, and piecing together scattered fragments of information with the help of conjecture. *37). The word malak in Arabic means 'message' *38). 'Khalifah' or vicegerent is one who exercises the authority delegated to him by his principal, and does so in the capacity of his deputy and agent. Hence, whatever authority he possesses is not inherently his own, but is derived from, and circumscribed by, the limits set by his principal. A vicegerent is not entitled to do what he pleases, but is obliged to carry out the will of his master. If the vicegerent were either to begin thinking himself the real owner and to use the authority delegated to him in whatever manner he pleased, or if he were to acknowledge someone other than the real owner as his lord and master and to follow his directions, these would be deemed acts of infidelity and rebellion. *39). This was not said by way of objection or protest. It was said rather by way of inquiry and in order to satisfy their curiosity; it is inconceivable that the angels could object to any of God's decisions. The word 'vicegerent' suggested to them that the proposed species of creation would be placed on earth with some authority. It was incomprehensible to them how a species of being which had been invested with discretionary power and authority could conform with the overall order of the universe, which is based on absolute and involuntary subservience to the Will of God. They thought that investing anyone with authority in any part of the universe would lead to mischief and disorder. It is this aspect which the angels were curious about. *40). This does not mean that the angels considered themselves suitable for 'vicegerency'. They merely wanted to point out that God's orders were already being carried out fully, that they The word tasbih has two meanings: (i) to proclaim glory and (ii) to exert oneself earnestly and energetically. In the same way taqdis has two meanings: (i) to celebrate or proclaim holiness and (ii) to purify. *41). This was an answer to the latter doubt expressed by the angels. The angels were told that the reason for the appointment of a vicegerent was best known to God alone and could not be understood by them. Despite the services rendered by the angels, something over and above their work was still required. God decided, therefore, to create a new species of being in the world and to invest it with some authority.
Share:

ZAKKAR GIDAN HAYA DA MOTAR HAYA

*_ZAKKAR GIDAN HAYA DA MOTAR HAYA_*

                             *Tambaya*
Assalamu alaikum Malam Shin ko akwai zakka akan Gona, Fili ,Gidan haya da Motar Haya?

                                  *Amsa*
Waalaikumussalam, To dan'uwa duk gonar da aka rika don ayi amfani da ita, to babu zakka a cikinta, haka nan fili, amma idan kasuwanci ake yi da su, kamar a siya a sayar to za'a fitar musu da zakka, idan sun cika nisabi kuma shekara ta zagayo musu, ko kuma ya zama  sun cika sharudan zakka idan ya hada su da abin da ke hannunsa.

Haka nan babu zakka a cikin gidan haya saidai idan aka tara kudin kuma shekara ta zagayo akan su, sun cika nisabi, to anan ne za'a fitar musu da zakka, ko kuma ya zama sun cika sharudan zakka idan ya hada su da abin da ke hannunsa.

Allah ne ma fi sani.

18/12/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

IDDAR MACEN DA BATA YIN HAILA DUK WATA

*_IDDAR MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA_*

                               *Tambaya*
Malam idan ya zama mace ba ta yin haila sai duk bayan wata uku, yaya idarta za ta kasance ?

                                  *Amsa*
To malam dole ne, sai ta yi jini uku kamar yadda Hanafiyya suka fada, ko kuma tsarki uku kamar yadda Malikiyya suka tafi akai, ko da kuwa duk shekara take yin haila sau daya, saboda Allah madaukaki ya rataya idda ne da samuwar jini, kamar yadda yake cewa a cikin suratul Bakara aya ta: 228 "Kuma matan aka saka, to za su jira tsawon jinane uku"

*_DON HAKA DUK TSAWON LOKACIN DA ZA TA ZAUNA TO DOLE SAI TA JIRA SU, KAMAR YADDA AYAR TAKE NUNAWA._*

Allah ne mafi sani.

