Wednesday, 15 May 2019

TA'ADDANCIN MASONIYYA 10

TA'ADDANCIN MASONIYYA 10

Har ila yau, kungiyar Masoniyya tana amfani da kafar
nishadi (Entertainment industry) domin jawo mutane
Izuwa ga tunani irin nasu. Ko dai a boye ko kuma a
bayyane, kullum yada akidar su suke yi. Hanyoyin da
'yan Masoniyya suke amfani da su wajen Dulmiyar da
mutane suna da yawa, amma manufar su guda ce.
Manufar kuwa ita ce ya Zamana kowa ya bi bayan su
domin Shiryawa zuwan Dujal. 

Wadannan mutane a
kullum suna nan suna ta kokarin ganin sun dasawa
mutane tunani, akida da kuma ra'ayi irin nasu a cikin
zukatan su ta yadda mutum a hankali tunanin sa
zai rika canjawa izuwa ga gurbataccen tunani irin na su
ba tare da ya fahimci hakan ba.

Wasu mutane da dama suna karyata bayyanar waɗannan mutane da kuma kungiyar su, sai dai kuma Alamomin bayyanar su
a duniyar Nishadi (Entertainment World) a bayyane
suke karara. Daya daga cikin Manyan makaɗan kasan Turai Wolf
Gang Amadeus shi ma dan Masoniyya ne, kuma shi ne
ya shirya wani sauti mai dankaren dadi wanda
Masoniyya suke amfani da shi a matsayin taken su. 

Ya tsara wannan sauti ne akan wani labari da aka samo
daga Misra tun a Zamanin Jahiliyya, labarin kunne ya
girmi kaka ne akan Avyus da Cyrus da kuma irin al'adun
da ake Gabatarwa na Addinin Bautar Gumaka da kuma
tsafi irin na Kabala, daya daga ciki Manya Manyan
Ginshikan kafuwar Masoniyya.

 Daga cikin wannan bakin
addini na Zamanin Jahiliyya ne aka samo Tambarin ido
daya wanda Masoniyya ke amfani da shi. Shaidun
wanzuwar Masoniyya a cikin duniyar Nishadi ana iya
samun su a cikin Wakoki da kuma Fina Finai na
wannan zamani da muke ciki waɗanda anan gaba zan yi sharhi akan su sosai in shaa Allaah. 

Michael Jackson shi ne
Mawakin da har yanzu ba'a taba yin kamar sa ba a
kasar Amurka, shi ne kuma Mawakin da ya fitar da
kundin Wakokin da har yanzu ba'a sami wanda ya fishi
kawo kudi ba a harkar Kasuwancin Wakokin duniya
gaba daya, to shi ma yana da alaka da 'yan Masoniyya.

Da zaka duba Ainahin bangon kundin Wakokin sa mai
suna "Dangerous" zaka ga abubuwan ban mamaki. Da
farko dai akwai Hoton ido dayan Masoniyya a jiki, sai
kuma Hoton wani Takadiri kuma fitaccen kafiri sannan
kuma Gawurtaccen Matsafi mai suna Aliester Crowley
(zan kawo muku Cikakken Tarihin sa Watarana in shaa
Allah), shi wannan mutumin dan Masoniyya ne daga
baya kuma ya koma Bautar Shaidan. Kuma shi ne ya
rubuta wani littafi mai suna "The New Law Of Man"
Wanda a cikin sa aka rubuta cewa, wai a karshen
Duniya wannan littafi shi ne zai maye gurbin Kur'ani
(A'uzubillah). Allah wadai da irin wadannan mutane da
ma sauran masu biye musu.

Zan ci gaba In Shaa Allah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*


TA'ADDANCIN MASONIYYA 09

TA'ADDANCIN MASONIYYA 09

Yayin da 'yan Masoniyya suka fahimci wannan al'amri,
sai suka sake kulla wani gagarumin tuggu wanda irin
sa bai taba wanzuwa a ban kasa ba, wannan tuggun
kuwa shi ne hana mutane' Yancin yin tunanin da ya
dace suyi.

Don ganin sun cirewa mutane 'Yancin yin
tunanin da ya kamata, sai Masoniyya ta kafa wata irin
katuwar Katangar KARFE tsakanin mutane da kuma
tunanin da ya kamata ace shi suke yi ta yadda kalilan
din mutane ne ke iya Ratsawa ta cikin wannan
katanga. Ita kuwa wannan katanga an sana'anta ta ne
ta hanya tattaro duk wasu hanyoyin rayuwar dan Adam
gaba daya. Kuma Makaman da suke Yakar mutane da
su suna nan a cikin gidajen mu suna Nishadantar da
mu da iyalan mu.

 Wadannan Makamai da su ne ake
amfani wajen Yakar tunanin mutane ba tare da sun
ankara ba, kuma wadannan Makamai su ne suke
canjawa mutane tunanin su a hankali Izuwa ga tunani
irin na Masoniyya ba tare da sun ankara ba. A wannan
Zamanin da mu ke ciki yanzu, mutane da yawa suna
Banzatar da lokutan rayuwar su ta hanyar rudu da
kuma ci gaban da zamani ya kawo, Talabijin, Sinima,
waya, Kwamfuta, yanar gizo, wasanni, Fina Finai, kade
kade, raye raye da wake wake sun zama wani bangare
na rayuwar mutanen wannan zamani namu.

 Dukkan
wadannan abubuwa suna dauke da wasu jiga jigan
bayanai da kuma Sakonni wadanda mafi Yawancin su
Gurbatattu ne, irin wadannan Sakonni na batanci da
shaidana a hankali suke samun wurin zama a zukatan
mutum, kodai cikin rashin sani ko kuma da gangan. Ta
hakane suke Cusawa Mutane sabbin dabi'u da munanan
halaye Iri daban daban, daga cikin abubuwan da suke
koyawa mutane ta wannan hanya ko kafa shi ne "yadda
ya kamata ace duniyar ta kasance" ko kuma yadda ya kamata ace rayuwar ita kanta ta kasance a bisa tsari da
tunani irin nasu.

 Irin wadannan munanan akidu da kuma
halaye su ake yadawa kullum a cikin wadannan kafafe.
A takaice dai, kafar yada labarai wa al'umma (mass
media) ita ce babbar hanyar da 'yan Masoniyya ke
amfani da ita wajen yada akidun su, dabi'un su, halayen
su da kuma burin su. Kenan idan har wannan kungiyar
tana da damar juya irin wadannan al'amura, to ba abun
mamaki bane don sun sami damar jawo dubban mutane
Izuwa ga wannan tsari na su, wato sabon tsarin duniya.

Wannan itace hanyar da Masoniyya ke bi don ganin sun dulmiyar da mutane izuwa ga sabon Allaah mafi girma wato kafirci. Don haka lallai ne mu kiyaye da irin abubuwan da muke mu'amala da su, kuma mu dinga kyakkyawan nazari akan irin wadannan abubuwan don KAUCEWA fadawa tarkon 'Yan Masoniyya.


Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*

🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

TA'ADDANCIN MASONIYYA 08

TA'ADDANCIN MASONIYYA 08

A haka Masoniyya tayi ta juya tunanin mutane da
yanayin su Izuwa fushi, kamar dai Faransawa, fushi sai
ya koma fada, amma a wannan karon basu bari Suka
sami matsala ba, irin artabun da suka sha da Napoleon
a Yurop ya koya musu darasi, don haka suka sa dokar
duk wani shugaba da zai fito daga cikin 'yan adawa to
dole ne ya bi DOKOKIN Masoniyya, hanya mafi sauki da
za'a tabbatar da an sami damar yin hakan ita ce, a
tabbatar da cewa shi kanshi shugaban dan Masoniyya
ne, kuma ba wani shugaba bane ya Jagoranci wannan yakin
neman' Yanci daga Birtaniya a Wancan lokaci ba face
George Washington.

 A Ranar hudu ga watan Yuli na
shekarar alif dubu daya da dari bakwai da saba'in da
shida (4th July 1776) Ne aka tabbatar da niyyar neman
'Ƴancin kan Amurka, yayin da a Ranar sha bakwai ga watan
oktoba shekara ta alif dubu daya da dari bakwai da
tamanin da daya (17th October 1781) kuma aka sami
galaba akan Birtaniya in da suka Mikawa Amurka' Yancin ta.

A wannan rana ce kasar 'yan Masoniyya ta farko ta kafu a duniya, kasar da zata wakilci
Masoniyanci ta kowace fuska. Alamomin wanzuwar
Masoniyya a kasar Amurka Bayyanannu ne, a jikin dalar
Amurka, akwai Hoton George Washington, shugaban
kasa dan Masoniyya na farko a duniya kenan, tare da
tambarin Masoniyya wanda ake kira "ido daya mai ganin
komai", (The All Seeing One Eye).

Tarihi ya nuna cewa,
dulmiyar da mutane izuwa ga bata, canjawa mutane
tunani tare da wasa da hankulan su, musamman ta
fagen siyasa, su ne Manyan abubuwan da 'yan
Masoniyya suke amfani da su wajen Mallakar duk kasar
da suka dira akan ta.

Da zarar sun kama ' yan siyasa,
attajirai da sauran Manyan kasar, sai kaga dare daya
kawai DOKOKIN wannan kasa ta canja izuwa ga tsari
da Tafarki irin na Masoniyya. To amma tunda hana jiki
ba yana nufin hana zuciya ba ne, sai Masoniyya ta
fahimci cewa burin su na son ganin sun mulki duniya
gaba dayan ta ya ta'allaka ne akan jawo dukkan
mutane daga kowane sashe na duniya izuwa ga tsarin
su.

A tunanin su idan suka yi hakan, Shikenan sun
kashe duk wata dama da wani ko wasu za su iya samu
wajen yin jayayya da su. Wannan dalili ne ya sa 'yan
Masoniyya suka bude kofar su ga kowa ga kowane irin
mutum daga kowane irin addini.


Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐
*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

TA'ADDANCIN MASONIYYA 07

TA'ADDANCIN MASONIYYA 07


Nathan Rothschild shi ne shugaban Bankuna na
wancan lokacin, amma saboda Kasancewar su
Yahudawa, sai ya Zamana ana nuna musu Banbanci.

Nathan sai yayi Amfani da wannan dama wajen hada
kan Jama'ar sa, inda ya yarda cewa zai baiwa Yurop
rancen kudi amma bisa Sharadin za'a dinga daukar
Yahudawa da Muhimmanci kamar sauran 'yan Yuropiya,
kuma za'a basu dama Suyi Kasuwanci irin wanda suke
so. Idan' yan Masoniyya suka ki yarda, kudin za su
koma wajen Napoleon. Ganin cewa ba su da wani zabi
face su Amince, sai suka sanya hannu a takardar
Yarjejeniyar hakan.

A wannan shekara ce sojojin Birtaniya,
Dutch da na Rasha suka dira a Waterloo dake kasar
Belgium inda suka hadu da dakarun Napoleon kuma
suka ci su da yaki. A wannan lokaci ne aka kama
Napoleon, dawowar da bai yi ba kenan. A karshe dai
Faransa ta koma Karkashin Mulkin Masoniyya.

 Duk da cewa Malaman Tarihi basu yi wani Cikakken Bayani
dangane da sa hannun Masoniyya wajen samun 'Yancin
kan Faransa ba, su' yan Masoniyyar sai da suka fito da
kan su suka bayyana irin rawar da suka taka wajen yin
hakan. A shekara ta alif dubu daya da dari tara da
hudu (1904), wani Dan Masoniyya mai suna Mac
Vadora Sambo ya furta wasu kalamai a bainar
jama'a inda ya ce "Masoniyya ta yi aiki tukuru ta
Boyayyiya kuma Jajurtacciyar hanya wajen haifar da
yakin neman 'Yancin kan Faransa, hakan yasa duk
muka yarda cewa Masoniyya tare da samun damar
Kaddamar da wannan Fafutikar ta neman' Yancin kai
tare da yarda da ni da aka yi, ya tabbatar da cewa kun
aminta da ni cewa, Masoniyya ce Ginshikin samun
'Yancin kan Faransa",!!!


A lokacin da iyayen Amurkawan yanzu
suka yada zango a dutsen play mouth, ba wai kala-kalan mutane daban daban kawai suka debo tare da su
ba, har dabi'un Masoniyya ma sun debo. Irin Zaluncin
da iyayen Amurkawan suka guda daga Yurop, sai ga shi
anan ma sun same shi a Karkashin Mulkin Birtaniya.

Domin su sami damar Mulkin wannan sabon wuri, sai
'yan Masoniyya suka yi amfani da irin tuggun da suka
Kullawa Faransawa. Duk da cewa Masarautar Birtaniya
tana Karkashin ikon Masoniyya ne, yakin neman' Yancin
Amurka ya zama dole ne ga 'yan Masoniyya, kuma
wadanda suke wannan yaki zaratan Azzalumai ne
wadanda zasu iya yin komai domin ganin biyan Bukatun su.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

TA'ADDANCIN MASONIYYA 06

TA'ADDANCIN MASONIYYA 06

Gurbatattun 'Yan Siyasar da Masoniyya ta tanada kuma
sai suka dinga yada Akidar Masoniyya ta ko ina. Manya
Manyan Lojinan Masoniyya (Masonic Lodges) kuma sai
aka bude su ga Sojojin Faransa, Manyan kasar da
Janarori duk aka dulmiyar da su Izuwa ga Gurbataccen
tunani irin na Masoniyya.

