TUN KAFIN AURE 39

TUN KAFIN AURE💐39
Wani azababben ciwon kai ta farka dashi lokacin da taji bugun kofa. Sai bayan asuba bacci ya sace ta, dan goge fuska tayi ta bude kofar. Amaka ce dauke da tray ga wani a kasa shima duk kwanukan abinci ne a ciki. Tace Amariya goodmorning...Hafsi ta dan saki fuska ta amsa tare da daukar tray din kasan suka shigo dashi. Amaka tace Madam say make you tell me wetin you wan chop for lunch. Hafsi tace what? Ita fa bajin pidgin english take ba. Ta dai gane lunch ta ce mata ta tafi kawai zata shigo. Har shabiyu tana jira ganin dai bashi da niyar dawowa gashi wayoyinsa duk ta kasa samu ta fito ta tafi main house. Babu kowa a falon sai akwatuna guda uku daga bakin kujera. Dakin Hajiya ta fara leqawa ta ganta tana daura laffaya. A'a mamana keda kike amarya me ya fito dake kuma. Nima shirin komawa Kano nake yi yanzu Rufai nake jira yazo muyi sallama sai a kaini iyaport. Hafsi tayi dan murmushi tace Hajiya bana son ki tafi. Allah sarki Mamana bakya so naje na gyara nawa auren ne? Tare fa aka kawo mu dake gashi muna neman wata daya. Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko mata Hajiya a rude tace haba Hafsatu kada ki karyar min da zuciya mana. Ki kara hakuri in Allah Ya yarda zaku sami zaman lafiya da Junaidu. Kirawo min shi mu yi sallama sannan ki goge idonki kada yace na taba masa mata. Kanta a kasa tace baya nan Hajiya. Dan bata rai tayi ina yaje kuma daga kai masa amarya. Mummy dake tsaye a bakin kofa tace garin yaya kika bari ya fita amarsu. Har kasa ta kai ta gaishe da mummy sannan soma kuka. Duk hankalinsu ya tashi aka suna tambayarta ko lafiya. Da kyar tace musu bai kwana a gida ba. Sai suka fara salati. Mummy ta dauki waya ta kira shi aka yi sa'a a kunne wayar take.

Tilly ta kalli wayar bari na daukar maka Juni boy. Kasan yau rana ta ce so duk mai kira yayi hakuri. Ba musu ya mika mata batare da yasan mai kiran ba. Hello ta fada bayan ta amsa wayar. Mummy a dan razane tace wacece? Ahhh tuni ta gane muryar jarababbiyar babar tashi. Tace matarsa ce Talatu don Allah a dena kira yana bacci ne idan da sako ki fada na gaya masa. Yadda take maganar a ladabce shi yasa Junaid ta kara lafewa jikinta yana mata cakulkuli please ki ajiye wayar anjima na kira. Karaf maganar sai a kunnen mummy tace Junaid da karfi. Tilly bata bare yaji ba ta ajiye wayar ba tare da ta kashe ba tana ta dariya please baby ka bari kaga jiya baka barni na runtsa ba.

Jefa mummy tayi da wayarta tana kuka mai tsuma zuciya. Maganar Junaid ta tabbata karuwa ce yarinyar nan. Suna tare bansan ko a ina ba amma suna tare. Hajiya tace inna lillahi wa inna ilaihi rajiun. Anya zan iya komawa kano kuwa salma? Yarona yana cikin matsala. Mummy tace ki tafi hajiya ai tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa zai daka. Rashin jin maganar iyaye yasa ya kwaso mana balai. Bari na tado Yallabai wallahi a nemarwa yarinyar nan saki tun wuri. Ni bazan iya kallon Safiya ba ina kallo dana yana wulakanta musu 'ya.

Tunda suka fara magana Hafsi ke kuka Mummy ta jawota ta rungume. A haka senator Rufai ya samesu. Bayan anyi masa bayanin abinda ke faruwa yace su kwantar da hankalinsu zaisa a nemo shi duk inda yake a kasar.

Wasa wasa sai da suka yi sati biyu a hotel suna shan soyayya. Hutu ya ratsa su da kyau don daga ci sai kwanciya. Ko kadan baya son Tilly amma ji yake idan ya rabu da ita komai na iya faruwa. Kashe mata kudi yake kamar hauka tana karbewa. Rosie master planner ma an manta da ita .A rana ta shabiyar Senator yasa aka yi freezing dukkanin accounts din Junaid. Matsayinsa yasa har aka nuna masa statement of account din dan nasa. Ba karamin barnar kudi yayi ba a iya kwanakin da baya gida. Senator Rufai ya shiga rudani sosai yadda junaid yake neman kara lalacewa.
Batul Mamman💖

Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive