Skip to main content

RAYUWAR DUNIYA ABAR TSORO CE*_RAYUWAR DUNIYA ABIN TSORO CE!_*

Mutuwa ba sallama, kuna tare da mutum yanzu ko kungama waya dashi yanzu zaka iya jin cewa ya mutu, Allah yasan hikimar da tasa ya boye mana lokacin mutuwa. Yanzu jama'a sun fara gane cewa mutuwa bata da alaka da rashin lafiya.
Shawara ta garemu anan shine: Kada ka/ki yarda ka jinkirta abubuwa biyu zuwa gobe, sati maizuwa, wata mai zuwa, sai kagama university, sai kayi aure ko kadawo daga Lagos. 
Abu nadaya shine, bauwata Allah abinda zai kusantar da mu ga Allah. Kada kace sai gobe..... zan tuba ko zan kiyaye sallah ko zan fara karatun al-Qurani ko wani aikin alkhairi. Goben fa ba tabbas kuma ma ida goben tazo kayi nayau kayi na goben zaka samu ladan yau da gobe kuma koda goben zatazo kasaba, idan kuma sai goben kafara ladan zai fara daga gobe ne.
Abu na biyu, jin dadin yaruwar ka ta hanyar halas da abinda Allah ya hore maka. Kada kace sai gobe....zan ci abinci mai kyau ko sutura mai kyau ko abin hawa mai kyau ko wani abu kamar haka, alhali kana son abin kuma kanada halin yin sa kuma halas ne Allah ya halasta. Goben ba tabbas kuma koda goben tazo ba dole kaji dadin abin ba kamar yadda zakaji dadin sa a yau. Kullum muna kara shekaru muna rage kyau da jin dadin abubuwan rayuwa. Duk tufafin da zaka/ki saka suyi ma ka/ki kyau a yanzu bazasu yiwa mahaifanka kyau ba, duk abincin dazaka ci yayi maka dadi yau badole yayi wa mahaifan ka dadi ba, saboda muna kara tsufa dadin duniya yana raguwa. Nafahimci cewa kullum ina koyon abubuwa a rayuwa ta hanyar karin shekaru fiye da yadda nike koyon su a littafe. Duniya Makaranta ce babba wacce cikin ta duk makarantu suke. 
Allah yasa mu cika da Imani

Rubutawar: ✍
*_Sheikh Dr. Jabir Sani Maihula {Hafizahulllah}._*

Daga: *_ZAUREN ADDIINU ANNASIHATU._*

Comments