 Lokacin da Masoniyya ta ga
cewa ta kama 'Yan Siyasa, Attajirai da kuma Yawancin
mutanen Faransa a Karkashin ikon ta, sai ta fara
kaddamar da Mummunar Manufar ta.

A Ranar sha hudu
ga watan Yuli shekara ta alif dubu daya da dari bakwai
da Tamanin da Tara (14th July 1789), wasu mutane da
ba'a san ko su waye ba, suka afka gidan yarin Basteel
dake Farisa (Paris). Wannan al'amari ne fa ya tadawa
mutane hankali, akai ta Surutai iri iri Musamman akan
irin raunin Mulkin Masarautar Farisa. Sai dai fushin 'yan
kasar bai samu gushewa ba har sai a shekara ta alif
dubu daya da dari Bakwai da casa'in da uku (1793).

A Ranar Ashirin da daya ga watan Janairu na wannan
Shekarar ce aka sarewa Sarki Louis XV kai a bainar
Jama'a, hakan ne ya kawo karshen Mulkin Gargajiya a
kasar Faransa. Daga nan ne kuma aka sake share
sabuwar hanyar da zata taimakawa Masoniyya wajen
cimma burin ta a Yurop. Bayan faruwar hakan,
Masoniyya gani take tamkar ta gama samun Ragamar
Mulkin kasar Faransa. Sai dai abinda ya biyo baya wani
al'amari ne da yayi matukar girgiza su sannan kuma ya
tayar musu da hankali.

 Wani Matashin Soja da ake kira
Napoleon Bonaparte ne ya taso da nufin mulkar
Faransa ko ta halin kaka. Amma Maimakon ya biyo ta
hannun Masoniyya, kawai sai ya kaddamar da kan shi a
matsayin sabon Sarkin Faransa.
Bayan an tafka yaki ne
daga karshe dai aka matsawa Napoleon har sai da ya
arce daga kan Karagar sa a shekara ta alif dubu daya
da dari takwas da goma sha hudu inda ya gudu Tsibirin
Corcica.

Shekara daya da faruwar hakan, sai ga
Napoleon ya sake bayyana a Farisa yana Tara sabbin
Mayaka domin sake Tunkarar Yurop. To anan fa sai
'yan Masoniyya hankalin su ya tashi, domin kasar
Birtaniya tare da Kawayen ta ba zasu iya jure fada da
Napoleon na tsawon wani lokaci ba face sai sun afka
cikin Matsanancin Talauci.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.


<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

TA'ADDANCIN MASONIYYA 05

TA'ADDANCIN MASONIYYA 05

Wannan sabon suna da kuma sabon tsarin da suka zo
da shi, shi ne ya baiwa Membobin kungiyar cin karen
su babu babbaka ya kuma kara musu kima a idon
duniya. Memba na farko da ya fara bayyana kan sa shi
ne Fredrick Yariman Wales (Fredrick The Prince Of
Wales), daga cikin Membobin su na baya kuma akwai
irin su Prince Philip mai Mulkin Edinborough har zuwa
kan Sarauniyar Ingila ta biyu (Elizabeth II), ita ma
babbar mai lura da Al'amuran kungiyar ce.

 Sai dai kuma, ta bayan fage, 'Yan Masoniyya suna da damar
yin tsafe tsafe, sihiri da Siddabaru.' Yan Masoniyya ba
wai mulkar kasar Birtaniya bane kawai a gaban su. Ina!
Burin su yana da matukar fadi da kuma girma.
A Shekarun da suka biyo bayan Bayyanar su munga
yadda yaki ya barke a tsakanin kasashe da dama da
Amurka. Sai dai duk wadannan abubuwan ba wai
Faruwa suke yi saboda ragwanta ko Sakacin al'umma
ba, a'a wannan ba komai bane face tuggu irin na 'yan
Masoniyya, Mutane ne' yan kalilan amma su ne ke
shirya tashin hankalin da ka iya addabar duniya baki
daya.

Duk wannan artabu zai faru ne daga kasar da
suka tsere daga cikin ta a Shekarun baya, daga nan
kuma Izuwa ga duniya baki daya.
A karni na sha
takwas (18th Century), Yawan cin Mutanen Kasar
Faransa suna fama da Talauci da kuma Karan cin
kayan Masarufi, yayin da Shugabanni da Attajiran su
kuma suke sheke ayar su tare da Almubazzaranci da
dukiya yadda ran su yake so. A Wancan lokacin, akwai
tazara sosai tsakanin mai kudi da Talakan Faransa.
Faruwar hakan ne ya baiwa 'yan Masoniyya damar
shirya wata gadar zare wacce zata canja kasar
Faransa, Canji na har abada. Masoniyya tayi amfani da
fushi da kuma qiyayyar dake tsakanin Jama'ar kasar
Faransa wajen rikita musu tunani. Kamfanonin Jaridu
kuma suka dinga zuga mutane wajen ganin an kau da
Mulkin Gargajiya (na Masarautu) a kuma kafa Siyasar
Dimokuradiyya ta hanyar 'Yanci, Cancanta da kuma
Kwarewa. Tarin Dukiyar da Masoniyya ta tara kuma sai
aka dinga amfani da ita wajen canja Akalalar Siyasar
Faransa tare da Cusawa Shugabanni ra'ayi da kuma
tunani irin na Masoniyanci.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176


*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

TA'ADDANCIN MASONIYYA 04

TA'ADDANCIN MASONIYYA 04


A shekara ta Alif dubu daya da dari uku da goma sha
hudu (1314), wannan kungiyar Mayaka ta 'Yan Tampula
(Knights Templers) sai suka hada hannu da Sarki
Robert The Bruce tare da Mayakan sa suka nufi
Ballack Burn domin su gwabza da Mayakan Ingila.

Idanun Sarki Robert sun ga abin mamaki a wannan
yaki, inda zaratan Jaruman Ingila har guda dubu
ASHIRIN da biyar (25,000 men) suka sha kashin tsiya a
hannun mutane dubu shida da doriya. A karshe dai,
kasar Scotland ta samu 'Yancin kai. To tun daga nan
ne fa sai wannan kungiyar Mayaka ta dawowa da kanta
martabar da aka santa da shi a baya ta yadda ba za'a
taba iya karya ta ba, kuma suka sha alwashin ba za'a
kara samun galaba a kansu ba. Sun kuma sha alwashin
su zasu koma juya kasar yadda suke so ta hanyar juya
Sarakunan kasar a tafin hannun su. Sai dai kuma idan
har suna so su cimma wannan buri, to dole ne acikin
biyu ayi daya : ko dai su mutu ko kuma sunan su ya
mutu.

Wadannan Mayaka dai sun samu wajen zama a
Rovelin Chapel na kasar Scotland wanda ya zama
shaidar wanzuwar su a Yankin Birtaniya har Izuwa
wannan lokaci da muke ciki.
A shekara ta Alif dubu
daya da dari shida da uku (1603), mutuwar Sarauniya
Elizabeth ta Farko (Queen Elizabeth I) ya jawo wa Ingila
zama ba tare da Magaji ko Magajiya ba. A bisa dacewa
da Cancanta, Sarki James na biyar (King James V) na
Scotland ya zama Sarkin Ingila a wancan lokacin. Yin
hakan ya sa Scotland da Ingila suka hade wuri daya
suka samar da sabuwar Masarauta. A dalilin hakan, sai
karfin wannan kungiya ya kara habaka ta yadda cikin
sauki suka kama zuciyar Birtaniya. Saboda kwarewa da
suka yi a fannin Munafurci da iya ladabin Kunama, sai
da wannan kungiya ta share sama da shekaru dari tana
aiwatar da Aiyukan ta a Sirrance.

A hankali suka dinga
bacewa daga bakin mutane har ya zamana da qyar ma
ake iya tuna sunan su. Sai dai kuma duk tsawon
wannan lokacin sunyi bakam ne suna ta kutsawa cikin
kowane sako da lungu na kasar.
A shekara ta Alif dubu
daya da dari bakwai da goma sha bakwai (1717),sai ga
shi sun sake bayyana a Yuropiya. Yanzu sun kara yawa
da kuma karfi, kuma a shirye suke su kawo sabon
tsarin samun 'yanci wa kansu daga halin da suka shiga
a baya,tare da samun Cikakken ikon yin hakan daga
Madafan Iko da sauran masu fada a ji na kasar Ingila.

Anan ne suka Laqabawa kansu wani sabon suna, sunan
da kusan kowa ya san shi sai dai ba kowa ya Fahimce
shi ba. Wannan sabon suna shi ne THE FREEMASONS!!
('Yantattun Magina (duniya).
'Yan Masoniyya kenan a
Kungiyance.


Zan ci gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

TA'ADDANCIN MASONIYYA 03

TA'ADDANCIN MASONIYYA 03

A Jerusalem, a hankali a hankali sai wadannan Mayaka
suka fara ja da baya daga koyarwar addinin Kiristanci,
in da suka koyi dabi'un Kabala, daya daga cikin manya
manyan Sashen tsafe tsafen zamanin Jahiliyya, tare da
yadda ake gudanar da tsafin da kuma yi masa hadaya
(da mutane).

Yahudawa sun koyi wannan tsafin ne
daga Bokayen Misra a lokacin cinikin bayi na zamanin
Sarki Fir’auna, daga baya kuma sai suka daukaka shi Izuwa Babila (Babylon) a zamanin Navakanazar.
A shekara ta Alif dubu daya da dari uku da bakwai
(1307), Sarki Philip na kasar Faransa yasa aka damqe
su bisa zargin su da ake yi da laifin kin yarda da
Almasihu, Luwadi, bautawa gumaka da kuma aikata
tsafe tsafe. A shekara ta Alif dubu daya da dari uku da
goma sha hudu (1314) Fafaroma Claymont na biyar
(Pope Claymont V) ya bayyana cewa duk mazaunan
wadannan Mayaka suna tababa da koyarwar addinin
Kiristanci, sannan ya sa aka kwace dukiyoyin su da
kuma Kadarorin su gaba daya. Shugaban su na wancan
Lokacin mai suna Chek The Moley kuma aka kamo shi
aka qona shi da ranshi a bainar jama'a.
Daga nan
Kungiyar ta Tarwatse. Sai dai kuma a lokacin da ake
tunanin an rushe su gaba daya, ashe ba anan gizo ke
saqar ba, domin wasu daga cikin su sun sami isa ga
tudun mun tsira, inda Suka sami mafaka da kuma
abokan Harkalla, sai dai ba a Faransa wannan dama ta
samu a gare su ba, a wata kasar ce daban wacce a
wancan lokacin ta ke matukar bukatar 'Yancin kai daga
turawan Ingila, wato Scotland.

A tunanin mutane da
dama, burin samun - Yancin kan Scotland ya rushe ne
a Sanadiyyar mutuwar William Wallace, amma ga Sarkin
Scotland na wancan lokacin, Robert The Bruce,
wanzuwar wadannan Mayaka a kasar sa ya samar
masa da wani babban Makami da zai taimaka masa
wajen cimma burin sa. Irin sanin Makama da dabarun
yaki da suke da shi sakamakon artabu da suka sha yi a
baya yasa suka zama zaratan Jarumai a fagen yaki fiye
da duk Mayakan da aka hada su da su.

Zan ci gaba In Shaa Allah


<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

TA'ADDANCIN MASONIYYA 02

TA'ADDANCIN MASONIYYA 02

Wadannan mutane sun sami sa'ar dulmiyar da mutane
da dama Izuwa ga gurbataccen tunani irin na su.

 Su wadannan mutane suna da qafa a kowane lungu, sako,
kwana Da kuma kowane irin kwararo na rayuwar mutane
a ko ina a cikin fadin duniyar nan.
Duk wani waje da
ake gudanar da wani muhimmin al'amari, to ka tabbatar
cewa suna da jami'ai a wajen. Sannan daga bayan fage
ne suka samu damar bullo da wata sabuwar dokar
siyasa, sabuwar dokar Kasuwanci kuma sabuwar dokar
Addini.

Babban muradin su shi ne su mamaye duniya,
ya zamana kowa su ya ke bi, kuma zasu iya yin KOMAI
don ganin burin su ya Cika.
Tsohon Shugaban kasar
Amurka, biri mai muguwar barna ya taba bayyana cewa
: "wannan shiri da kuke gani ba wai na karamar kasa
ba ce kawai, tunani ne mai fadin gaske, sabon tsarin
duniya", (New World Order).
Yanzu ashe har wani ya
isa ya kawo wani tsari da ya fi na Allah??? Sam bai
Yiwuwa.


Sai dai kuma, asalin wannan shiri na sabon
tsarin duniya (New World Order) ko kuma in ce sabuwar
dokar duniya da ake son kafawa, ba daga fadar Amurka
abin ya soma ba. Asalin shi ya fara ne tun daga wani
katafaren yaki da aka yi a shekara ta alif dubu daya da
casa'in da biyar (1095) a Cleremont da ke kasar
Faransa.

