*Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 3,449:*
=
Shin meye matsayin irin sakonninda mutane suke turawa na neman afuwa da yafiya aduk sadda watan ramadan yamatso????
=
=
Amsa
=
_Toh wannan babu shakka bidi'ane kawai, kuma aikin jahilcine kasantuwar mutane idan basa karatu suka za6i su zauna da jahilci to babu abinda bazasuyiba su basu daukeshima abakin komaiba. Wannan irin sakonninda ake tutturawa wai mutum yace kuyafemai kaza kaza saboda ramadana ya matso wannan aikin jahilcine, wato irin yadda mutane suka nutse cikin jahilci shine ya jagorancesu zuwaga hakan harsuke ganin hakan abune mekyau alhalin kuma abun zargine. Lallai ana jiyewa mutane tsoro karsu shiga cikin Fadin Allah gameda wadanda aka qawata musu mummunan aikinsu se suke ganinshi amatsayin mekyau, Allah ta'ala ya tsaremu*****_
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
.
17-08-1439
04-05-2018
=
=
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika
-
This is default featured slide 1 title
Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.
-
This is default featured slide 2 title
Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.
-
This is default featured slide 3 title
Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.
-
This is default featured slide 4 title
Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.
-
This is default featured slide 5 title
Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.
MENENE HUKUNCIN IRIN SAKONNIN NEMAN GAFARA DA AKE TURAWA GABANIN RAMADAN?
MAI TAKABA ZATA IYA FITA SALLAR IDI?
MACE ZATA IYA BAIWA MIJINTA ZAKKA?
HIKIMAR RUBUTA BASHI
DON ALLAAH INA WANNAN SAKON YA SAMO ASALI?
INA DA MIJI AMMA YANA HILDA DA MATAN BANZA
HUKUNCIN SANYA HOTON MACE A DP
INA GASKIYAR WANNAN TARIHIN?
MENENE HUKUNCIN RAGE SUNA?
THE HOLY QURAN
YA HALATTA NA CIRE HIJABI BAYAN SALLAH KAFIN AZKAR?
DA WANE LOKACI YA KAMATA MUTUM YAYI SALLATUL FAJR
*DA WANE LOKACI YA KAMATA MUTUM YAYI SALATUL FIJIR?*
:
DAGA ZAUREN
*HISNUL MUSLIM*
:
*TAMBAYA*
Assalamu alaikum warahmatuhla wabarakatuh Don Allah menene hukumci salatul fijir,dawana lokaci ya kamata arinka yin shi sannan kuma mene faidar sa.Allah y saka da alkhairi
:
*AMSA* Wa'alaikumussalam Warahamatullahi wabarkatuhu
:
Salatul raka'atanin fajir anayinshine, bayan fitowar alfijir.. Kuma raka'a biyu akeyi!
:
Sannan falalan ta yadda yazo a hadisai ingantattu "tafi duniya da abinda ke cikinta"
:
Ibni hajar yakawo hadisin acikin bulugul maram
:
Wallahu a,alam
*Muhammad Auwal Abu jaafar*
*Masu buqatan shiga Wannan Zaure na hisnul Muslim suyiwa daya daga cikin wadannan number magana ta whatsApp*
*+2348065523065*
*+2349039510396*
Domin Neman Karin bayani akan wata fatawa sai Ku kira wannan numbar↓
*+2347065588557*
ﺳﺒحاﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ، ﺍﺷﻬﺪ ﺍﻥ ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻧﺖ ﺍﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺍﺗﻮﺏ ﺍﻟﻴﻚ ،
Kuna iya samun mu ta facebook ta wannan link indanke Qasa
https://mobile.facebook.com/Hisnul-Muslim-667684316700356/?fref=none
MATAMBAYI BAYA BATA
SHEKARU NAWA ABU HURAIRA YA LAZIMCI ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM
*_SHEKARU NAWA ABU-HURAIRAH (R.A) YA LAZIMCI ANNABI S.A.W?_* *Tambaya* Assalamu alaikum Mallam don Allah ina son in san shekara nawa aba hurera yayi a raye da manzon Allah, kuma bayan rasuwar manzon Allah shekara nawa yasamu araye? Nagode malam. Muna musune da wani Dan shi'a *Amsa* Wa'alaikumus Salam, To dan'uwa Abu-hurairah ya lazimci Annabi ﷺ tsawon shekaru uku, kamar yadda Bukhari ya rawaito a sahihinsa 1\359, sannan bayan Annabi ﷺ ya bar duniya ya yi shekaru 47 kafin ya rasu, don haka Abu-hurairah ya rasu a shekara ta 57 bayan hijra. Wasu daga cikin malaman tarihin suna cewa: Abu-hurairah ya musulunta tun a shekara ta bakwai a watan Safar lokacin yakin Kaibar, don haka sai ya zama ya rayu a musulunci kafin Annabi ﷺ ya bar duniya, shekaru hudu da wata daya, sai a dauki abin da aka rawaito a Bukhari a matsayin gwargwadon lazimcitarsa ne shekaru uku, kamar yadda ibnu Hajar ya fada a Fathul-bary 6\608.. Allah ne mafi sani. Don neman Karin bayani duba : Al-isaabah fi-tamyizissahaabah 7\444. 26\2\2015 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
TAYI ALWALA DA RUWAN FITSARI HAR TAYI SALLAH BATA SANI BA
ZAN IYA CI GABA DA ZAMAN AURE DA MASHAYIN GIYA?
ZAN AURI KANWAR MATAR MAHAIFINA KO YA HALATTA?
YA MATSAYIN SHAFA A KAN SAFA YAYIN ALWALA
Friday Messages 177
Best prayer is always for the best people like you, on this beautiful Friday, I wish U the strenght of Faith, the reality of Hope, the joy of Charity and the contentment of a Happy Heart. May The Almighty-Allah grant U good health... May Allah reward every little U do in multiples, may all your wishes and desire be accomplished, may all your sins and shortcomings be forgiven, Amin thumma Amin. Jumaat Mubarak
Friday Messages 176
May Allah enveloped us with d great blessing of d first 10days of dis month of d months (RAMADAN) & guide us with protection of suratul fatiha & protect us with d power of ayatul kursi Jmmt mbrk/Ramdan krm
FRIDAY Messages 175
Yaa Allah you saved Yunus from Fish, Ibrahim from fire, Musa from Fira'un, Yusuff from well, Muhammed (SAW) from Quraish save us from every difficulties of life , turn all our expectations into reality because you turn egg into bird , seed into tree , fluid into human , hardship into relief and cloud into rain. Answer our secret prayers and prosper the work of our hands, wipe away our secret tears and bless us with multiple grace.Ameen, jumaat Mubarak.
Friday Messages 174
O Allah, never let our heart be disturbed by the trials of life, open the doors of your mercy to us, ease our ways of life, Accept our worship, Bless our time and end, Comfort our graves, forgive our sins and grant us favour in everything we do, and never forsake us in this world and hereafter. Juma'at mufeedah.
MACE MAI MATSANANCIYAR SHA'AWA
NAU'UKAN ALJANU DAKE CIKIN DUNIYA
WISE WORDS
ZAN IYA AUREN MAZINACIYA?
WADANNE ABUBUWA NE IDAN SUKA BI TA GABAN MAI SALLAH SALLAR SA TA BACI?
TAYI ZINA TANA IDDA
SHUGABANCIN MACE A MUSULUNCI
SHIN MAI CIKI TANA YIN HAILA?
MUNA RIGIMA DA MIJINA SABODA YANA KASHEWA BUDURWAR SA KUDI
MANUFOFIN DA SUKA SA AKA HARAMTA ZINA
DUK YARAN DA MUKE HAIFA DA MIJINA SIKILA NE, ZAN IYA NEMAN YA SAKE NI NA AURI WANI?
INA SON BAYANI AKAN 'YAN TABLIG, SABODA MIJINA YANA BIN SU
MAY WE NOT BE LAID ASTRAY
Friday Messages 173
May Allah solve ur simple & most difficult problems, protect u & ur family from all evils & may He be ur guide at all times Ameen. JUMA'AT MUBARAK.