27/12/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *MIFTAHUL ILMI* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

Today's Verse

Surah Al-Anaam, Verse 1:
الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَجَعَلَ الظُّلُمَاتِ وَالنُّورَ ثُمَّ الَّذِينَ كَفَرُوا بِرَبِّهِمْ يَعْدِلُونَ

All praises and thanks be to Allah, Who (Alone) created the heavens and the earth, and originated the darkness and the light, yet those who disbelieve hold others as equal with their Lord.
(English - Mohsin Khan)

Surah Al-Anaam, Verse 2:
هُوَ الَّذِي خَلَقَكُم مِّن طِينٍ ثُمَّ قَضَىٰ أَجَلًا وَأَجَلٌ مُّسَمًّى عِندَهُ ثُمَّ أَنتُمْ تَمْتَرُونَ

He it is Who has created you from clay, and then has decreed a stated term (for you to die). And there is with Him another determined term (for you to be resurrected), yet you doubt (in the Resurrection).
(English - Mohsin Khan)

Share:

INA SHIRIN AURE SAI TSOHON MIJINA YACE DAMA CAN YAYI MIN KOME

*_INA SHIRIN YIN AURE, SAI TSOHON MIJINA YA CE DAMA CAN YA YI MIN KOME?_*

                              *Tambaya*
Malam mijina ya sake ni bayan na kammala idda, saura kwana uku na yi aure sai ya zo ya ce dama ya yi min kome, amma bai sanar da ni ba ne, don Allah malam yana da hakki, ko kuma na kyale shi na yi aurena?  saboda gaskiya ina son wancan, amma kuma ba na so na sabawa sharia?

                                   *Amsa*
To 'yar'uwa tabbas miji yana da damar da zai yiwa matarsa kome mutukar tana cikin idda, kamar yadda aya ta: 228, a suratul bakara take nuni zuwa hakan, Amma mutukar bai yi mata kome ba har ta kammala idda to ba shi da dama akan ta, amma zai iya shiga cikin manema.
Idan ya yi da'awar cewa ya yi mata kome tun tana idda, amma bai sanar mata ba ne sai bayan ta kammala idda, to ba za'a gaskata shi ba, sai ya kawo shaidu, wadanda za su tabbatar da faruwar hakan.
Yana daga cikin ka'idojin sharia toshe duk hanyar da za ta kai zuwa barna, idan aka bar abin a bude, wanda yake kin matarsa, zai iya mata mugunta, ta wannan hanyar, hakan yasa malamai suka ce sai ya kawo shaidu za'a gaskata shi, idan kuma bai kawo ba za ta iya zuwa ta yi auranta.
Saidai wasu malaman suna cewa: idan har matar ta gaskata shi, to ya isa, ko da bai kawo shaidu ba.

Duba: Al-mabsud 2\23 da Mawahibul-jalil 5\408

Allah ne mafi sani.

29/12/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

ZUBAR DA CIKI WATA BIYU SABODA TSORON TALAUCI

*_ZUBAR DA CIKI WATA BIYU SABODA TSORON TALAUCI !!!_*

                            *Tambaya*
Assalamu Alaikum DR. Ko yana halatta mace ta zubar da cikin da bai wuce wata biyu ba saboda tana shayarwa kuma batada cikakkiyar lafiya ga talauci sosai awurin mijinta baya iya cida ita, sai tafita tayi qwadago ta nemowa yaranta abinci.?

                               *Amsa*
Wa'alaykumussalam, To dan'uwa Malamai sun yi ijma'i akan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai, idan ya kai wata hudu, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba.

Amma sun yi sabani game da zubar da ciki kafin ya kai watanni hudu, wasu sun haramta, wasu kuma sun halatta wasu sun karhanta

Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin da bai kai wata hudu ba, idan akwai lalura.

Idan aka zubar da ciki kafin ya cika wata hudu saboda matsalar da likita ya tabbatar yaron ko Uwar za su fuskanta, ko kuma tsoran tagayyarar yaron bayan ya fito, ba za'a ce kun yi laifi ba, tun da bai zama mutum ba, kuma ba za'a tashe shi ranar alkiyama ba.

Don neman karin bayani duba Ahkamu al-janin fil-fiqhil islamy na Umar Ganam
"Babu wata rai face azurtata da abincinta yana wajan Allah", Kamar yadda aya ta: 5 a Surat Hud ta tabbatar da hakan.

Kada ka taba fargabar arzikin yaronka saboda Allah ne yake azurta shi tun yana ciki, kamar yadda ayoyi da hadisai Suka tabbatar.