A karni na sha daya (11th Century), Kasar
Yuropiya tana karkashin shugabancin wani babban Coci
ne wanda ya sami babban matsuguni a zukatan dubban
jama'a. Irin wannan karfin mabiya da suka samu ne ya
sa Fafaroma Erwind na biyu (Pope Erwind II) ya samu
damar kaddamar da yaki akan musulman wancan
lokacin domin ya kwato Jerusalem.
A Sanadiyyar
wannan yaki ne aka yiwa matayen Musulmai da yawa
Fyade, sannan aka hallaka su, aka karkashe yara da
tsofaffi har sai da ta kai cewa jinin dake kwaranya a
kasa gab yake da ya kawo guiwoyin dawakan dake filin
yakin.

 Ana cikin wannan yanayi na hatsaniya ne, sai
wata kungiyar Mayaka ta bayyana, Mayakan da suka
kware wurin iya yaki, Mayakan da zasu iya bin kowace Hanya
don ganin burin su ya cika komai runtsi da tsananin
dake cikin yin hakan.
Bayan shekaru ASHIRIN da karbe
Jerusalem daga hannun Musulmai, sai jagorancin
wannan wuri ya fada hannun wadannan Takadiran
Mayaka masu zaman Zuhudi da ake kiran su da 'The
Knights Of The Temple Of Solomon' (wato Mayakan
Majami'ar Salamon) ko kuma 'Knight Templers' kawai
(wato Mayakan Majami'a).
Ni kuma sai na kira su da
suna 'Yan Tampula'.

Zan ci gaba In Shaa Allaah.


<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

TA'ADDANCIN MASONIYYA 01

TA'ADDANCIN MASONIYYA 01

Bismillahir Rahmanir Raheem
Assalamu Alaikum WarahmatullAllah Wabarakatuhu.

A Ranar Biyu ga watan Agustan shekara ta alif dubu daya
da dari tara da casa'in (2nd August 1990) ne Rundunar
mayakan shugaba Saddam Hussein na Iraqi suka sami
galaba akan dakarun kasar Kuwait.

 Saboda tsoron kada
Iraqi ta kai hari wa Saudi Arabia, sai Amurka tare da
kawayenta suka barbazu a yankin domin su kafa wani sabon tuggun.

A dalilin hakan ne aka samu wasu
zantuttuka, hadaka da kuma tataburzar da ta kai
mutane izuwa qangin da babu madogara sai Allah. A
Ranar sha bakwai ga watan Agustan shekara ta alif
dubu daya da dari tara da casa'in da daya (17 August
1991) ne wannan tuggu da Amurka da kawayenta suka
shirya ya fara fashewa, in da aka tafka kazamin yaki.

Jama'a da dama sun ga yadda abin ya faru ta kafafen
sadarwar I.F,CNN da BBC, Yadda aka yi amfani da
tsabar fifiko a bangaren makamai, siyasa, qarfin mulki
da kuma qarfin tattalin arziki wajen murkushe dakarun
Shugaba Saddam Hussein. Sai dai kuma abin da
Yawancin mutane basu gane ba shi ne, ta bayan fage,
wannan yaki dama a shirye yake, kuma an tafiyar da
shi yadda ake so ne a karkashin jagorancin wasu
batattu kuma la'anannun mutane bisa tsarin wata
kungiya. Kungiyar da ta samar da wani mutum mai
karfin iko a cikin zaratan jaruman yaki, mutumin da
kafin qiftawa da bismillah ya samu iko akan kaso daya
cikin biyar din man fetur din duniya shi kadai.

 Sai dai
kuma shi ba komai bane face karen farauta daga cikin
sauran Karnukan Farauta, kamar dai yaron da ya zauna akan
kujerar da aka daura shi. Ga kuma yakin GULF WAR a
gaban shi (bayan tarin makamai da aka bashi) domin
ya samu abin tabi.
Wadanda suka shirya wannan tuggu
ba baki bane, domin sun yi kaurin suna wajen shiryawa
da kuma tsara manya manyan aiyukan ta'addanci da
cin zarafi iri iri da suka faru a tarihi. Su suke shiryawa ko
kulla duk wani mashahurin yaki, tawaye, juyin mulki, kai
hare - hare, kashe kashe na babu gaira babu dalili.

Wani abin takaici kuma shi ne, su suke sarrafa duk
wani abu da kake gani, ji ko kuma karantawa, idan har
ba duka ba to su ke sarrafa kashi casa'in cikin darin
wadannan abubuwa. To wai Shin su waye wadannan??
Kuma me suke takama da shi?!
Zan ci gaba In Shaa Allaah.


<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Hãïmâñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*

Tuesday, 12 March 2019

ALLAAH YA SANYA TSAYAR DA ADALCI A BAYAN ƘASA...

Allah Ya Sanya Tsayar Da Adalci A Bayan Kasa Ya Zama Sharadin Samun Zaman Lafiya Da Cigaba Mai Dorewa!

Daga Imam Murtadha Gusau

Talata, 12 Mayu, 2019

Bismillahir Rahmanir Rahim

Lallai dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna yabon sa, muna neman taimakon sa, kuma muna neman gafararsa. Muna neman tsarin Allah da kariyarsa daga sharrin munanan ayyukkanmu. Duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, kuma duk wanda Allah ya batar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa lallai babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad, bawan sa ne kuma Manzon sa ne. 

Salati da sallamawa da tsira su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da matansa da duk wanda yayi imani da shi kuma yayi aikin kwarai har zuwa ranar tashin kiyama.

Bayan haka:

Ya ku bayin Allah! Ku sani, lallai Allah Ya umarce mu da tsayar da adalci a bayan kasa, kuma ya sanar da mu cewa, da adalci ne sama da kasa suka tsayu. Kuma shine ginshiki da tushen samun zaman lafiya da cigaba masu dorewa a cikin al'ummah. Sannan nagartattun malamai, salihan bayin Allah, irin su Shaikhul Islamu Ibn Taimiyya da Sheikh Usman Dan Fodio da Malam Abdullahin Gwandu sun shaida muna cewa:

"Allah yana taimakon daular da ta tsayar da adalci koda kafira ce, a yayin da Allah yake durkusar da daular da take zalunci koda Musulmi ke shugabancin ta."

Ya ku 'yan uwana masu daraja! Darasin mu na yau yana bayani ne akan muhimmancin adalci, wanda a yau mu al'ummar Musulmi yake neman yayi karanci a tsakanin mu.

Allah Madaukaki Ya umurci Musulmi da su tsai da adalci ta kowane hali, inda Yace: 

“Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kuma kada kiyayya da wadansu mutane ta dauke ku akan ba zaku yi adalci ba. Kuyi adalci shine mafi kusa da takawa.”

Kuma Allah Yace: 

“Kuma idan kun fadi magana to kuyi adalci, kuma koda ya kasance ma’abaucin zumunta ne….”

Kuma Allah Ya sake cewa:

“Lallai Allah Yana umurninku da adalci da kuma kyautatawa…”

Kuma Allah Yace:

"Hakika mun aiko Manzannin mu da hujjoji bayyanannu, kuma mun saukar masu da littafi da ma'auni (na tsayar da adalci) domin mutane su tsayar da adalci tsakaninsu..."

Kuma Allah ya fada a Hadisil Qudusi cewa:

"Na haramta zalunci ga kaina, kuma na sanya shi ya zama haramun a tsakanin ku, saboda haka kada ku zalunci junanku."

Ya ku Jama'a! Adalci shine, bai wa kowa hakkinsa da Shari'a ta tabbatar masa, ba tare da nuna ko wane irin banbanci ba. Kuma duk inda ake tsayar da adalci, to lallai zaka samu zaman lafiya, son juna, walwala, cigaba da jin dadi a cikin al'ummah da tsakankanin jama'ah sun yawaita. A Musulunci, tsayar da adalci yana daga cikin manyan kyawawan dabi'u. Wannan ya nuna kenan duk inda Musulmi suke, indai har Musulmin gaskiya ne, to zaka same su sun rungumi adalci.

Kuma Alkur'ani Mai girma ya bayyana karara cewa Allah ya umurci mutane da dukkan al'ummomi masu neman zaman lafiya da cigaba, su mu'amalanci juna da kyakkyawar mu'amala, tausayi da tsayar da adalci a duk halin da suka samu kansu a ciki. Kuma kowa yana sane da cewa, Allah yana son adalci, kuma yaki jinin zalunci, kuma baya son azzalumai.

Ya ku bayin Allah! Lallai ku sani, Allah ya wajabta wa dukkanin mutane, suyi kokari wurin ganin cewa an tabbatar da adalci a bayan kasa, domin samun zaman lafiya mai dorewa. Shi yasa Allah ya aiko Annabawa, kuma ya hado su da dokoki, domin su taimakawa mutane wurin tsayar da adalci. Wahayin da suka karba daga Allah ya nuna hanyar da za'a bi a tsayar da adalci a cikin al'ummah. Misali, yiwa talakawa adalci, maza da mata, kai hatta makiyan mu an umurce mu da yi masu adalci.

Wajibi ne Musulmi su hadu, su hada kai domin su dakatar da rashin adalci da zalunci a cikin al'ummah. Wannan aiki ne da Allah ya dora masu. Abune da sam bai dace ba Musulmi su zuba ido, su rungume hannuwansu, suna kallo ana tafka zalunci da rashin adalci ba tare da sun dauki matakin da ya dace wurin tsayar da shi ba.

Ya ku 'yan uwana masu albarka! Kamar yadda kuka sani, aiki da dokokin Allah da shari'arsa wajibi ne a wurin dukkan Musulmi ta ko wane hali. Sannan duk Musulmi yasan da cewa siyasa ta kasu kashi-kashi, akwai siyasar Musulunci sannan akwai wadda ba ta Musulunci ba. Misali, siyasar Dimukradiyya ai ba tamu bace mu Musulmi. Domin a Musulunci muna da tamu siyasa, wato ta Shari'a. Kawai mun samu kan mu cikin wani yanayi ne mu Musulmin Nigeria. Sai aka wayi gari muna yin siyasar Dimukradiyyah a bisa lalura. Wannan tsari na Dimukradiyyah, bakon tsari ne a Musulunci, da muka amince muyi shi, amma a bisa lalura. Kenan ya zama wajibi in dai har muna son zaman lafiya mai dorewa a tsakankaninmu, muyi wannan tsari a bisa dokokin sa da tsarin sa da masu shi suka tsara shi a kai, na ganin cewa duk wanda yaci a bashi, wanda Allah ya ba a bashi, kar ayi wa kowa kwace da nuna fin karfi! Domin matukar aka kaucewa wannan, to lallai zamu jefa kan mu cikin tashin hankali, fitina da rudani. Allah ya kiyaye, amin.

Ya ku bayin Allah! Bari in tambaye mu don Allah, shin yanzu abubuwan da suka gudana a wannan kasa tamu mai albarka Nigeria, na zaben da aka gudanar na Gwamnonin jihohi, shin akwai niyyar tabbatarwa da wasu adalci kuwa? Amsa ita ce: ga alamu, a'a.

Kuma shin me yasa ne dukkanin jihohin da akace zabe bai kammala ba, jihohi ne da ake ganin jam'iyyar adawa ta PDP ta ke kan gaba? Shin me ake shirin yi anan? Shin ana son a murde masu ne? Shin ana da niyyar tabbatar da adalci a wannan al'amari? Amsa dai ita ce: bamu ga alamun hakan ba!

To wallahi, muna kira da babbar murya, kuji tsoron Allah, kar ku jefa mu cikin rikici da tashin hankali! Don Allah duk wanda Allah ya ba mulki ku bashi, kar kuce zaku murde, ku hana masa. Kuyi wa kowa adalci. Wannan shi zai sa mu samu zaman lafiya da cigaba mai dorewa.

Ina mai girma Shugaban kasar mu Muhammadu Buhari? Kar kayi shiru akan wannan al'amari, kasa baki don Allah, ka nuna masu duk wanda Allah ya bai wa a bashi. Ka tuna fa, kirarin ka shine MAI GASKIYA. Kar ka bari wasu miyagu su bata maka tafiyar ka. Yi kokari yadda ka fara lafiya ka gama lafiya! Kar ka yarda a danne hakkin wasu. Ka sani, Allah yana kallon ka, sannan duniya tana kallon ka!

Ina kwamitin zaman lafiya na su mai girma tsohon shugaban kasa AbdulSalam Abubakar, su Mai Alfarmah Sultan, su Reverend Matthew Hasan Kuka, su John Onaiyekan? Ya kamata ku sa baki a cikin wannan al'amari, ku tabbatar da cewa duk wanda yaci zabe an bashi, domin tabbatar da samun zaman lafiya a kasar mu mai albarka, Nigeria.

Ina Sarakunan mu suke? Kune fa iyayen wannan al'ummah! Ya zama wajibi ku bada gudummawar ku wurin ganin an kaucewa tashin hankali. Duk wanda Allah yasa yaci zabe a bashi hakkinsa.