Friday Messages 172
O Allah! Open Your various ways of blessings and protect us from all the evil tricks that emanate from shaytan and his allies among men and jinn, Overlook our shortcomings and forgive our sins, both apparent and hidden; major and minor. For You are the Most-Forgiving, the Most-Merciful.... AMEEN JUMAA'T MUBARAK
FRIDAY MESSAGES 170
As we witness this glorious month (Ramadan), may all your prayers be answered, May Almighty Allah S.W.T accept it as an act of Ibadah and may you and your entire family receive the full blessings and favour of this month.Wishing you Allah's Guidance, Protection and Blessings during and beyond this month. Ameen! Jumma'a Mubarak.
Friday Messages 171
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"
May Almighty Allah shower his Rahma & Salama on you & your family. Prevent you from evil act and calamity, grant you with a mind free of worry, a heart free of sadness and a body free of sickness. May almighty Allah uplift your value, forgive your past, bless your present, grant you and your Family manifest Victory Fid-duniya Wal-Akhirat. Juma'at Mubarak.
FRIDAY MESSAGES 169
On this beautiful Friday, I wish all Muslim ummah the strenght of Faith, the reality of Hope, the joy of Charity and the contentment of a Happy Heart. May The Almighty-Allah grant us good health... May Allah reward every little we do in multiples, may all our wishes and desire be accomplished, may all our sins and shortcomings be forgiven.
Ameen.
Jumma'at Mubaraq.
*_Ibrahim_* *_Tafida_*
KURAKURAI GUDA 15 NA RANAR JUMA'A
LIST OF GOOD MANNERS THAT WE CAN LEARN FROM THE GLORIOUS QUR'AN
FALALAR RANAR JUMA'A
HUKUNCIN KARBAR HAYAR DA ZATA KAI GA MALLAKAR ABU
*_HUKUNCIN KARBAR HAYAR DA ZA TA KAI GA MALLAKAR ABU_*
*Tambaya*
Assalamu alaikum.
Menene hukuncin shari'a akan irin yanda mutane suke yi, na sayan abin hawa su bawa direba da sharadin cewa : a kullum zai kawo wani ayyanannen kudi (kamar N500), har na zuwa tsawon kamar shekara, akan cewa idan ya shekara yana kawowa abin hawan ya zamo na sa.
*Amsa*
Wa'alaikumus Salam, To dan'uwa wannan ciniki daga baya ya shigo cikin kasashe musulmai, amma malamai magabata ba su san shi ba, saboda da can a kasashen turawa aka san shi, don haka malaman wannan zamanin suka yi sabani akan wannan mas'alar, akwai wadanda suka halatta wasu bangarori na wannan mua'amala, saidai fatawar manyan malaman Saudiyya da kuma kwamitin fatawa na din-dai-din ita ce: haramta wannan nau'i na haya kamar yadda suka tabbatar da hakan a zamansu na ranar:29/10/1420 saboda ya kunshi zalunci, domin zai iya yiwuwa, mutum ya sare kafin ya kai lokacin da aka diba masa, ka ga kudin da ya biya a baya, ba zai ci gajiyarsu ba, sannan ciniki biyu ne cikin ciniki, don haka ya haramta, kuma hanya ce da za ta jawo talakawa su dinga cin bashi, ba tare da sun damu ba.
Allah ne ma fi sani.
6/4/2014
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
KARBAR NA GORO A MA'AIKATUN GWAMNATI
*_KARBAR NA-GORO A MA'AIKATUN GWAMNATI!!!_*
*Tambaya?*
Assalamu alaikum malam ni ma'aikacin ne da nake aiki a ma'aikatar binciken kudi (state audit), ina cikin team, akwai wasu kudi da ma'aikatar da aka turamu bincike suke bayarwa, kamar haka:
1. Kudin Refreshment, maimakon duk rana su kawo mana abinci, sai duk wata sai su bamu dukiya har mu qare aikinmu.
2. Kudin sallama. Idan muka kammala sai ma'aikatar ta bamu kudin a matsayin sallamar bakinta.
3. Wasu kudin da ban san ta ina suke fitowa ba, sai dai kawai team leader namu ya kira ni ya bani, dama kuma ko wadancan nau'i 2 da na fada, kirana kawai yake, ya bani abinda zai bani, ba tare da na san a hannun wa ya mso ba, nawa ya amso, ko makamancin haka.
