Thursday, 24 January 2019

DAGA ƳAN SHI'A 05

A addinin Saqeefawa sun tafi akan cewa: Manzon Allah (A.S) Yabar jama'ar Musulmai kara zube ba tare da yayi wasici ga wanda zai zamo Khalifa bayan sa ba.

Shine dalilin da yasa wasu tsirarun, sahabbai suka tafi taro a Saqeefa suka zabi abubakar a matsayin khalifa.

-Abubakar baibar duniya ba sai da yayi wasici da Umar a matsayin wanda zai jagoranci jama'a.

-Umar bai mutu ba sai da ya samar da kwamiti karkashin Abdurrahaman bin Aufu da zasu za'bi
khalifa bayan sa.

Abun Lura: Idan 'daliban ilimi zasu lura da wannan abu zaisa su iya fahimtar wasu abubuwa cikin Addinin Saqeefawa kamar haka:

-Manzon Allah Yabar jama'a cikin ru'du bai iya nuna masu wanda zasu koma gare shi ba a
matsayin Khalifan sa.

Wanda hakan ne sanadiyyar rarrabuwar kai da tashe tashen hankulan da al'ummar musulmai ke ciki tun bayan shahadar Sa (A.S).

TAMBAYOYIN MU ANAN SUNE:

-Idan har Manzon Allah (A.S) zaibar Al'umma kara zube su zabawa kansu jagora a Saqeefa,
mai yasa Abubuakar baibi sunnar Annabi ba yabar al'umma su zabi wanda shine sukaga yafi da cewa?

-Mai yasa Umar ya kafa kwamitin zaben Khalifa maimakon yabar jama'a su zabi wanda suke so
kamar yadda sukayi a Saqeefa?

Kamar yadda cikin wannan tsokacin ba zagi ko cin mutuncin wani, bamu yarda wani yazo yayi zagi ko cin mutunci ba.

FREE ZAKZAKY

-Muhammad Jiddah Nguru


EmoticonEmoticon