Ina Malaman mu na Musulunci? Shin kun manta da umurnin Allah na tsayar da adalci?

Ina Fastoci suke? Shin ina zancen tabbatar da adalci da kuke karantawa a littafin ku?

Duniya fa tana kallon abunda yake faruwa a Nigeria! Kuma dukkanin mu muna sane da illar da rashin adalci yake haifar wa mara dadi. Don Allah mu hadu muyi wani abu akai.

Irin abun da muke gani, da abubuwan da suke faruwa, yanzu dai kam babu wata Dimukradiyyah a Nigeria. Misali:

1. A Jihar Kano an ce zabe bai kammala ba, saboda jam'iyyar PDP ta adawa ce ke kan gaba!

2. A Jihar Sokoto an ce zabe bai kammala ba, anan ma PDP ce ke kan gaba!

3. A Jihar Plateau ma an ce zabe bai kammala ba, nan ma PDP ce ke kan gaba!

4. A Jihar Adamawa an ce zabe bai kammala ba, nan ma PDP ce ke kan gaba da kuri'u mafiya rinjaye!

5. A Jihar Bauchi an ce zabe bai kammala ba, nan ma don sun ga PDP ce ke kan gaba!

6. A Jihar Benue ma haka, sun ce zabe bai kammala ba, saboda Jihar PDP ce!

7. Haka abun yake a Jihar Rivers, an dakatar da duk wasu harkokin zabe, saboda Jihar PDP ce!

Amma saurara kaji wani abun mamaki, ikon Allah:

1. A Jihar Kaduna an ce zabe ya kammala, saboda APC ce tayi nasara!

2. A Jihar Niger zabe ya kammala, saboda APC tayi nasara!

3. A Jihar Kebbi, zabe ya kammala, saboda APC ce tayi nasara!

4. A Jihar Katsina, nan ma zabe ya kammala, saboda APC ce ta lashe zaben!

5. A Jihar Gombe, zabe ya kammala, saboda APC tayi nasara!

6. A Jihar Jigawa, zabe ya kammala, nan ma saboda APC ce ta ci!

7. A Jihar Nasarawa, zabe ya kammala, saboda APC ce tayi nasara!

8. A Jihar Kwara, zabe ya kammala, saboda APC ce tayi nasara!

9. A Jihar Borno, anyi kammalallen zabe, domin APC ce ta cinye!

10. A Jihar Yobe, nan ma babu matsala, domin ta APC ce!

11. A Jiha ta Zamfara ma anyi kammalallen zabe, saboda jam'iyya mai mulki ta APC ta ci zabe!

Ya ku 'yan uwana masu daraja! Yanzu don Allah zaku gaya mani cewa, wannan abun gaskiya aka bi wurin tabbatar da shi? To in dai har ku kun yarda, ni dai kam wallahi, sam ban amince ba.

Maganar gaskiya wannan sharri ne da magudi da rashin adalci irin na 'yan siyasa. Kuma wadannan 'yan siyasar da ke kokarin tafka rashin adalci, wallahi, basa son zaman lafiyar Al'ummar su, musamman ma arewa. Suna son su jefa mu cikin wani sabon tashin hankali da rikici. Allah ya tsare, ya kiyaye, kuma Allah ya mayar masu da aniyar su, amin.

Don Allah me yasa ne duk inda jam'iyyar APC ta lashe zabe suka sanar da cinye zaben, amma kuma duk inda jam'iyyar PDP ta ke kan gaba suka ce wai ba'a kammala zabe ba?

Kuma wai a haka ne za'a gaya muna wai ana yin Dimukradiyyah. Wace Dimukradiyyar kenan? Dimukradiyyah ko dai yaudara?

Wallahi bai kamata ku rinka wahalar da jama'ah ba, matukar kun san kama karya da rashin adalci zaku yi. Yanzu don Allah abunda ya faru a Kano ba abun kunya bane? Ace irin wadannan mutane sune suke jagorantar al'ummah Musulma irin Kano?

Muna Addu'a Allah ya ceto yankin mu na arewa da Nigeria baki daya, daga sharrin da wadannan mutane ke kokarin jefa su, amin.

Ta yaya zaku ce kuyi amfani da karfi ku kwace mulki daga hannun wadanda Allah ya bai wa, sannan kuce kuna son zaman lafiya? Zaman lafiyar naku ne? Ba Allah yake da shi ba? Sannan ya baku idan kun tsayar da adalci?

Amma babu komai, ku da Allah, da kuma jama'ar Nigeria masu kokarin ganin an tabbatar da adalci ga kowa da kowa!

Ya ku 'yan uwana masu daraja! Ina kara tunatar da ku, Allah Madaukaki Ya siffanta kan sa da cewa Shi Mai umurni ne da yin adalci, Mai kuma hanin yin zalunci ne. Yace a cikin suratun Nahl aya ta 90:

"Lallai Allah yana yin umurni da yin adalci, da ihsani, da yin kyauta ga ma'abucin kusanci, Yana hanin aikata alfasha, da munkari, da zalunci, Yana muku wa'azi kila za ku wa'azantu."

Sannan Ya haramta wa kanSa zalunci, ya kuma haramta wa bayinsa yin zalunci.

Sannan lallai yana daga cikin abin da addinin Musulunci ya shahara da shi: haramta zaluntar Jama'a. Kuma lallai yana daga cikin abin da addinin Musulunci ya shahara da shi: wajabta taimakon wanda ake zalunta.

Babu ta yadda za ayi Musuluncin mutum, da mutuntakar sa su cika matukar ba ya kokarin tunkude wa al'ummar sa zalunci da rashin adalci.

Sannan lallai abu ne da yake wajibi a kan dukkan wani mai iko, yayi dukkan abin da zai iyayi na halal domin ya tunkude wa al'ummar sa zalunci da aukuwar tashin hankali da fitina.

Imamul Bukhari ya ruwaito Hadisi cikin Sahihin sa daga Sahabi Anas Dan Malik Allah Ya kara masa yarda ya ce:

"Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yace: "Ka taimaki dan uwan ka yana azzalumi ko yana wanda aka zalunta" sai wani mutum ya ce: Ya manzon Allah zan taimake shi in yana wanda aka zalunta (in kwato masa hakkinsa), to amma in yana mai zalunci ta yaya zan taimake shi? Sai yace: Ka hana shi yin zalunci wannan shine taimakon ka gare shi."

Sannan Imamu Muslim ya ruwaito Hadisi daga Sahabi Jabir Dan Abdullahi yace:

"Wasu yara biyu sun yi fada da juna, daya daga cikin Muhajirai yake, dayan kuwa daga cikin Ansarawa, sai Muhajirin ya daga murya ya nemi taimakon Muhajirai, shi kuwa ba'ansaren ya daga murya ya nemi taimakon Ansarawa, sai manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya fito yace: Wane irin kirayen jahiliyya ne haka? Sai suka ce: Ya Manzon Allah yara ne biyu suke fada da juna, sai dayan su ya doki dayan su a duburarsa. Sai (Annabi) yace: Babu laifi, mutum ya taimaki Dan uwan sa yana azzalumi ko yana wanda ake zalunta, in ya kasance azzalumi ne sai ya hana shi yin zaluncin, wannan shine taimakon sa gare shi, in kuma ya kasance wanda ake zalunta ne sai ya taimake shi."

Sannan zunubi ne babba mutum ya ga ana kokarin wulakanta wasu muminai a gaban sa, kuma ya kame hannayen sa da bakin sa, ba tare da yayi wani yunkuri domin ya kawo masu agajin da zai iya ba.

Ya ku 'yan uwana Musulmi! Kuma yana da kyau ku sani, a dokokin Musulunci, da kuma aqidah da manhajin Ahlis-Sunnah wal Jama'ah, duk wanda Allah (SWT) ya ba mulki, ko ta wace hanya ne, kuma ko da baka so ya zama shugaba ba, to kayi hakuri, kayi masa da'a da biyayya, matukar bai umurce ka da sabawa Allah ba. Sannan kayi masa Addu'a da fatan Allah ya bashi ikon yin adalci ga kowa da kowa, hatta wadanda basu tare da shi. Kuma kayi masa Addu'ar Allah ya bashi ikon sauke nauyin da ya dora masa. 

Ya Allah, ina rokon ka, don tsarkin sunayen ka, kayi wa dukkanin shugabannin mu jagora akan tafarki madaidaici da ka yarda da shi, amin.

Wassalamu Alaikum... Dan uwanku:

Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi, Nigeria. Za'a same shi ta: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.

Saturday, 9 March 2019

ALLAAH GIVES POWER AND LEADERSHIP TO WHOM HE WILLSƳAN NIJERIYA KU DAWO HANKALIN KU

*'YAN NIGERIA KU DAWO HANKALINKU.*


Assalamu Alaikum Warahmatullah. 

Barkanmu da safiya, dafatan mun wayi gari lafiya. Allah Madaukakin Sarki Ya sada mu da dukkan alkhairan da ke cikin wannan rana. 

Da fari ina taya Shugaba Muhammad Buhari murnar sake samun nasarar lashe za6e na zama shugaban kasar Nigeria. Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi ikon yin adalci. 

Sai dai wani hanzari ba gudu ba 'Yan uwa! 

Kada mu ta6a tunanin cewa don Buhari ya hau matsalolinmu sun kare a Nigeria. Kada mu ta6a tunanin Buhari zai iya azurtawa ko ba da kariya ga jama'ar Nigeria. Kawo karshen matsalolin Nigeria ya dogara ne ga yawan addu'o'inmu da ibadunmu da rashin sa6a wa Allah. 

'Yan uwa kamar yadda muka yi ta addu'a kafin za6e har Allah Ya ba Shugaba Buhari nasara, to mu ci gaba da yi masa addu'ar Allah Ya sawwake masa dukkan al'amuran mulkinsa kuma Ya ba shi ikon tabbatar da mulkin adalci ga Al'ummar Nigeria. 

Mu ci gaba da yi masa addu'ar Allah Ya kare shi daga kaidin marasa son ci gaban Musulunci da Musulmai da sauran Al'ummar Nigeria. 

Kada mu dogara ga Buhari ko mu sakankance cewa Shi ne zai iya komai. Wallahi yana matukar bukatar addu'armu, don haka mu hankalta 'yan uwana. Allah muke roko Ya ba wa Shugaba Muhammad Buhari ikon karkata zuwa ga dai-dai kuma Ya haďa shi da jagorori masu kudurin kawo ci gaba a wannan kasa ta mu. 


Allah Ya sa mu dace. 


*✍🏿Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*


ANYA AKWAI MAZA A GIDAJEN KUWA?

*ANYA AKWAI MAZA A GIDAJEN KUWA*?

🧕🏻Yanzu mata suna fita waje, suna bayyana surorin jikinsu ga mutanen waje, ba tare da sun rufe jikkunansu yadda shari'ah tace ba.Wasunsu ma matan Aure ne.

🤔 Abin tambaya anan : Shin anya akwai Maza acikin gidajen da matan nan suke kuwa? Shin kodai mazajen gidan sunaso ne Allah ya haramta musu Aljannah sbd Sun Zama *Dayyus* (Mara Kishin iyalansa). 

*" Dukkaninku makiyaya ne, kuma dukkaninku sai abintambaya ne dangane da kiwon da Aka bashi. "* 

_Allah yasa mudace kuma yakara tsare mana imaninmu kuma yasa mucika da kyau da Imani._

✍🏻 *Idris M Rismawy*

ƘARYACE-ƘARYACEN WATAN RAJAB

KARYECE-KARYACEN WATAN RAJAB 

*_HADISAI MARAR SA INGANCI DA HADISAN KARYA GAME DA FALALAR WATAN RAJAB_*

HADISI NA FARKO 
1-(Yin azumin yinin farko na watan Rajab,yana kankare laifukan shekara ukku,a yini na biyu kaffarar shekara biyu,a yini na ukku kaffarar shekara guda,sannan daga nan kowane yini yana kaffarar wata guda)
Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba
@ﺿﻌﻔﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺿﻌﻴﻒ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ - ﺭﻗﻢ : ‏( 3500 )


HADISI NA BIYU
2-(Ya kasance idan ya shiga watan Rajab yana cewa; ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺑﺎﺭِﻙْ ﻟﻨﺎ ﻓﻲ ﺭﺟﺐٍ ﻭﺷﻌﺒﺎﻥَ ، ﻭﺑﻠِّﻐﻨﺎ ﺭﻣﻀﺎﻥ )
Shime Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba daga Manzon Allah SAW ba.
@ﺿﻌﻔﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺿﻌﻴﻒ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ – ﺭﻗﻢ :‏( 4395 ).