Allah ne mafi sani.

16/01/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

YADDA AKE WARWARE SIHIRI

*_YADDA AKE WARWARE SIHIRI_*

                             *Tambaya*
Assalamu alaikum Dan Allah malam a fitar dani cikin duhu game da abin da yake damuna Mahaifiya ta ce ta je gurin malami ai mata naganin ciwon mara dz yake damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma likitoci sun yi scanning sunce ba komai to sai malamin ya ce mata asiri aka yi mata, kuma zai yi mata magani nan take ta haife abinda yake cikinta amma za ta kawo tunkiya da dubu bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya malam zuciyata ba ta aminta da malaman ba ne shi yasa ! Na keso ka bani fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a addini? Idan bata halatta ba wacce hanya zan bi wajen qin biyan kudin da kuma sanar da ita, saboda ina da matsala , ta bangaren aqeeda mun banbanta? Wassalam na gode malam Allah ya qara basira.

                                    *Amsa*
Wa'alaikumus salam, To 'yar'uwa tabbas ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur'ani, wasu malaman sun yi bayani cewa : ana iya warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta: 117 zuwa ta 122, na suratul A'araf, sai kuma aya ta: 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da aya ta: 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai.
Amma bai halatta ki taimaka mata ba, wajan bada wadannan kayan da boka ya nema, saboda ba'a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah.

Ya wajaba ki yi mata nasiha cikin hikima, ki sanar da ita cewa: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:" "Duk wanda ya je wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba'in" kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2230. Kin ga in mutum ya mutu a wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari'a ta yarda da ita, a wani hadisin kuma yana cewa: "Duk wanda ya je wajan boka ya gaskata abin da ya fada, to tabbas ya kafurce da abin da annabi Muhammad ya zo da shi" kamar yadda ya zo a Sunanu-abi-dawud hadisi mai lamba ta: 3904, kuma Albani ya inganta shi

*_INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZA KI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO KAN HANYA_*

Allah ne mafi sani.

12\4\2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

MAGANIN CUTAR SIKILA

*_MAGANIN CUTAR SIKILA!!!_*

                            *Tambaya*
Malam muna da wata yarinya da take fama da cutar sikila, to shi ne mu ka je wajan mai magani, sai ya ce mana mu samu naman kunkuru da jininsa, idan muka yi amfani da shi za ta samu sauki, shi ne  muke so mu ji halaccin hakan a wajan malamai?

                                  *Amsa*
To 'yar'uwa Allah madaukakin sarki, bai saukar da cuta ba, saida ya saukar da maganinta, sannan kunkuru yana daga cikin namun da ya halatta a ci, sannan kuma yana kara jini kamar yadda wasu manazarta suka fada, shi kuma sikila yana da karancin jini.

Idan ya tabbata a likitance cewa namansa yana maganin cutar skila, to za ku iya amfani da shi, amma ba za ku iya amfani da jininsa da ya kwarara ba, saboda Allah ya haramta amfani da jinin da ya kwarara, kamar yadda hakan ya zo a suratu Al'an'am aya ta: 145, amma abin da ya ragu na jini a cikin namansa, wannan ya halatta ayi amfani da shi.

Masana likitanci suna cewa, sikila wani rauni ne a cikin jini, don haka ba cuta ba ce, balle har ta warke, amma akwai magungunan da suke rage mata kaifi, daga ciki akwai OSPEN da FOLIC ACID.

Allah ne mafi sani.

28/12/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

HUKUNCIN SHAN RUBUTU

*_HUKUNCIN SHAN RUBUTU?_*

                             *Tambaya:*
Assalamu alaikum malam inada tambaya da Allah menene hukuncin shan rubutu irin Wanda ake rubuta wasu ayoyi sai a wanke a sha.

                                   *Amsa*
Wa'alaikumus salam, To malam ba'a samu hakan daga annabi tsira da amincin allah su tabbata a gare shi ba, haka nan sahabbansa, saidai an rawaito halaccin hakan daga wasu daga cikin sahabbai kamar Ibnu Abbas, ya zo a Zadul-ma'ad "Ibnu Abbas ya yi umarni  a rubutawa wata mace mai tsananin nakuda wasu ayoyi na Alqur'ani, don ta samu sauki" haka kuma an rawaito halaccin hakan daga wasu tabi'ai kamar Mujahid, wannan kuma shi ne maganar Imamu Ahmad.

