Sunday, 30 December 2018

SHIN YA HALATTA NA TAIMAKAWA KIRISTA DA JINI?

*_SHIN YA HALATTA NA TAIMAKAWA CRISTER DA JINI?_*
                           *Tambaya*
Assalamu alaekum! Malam dan girman Allah ko ya halatta mutum ya baiwa christa jini a asibiti, ganin cewar christan ya shiga wani
hali kuma akwai sanayyah tsakanina da shi?


                             *Amsa*
To malam wannan mas'alar tana daga cikin mas'aloli sababbi wadan da ba'a san su ba a can baya, amma kuma Mujamma'u fiqhul-islamy da ke Makka a saminarsu ta takwas wacce aka yi a ranar 19-28 na janairun shekarar 1985, sun tabbatar da halaccin taimakawa crista da jini idan yana rashin lafiyar da ake bukatar hakan, mutukar ana zaman lafiya da shi, saboda hakan yana daga cikin tamakekeniyar da Allah ya yi umarni da ita, kamar yadda Allah yake cewa a cikin suratul-Mumtahanah aya ta: 8, "Allah ba ya hana ku ku kyautatawa kafiran da ba su yake ku ba" sannan hakan zai kara fito da alkairin da yake cikin musulunci, ta yadda wasu za su yi sha'awarsa.

Amma idan akwai yaki tsakaninsa da musulmai to bai wajaba a ba shi ba, sai in ya kasance ribatacce ne a tsakanin musulmai, ko kuma ana tunanin hakan zai iya jawowa ya shiga musulunci.

Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba Fatawaa Nurun Aladdarb: 1/376.

10/02/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.


EmoticonEmoticon