Saturday, 5 January 2019

DAIDAITA TSAKANIN NAMIJI DA MACE A RABON GADO!!!!

DAIDAITA TSAKANIN NAMIJI DA MACE A RABON GADO!!!!
                        *Tambaya?*
Assalamu alaikum mallam menene hukuncin wanda ke kokarin ganin an baiwa mace kason da aka bawa namiji wajen rabon gado?


                           *Amsa*
Wa'alaykumussalam, Ya sabawa Allah, Hakan kuma zai iya fitar da Shi daga musulunci in har ya yi gangancin hakan, saboda kokari ne na warware hukuncin da Allah ya zartar.

Allah ya yi alkawarin wuta mai kuna ga duk wanda ya sabawa ayoyin rabon gado a cikin aya ta 14 a suratun Nisa'i.

Wanda ya yi kira a daidaita namiji da mace a rabon gado saboda jahiltarsa da shari'a ba za'a kafirta shi ba, Saboda ba duk wanda ya aikata kafirci ba ne yake zama kafiri kamar yadda aya da hadisai da yawa suka tabbatar.

Allah ne mafi sani.

14/10/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑 _*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.


EmoticonEmoticon