Don haka  mutum ya karanta ayoyin shi ne ya fi, domin shi ne ya tabbata a ingantattun hadisai, saidai wanda ya rubuta ya sha ba za'a aibanta shi ba, tun da yana da magabata.

Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba : Zadul ma'ad 4\170 da Majmu'ul fataawaa 19\64.

02/12/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

HUKUNCIN FADIN ASSALAMU ALAIK

*_HUKUNCIN FADIN ASSALAMU ALAIK !!!_*

                               *Tambaya:*
Assalamu alaikum, malam jamilu  Idan mutum zai yiwa dan uwansa sallama zai iya cewa Assalamu alaika idan shi kadai ne?.

                                    *Amsa*
Malaman Malikiyya, sun hana cewa Assalamu alaika, saboda ba'a samu hakan daga daya daga cikin magabata ba, kamar yadda ya zo a FAWAKIHUDAWANY

Amma malaman Shafiiyya da hanabila sun halatta hakan, kamar yadda ya zo a Almajmu'u na Nawawy da Kashshaful Kanna'a.
Don han haka abin da ya fi shi ne fadin Assalamu alaikum ko da ga mutum daya ne.

Allah ne mafi sani.

1/1/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

HUKUNCIN LADANCI A SALLAH

*_HUKUNCIN LADANCI A SALLAH?_*

                             *Tambaya*
Assalamu alaikum Malam Meye hukuncin ladanci a sallah haram ne ko in akayi ba laifi ?

                                   *Amsa:*
Wa'alaikum assalam To dan'uwa mutukar liman yana daga murya, to yin ladanci bidi'a ne kamar yadda wasu malaman suka fada.

Amma idan liman yana da lalura ko rashin lafiya ko kuma masallacin yana da girma ta yadda dukkan mamu ba za su ji muryarsa ba, to ya halatta, saboda a lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi rashin lafiya, sayyidina Abubakar ya kasance yana daga murya da kabbara saboda ba'a jin na Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito

Allah ne mafi sani.

9/1/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

WAI SHIN ME AKE NUFI DA KYAKKYAWAN CIKAWA?

*WAI SHIN ME AKE NUFI DA KYAKKYAWAR CIKAWA?!*

Shehin Malami Shaikh “Khãlid bn Abdirrahmãn Ash-Shãyi'e” Yace:

ﺣﺴﻦ ﺍﻟﺨﺎﺗﻤﺔ ﻫﻮ: ﺃﻥ ﻳﻮﻓﻖ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﻗﺒﻞ ﻣﻮﺗﻪ ﻟﻠﺘﻘﺎﺻﻲ ﻋﻤﺎ ﻳﻐﻀﺐ ﺍﻟﺮﺏ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ، ﻭﺍﻟﺘﻮﺑﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﻭﺍﻟﻤﻌﺎﺻﻲ، ﻭﺍﻹﻗﺒﺎﻝ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻄﺎﻋﺎﺕ ﻭﺃﻋﻤﺎﻝ ﺍﻟﺨﻴﺮ، ﺛﻢ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﻮﺗﻪ ﺑﻌﺪ ﺫﻟﻚ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺤﺎﻝ ﺍﻟﺤﺴﻨﺔ،

ﻭﻣﻤﺎ ﻳﺪﻝ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻤﻌﻨﻰ ﻣﺎ ﺻﺢ ﻋﻦ ﺃﻧﺲ ﺑﻦ ﻣﺎﻟﻚ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ‏( ﺇﺫﺍ ﺃﺭﺍﺩ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻌﺒﺪﻩ ﺧﻴﺮﺍً ﺍﺳﺘﻌﻤﻠﻪ ‏) ﻗﺎﻟﻮﺍ : ﻛﻴﻒ ﻳﺴﺘﻌﻤﻠﻪ؟ ﻗﺎﻝ : ‏(ﻳﻮﻓﻘﻪ ﻟﻌﻤﻞ ﺻﺎﻟﺢ ﻗﺒﻞ ﻣﻮﺗﻪ)

ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺘﺪﺭﻙ.