4. Akwai wadanda na san wani mai karin kudi ne ya bayar don a bar shi da karin, suma idan naga sanda ya bayar zai bani, wani wanda ban san sunyi shirinsu ba ba zai ba ni ba.
5. Akwai wadansu mutane da shekarunsu sun kai su aje aiki, ko wasu masu qarin kudi ko ma wasu ghost workers ne babu su wasu ke cin kudin, sai idan nazo rubutu report sai yace kada nayi musu query ya sanda su.
6. Akwai wadanda ake riqe albashin su idan basu zo sukayi verification ba, tanan ne ake, idan mutum yazo sai ayi clearing nashi a bashi salary dinshi, idan bai zo ba ghost workers ne, wani ne ke cin kudin shi, sai a dinga rabe wannan albashin kafin a rubuta report a debe shi a payroll.
7. Shin ya matsayin daukar mataki akan mai qari da yawa kamar mai karin step 7 ko 6 a kyale mai 1?
8. Ko alfarma na shiga ta wannan aikin don kawai sanayya, amma ka dauki mataki ga wanda baka sani ba?
*Amsa*
Wa'alaikum assalam
1. Ina muku wasici da tsoran Allah a duk aikin da kuke yi.
2. Duk kudin da kuka San ba halal ba ne ku nisance su, hakan Shi zai sa Allah ya muku albarka a rayuwarku.
3. Bai halatta ma'aikacin gwamnati ya amshi kowanne irin lada ba akan aikinsa da yake amsar albashi akai ba, saboda Fadin Annabi ﷺ (Duk Wanda muka ba Shi aiki kuma muka ba Shi lada akan haka, to duk abin da ya amsa bayan haka ya zama haram) kamar yadda Abu Dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (2943).
4. Amsar kudin-goro a wajan masu laifi da niyyar suturta su yana daga ha'inci da kuma rashawar da Allah ya tsinewa mai amsarta, kamar yadda hadisin Tirmizi mai lamba ta: (1336) ya nuna Hakan.
5. Duk wanda ya kiyaye Allah, tabbas zai kiyaye shi, wanda ya keta dokokinsa zai same shi a Madakata, tsarkake abinci na daga cikin hanyoyin karbar addu'a.
6. Kudin gwamnati haķki ne na jama'ar kasa, taimakawa wani ya ci ba bisa ka'ida ba magudi ne da zai sa su tsaya da shi ranar Alkiyama a gaban Allah.
7. Zunubi Shi ne abin da ka yi amma yake maka yawo a rai kuma ka ji tsoran kar mutane su yi tsinkayo akai.
Allah ne mafi sani.
12/02/2017
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
BAFFANA YANA YAWAN RAZANA A BACCIN SA
*_BAFFANA YANA YAWAN RAZANA A BACCINSA, A TAIMAKA MANA!!!_*
*Tambaya*
Assalamu alaykum: Mallam ina bukatan shawara ko mafita in Allah yasa kanada masaniya akai.
Uncle dinane ya kasance yakan yi mafarki da dare sai yake razana wani lokaci ya tashi da gudu ko yake kai duka, hakan wlh har yasa yakan ji ciwo sosai.
Kuma ya kanyi addu'o'i kamar karanta Kulhuwa, falaqi, Nasi, da ayatul qursiyu amma kuma abun yakan dame shi. Mafarkin nawani kamar macijine kebinsa.
Allah saka da alkhairi ya kuma sa mu samu mafita daga gareku ameen.
*Amsa*
Wa'alaikum assalam, Duk lokaçın da ya yi mafarki ya razana ya dinga karanta addu'ar da ta tabbata daga Annabi s.a.w. a hadisin Tirmizi mai lamba ta: 3528.
أعوذ بكلمات الله التامات من غضبه وعقابه وشر عباده ومن همزات الشياطين وأن يحضرون
In har ya yi tofi sau uku a hagunsa ya canza bangaren kwanciyarsa, ba abin da zai cutar da shi, bayan haka.
Allah ne mafi sani.
11/04/2016
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
IDAN MAKUSANTA BIYU SUKA MUTU TARE ZASU GAJI JUNAN SU
*_IDAN MAKUSANTA BIYU SUKA MUTU TARE, ZA SU GAJI JUNANSU??_*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum.