HADISI NA UKKU
3-(An kira watan Rajab ne da suna Rajab saboda yana tattaro alkhairi mai yawa ga watan Sha’aban da Ramadhana)
*Shime Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba daga Manzon Allah SAW ba*.
@ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻣﻮﺿﻮﻉ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﻀﻌﻴﻔﺔ - ﺭﻗﻢ :‏( 3708 )

HADISI NA HUDU
4-(Fifiko da falalar watan Rajab akan sauran watanni,kamar fifiko da falalar alqur’ani ne akan sauran zikirai)
*Shime Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba daga Manzon Allah SAW ba*.
@ﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﺣﺠﺮ ﻣﻮﺿﻮﻉ ﻓﻲ ﺗﺒﻴﻴﻦ ﺍﻟﻌﺠﺐ - ﺭﻗﻢ :‏( 25 )

HADISI BA BIYAR 
5-(Darare guda biyar ba’a mayar da addu’o’insu;daren farko na watan Rajab…………)
*Shime Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba daga Manzon Allah SAW ba*.
@ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻣﻮﺿﻮﻉ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﻀﻌﻴﻔﺔ - ﺭﻗﻢ : ‏( 1452 )


    ALLAH NE MAFI SANI 


MU HAƊU A DARASI NA GABA INSHA ALLAH


SIYASAR JAHAR KADUNA, ADDINI KO JAM'IYYA?

*SIYASAR JIHAR KADUNA ADDINI KO JAM'IYYA?*

Duk mutumin da ke bibiya da lura da abinda ke faruwa na harkar siyasa a jihar Kaduna baya bukatar k'arin bayani. Domin abin a fili yake kamar misalin hasken rana ce ta fito, baka bukatar ace maka ta fito. Kuma yana da kyau duk wani mai hankaki d'an jihar Kaduna ya fahimci cewa: siyasar jihar Kaduna ba jam'iyya ba ce Addini ce, saboda haka dole mu fito a matsayin mu na Musulmai musu kishin Addinin mu mu nuna kishinmu kuma mu zabi wanda zai kare mana Addinin mu da rayukan mu.

Kuma mu sa ni cewa zaben jihar Kaduna:

1) Zabe ne tsakanin Imani da Kafirci.

2) Zabe ne tsakanin Musulunci da Kafirci.

3) Zabe ne tsakanin Mumunai da Munafikai.

4)Zabe ne tsakanin masu kishin kasarsu da marasa kishinta.

5) Zabe ne tsakanin masu kaunar sahabbai da masu zaginsu.

6) Zabe ne tsakanin masu son fadan addini da masu kyamatar fadan addini.

7) Zabe ne tsakanin masu son zaman lafiya da masu son tashin hankali.

8) Zabe ne tsakanin masu son cigabar jihar Kaduna da kiristocin kudancin Kaduna masu son tashin hankali da kashe-kashe.

*KUKUN KURCIYA JAWABINE MAI HANKALI SHI KE GANEWA!*

*Dan uwanku a Musulunci: ✍*
*Abu Ja'afar*
*Yusuf Lawal Yusuf*
25th Jumãda al Ãkhirah, 1440H.
{03/03/2019}.

Today In History


On This Day March9

1776 – The Wealth of Nations by Scottish political economist Adam Smith (bust pictured) was first published, becoming the first modern work in the field of economics.

1862 – American Civil War: In the world's first battle between two ironclad warships, USS Monitor and CSS Virginia fought to a draw near the mouth of Hampton Roads in Virginia.

1932 – Éamon de Valera, one of the dominant political figures in 20th-century Ireland, became President of the Executive Council of the Irish Free State.

1944 – World War II: As part of the Battle of Narva, the Soviet Air Forces heavily bombed Tallinn, Estonia, killing up to 800 people, mostly civilians.

2010 – The first legal U.S. same-sex marriages south of the Mason–Dixon line took place in Washington, D.C.UKU-BALA'I 30

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
 
BABI NA TALATIN.

💕💕 *_Kibiyar Ajali Taken Sone, Ya Mamayen da Gangawa, Yai Min Barin Makauniya_* 💕💕
       -- *Hamisu Breaker*

Tunda ta dago labulan dakin ta sanyo kai take dubanta da kallo kamar wacce taga bakuwar fuska, sosai ta lura da Mariya cikin yan kwanakin nan gabadaya ta sauya kamar ba ita ba sai sanyi jiki da rashin son magana ko aiki take yi haka take zama wata sukuku duk ta rame sai idanu da sukayi mata zuru-zuru ga tsayi da takuma yi sosai.
Gyaɗa kai Umma tayi kafun ta kau da kanta daga kallon da takeyi mata sosai ta fahimta sosai ta gane akwai abin da ke dawainiya da 'yarta wanda yake haifar mata da damuwa sosai a zuciya da ma jiki baki daya ba ta san mai Mariya take nufi da hakan ba ba ta san wacce irin rayuwa ta daukarwa kanta ba na zama cikin damuwa sosai ita kanta abin ke damunta a zuciyarta sai dai tana boyewa ne saboda ita Mariyar domin ba ta bukatar ta ganta itama cikin damuwa abubuwa da yawa suke nukurkusar zuciyarta musamman batun mahaifin Mariya ba shi babu dalilin sa anyi cigiyar amma ina ta sha fita ba tare da kowa ya sani ba ta nufi cikin gari amma ina haka take dawowa jiki a sage tasha zama tayi kukan dare domin rage radadin dake damunta in abun yayi mata yawa alwala take daurowa ta kaiwa Allah kukan ta akan ya bayyanar mata da mijinta in har yana raye a filin duniyar nan.
Wasu kwalle taji sun kawo mata ziyara cikin idanuwanta da sauri ta shafe su kafun Mariya ta gani. Dago kanta tayi tana duban Mariya dake tsaye tana zare hijabin makarantar da ta dawo kafun ta zube kan katifar tsakar dakin idanuwanta gabadaya ta daga sama tana kallon rufin dakin.
"Mariya!".
Umma ta fadi cikin wata irin murya mai zurfin gaske tana sauke idanuwanta akan Mariya da ta dago tana dubanta daga kwance.
"Tashi mana magana nake so muyi".
Wani irin yatsine fuska tayi kamar wacce zata fashe da kuka gabadaya bata so taji ana yi mata magana komai take ji ba dadi zuciyarta take ji wani iri tana yi mata ciwo mai girman gaske bata so a fiye tuhumanta akan abin da ke damun ta domin bata da abin da za ta iya cewa tasan Umma kuma tambayar ta za tayi gabadaya sai taji wani ba dadi a hankali ta shiga kokarin tashi tana cizon laɓɓanta kamar zata tsinke su zama tayi sosai kanta a kasa domin bata bukatar Umma ta gane yanayi da take ciki domin ta tabbata duk wanda ya kalli idanuwanta sai yayi zargin wani abu daban ita kanta ta san tana cikin tashin hankali sosai take jin canji yanayi a jikinta sosai ta lura da komai nata ya sauya ji take yi kamar ba ita ce ba zuciyarta take ji tana wani irin ciwo mai matukar raɗaɗi da zafi ga kasar ruhinta da yake furzar da wani zazzafan huci.
"Mariya akwai abin da kike boye wa a ranki, wanda kika kasa bayyanar dashi a filin rayuwarki na lura dake kusan wata guda kenan gabadaya kin sauya kamar wacce bata da lafiya Me yasa haka?".
Umma ta fadi cikin sanyin murya
Mariya kamar jira take yi Umma ta idar sai hawaye shar-shar sun fara zubo mata wani kuka take ji yana zuwa mata da sauri ta kai hannunta tana rufe bakin nata zuciyarta taji tana yi mata wani irin zafi da raɗaɗi kamar zata fasa kirjinta tayo waje kanta taji yana juya mata komai take kin na filin duniyar yana zama kunci a gareta ji take yi kamar ta mutu ta huta da wannan rayuwar ta duniyar nan ita kanta ta sani tana cikin tashin hankali zuciyarta ciwo take yi ciwo mai girman gaske wanda ko tantama ba tayi shine ajalinta.
Ware idanu Umma tayi sosai tana kallon ikon Allah wai na kwance ya fadi hawayen da take gani a fuskar 'yarta ya sanyata faduwar gaba.
"Yaa Salam! Mariya meye haka nake shirin gani hawaye a idanuwanki da girman ki me aka yi miki har haka ya sanya ki zubda hawaye".
Runtse idanu tayi tana jin yarda zuciyarta ke zafi da wani irin huci kirjinta take ji yana kartawa da wani tashin hankali mai girman gaske.
Laɓɓanta ta shiga motsawa sosai muryarta tayi rauni jikinta har rawa yake yi.
"Inda mahaifina na filin duniyar nan ba yarda za ayi na kasance a haka, inda mahaifina na kusa dani ba yarda za ayi rayuwata ta kasance a haka, inda mahaifina na filin rayuwata ba wanda ya isa ya saka ni gaba ya dasa min ciwon rai. Ban san me ke kokarin shigowa rayuwa ta ba, Ban san me yake shirin faruwa dani ba, ban san wani irin BALA'I bane yake zawarcin rayuwa ta ba...".
A firgice Umma take dubanta kamar wacce ta ga sabuwar halitta wani irin bugu take jin zuciyarta nayi daga kirjinta sosai taji duniyar na juya mata tsoro take ji yana kara girma a gareta komai taji lokaci guda na duniyar na juya mata tsoronta daya ba damuwar batar Mijinta bane ya sanya 'yarta cikin tashin hankali har haka gabanta taji ya sauya bugu da sauri-sauri a hankali ta shiga nuna Mariya da hannu idanuwanta na kawo kwalla ita kuwa Mariya sai kaar sautin kukan ta take yi kamar wacce ake bugu.
"Mariya karki ce dani damuwar rashin mahaifinki ce ta kai ki har haka, karki ce dani jarabawar da Allah ya dorawa rayuwarki kike kokarin butulce masa karki ce mani kin kasa YARDA DA ƘADDARA ba fa ke kadai wannan abun ke damu ba ni fa Mijina ne shi kadai ne yayi mani saura a rayuwata bani da kowa sai shi akan sa na rasa iyaye na ga shi yanzu shima na rasa shi amma nayi TAWAKKALI na mikawa Allah kuka na domin shi kadai ne zai yi mani duk wata maganin matsalata Mariya ki sassautawa rayuwarki rayuwa bata son a dauke ta da zafi ke fa yarinya ce wacce take matakin kuruciyarta.
Bai kamata ace kin matsawa rayuwa ba karatu kike yi ya kamata ace kin ajje komai a gefe ki bar komai a zuciyarki sannan ki mikawa Allah lamarinki".
Sosai Muryar Umma tayi sanyi zuciyarta take ji tana zafi da wani irin raɗaɗi mai girman gaske mikewa tayi kan kafafuwanta tana jin yarda idanuwanta suke kawo ruwa ficewa tayi daga cikin dakin domin ba za ta iya zama ba ta tabbata in ta zauna dukkannin su sai an rasa mai rarrashin dan'uwansa a cikinsu.
Kwanciya Mariya ta koma tayi tana faman ajjiyar zuciya mai sanya kirjinta zafi sosai runtse idanuwa ta tayi ba abin da take hangowa sai tashin hankali mai girman gaske a bangarori UKU wanda suke shirin haifa mata da BALA'I UKU.
Ba ta san ya rayuwarta zata kasance ba cikin lokacin nan ba ta san ya za tayi ba sosai komai ya tsaya cak! a kwanyarta ina ma ta san a shafin rayuwarta akwai wannan masifar da ta roki Allah ya kasheta tun a cikin Ummanta ba ta san haka duniyar take ba da kwazazzaban tashin hankali da bata shigo ta ba amma ina ikon Allah sai kallo duk mai sauran rai a duniyar nan yana DA SAURAN KALLO.
Iskar da taji ta shigo cikin dakin ne ya sanyata sauri buɗe idanuwanta da suke rufe sun kaɗa sunyi jajir kofa ta kalla Hafsi ta gani tsaye tana watsa mata wani irin kallo tana faman yatsine fuska gami da tsaki sosai ta hango kiyayya tsantsa cikin idanuwan Hafsi tun da take da ita bata taba ganin tayi mata irin wannan kallon ba mai cike da tsana da sauri ta tashi zaune tana cizon laɓɓa.
"Yo me akai da maza, ai yanzu a ka fara zaman kishi da uwar miji, ki je waje ana kiran ki".
Tana fadin haka ta buga wani uban tsaki kamar zata tsinke harshen ta ta fice daga cikin dakin.
Fakare Mariya tayi tana kallon ikon Allah wai uwar miji da cin kazar amarci wasu hawaye taji sun zuba mata a zuciyarta ta na ayyanawa anya tana da sa'a a filin duniyar nan anya kuwa ba wani laifi tayi wa ubangiji ba yake hukuntata ta wannan hanyar.
"Astagafurullah wa'atubu ilai".
Ta shiga fadi kafun ta shiga kokarin komawa ta kwanta tayi luf! kamar wacce bata numfashi tunanuka ne taji sun addabi zuciyarta da kwanyarta da sauri ta mike tana goge fuskarta ta zura hijabin ta akan kayan makarantar da ba ta cire ba waje ta fito ta zira takalmin ta tana dube dube kafun ta jiyo karar saukar ruwa cikin bandakin su ajiyar zuciya ta sauke don ta tabbata Umma ce a hankali tayi hanyar waje Hafsi dake tokare bakin kofa tana kallonta wani mugun tsaki taja fuskarta a hargitse kamar zata fashe da kuka ta juya ta koma cikin dakin kamar wata sabon kamu bakin gadon karfe ta zauna ta na faman turo baki gaba tana wani kumbure-kumbure kamar zata fashe.
Dubanta Goggo Marka ta shiga yi da mamaki ganin yarda take hauhawa kamar fulawa taji yis.
"Ke kuma meye haka na ga sai faman hawa kike kamar fulawa?".
Sake turo baki tayi gaba tana buga kafa a kasa.
"Haba Goggo wai ni nafi kowa bakin jini ne a garin nan ace kullum nikenan ina zaune ko matayi babu".
Zaro ido Goggo Marka tayi tana ajje kaɗin da take yi kafun tashiga sallallami tana tafawa hannaye baki sake.
"Muhammadu dan abdullahi me nake shirin gani Hafsi".
Kau da kai tayi tana turo baki gaba.
"Ni gaskiya na ga ji kina kallon Mariya sai zarya samari masu zunduma-zudunman motoci suke mata jiniya a kofar gida nikuwa ko 'ya'yan gidan Malam Shehu bana gani".
"Iyee to ai shikenan bara na zo na sanya a rubuce miki suratul-Yusufa ki shanye tun da kin rasa mashinshi ne sai mu ga yarda Allah zai yi".
Goggo Marka ta fadi tana mai bankamata harara kamar idanuwanta za su zubo kasa.
"nifa gaskiya Goggo kisan yarda za kiyi dani ba yarda za ayi ace Mariya ta fini farin jini samari kanta kawai suke zarya nikuwa kamar na hadiyi jaɓa don bakin jini dame ta fini ki duba fa ki gani".
Ta fadi tana mai mikewa tana jujjuya jikinta.
Mamaki fal! zuciyar Goggo Marka gabadaya ta rasa ma abin da zata ce sai faman bin Hafsi take yi da ido ba tayi zaton Hafsi za tayi haka ba ba taba zaton irin wannan maganar zata fito daga bakinta ba ba kunya ba tsoron Allah.
Girgiza kai tayi tana mai sake duban Hafsi kwalla ta gani a idanunta tana yatsine fuska kamar zata rushe da kuka da sauri ta ware idanu ciki da tu'ajibi.
"Samarin Mariya Uku kuma duk masu Mota ni kuwa ko mai keke bani dashi ni gaskiya ba zan yarda ba ni dai kawai ki san yarda zakiyi dani na gaji nima saurayi nake so na ganni dashi in ba haka ba ai sai Mariya ta rainani sosai da sosai".
"Ya isa haka Hafsi yi shiru zauna muyi magana".
Turo baki tayi tana zauna sai faman kumburi take yi.
"Ke kina da wanda kike so?".
"Na fa ce miki ba wanda yace yana sona sai fa kwanaki Danliti mai gini yace wai ni yake so ni kuma ba abin da zan yi dashi katon hanci gareshi ga kunnuwa fala-fala".
Kuri Goggo Marka tayi mata dariya ta so kama ta amma sai ta kanne tana mai cewa.
"Naji to ke yanzu wa kike so?".
farrr! tayi da idanunta tana mai saka dan yatsa cikin baki kamar mai son tunano wani abu kafun ta dubi Goggo.
"ni so nake yi na samu mai mota irin na Mariya ko ma ta ban saurayin ta guda daya a ciki".
"Shikenan waye a cikin su kike so nayi miki Alkawari zaki same shi Hafsi farin cikinki shine nawa yo me akayi da waccan mai kalar zazzafin shawarar ki sha kurumin ki ko duka samarin kike so zaki mallake su....".
Wani ihu tayi tana mai kaiwa Goggo cafka tana rungume ta sai faman kyalkyalar dariya take yi.
"zo muje na zabi wanda ya zo yanzu gashi can a waje zo muje ki ganshi mai kyau ne motarsa luntsumemiya gashi dan gayu".
"Nifa tsiyata dake gajen hakuri wallahi Hafsi me zamu je yi kuma ke dai kwantar da hankalin ki kamar kin yi bako ya mutu ki bar komai a waje na shi da kansa zai zo yana rokonki ki so shi".
Wata irin dariya ta sake yi kafun ta mike tana tikar rawa.
Ita dai Goggo Marka baki ta saki tana kallon ikon Allah.
Tsagaitawa tayi da rawar da take yi ta shiga dube-dube kafun ta hango abin da take so kwanon soson wanka ta dauka tana duban Goggo Marka sannan ta fice.
Goggo Marka ta margaya kai tana mai fadin.
"ai sha kuruminki magana ai kuma ta kare mata tace da mijinta shege".
******
Tun da Mariya ta doshi soron gidan su take ji gabanta na tsananta faduwa sosai take jin wani iri kamar ta koma amma wani sashi na zuciyarta na ingizata da taje ta gano waye sai da ta tsaya ta numfasa gami da saita kanta sanan tayi shahadar kuɗa ta fice gabadaya fuskarta a kasa.
Tsaye yake jikin motarsa kansa na duban takalman dake kafarsa kallo daya zakayi masa ka gano irin ramar da yayi sosai da sosai ya kara haske duk da duhun fatar da yake da ita takun da yaji ne ya sanya shi dago kansa a daidai lokacin ita ma Mariya ta dago kanta gabadaya suka sarke juna da kallo zuciyoyinsu suka shiga bugu da sauri-sauri kowa ya kasa dauke ido daga kallon dan uwansa sai da suka shafe tsayin lokaci kafun Mariya taja wani dogon numfashi kafafuwanta taji sun shiga rawa sosai ji take yi kamar zata zube kasa.
"Yaa Rabbi!".
Ta furta cikin wani irin yanayi na rashin hayyaci a hankali tashiga juyawa domin komawa cikin gida gaban ta ji yana duka ba ta san abin da yasa ta fito ba, bata san ya akayi ba ta fito ba ba tare da ta san waye ba tajima da ajje Huzaif a gefe duk da kullum zuciyarta sai ta yi mata tunanin shi bata so ace sun sake haduwa ba domin bata bukatar sake ganinsa domin ganin sa ba karamin sanya ta yake yi cikin tashin hankali ba.
Ciwon zuciyarta daɗuwa yake yi tashin hankalin ta karuwa yake yi duniyarta sake rikicewa take yi a duk lokacin da tayi arba da Huzaif ba ma Huzaif ba duk wani wanda yake da takomashin sanya zuciyarta tashin hankali.
"karki yi mani haka Mariya zuciyata zata iya bugawa a ko wani lokaci in har kika ki tsayawa ki saurare ni ban san ya ba zuciya tana kuna ruhina na ciwo gangar jikina ya zama kamar ba nawa ba".
Numfasa yasake yi yana jin yarda kirjinsa ke harbawa da duk wani tashin hankali da yake ciki zuciyarsa ciwo take masa ciwo mai tsanani.
"Rayuwata na cikin hatsari komai nawa ya shiga ruɗani ban san ya zan kwatanta miki tashin hankalin da duniya ta take ciki ba na rokeki ki saurare ni Mariya".
A hankali ta fara tsaigatawa da tafiyar da take yi gabadaya taji duniyar na juya mata kafafuwan take ji kamar suna narkewa jikinta rawa yake yi zuciyarta lokaci guda ta sauya da bugu tana buɗe shafin da ta baiwa Huzaif ya zauna a ciki runtse idanu tayi tana jin yarda zuciyar ta ta ke kartawa kamar ana soka mata KIBIYAR AJALINTA.
A hankali ya shiga takowa yana jin yarda bugun zuciyarsa ke canza bugu da wani irin yanayi game da Mariya numfashi yake ajjewa da duk kamshi da yake ji yana tasowa daga jikin Mariya yana haifar masa da wani irin yanayi na kasala a jikin sa da zuciyarsa gabanta ya karaso ya tsaya yana mai juya idanuwansa da suka kaɗa kadan fuskarsa cike da yanayi na rauni hannunsa ya kai saitin in da yake zaton zuciya na wajan ajje.
"Mariya kin ga nan dina ji nake yi kamar KIBIYAR AJALI ake sokamin ji nake yi kamar KASKON WUTA ake sauke mani a wajan Mariya sosai nake jin wani iri a game dake sosai nake jin zuciya tana kara buɗe fili mai girman gaske a game dake komai ma da komai na zuciyar ke ce a cikinsa...".
"Ya isa haka Huzaif ya isa nace maka na gaji da jin wannan kalaman ka bar ni haka in har ba so kake yi kwanyarta ta tarwatse ba in har ba so kake yi zuciyata ta buga ba na mutu hankalin ka ya kwanta".
Numfashi ta shiga ja ta kai hannayenta duk biyu tana rufe bakinta jin kalaman nasa take yi kamar saukar narkakkiyar dalma a zuciyarta jin sa take yi kamar yana doka mata ganga mai matukar kara a cikin kunnuwanta sosai taji bugun zuciyarta ya sauya komai take ji na jikinta yana narkewa kamar ruwa.
'Yaa Allah'.
Ta furta a can kasar zuciyarta da take ji tana kecewa da tashin hankali mai girman gaske.
"Mariya...".
"Nace maka ya isa haka ka bar zuciyata ta huta mana Huzaif".
Ta sake katse shi tana toshe kunnuwanta da take ji kamar za su tsinke.
Runtse idanu Huzaif yayi yana jin sautin muryarta na amsa sauti mai girma a kunnuwansa da kwanyarsa sosai ya ji zuciyarsa na bugawa da yanayin da Mariya take nuna wa a gareshi numfashinsa yake ji ya canza yanayi yana sama da kasa kamar zai dauke cikin yanayi na ciwo yake cizon laɓɓansa.
"Baki so na ko Mariya baki kauna ta bakya son gani na a filin duniyarki ko kiyi hakuri zuciyata ce ta matsa min zuciya ta kasa hakuri gabadaya ta hauka ce a dalilin ki ba ta jin sautin komai sai naki Mariya ki taimaka Huzaif din ki ne fa".
Ya karashe muryarsa na karyewa da yanayi na son kuka a hankali yake hadiyar wani abu mai tauri da ya tsaya masa a kirji zafi yake ji zafi na sosai da sosai kansa yake ji yana kokarin darewa biyu nauyi yake ji yayi masa ji yake yi kamar bana sa ba.
A hankali ya fara juya yana kai kawo kamar wani sabon hauka.
"Ban sani ba ashe zuciya ta tayi ganganci, ban san zuciya ta hauka take yi ba, ban san wai dama hauka nake yi ba, ban san dama ban dace da wajan da zuciya ta kawo ni ba, ban dan dama ni kadai nake jin irin wannan yanayin ba a zuciya komai nawa ya sauya ya canza kamar bani ba, kamar ba Huzaif ba duniyar ta yi wani iri ba dadi komai ma ba dadi".
Sosai Mariya ta tsorata da yanayin da taji yana sambatu idanuwanta sosai suka fito waje kanta ta ji ya shiga juyawa kamar zata zube kasa runtse idanu tayi zuciyarta na wani irin bugu da sauri-sauri.
"Yaa hayyu Yaa Kayyum".
Kawai take fadi wasu zafafan HAWAYEN ZUCIYA ne taji suna saukar mata jin su take yi kamar tafasassu.
"Shikenan Mariya na tafi...na tafi tun da ba ki son ganina na takura miki ko yi hakuri shikenan na tafi".
Ya fadi yana mai daga mata hannu murmushi a fuskarsa mai sanya zuciya ciwo mai girma a hankali ta shiga motsa laɓɓanta.
"Huzaif!".
Ta fadi da wani irin yanayi mai girman gaske cak! Ya tsaya yana mai juyowa gabadaya idanuwansa sun kaɗa sun yi jajir.
"Kar ka tafi kayi hakuri karka ga laifi na nima ba yi na bane laifin zuciya tane ban san ya zan yi ba komai ya kulle a cikinta ta kasa daukar komai ma".
Duban ta yake yi da wani irin yanayi cikin idanuwanta yake hango wasu abubuwa masu girman gaske su na sanya jikinsa narkewa da wani irin yanayi.
Baki ya shiga motsawa yana nuna ta da hannu magana yake son yi amma ya kasa sai faman girgiza kai kawai yake yana sakin wani yaƙe mai girma a fuskarsa.
Wani dogon tsaki suka ji an saki duk kan su suka juya suna duban in da suka ji sautin na tashi.
Hafsi ce tsaye ta rike kugu sai faman kumburi take yi kamar zata tarwatse wani kallon tsana da ƙi ta sake jifan Mariya dashi tana faman huci kamar kububuwa kafin ta juyar da kallonta wajan Huzaif tana kare masa kallo zuciyarta take ji tana shiga yanayi game dashi girgiza kai tayi tana mai tsartar da yawu a hankali ta juya tana kallon Mariya ita ma ita take kallo cike da mamaki da tu'ajibi.
"Huzaif sai anjima"
Mariya ta fadi cike da wani yanyi mai ciwo yana kokarin yin magana amma ina har ta shige cikin soro duban Hafsi yayi cikin haushi da takaici ji yake yi kamar ya shake ta don bakin ciki dunkule hannu yayi yana bugun iska yana mai cizon laɓɓa da sauri ya juya jikin sa sai kyarma yake yi ya isa wajan motarsa a hanzarce yayi mata key ya fizge ta rai bace har yana baɗe Hafsi da kura ya bar unguwar.
Wata irin shewa tayi tana tafa hannunta sannan ta juya cikin sauri ta fada cikin gida ranta fes!!...


