SHARHIN FIM ƊIN THOR
SHARHIN FIM DIN THOR

* Bada Umarni - Kenneth Branagh

* Daukar Nauyi - Kevin Feige 

* Tsarawa - Ashley Edward Miller/ Zack Stentz /Don Payne

* Labari - J. Michael Straczynski/Mark Protosevich

Thor Fim din jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2011 a Kasar Amurka. Labarin Fim din Ya samo asali ne Daga Littattafan almara mai suna Thor wanda Stan Lee, Larry Lieber da Jack Kirby Suka rubuta a ƙarkashin kamfanin Marvel Comics. Kamfanin Marvel Studios shi ne Ya dauki nauyin shirya Fim din, yayinda Kamfanin Paramount Pictures Ya yaɗa shi. Fim din shi ne Fim na hudu Daga cikin Fina-Finan Duniyar Marvel Mai suna Marvel Cinematic Universe (MCU).    

A Cikin wannan Fim, an nuna Thor a matsayin Yariman da aka kora Daga Kasar su tare da gudumarsa mai suna Mjolnir bayan an Kwace masa dukkan wani karfin sihirin sa. An fitar da wannan Fim ne a ranar 17 ga watan Afrilun 2011 a Sydney, Australia, yayinda kuma aka sake shi a ranar 6 ga watan Mayun Shekara ta 2011 a Kasar Amurka. Fim din Ya Kawo kudi sosai a Kasuwar Fina-Finai ta duniya baki daya, sannan an yabawa Jaruman Fim din bisa Kokarin da Suka yi a cikin sa. Sai dai hakan bai hana wasu masu sharhin Fina-Finai caccakar Fim din ba, Musamman akan ingancin labarin Fim din. Anyi na biyu da na ukun Fim din.


LABARIN FIM DIN

A shekara ta 965 AD, sarkin dake mulkin daular Asgard da ake kira da Odin, Ya ƙaddamar da yaki akan Wasu Samudawan Sanyi Mazauna daular Jotunheim hadi da shugaban su mai suna Laufey. Odin yayi hakan ne domin Ya hana Samudawan Mamaye daulolin rayuwa tara da ake da su da suke ta Kokarin yi. Mayakan Asgard, Karkashin Jagorancin Odin, sun samu Nasara akan wadannan Samudawan Sanyi inda har ma Suka yi Nasarar Kwamushe Sirrin karfin wadannan Samudawa dake cikin wani Dan karamin akwatin gilashi.

A Yanzu Kuma, Dan Odin, wanda ake kira da Thor Ya shirya tsaf domin zama sabon sarkin Asgard, harma an sa ranar bikin nada shi sarauta. Ana tsaka da wannan shagali ne, kwatsam Sai wasu Samudawan Sanyi Suka kawo wani harin Sumame da nufin su dauke wannan akwatin gilashi nasu da Odin Ya Kwamushe a shekarun baya. Duk da Cewa an Sheke wadanda Suka kawo harin sumamen kuma Odin Ya nuna barin su shi ne abinda yafi, Jin haushin Cewa sun rusa masa burin sa na son ganin Ya zama sarki a wannan rana yasa Thor Ya yanke Shawarar Kai ziyara daular su domin Ya koya musu darasi.

Yayinda zai tafi, Sai Ya nemi taimakon Loki, abokinsa kuma Dan Uwansa (Agolan Gidansu), Kawarsa Sif Da kuma Jarumai Uku, wato Volstagg, Fandral da Hogun inda Suka rankaya su shida Suka tafi Johunheim. Anyi Bata-Kashi sosai a can din kafin Daga baya Odin yazo Ya cece su. Wannan Al'amari ne Ya janyo Rugujewar Yarjejeniyar zaman Lumanar da akayi a tsakanin daulolin biyu Shekaru Aru-Aru da Suka gabata. Wannan Danyen Hukunci da Thor Ya yanke ne yasa Odin Ya fusata inda har takai ga Ya kwace duk wani karfin sihiri da Thor yake dashi, sannan kuma Ya kore shi, bayan doguwar tafiya ne Sai Thor Ya fado wannan daular tamu ta mutane tare da Gudumarsa wato Mjolnir. Sai dai kafin Ya aiko Gudumar, Odin Ya Sihirceta da wasu dalasiman tsafi ta yadda babu mai Iya sarrafa ta face wanda Ya Cancanta.

Thor da Gudumarsa sun fado ne a New Mexico ko da take sun fado ne a wurare Mabanbanta. Wata jami'ar Binciken Kimiyya da fasaha mai Suna Dakta Jane Foster ce ta tsinci Thor bayan Ya fado akan Motarta a dai dai lokacin da suke Kokarin gudanar da wani bincike ita da malamin ta Dakta Erik Selvig da kuma Mataimakiyar ta mai suna Darcy Lewis. Mutanen dake yankin kuma Sai Suka tsinci Mjolnir, Amma an rasa wanda zai ko motsa ta, hakan yasa Suka maida wurin da ta fado Wata Majalisa ta gwada jarumta da basira. Daga baya ne kuma Sai Wani Jami'in Kungiyar S.H.I.E.L.D mai suna Phil Coulson yasa aka zagaye wurin gami da kwashe kayan Jane Foster domin Ya gudanar da Nasa Binciken kan yadda aka yi Thor tare da Gudumarsa Suka fado.

