Skip to main content

Wayyo Rayuwa!

💙💙💙💙💙💙💙💙
~*_WAYYO RAYUWA_*~
💙💙💙💙💙💙💙💙

BISMILLAAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir Raji'un.

Yaku ƴan uwana masu karatu, wannan labari da zan baku ya faru ne da gaske, domin na san wacce abin ya faru a kanta ba wai labari aka bani ba. 

An yi wata budurwa Musulma kuma Bahaushiya wacce ta bar gida ta shigo bariki ta kama ɗaki ta ci gaba da sheƙe ayar ta. Baya ga bin maza da wannan budurwa take yi, tana shaye-shaye, sannan kuma tana harkar maɗigo. 

Tun a lokacin da take ganiyar ƴammatancin ta wani babban mai muƙami a cikin sojoji ya nuna yana so ya aure ta, ya gina mata tamfatsetsen gida kuma ya shirya komai na auren, kawai amincewar ta yake nema, amma baiwar Allaah nan ta ƙi amincewa. 

Daga baya tazo tayi wata ƴar rashin lafiya duk ta bi ta rame, ya zamana kaurin jikin ta bai wuce ka rutsa shi ba da yatsu biyu. Wannan bai sa fa ta dawo hayyacin ta ba. Watarana kwatsam sai wani mugun ciwo ya kamata har aka kwantar da ita a asibiti bayan wasu ƴan kwanaki sai aka maida ita gida, a can ne Allaah yayi mata rasuwa.


Wannan al'amari ne ya sa na tuna da wata mace ita ma da ta fito bariki tun tana budurwa har takai kusan shekaru tamanin a duniya bata daina bariki ba, ma'ana ta zama irin tsofaffin nan na bariki.

A ranar da matar nan ta mutu sai da aka rasa wanda zai mata wankan gawa ma ballantana ayi mata sallah, daga ƙarshe dai wani ɗan shaye-shaye aka kira aka bashi kuɗi ya ɗauki gawar yaje ya haƙa rami a daji ya binne ta.

Yaku ƴan uwa na masu daraja, ina so mu dubi waɗannan Labarai guda biyu da kyau, Fisabillahi wace riba ce waɗannan mata suka ci a rayuwar su? Tsakani da Allaah Labaran su bai yi Kamanceceniya da halayyar wasun mu ba dangane da ƙin tuba da komawa zuwa ga Allaah?

Ina fatar Allaah Ya Shirye mu, Ya Ƙara mana imani, ya nuna mana gaskiya kuma ya bamu ikon binta, ya nuna mana ƙarya kuma ya bamu ikon guje mata.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika.

<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...


Comments