Malam wani uba da danshi suka rasu alokaci daya kuma shi uban mai kudi ne.dan kuma ya rasu ya bar matar shi da ciki kuma bai bar komai ba. To Malam tambayata anan yaya zaa raba gado? Shin zaa rabu dukiyar baban ne da ya rasu tare da dan sai a ba matarshi da abinda ke cikinta ka sonshi koko shi dan tunda tare ya rasu da baban bashi da gadon dukiyar shi??
*Amsa*
Wa'alaikum assalam. Idan Makusanta biyu suka mutu tare, ba'a San Wanda ya riga mutuwa ba, to babu gado a tsakaninsu a zance mafi inganci, saboda yana daga cikin sharudan gado tabbatar da mutuwar Wanda Za'a gada Kafin Wanda zai yi gado, nan kuma ba'a samu tabbacin ba, don haka ba za su gaji juna ba, saidai kowa wasu magadan na shi na daban su gaje shi.
Allah ne mafi sani
14/04/2018
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU KO ZAN IYA YIN ADDU'AR BUDE SALLAH?
*_NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU, KO ZAN IYA YIN ADDU'AR BUDE SALLAH?_*
*Tambaya:*
Aslm inada Tambaya Malam, Shin idan an fara sallah ka zo za ka bi, za ka karanta addu'ar da ake yi ne bayan kabbarar harama?
*Amsa*
To dan'uwa abin da malamai suka fada shi ne: mutukar ya riski liman a mike, to zai yi addu'ar bude sallah, sannan ya karanta fatiha, ko da kuwa a raka'a ta biyu ne, saidai idan ya riski liman a ruku'u, to zai shiga tare da shi, kuma addu'ar bude sallah za ta fadi daga kansa, saboda wurin yinta ya wuce.
Raka'ar da ka fara samu tare da liman, ita ce raka'ar farko a wajenka, wannan ya sa za ka yi addu'ar bude sallah, ko da kuwa shi liman a raka'a ta uku yake ko ta hudu, wannan shi ne zance mafi inganci.
Idan ka riski liman a tsaye amma abin da ya rage ya yi ruku'u, ba zai isa ka karanta addu'ar bude sallah ba, sannan ka karanta Fatiha, to za ka karanta fatiha, ka bar karanta addu'ar bude sallah, saboda addu'ar bude sallah sunna ce, karanta fatiha ga mamu wajibi ce a wajan wasu malaman.
Don neman Karin bayani duba Al-majmu'u na Nawawy 3/276 da kuma Majmu'ul fataawa 30/150.
Allah ne mafi sani.
11\4\2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
ZAKKAR NOMAN RANI
*_ZAKKAR NOMAN RANI_*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum, Malam Dangane da zakkar amfanin gona da ka noma ta hanyar noman rani da aka yi amfani da ban ruwa na inji kuma da akayi lissafin abinda aka kashe sai ya zama kayan da aka samu bai biya kudin wahalarsa ba, yaya zakkarsa zata kasance?
Allah ya kara budi!
*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, duk da haka za'a bada zakkarsa mutukar ya kai Sa'i 300.
Za'a fitar da daya bisa ashirin, 1/20 na abin da aka samu, wato in Sa'i dari uku ne sai a bayar da Sa'i sha biyar, in dari hudu ne sai a bada Sa'i ashirin، kamar yadda hadisin Buhari mai lamba ta: 1483 ya nuna hakan.
In har bai kai wancan mikdarin ba to babu zakka a ciki.
Shari'a ta rataya zakkar kayan amfanin gona ne da samun Sa'i dari uku, Hakan kuma ba Shi da alaka da faduwa ko samun riba a noman.
Allah ne mafi sani.
18/04/2017
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
ZAN IYA ZAMIYAR BASHI NA DAGA ZAKKA
*_ZAN IYA ZAMIYAR BASHINA DAGA ZAKKA??_*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum. ya sheikh. Ina da tambaya. Idan ina bin mutum bashin kudi kuma zanyi zakka, zan iya cewa na bar mai abinda nake binshi a matsayin zakka?