Yayinda Thor Ya samu labarin Cewa Gudumarsa tana kusa, Sai Ya tafi inda take domin Ya dauki abinsa. Anan ne Ya lallasa Jami'an S.H.I.E.L.D bayan sun nemi hana shi kaiwa ga Gudumar, Sai dai bayan Ya isa gare ta, Sai shima ta gagare shi dauka. Da taimakon Dakta Erik Selvig dai aka samu aka sake shi. Daga nan ne Thor Ya gane abinda Ya faru, Don haka Sai Ya karbi kaddara kawai Ya yanke Hukuncin zama a wanna Lardin domin Ci gaba da rayuwar sa. A garin haka ne ma dai har Soyayya ta fara kulluwa a tsakanin sa da Dakta Jane Foster.

Can kuma a Asgard, Loki Ya gano cewa shi Dan Laufey ne ba Odin ba, hakan yasa shi Ya kulla wani tuggu inda Ya baiwa Laufey damar shigowa Kasar domin Ya Kashe Odin. A wannan lokaci kuwa, Odin Ya fada wani nannauyan bacci domin kula da lafiyar sa. Hakan Ya baiwa Loki damar ɗanewa kan karagar Asgard a matsayin mukaddashin Odin. A yayin da Jaruma Sif da sauran jaruman nan uku Suka ga Abu yaki ci yaki cinyewa, sai Suka yanke shawarar dawo da Thor gida domin Yayi maganin al'amarin. Wannan dalili ne yasa Suka je wajen Heimdall wanda shi ne ke gadin gadar da ke baiwa mutanen Asgard damar ziyartar sauran dauloli domin Ya basu damar zuwa daular mutane su ceto Thor.

Da Loki Ya Fahimci haka, sai Ya tura musu wani jibgegen Sakago mai suna Rusau domin Ya Kashe su. Jaruman dai sun sami damar haduwa da Thor, sai dai kafin su Gama murnar haduwa da juna kwatsam sai ga wannan Sakago Ya bayyana. Bayyanar sa ke da wuya Ya fara rusa gidajen Jama'a. Ganin wannan al'amari yasa Thor Ya Sadaukar da kansa domin Ya ceci rayuwar wadanda basu ji ba basu gani ba. Bayan rusau Ya mazge Thor har Ya kusan mutuwa, sai wannan sadaukarwa da yayi ta sa Ya samu Cancantar sake samun damar sarrafa Mjolnir. Don haka, sai gudumar ta zo gare shi inda ta sabunta masa karfin jikin sa da kuma na sihirin sa. Aikuwa nan take Ya Sambade wannan Sakago. Bayan Ya Sambade wannan Sakago ne kuma sai Suka yi Bankwana da Jane Foster tare da yi mata alkawarin zai dawo gare ta, sannan Ya Jagoranci Su Sif Suka koma Asgard.

A can kuma Asgard, Loki Ya yaudari Laufey kuma Ya Kashe shi, sannan Ya bayyana asalin manufarsa da cewa dama so yake yi Ya Kashe Laufey sannan yayi amfani da wannan gadar tsafi wajen hallaka daukacin halittun dake Jotunheim. Loki na tsaka da zartar da wannan hukunci na sa ne Thor Ya iso Asgard kuma Ya yaki Lokin. Ganin cewa babu wata mafita domin dakatar da wanna Bala'i da Loki Ya Kaddamar a kan ahalin Jotunheim, sai Thor Ya ruguza wannan gadar domin hana hakan aukuwa. A dai dai wannan lokaci ne kuma Odin Ya farka daga dogon baccin sa inda yazo Ya ceci 'ya'yan nasa a yayinda suke gab da fadawa ramin da ruguza wannan gadar Ya haifar. Amma shi Loki Sai Ya fada ramin da gangan bayan Odin yaki amincewa da cancantar aikin da ya aikata, hakan Ya sa kowa yayi tunanin cewa loki Ya mutu.

Bayan wannan kura ta lafa, Thor Ya shirya da Mahaifinsa, sannan Ya aminta da cewa lallai bai cancanci Ya zama sarki ba. Yayinda a lardin mutane kuma an nuno Jane Foster tana ta Kokarin ganin ta samu hangar zuwa Asgard.

A wata fitowa ta karshe kuma, an nuno Dakta Selvig a wata Ma'aikatar S.H.I.E.L.D inda Darakta Nick Fury Ya Bude wani Dan akwati Ya nuna masa wani Abu a ciki tare da bukatar yayi nazari akan sa. Sannan an nuno Loki wanda yake boye a bayan fage ta hanyar amfani da tsafi yana zuga Dakta Selvig da ya yarda, shi kuma Ya yarda din.

JARUMAN FIM DIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO DA SHI A CIKIN SA

* Chris Hemsworth - Thor

* Natalie Portman - Jane Foster

* Tom Hiddleston - Loki

* Stellan Skarsgard - Erik Selvig

* Colm Feore - Laufey

* Ray Stevenson - Volstagg

* Idris Elba - Heimdall

* Kat Dennings - Darcy Lewis

* Rene Russo - Frigga

* Anthony Hopkins - Odin

* Tadanobu Asano - Hogun

* Josh Dallas - Fandral

* Jamie Alexander - Sif

* Clark Gregg - Phil Coulson

* Samuel L. Jackson - Nick Fury

* Jeremy Renner - Clint Barton


<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive