Tuesday, 1 January 2019

DARASIN RAYUWA

Wani Sarki Ne Ya Tara Waziransa Guda Uku, Ya
Basu Buhu Yace: "Kowanne Ya Tafi Gidan Gona
Ya
Samo Mini Kayan Marmari"
Wazirai Suka Tafi.
* NA FARKO: Ya Ce:"Ai Da Alama Sarkina Yana Son Ya Ci Ne, Saboda Haka Ya Dukufa Da Nemo
Kayan Marmari Masu Kyau".
* NA BIYU: Ya Ce:"Ai Sarki Ba Wani Tsayawa Zai
Yi Yana Kula Ba, Saboda Haka Bari Na Kwaso
Masa Masu Kyau Da Marasa Kyau Da Danyu".
* NA UKU: Kuma Ya Ce:"Ai Kawai Sarki Bama Zai Duba Ba, Saboda Haka Bari Kawai Na Kwaso
Ganyaye, Da Shara Na Cika Buhu".
.
Kwatsam!
Suna Dawowa Sai Sarki Yasa a Kai Su Kurkuku,
Kada a Bawa Kowa Abinci Kowa Ya Ci Abinda Ya Kwaso Har Tsawon Wata Daya.
.
• To Anan Fa Waziri Na FARKO Yayi Ta Cin
Kayan Marmarinsa Lafia Lau.
• Na BIYU Kuwa Yayi Nadama Saboda Ya Hado
Da Marasa Kyau. • NA UKU Kuwa Yaita Cin Shara Da Ganyen Da
Yabo Har Ya Mutu.
TSOKACI: "Ku sanya a ranku cewa kune aka sa
awannan kukurku (KABARI) kun ga duk abinda
kuka
tsinko na Alkhairi ko Sharri a duniya shi xaku gani, Sabi da haka, Yan uwana masu daraja mu
dage wajen kwaso
abubuwan alheri, domin samin sakamako mai
kyau."Allah yabamu sa'ah!Amiiin!!


EmoticonEmoticon