*Amsa*
Wa alaikum assalam, Malamai sun yi sabani a wannan mas'alar zuwa zantuka guda biyu:
1. Ba ya halatta mutum ya mayar da bashin da yake bin wani a matsayin zakka, saboda Zakka hakkin Allah ne, yin hakan kuma zai zama ya amfanar da kansa da zakkar saboda in ba ta hanyar ta ba da kudinsa ba za su fito ba, Wannan ita ce fatawar Malaman Hanafiyya da Hanabila sannan kuma ita ce fatawar malaman Malikiyya in ban da Ash'habu, hakan kuma shi ne mafi inganci a wajan Shafi'iyya.
2. Ya halatta ya mayar da bashinsa da yake kan wani ya zama Zakka, saboda in da zai ba shi zakkar ya dauke ta ya biya shi bashi da ita da ya halatta ya amsa, wannan ita ce fatawar Ash'habu daga Malikiyya sannan kuma Kauli ne a mazhabar Shafi'iyya kamar yadda Nawawy ya ambata a Almajmu'u.
Don neman Karin bayani duba: Almausua Alfiqhiyya 23/131.
Duk da cewa babu nassi yankakke bayyananne a mas'alar a iya bincikenmu, Saidai fatawar manyan malamai na rashin yin *ZAMIYAR* ita ce ta fi rinjaye, saboda kubutar da wuyaye daga yiwuwar kuskure yana da kyau sannan fita daga sabanin Malamai abin so ne.
Allah ne mafi sani
19/04/2018
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
BA'A IDDAR SAKI DA WATA UKU
*_BA'A IDDAR SAKI DA WATA UKU!!!_*
*Tambaya:*
Assalamu Alaikum Malam ina da tambaya don Allah mace ce tana shayarwa amma bata jini, sai mijinta ya sake ta, to wai za ta kirga watannin ne na iddanta ko ya zata yi?.
*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Idan aka saki mace tana shayarwa, ya wajaba ta jira tsarki uku, ko da kuwa za ta yi shekara uku kafin ta gama, Ba'a idda da watanni uku sai ga wacce ba ta fara haila ba, ko kuma wacce ta yanke kauna daga haila saboda tsufa, kamar yadda aya ta: 4 a suratu Addalak ta tabbatar da hakan.
Allah ne mafi Sani.
22/04/2016
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
YA SAKE MU SAKI DAYA SAI YA MUTU KAFIN MU GAMA IDDA, KO MUNA DA GADON SA?
*_YA SAKE MU SAKI DAYA, SAI YA MUTU KAFIN MU GAMA IDDA, KO MUNA DA GADONSA?_*
*Tambaya*
Malam mutum ne yana cikin halin rashin lafiya, ya saki matansa har guda biyu saki daya, kuma bai dawo da su ba har ya mutu, kuma ba su gama iddah ba, yaya za'a yi ? za su yi masa takaba, kuma suna da gadonsa, ko ko a'a ?
*Amsa*
To dan'uwa mutukar yadda ka sifanta, haka abin yake, to za su bar iddar saki, su koma iddar mutuwa, kuma za su ci gadonsa, saboda suna nan a matansa, tun da saki daya ne, Ibnu-khudamah ya hakaito ijma'in malamai akan haka.
Don neman Karin bayani duba: Al-mugni 8\94.
Allah ne mafi sani.
9\5\2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
WANDA YA MUTU YANA SHAN TABA BAI TUBA BA
*_WANDA YA MUTU YANA SHAN TABA SIGARI, BAI TUBA BA?_*
*Tambaya*
Assalamu Alaykum, Ina fatan Dr yana Lafiya. Dan Allah mene ne Hukuncin Mai shan taba (sigari), har ya mutu bai tuba ba?. Na gode.
*Amsa:*
Wa'alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Dukkan wanda ya mutu yana shan taba (sigari) bai tuba ba, yana karkashin ikon Allah, in ya so ya gafarta masa, in ya so ya kama shi da zunubin shan tabar da ya yi, saboda shan taba haramun ne, saboda ta kunshi cuta, kuma duk abin da yake cuta ne tsantsa haramun ne, kamar yadda ayoyin Alqur'ani da hadisan manzon Allah suka tabbatar.