→•••MA'ANA:-
KYAKKYAWAR CIKAWA Shine:
Yakasance kafin mutuwar bawa Allah yayi masa Muwafaqa ya datar dashi da (abubuwa kamar haka):

→Nisantar Abinda ke fusata Allah (s).
→Da Tuba daga Zunubbai da Sabon Allah,
→Da Fiskantar Ayyukan Da'a da Alkhairi,

Daganan Sai mutuwarshi ta kasance Acikin wannan kyakkyawan Hali,

Daga Cikin Abinda ke Nuni da Wannan Ma'anar: Akwai Hadisin da ya Inganta daga Anas Dan Malik [Ra] yace:
Manzon Allah s.a.w yace:

“IDAN ALLAH YA NUFI BAWANSHI DA ALKHAIRI SAI YA DAUKESHI AIKI” Sai Sahabbai sukace:
Taya Allah Zai Daukeshi Aiki?
Sai yace:

“ZAI DATAR DASHI DA KYAKKYAWAN AIKI KAFIN MUTUWARSHI”

(Imam Ahmad da Imam Tirmizi Suka Riwaitoshi, Imam Hãkim ya Ingantashi a Mustadrak).

📚علامات وأسباب حسن الخاتمة وسوء الخاتمة ص٣

Allah yayimana Muwafaqa Da Ayyukan Alkhairi Ya Amshi Rayukan mu Akan su!

Share:

FIRM BELIEF AND PERFECT RELIANCE ON ALLAAH SHOULD BE OUR PRIORITY AS MUSLIMS

FIRST REMINDER. Yaumu Al-thalaatha, 9th day of RAJAB (Tuesday 27th March). *_FIRM BELIEF AND PERFECT RELIANCE ON ALLAH SHOULD BE OUR PRIORITY AS MUSLIMS_*. Bismillaahir Rahmaanir Raheem.

Allah, the Exalted, says:
"The believers are only those who, when Allah is mentioned, feel a fear in their hearts; and when His Verses (this Qur'an) are recited unto them, they (i.e., the Verses) increase their Faith; and they put their trust in their Creator(Alone)(8:2). 

Ibn `Abbas (May Allah be pleased with them) said: When (Prophet) Ibrahim (Abraham) was thrown into the fire, he said: "Allah (Alone) is sufficient for us, and, He is the Best Disposer of affairs.'' So did Messenger of Allah Muhammad (Sallallaahu Alaihi Wasallam) when he was told: "A great army of the pagans had gathered against him, so fear them". But this (warning) only increased him and the Muslims in Faith and they said: "ALLAH (Alone) is sufficient for us, and HE is the Best Disposer of affairs (Hasbunallah wani-imal wakeel )". [Al-Bukhari].

So as Muslims, Even in the worst circumstances one should always have faith and trust in ALLAH and recite the above verse and in shaa ALLAH nothing can touch us except if it's a test from ALLAH on our eemaan (faith) in HIM. *_We ask ALLAH to increase us in knowledge, wisdom and courage to be able to rely only on Him for all our affairs_*. AMIN
Am your Brother in Islam
SA'AD SULEIMAN MUHAMMAD (SS TIGA)

Share:

TA AURI WANDA BAYA IYA JIMA'I HAR SUKA RABU SHIN ZATA YI IDDA?

*_TA AURI WANDA BAYA IYA JIMA'I HAR SUKA RABU, SHIN ZATA YI IDDA?_*

                               *Tambaya:*
Assalamu Alaikum Malam Wani bawan Allah ne ya Auri kanwata, sai daga baya muka gane ya ha'incemu sakamakon rashin mazantaka da baya dashi, daga baya da asirinsa ya tonu sai ya saketa, shin malam za tayi Idda ne ? don babu wata mu'amalar Aure da ya taba shiga tsakaninsu.

                                    *Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Mutukar ba su taba kwanciyar aure ba, ai babu idda akanta, kamar yadda aya ta: 49 a suratul ahzaab take nuni zuwa hakan.

Allah ne mafi sani.

21 Muharram, 1437

(03/11/2015)

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form