  *_KAMALA MINNA_*😍😍😍


UKU-BALA'I 29

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
 
BABI NA ASHIRIN DA TARA.

Cikin wani irin yanayi ta kai wayar kunnan ta sai faman jan numfashi take yi daƙyar idanuwanta sun kada sunyi jajir kamar an watsa mata barkono zuciyarta take ji tana mikata cikin wani irin waje mai dauke da tashin hankali mai girman gaske komai take ji ya tsaya mata cak! ji take yi kamar motar ta ta tuntsiran da ita ta mace ko ta huta da wannan tashin hankalin da kunar da zuciyarta ke yi tana babbaka duk wani sashi na kirjin ta ruhinta take ji yana wani irin fizga mai haifar mata da wani matsanan cin ciwo a dukkan sassan jikinta.
Girgiza kai take yi tana jin yarda yake wani irin sarawa da duk tashin hankalin da take ciki komai take ji a wannan lokacin yana barazana da duk ragowar farincikin da yayi sauya a gareta na filin duniyarta.
Ba ta san abin da ya sa ta fito yau ba bata san mai alkalamin ƙaddararta yake kokarin rubuto mata ba sosai take jin zuciyarta na haifar da wani kunci mai radadin gaske sosai take jin duk wani sashi na jikinta yake narkewa kamar ba na ta ba kafafuwan da suke kan giyoyin motar take jin su kamar ba a jikin ta suke ba ta tabbata da a tsaye take ba za su iya daukar gangar jikinta ba.
Nisawa tayi a daidai lokacin da taji iska mai nuna alamun an daga wayarta ta buso cikin kunnuwan ta runtse idanu tayi gami da tura laɓɓanta gabadaya cikin bakinta tana cizawa kamar zata fizgesu daga mazauninsu.
A hankali ta fara gangarawa gefen titin domin ba zata iya furta ko da kalma daya a yarda take jin zuciyarta ba, ba za iya motsa wani sashi na laɓɓanta a cikin halin tuki ba ji take yi kamar in ta motsa su komai zai tarwatse a gareta.
Sai da ta shafe mintina biyu kafun ta ja wani dogon numfashi ta fesar mai matukar ciwo.
"Alhaji Abdulwahaab".
Ta fadi can kasar makoshin ta kamar wacce akayi wa dole sai ta ambaci sunan.
"Na'am Areefa".
Ya ansa da yanayi na farinciki a muryarsa.
Runtse idanu tayi kafun ta sake jan numfashi.
"Kana ina Please I need your help right now?".
Yanayin da take furta kalmar cikin sauti mai rauni ya sanya Alhaji Abdulwahaab yin sanyi sosai.
"What is wrong with you Areefa me ke faruwa dake ne naji muryar ki So Sad?".
"Kana ina right now Alhaji Abdulwahaab don Allah ina son ganin ka ko a ina kake ka fada min gani nan zuwa".
Sosai muryarta tayi rauni kamar zata fashe da kuka a hankali ta kai hannunta baki tana toshewa.
"Ok...Cool down Please yanzu haka ina Muhabbir Coffee daidai Alo-Vera Hotel ki zo nan ki same ni".
Ba ta ji ra abin da zai ce ba da sauri ta sauke wayar tana cilli da ita kan kujerar dake gefen ta wani wawan ribas tayi tare da juya akalar motar ta koma kan titin sosai ta hau hanya.
Zabga gudu take yi kamar wacce zata tashi sama ita akaran kanta ba ta san ta nayin sa ba zuciya ce kawai ke aikinta domin ba ta cikin hayyacita motoci da yawa sai dai su kauce mata domin sun lura ba ta cikin hayyacin ta cikin mintina kalilan ta hau titin da zai kai ta alo-vera Hotel kwanar da zata sha saitin W. I .WUSHISHI ESTATE. Sukayi a rangama da wata motar saura kadan su haye juna Allah ya tsagaita amma duk da hakan ta bugar wa mai motar fitilu har sun dan tsage hannu kawai ta daga masa alamun bashi hakuri ta shiga layin girgiza kai yayi mai motar don ya lura bata cikin hayyacin ta.
Tun kafun ta isa Muhabbir Coffee din tayo parking din motarta gefe guda ta fito cikin hanzari murfin motar ma da kafarta ta tura ta shiga sauri kamar zata kifa har tana turgudewa Allah ya taimaka bata je kasa ba.
Ta shiga Get din wajan ta shiga rarraba idanu can gefe guda ta hango shi yana dago mata hannu kamar wacce aka ingiza haka ta tafi tana isa ta tsaya kinkam! A tsaye tana mai da numfashi ta shiga nuna kanta da hannu kirjinta sai faman dagawa yake yi idanuwanta na juyawa kamar mai shirin zubewa a kasa da sauri Alhaji Abdulwahaab ya mike don ya lura bata cikin hayyacinta jakarta ya riko ya ajje kan Table din dake wajan kafun ya riko hannunta ya zauna da ita sosai gorar ruwan dake ajje a wajan ya murɗewa kai ya tsiyaya cikin Glass Cup ya mika mata kau da kai tayi cikin wani irin yanayi.
"Haba mana anshi ki sha ko kya samu sa'ida a zuciyarki".
"Bana tunanin ruwa zan yi mani wani amfani a halin da nake ciki a yanzu".
Ta fadi cikin wani irin yanayi tana daura hannayenta saman goshinta da take ji kamar zai dare gida biyƴ.
"Ki ansa ki sha Areefa ruwa zai miki abin da baki taba zato ba".
Ba ta bukatar surutu da yawa don haka ta anshi ruwan ta kai bakinta aiko sai gashi ta take ruwan gabadaya ta dire kofin da karfi har sai da ya tsage don wahala runtse idanuwanta tayi tana faman sauke ajiyar zuciya a hankali gumi ya karyo mata saman goshi idanuwanta a lumshe sosai taji wani sashi na zuciyarta da ruhinta sun yi sanyi kadan da ta sha ruwan.
Lokaci guda ta ware idanuwanta kan na Alhaji Abdulwahaab da yayi kuri yana dubanta nisawa tayi cikin fesar da wani zazzafan huci.
"Wai ni Dr.Erena yake so har yana ikirarin zai aure ni".
Ta fadi tana runtse idanuwanta zuciyarta take ji tana kartawa da wani irin tashin hankali mai girma wata irin tsana mai tsanani da take ji akan Dr.Erena take samun fili a zuciyarta tana kara hauhawa sosai take jin kalamansa na ansa kuwwa a kwanyarta da zuciyarta.
Da na sani take yi na zuwan Company yau da na sani take yi da har ta je Office din sa ta saurare shi dana sani take yi da har ta bari kunnuwanta su ka jiyo mata kalaman da suke kokarin tarwatsa mata zuciya.
Wasu hawaye ne masu tsananin dumi taji suna biyo fuskarta da sauri ta ware ido tana kai hannayenta tana taba su murmushi take saki mai tsananin ciwo kafun ta dubi Alhaji Abdulwahaab mamaki fal a zuciyarta da fuskarta murmushi taga yanayi har hakoransa na bayyana kafun ya mike kan kafafuwansa yana taku a hankali hannayensa goye a bayan sa.
Juyowa yayi ya dubi Areefa har lokacin murmushin bai kau ba sai ma kara fadada da ya yi dawo wa yayi ya zauna sosai yana daura kafa daya kan daya ya jawo Mug din Coffee yana kaiwa bakin sa da wani irin yanayi na nishadi sai da ya kurba sosai sannan ya dire ya daura hannunsa kan Table din yana dan kwankwasawa har zuwa lokacin idanuwansa na kan Areefa da tayi fakare tana dubansa a wani irin yanayi mai cike da mamaki da AL'AJABI mai girma gaske wanda ya kusan sanya zuciyarta tsalle sama. 
"wondefull Story".
Ya fadi yana mai girgiza kai cike da farin ciki kafun ya dora da fadin.
"Sosai da sosai naji dadin wannan ranar a daidai wannan lokacin da na samu daddadar lamari irin wannan How Comes na ce miki yau ce ranar farko da nake hango cinmma nasarata akan Dr.Erena".
Mikewa ya kuma yi kan kafafuwansa hannunsa rike da Mug din Coffee.
"Areefa ya kamata ace wannan lamarin ya samu nishadi a filin duniyar rayuwarki a yanzu...".
"Alhaji Abdulwahaabbb!!".
Areefa ta fadi cikin wani irin sauti mai haifar da ɗaci a saman zuciya tana mikewa kam kafafuwanta idanuwanta a warwaje tana dubansa ciki da kunci zuciyarta na wani irin zafi.
"Ban san mai yasa kake farin ciki da haka ba, Ban san mai yasa kake so nayi farin ciki da wannan lamarin ba, shin ka mance abin da ke tsakanani da Dr.Erena, shin ka mance abin da yasa na ke zaune a INUWA DAYA tare dashi, shin ka mance bani da makiyi a filin duniyar nan sam dashi, shin ka manta ba wanda na tsana duniyar nan na ke son na ga bayansa sama da Dr.Erena".
Runtse idanu tayi tana jan numfshi kafun ta ciji laɓɓanta tana dakune fuska.
"Alhaji Abdulwahaab ta ya ya ke zaton zan yi farin ciki, ta ya ya kake zaton ko hakorana zan bayyana a fili a dalilin wannan maganar haba mana Alhaji Abdulwahaab kayi tunani mana".
Ta karashe tana komawa saman kujera ta zauna hannayenta dukka biyu ta dafe kanta dasu wani irin yanayi take jin zuciyarta na haifa mata wanda take jinsa kamar kirjinta zai kama da wuta ya babbake duk wata halitta dake da gurbi a filin kirjin nata ba ta san mai yasa ma ta zo wajan Alhaji Abdulwahaab ba tayi tunani zai ce da ita wani abu akan wannan lamarin ba amma sai taga sabanin haka wai farin ciki yake yi har ma da dariya.
"Yaa Salam".
Ta fadi tana saukar da hannunta daya tana dafe kirjinta dake ji yayi mata wani irin nauyi mai girman gaske.
"AREEFA!".
Alhaji Abdulwahaab ya fadi da murya mai zurfi. Dago kai tayi ba tare da ta ansa shi ba illa ido da ta zuba masa.
"Wannan lamarin da ya faru nasara ce a tsakanin ni da ke".
Kau da fuskarta tayi jin zuciyarta na kara rura wutar zafin da take ji.
"Nasan zaki ji ba dadi amma wannan hanyar ita ce ta dace ki bi don cimma kudirin ki har ma da nawa".
Girgiza kai ta shiga yi tana yatsine fuska kafun ta mike kan kafafuwanta tana dubansa.
"Ina! wannan ba hanyar mafita bace Alhaji Abdulwahaab bana hango nasara ta a wannan hanyar".
"Don ya furta ya na son ki ko shine kike wa kallon rashin nasara?".
Ta gaji da sauraron kalaman sa domin ranta ya fara baci ba za ta iya cigaba da zama ta na sauraronsa ba.
Hannu ta saka ta janyo jakarta kafun ta dube shi.
"Tafiya zan yi nayi tunanin in na zo maka da maganar nan zan samu mafita a gareka domin cimma burinmu da KUDIRI ashe ba haka bane".
Ta karashe tana takawa kan kafafuwanta.
"Areefa".
Ya fadi yana mikewa da sauri ya isa gabanta yanayin sa ya sauya sosai yake jin tausayin Areefa sai dai wani abu guda yake hango wanda wannan hanyar ce kawai da suka samu ita ce dama da ya kamata ace sunyi amfani da ita kar su sake ta kubace musu.
"ki tuna Areefa kudina ya ansa da sunan muyi haɗaka wajan bude Company kudin da bana wa ba kudin Marayu wanda sam bani da hakki a cikin su kudin da suke zama masifa ga duk wanda ya cisu ya kamata ki tuna ba yarda za ayi na so bayar da gudun mawa ya cutar dake nima ina bukatar naga Dr. Erena ya shiga tashin hankali ina so naga Dr.Erena ya fada cikin halin masifa domin ba mutum bane mai tausayi ba mutum bane mai imani jahadi zakiyi sosai yaci zarafin mutane da ba su ji ba su gani ba sosai ya zalunci mutane wanda na tabbata har dake a ciki. AL'UMMA zaki taimakawa jama'a duniyar na zaki ceto daga fadawa komarsa damarki ce wannan lokacin ki ne wannan Areefa kiyi amfani da ita nasara na tare dake mutane da yawa za su shi miki albarka za suyi miki fata nagari za suyi miki addu'a ki gama da duniya lafiya na rokeki ke kadai ce zaki iya wannan aikin".
Komawa yayi ya zauna yana mai ajjiyar zuciya tausayin Areefa yake ji sosai a ransa ya sani dole taji ba dadi a ranta dole tashiga wani hali na tashin hankali