Allah ne mafi sani.
11/05/2016
03/08/1437
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
SHIN ZA'A IYA YIWA DAN SHI'A SALLAMA?
*_SHIN ZA'A IYA YIWA DAN SHI'A SALLAMA?_*
*Tambaya*
Assalamu'alaikum warahaamatullahi wabarakatuhu Malam shin zan'iya yiwa dan Shi'a
*Amsa:*
To dan'uwa tabbas 'yan shi'a suna da akidu wadanda suke warware musulunci, Daga ciki akwai zagin sahabban da Allah ya yarda da su, da riya tawayar qur'anin da Allah ya yi alqawarin kiyaye shi.
Ba duk mutumin da ya riya abubuwan da suka gabata ba za'a kira shi da kafiri, dole sai an tabbatar da cewa ya yi su ne bisa ilimi, Kuma ba shi da wata Shubha wacce ta kasa warwaruwa.
Yana daga cikin ka'idoji a wajan malaman akida ba duk wanda ya aikata kafirci ake cewa kafiri ba, don haka jahilai a cikin 'yan shi'a da gama-gari wadanda suka shiga shi'a saboda talauci ko kuma zaton cewa addinin gaskiya ne ba za mu kafirta su ba, ko da kuwa suna riya wadancan abubuwa da suka gabata, saboda akwai hadisai da yawa da suke nuna uzuri ga wanda ya aikata kafirci da kuskure.
Don haka duk dan shi'an da ka san jahili ne kana iya masa sallama, kyakykyawar mu'amala tana iya sanyawa mutum ya gane gaskiya.
Allah nai mafi sani
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
YIN SALLAR NAFILA BAYAN SALLAR JUMA'A
_*YIN SALLAR NAFILA BAYAN SALLAR JUMA'A*_
_Sunnace ga wanda yaje Sallar juma'a yayi Nafila bayan juma'a raka'a hudu a masallaci ko raka'a biyu a gida. An ruwaito adadin raka'oin da suka tabbata anayi na sallar Nafila bayan Sallar juma'a acikin Hadisai da dama ga kadan daga cikin su:_
_*1-ANAYIN RAKA'A GUDA BIYU(2)*_
_Daga *Ibn Umar R.A* yana cewa: *"Annabi ﷺ ya kasance baya yin Nafila bayan Sallar juma'a har sai ya juya sanna yayi Sallar raka'a biyu"*_
*@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ( 937 ) ﻭﻣﺴﻠﻢ ( 882 ) .*
_Awata Riwayar: *"Annabi ﷺ ya kasance baya yin nafila bayan juma'a har sai ya fita daga Masallaci sai ya Sallaci raka'a biyu a gidansa".*_
*@ ﻣﺴﻠﻢ ( 882 ) ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺰﺍﺩ ( 1/440 )*
_Awata Riwayar: *"Ya kasance idan yayi Sallar juma'a sai ya shiga gidansa sai yayi Raka'a guda biyu ko hudu na Nafila".*_
_*2-ANAYIN RAKA'A HUDU(4)*_
_Daga *Abi Hurairata R.A* yana cewa: "Lallai Annabi ﷺ yace: *(Idan dayanku yayi Sallar juma'a to yayi raka'a guda hudu a bayanta ta nafila).*_
*@ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ( 881 ).*
_Awata Riwayar: *Annabi ﷺ* yana cewa: *(Idan dayanku yayi Sallar juma'a to yayi Sallar nafila raka'a hudu bayanta).*_
_Awani lafazin: *(Wanda zaiyi nafila bayan juma'a to yayi raka'a hudu).*_
*@ ﻣﺴﻠﻢ ( 881 ).*
_*Shiekul Islam ibn Taimiya Allah* yayi masa Rahama yana cewa: *"Idan dayanku zaiyi nafila bayan juma'a a masallaci sai yayi raka'a hudu, Amma idan a gidane sai yayi raka'a biyu".*_
_Mafi yawan Malaman Fiqhu sun tafi akan: "Mustahabbine akan wanda yaje sallar juma'a yayi nafila raka'a hudu, wannan shine maganar *Ibn Mas'ud* da wasu daga cikik Sahabbai"._