Amma kuma jahadi za tayi taimakon mutane za tayi ya sani Dr.Erena yana da hatsari Areefa kawai zata iya yin komai in tayi taka tsantsan ba tare da ya gano ta ba musamman yanzu da ya nuna yana sonta ya sani sosai hankalinsa zai karka akanta da komai na shi ya sani Dr.Erena bai iya son abu ba yana nuna maitarsa a fili kuma yana bi ko ta halin k'ak'a ne don ganin ya cimma burinsa akan abin da yake so.
Areefa da ta kasa tafiya tun lokacin da Alhaji Abdulwahaab ya fara bayaninsa gabadaya jikinta yayi sanyi sosai taji zuciyarta narkewa da wani irin rauni mai girma a hankali ta juyo ta dube shi kafun ta gyada masa kai shima kai ya gyada mata don bai gane in da ta dosa ba.
A hankali ta juya ta fara tafiya a jiki a sanyaye zuciyarta na shiga wani iri yanayi tana cakuda maganganun Alhaji Abdulwahaab a zuciyarta da kwakwalwarta har ta fice daga wajan ta isa inda ta ajje motarta tashiga sai da ta shafe mintina kanta akan sitiyari domin komai take ji ya tsaya mata cak! gabadaya taji duniyar tayi mata wani gin-girin-gim kafun ta yi wa Motar Key ta falle kan titi.
*******
A hankali ta turo kofar falon idanuwanta a rufe kadan saboda raɗaɗin da taji sunayi mata kamar jijiyoyin su zasu tsintsinke haka ta zuro kafa cikin falon tana mai ware idanuwanta baki daya tana kokarin gayyato natsuwa ko ya ya ne bata so Hajiya Layla ta san tashin hankalin da tashiga sosai da sosai bata so ta gane tayi kuka da idanuwanta bata so ta saka ita ma cikin tashin hankali don ta tabbata itama akwai abin da ke damun filin rayuwarta.
Nisawa take yi a hankali zuciyarta na kara matsewa wani irin yanayi mai girman gaske idanuwanta ta sauke a inda take tsammanin samunta kamar ko yaushe da ta maida wajan zaunin ta har in ita ba ta nan.
Hango tayi zaune ta zabga tagumi da hannu daya hannu guda m
Kuma rike yake da wani kwali wanda bata gama hakikance na mane ne ba amma zuciyarta ta buga lokacin da taga Hajiya Layla ta kura masa idanuwa ko kaftawa bata yi.
Kara ware idanuwa tayi tana fiddo su kamar wacce zata barsu su faɗo kasa nisawa take yi da wani irin yanayi ganin kwalin dake hannunta sosai ta tsorata tana sakin jakar dake hannunta tana faduwa kasa ba tare da ta sani ba kafafuwanta taji sun shiga rawa kamar za su kasa daukar gangar jikinta da sauri ta fara taku tana haɗe hanya har ta isa gareta ba tare da ta sani ba.
Hannu ta kai ta ansa kwalin cikin wani irin yanayi mai nuna alamun mamaki matuka gaya idanuwanta take yawatawa kan kwalin ba tare da tace kazil ba ta shiga bin Hajiya Layla da kallo wacce ita ma ansar kwalin da Areefa da tayi a hannunta shi ya dawo da ita hayyacinta ta shiga duban Areefa a daidai lokacin kwalla masu yawan gaske wanda suka jima tare a idanuwanta suka zubo ta shiga girgiza kai.
"Maama".
Areefa ta fadi da muryarta mai zurfi idanuwanta da tuhuma acikin su take dubanta tana mai gyada kai tana jin yarda zuciyarta ke kara matsewa da mamakin da bata yi zaton taddashi a gidan ba.
"Dama Da...ma ba ki dai...na baaa!".
Ta sake fadi muryarta na rawa kalmomin da take fadi suna rarrabuwa da junansu.
Wani kuka ne ya kufcewa Hajiya Layla hannu ta saka ta toshe bakin ta kafun ta shiga girgiza kai.
"A,a Areefa wallahi na daina ban sha yanzu kwata-kwata ko kaunar ta bana yi kisan nayi miki alkawari har gaban abada ba zan sake ba".
Girgiza kai Areefa ta shiga yi tana mai zubewa a wajan numfashi take ja dakyar zuciyarta na wani irin zafi da radadi kafun ta fesar da wani zazzafan huci.
"Haba mana Maama sau nawa za muyi maganar nan dake na fada miki illar wannan abun likitoci ma sun fada miki wanda suke k'irk'irarta ma sunyi nuni da cewa tana da illa ga rayuwar duk mai ta'amali da ita ya kamata ki san wannan ya kamata ki duba halin da kike ciki ya kamata ace kin ceto sauran rayuwarki da tayi saura a filin duniyar nan kina ji likita ya fadi ta fara baki matsala sosai wanda yace in ba daina wa kikayi ba to tabbas nan da dan lokaci kadan zaki rasa rayuwarki gabadaya ni kuma ba zan so haka ba Maama AKWAI ILLA a rayuwar shan taba tana da matukar hatsari ga duk mai rayuwa da ita kin sani kuma kinji a jikinki lokacin da kika kwanta rashin lafiya kin ga yanayin da kika shiga na tashin hankali da kyar da taimakon Allah ki ka samu kan ki sosai likitoci suka nuna miki dokoki da zaki bi sannan kiyi kokarin fidda sha'awarta a rayuwarki ko ganinta ki nisanta daga rayuwarki haba mana Maama me yasa haka me ya kawo kwallin taba cikin nan gidan?".
Areefa ta karashe cikin muryar rawa da son fashewa da kuka tasowa tayi ta iso gareta ta kama hannayenta ta rike su gam!. Tana mai a jiyar zuciya laɓɓanta take tura cikin bakinta tana cizawa a hankali.
"Me ya kawo kwallin sigari nan gidan Maama?".
Ta sake fadi idanuwanta na kawo kwalla kafun ta rintse idanu.
"Nayi dana sani a rayuwa ta nayi tir da rayuwar da nayi a duniyata duk a dalilin rashin 'yanci yau na ga illar rashin iyaye yau na ga illar haihuwata da kayi a titi ban san me nayi wa iyayena ba suka yasar dani suka tafi suka bar ni a titin Allah ban san mai yasa sukayi mani haka ba yanzu ga shi nan na rayuwa cikin rashin amfani na tashi cikin rashin 'yanci na rasa mai kwaɓata na rasa mai kula min da rayuwa har ya nuna min kuskure na rayuwata gabadaya ba tayi amfani a duniyar nan ba ni ban yi aure ba balle na samu zuri'ar da za su ji k'ai na ni ban yi rayuwar yanci ba rayuwar titi nayi wacce ba zan ce miki ga yarda na kasance a rayuwata a shekarun yarinta ta ba".
Nisawa tayi wasu hawaye suka zubo mata kafun ta cigaba da fadin.
"kawai na yi rayuwa ce a yarda ta zo mani a yarda Alkalamin kaddara ya zana min wani fannin kuma da nawa kason na lalacewar rayuwata ban san dadin iyaye ba ban san su waye iyaye ba ban san ya yaro yake ji a wajan iyayen sa ba ban san wacce irin kauna ce da ake fadi ana ji a wajan UWA DA UBA ba iyayena sun kasance ne bakin titi da wajan masu abincin saidawa nan ne suka kasance jigon rayuwa ta su ne suka kasance iyaye a gareni har lokacin da na dauki kazamar rayuwa da nake zaton ita ce mafita a gareni na daura a duniya ta".
runtse idanu tayi tana jin yarda kirjinta ke harbawa da duk wani ɗaci gami da zafi a ranta.
"Areefa na daina shan sigari tun da nayi miki alkawari yau ma fita nayi aka zageni aka tsine mani har ake kokarin marina akan sigari wai don kawai nace na daina yaro karami wanda in a haife ne na haife shi in jika ne ma zan iyayi dashi amma akan abin banza abin Allah wadai ya zage ni yana jifana da kwalin sigari dake hannunsa Yaa Allah wannan wacce irin rayuwa ce Areefa nayi dana sanin rayuwa a duniyar nan".
Wata irin zabura tayi idanuwanta a warwaje hannayenta saman kirjinta.
"Maama zagi fa kika ce waye ya zage ki fada min waye shi na nuna masa ke ma kina da gata a rayuwarki rashin iyaye ba hauka bane zan nuna masa kina da gata kuma kina da 'ya a filin duniyar nan da ta san darajar ki da kimarki ki fada min shi please Maama".
Cikin sauti take maganar kamar wacce ta fice daga hayyacin ta da sauri Hajiya Layla ta mike ganin Areefa na kokarin ficewa daga gidan sosai ta rikota ta zauna da ita tana mai kwantar da ita a jikinta tashiga shafa mata baya a hankali har zuwa lokacin idanuwanta na zubda hawaye masu tsananin zafi da take ji kamar za su keta mata duk wani sashi na kirjinta.
"ki bar komai na yafe masa rayuwa ce ta zo da haka inda ban yi harkar shan sigari ba ba yarda za ayi ya tare ni a hanya har ya ci mani mutunci in ba don ya ga alamun nayi shaye shaye ba a zamani na ba yarda za ayi ya dube ni yace na bashi sigari komai ya faru ni ce sanadi ni ce sila Areefa ki bar komai na yafe masa".
Da sauri ta dago kanta tana duban Hajiya Layla da take shafe hawaye.
"Haba mana Maama hawaye fa ya sakaki zubdawa akan mi zaki ce a bar shi bayan ya ci miki mutunci".
"ki bar shi nace kawai ki bar shi komai ya wuce a wajena har a zuciyata na yafe masa fata na Allah ya shirye shi ya sa daga kaina ya daina abin da yake yi domin na lura illar shaye-shaye yawa gareta ba abin da ba zata iya sanya wa ka aikata ba wanda zai cutar da rayuwarka sosai AKWAI ILLA sosai da sosai".
Ta karashe tana mai kalato murmushi tana daurawa a fuskarta domin kwantarwa da Areefa hankali domin bata so ta sake sanya rayuwarta a damuwa nan ta shiga bubbuga bayanta domin kwantar mata da hankali.
Wani numfashi a Areefa taja mai tsayi kafin ta saki ajiyar zuciya.
"Maama ke dama baki da iyaye dama ke ma marainiya ce kamar ni".
"Ya isa haka Areefa mu bar wannan zance haka ba shi da amfani".
Ta katse ta da wani irin yanayi da ta ji zuciyarta na shiga da tashin hankali mai girma.
"Mai ya dawo dake wannan lokacin ba tare da lokacin tashi ya yi?".
Ta fadi domin kau da zancen da Areefa ta dauko.
Da sauri ta tashi zaune tana duban idanun Hajiya Layla kafun taji wata irin tsanar Dr.Erena ta sake samun fili mai girma a zuciyarta a hankali ta shiga cizon laɓɓanta tana runtse idanu.
"Dr.Erena Maama".
Ware idanu tayi kafun ta mike tsaye tana kai kawo a tsakar falon lokaci guda ta tsaya cak! fuskarta ta kara cakuɗewa da bacin rai mai girman gaske.
"Ba dai kin yi sake ya gano ke wa ce ce ba in kuwa haka ne komai zai wargaje mana".
"A,a Maama wai cewa yayi yana sona har cewa yayi zai iya aure na in har na yarda dashi".
Zare idanu tayi waje bakin ta na buɗe ta iso ta zauna tana janyo Areefa jikinta gami da sarke hannayensu waje guda wani murmushi na takaici ta sako kafun ta dubi Areefa sosai da tayi fakare tana dubanta ganin abin da ke fuskarta.
"Lokaci ya zo Areefa lokacin da nake dako ne Allah ya kawo mana shi tabbas lokaci ne ya zo tsakanimu da Dr.Erena".
"Ban gane ba Maama?".
Areefa ta fadi a dan tsora ce tana kwace hannayenta daga cikin na Hajiya Layla.
"Karki damu kawai ke dai ki kwantar da hankalin ki ki cigaba da zuwa aiki karki sake ko da wasa ki nuna masa baki amince ba sannan gobe karki sake ki ce ba zaki office ba ki shirya ki je ki bar komai a hannu na".
Cikin rashin fahimta da kara bayyanuwar mamaki ta shiga motsa laɓɓanta tana kokarin yin magana amma Hajiya Layla ta hana ta tana mai cewa.
"Maza ta shi ki je ki watsa ruwa ki ci abinci ki huta kafin lokacin Sallah yayi".
Ba musu ta mike zuciyarta da wani irin AL'AMARI wanda ta kasa gane kansa sosai kanta ya kulle sosai taji tunanin ta ya kasa buɗe mata wannan lamari wanda ya jefata a duhu sosai da sosai haka ta ja jiki tana duban Hajiya Layla har ta isa dakinta.
Mikewa Hajiya Layla tayi tana kai kawo cikin falon hannayenta take hadawa waje daya tana bugawa wani irin yanayi take ji a jikinta sosai taji dadin maganar nan da Areefa ta fadi mata komai take hangowa ya canza sosai take hango nasara a tsakanin ta da Dr.Erena za ta nuna masa ita wacece kuma za ta nuna masa mace ma daraja gareta a duniyar nan ba kamar yarda ya dauka ba...


 *_KAMALA MINNA_*😍😍😍