*@ ﻣﺼﻨﻒ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ "* *( 2/40 41- ) ،ﻭﻫﻮ ﺍﺧﺘﻴﺎﺭ ﺍﻟﺤﻨﻔﻴﺔ ،ﻛﻤﺎ ﻓﻲ " ﺭﺩ ﺍﻟﻤﺤﺘﺎﺭ " ( 2/12 13- ) ، ﻭﺍﺧﺘﻴﺎﺭ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲﻓﻲ " ﺍﻷﻡ " ( 7/176 )*
_*Imam Ahmad* yana cewa: *"Wanda ya so yayi raka'a biyu ko raka'a hudu".*_
*@ ﺍﻟﻤﻐﻨﻲ " ( 2/109 ) .*
_Amma abinda yafi shine wanda zaiyi nafilar a masallaci yayi Raka'a hudu wanda zaiyi a gida sai yayi raka'a biyu. Wannan shine ra'ayin ibn Qaiyim da Ibn Taimiya._
*@ ﺯﺍﺩ ﺍﻟﻤﻌﺎﺩ " ( 1/417 ) .@ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﻟﻠﺠﻨﺔ ﺍﻟﺪﺍﺋﻤﺔ ( 6/131 )*
_*Allah* ne mafi sani._
Rubutawa:- Mustapha Musa
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
ME YASA ALJANU SUKE SHIGA JIKIN MUTANE?
*_MEYA SA ALJANU SUKE SHIGA JIKIN MUTANE?_*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum malam, me yake kawo aljanu jikin Dan adam, Kuma meza a yi a rabu da su?
*Amsa:*
Wa'alaikum assalam sakaci da ibada da zikirori na daga cikin abubuwan da suke kawo aljanu,duk mutumin da yake yawan azkar yake kuma kiyaye dokokin Allah,da wuya aljani ya shiga jikinsa, Saboda şu zikirorin safe da yamma da na kwanciya bacci da shiga bandaki da fitowa suna kariya daga shaidanu.
Saidai ko da mutum yana da nagarta, aljani yana iya shiga jikin mutum ta hanyar sihiri ko kambun baka, ko yawan fushi.
Ayoyin Alqur'ani na korar aljani daga jikin dan'adam,musamman Suratul Bakara da Kula'uzai biyu da ayatul kursiyyu da surorin tauhidi guda biyu.
Allah ne mafi sani.
11\5\2016
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
SHIN MUTUM ZAI IYA YIWA IYAYEN SA WA'AZI?
*_SHIN MUTUM ZAI IYAYIWA IYAYENSA WA'AZI?_*
*Tambaya*
Wai shin mutum xai iyayiwa iyayensa wa'axi, Ko kuma inyaga baxai iyaba sai yasamu wanda suke fadamasa yaji suka mar nasiha akan abinda yakeyi, Bayan hakan yafaru sai mahaifinnasa yace wlh shi baiyafemasa ba sannan yace inhar shine mahaifinsa baxai daba jindadi ba arayuwarsa
, to waishin yahukuncin yake a addini
*Amsa*
Assalamu Alaikum, Babu shakka ana yiwa kowa wa'azi har mahaifa, sai dai da bambamci yadda akewa mahaifa wa'azi da kowa.
*Hujja*
Annabi Ibrahin A.S ya yiwa mahaifinsa wa'azi amma cikin laluma ta tausasa harshe, yana kiransa da *YA ABATI* (ya baba) kamar yadda suratul (MARYAM) taba da labari.
*Nasiha*
Duk wanda zai yiwa iyayensa wa'azi to ya kasance mai biyayya ne a tare da su, ya kasance mai yi musu hidima, da duk sauran mu'amala mai kyau wacce ta rubanya yadda akewa kowa wanda basu ba.
Kuma babu laifi idan da ya saka wani wanda iyaye suke ganin girmansa ya yi musu wa'azi.
*Hukunci*
Wanda duk ya kasance haka to babu laifi ko da iyaye sunyi masa baki, insha Allah babu abin da zai sameshi sai dai yayi kokari kada ya gajiya dayi musu wa'azi ta duk hanyar da zai sa su iya fahimta.
*ALLAH S.W.A YA KARA FAHIMTAR DA MU AMEEN*