HIRA TSAKANIN ASYKHALEEL DA MARUBUCIYA BEBAH WADATAHIRA TSAKANIN ASYKHALEEL DA MARUBUCIYA BEBAH WADATA
April 21, 2017asykhaleel
_*HIRA DA MARUBUTA*_
_*Assalamu Alaikum… Barkanmu da sake saduwa a cikin shirin namu Wanda Asy Khaleel ta shirya kuma ta gabatar, kubiyoni danjin wacece jarumarmu ta wannan Rana*_
************
_*Asy Khaleel* Assalamu Alaikum, Barkanki da shigowa wannan filin namu mai Albarka_
_*Beebah Wadata* waalaikis salam yawwa barka dea_
_*Asy Khaleel* Madallah, to bakuwar Mu ta wanna Rana da fatan kin iso lfy lau, sannan muna farin cikin ganin ki a wannan filin namu mai albarka tare da dinbin nishadantar wa, batare da bata lokaci ba zamu fada cikin shirinmu ne Kai tsaye…. Masu sauraronmu da masoyanki zasuyi matukar sanjin cikakken sunanki da tarihinki a takaice_?.
_*Beebah Wadata* Na iso lapia, ina farin cikin kasancewa a wannan fili, Ni dai sunana Habiba Muhammad Wadata, Ni yar garin sokoto ce_
_*Asy Khaleel* Masha Allah, zamuso jin Mai yaja raayinki har kika tsinci kanki cikin ONLINE HAUSA WRITERS, kuma wani nvl kika fara rubutawa, wani year,? xuwa ynx nvls dinki nawa_?
_*Beebah Wadata* toh wato abinda yasa na fara rubuta novel,tun ina jss3 na fara karantawa,amma aboye saboda mom dina bata barin mu,lokacin da tasani nasa zata hanani amma kuma unfortunately sai ta kyaleni,Na Dade ina karantawa har nakai ss2,hakanan kawae naji bari na rubuta littafi,Na farayi a exercise buk,tun ina na shirme har na fara rubata na kirki *Masoyiyata*,Kuma shi na fara rubutawa a online, Na fara a Feb 2016_
_novel dina biyar(5) Na tsani aure,masoyiyata
,Auren qarya,Rashin uwa,Ban yi tunani ba,ban k’arasa wasu bah_
_*Asy Khaleel* Masha Allah, Allah ya Kara baseera, A cikin wadannan novels din da kika ambato wannene yafi kwanta maki a rai kikafi so? Sa’annan wannene yafi karbuwa gun readers_?
_*Beebah Wadata* Ameen nagode……toh wanda yafi kwanta min rai *Na tsani aure*, Wanda yafi karbuwa gurin readers *Auren qarya* am still on it mutane dawa suna yawan yi min mgna naki karasa plx nayi saura na k’arasa musu_
_*Asy Khaleel*: Malama Beebah Nida masu sauraro muna bukatar jin Mai yaja raayinki har kikafi San NA TSANI AURE cikin nvls dinki_?
_*Beebah Wadata* littafin na tsani aure,littafi ne da yake fadakarwa,nishadantarwa,game da waazantarwa,littafi ne da nasha wahala sosai gurin yinsa ta ganin yadda zai fadakar da mutane,rayuwar maarautan cikin littafin abin haushi ban tausayi da kuma ban daria,a times indan ina typing nashi nakanyi daria in fact komai na littafin yana burgeni I can’t really expressed hw I lyk d buk_
_*Asy Khaleel*: Madallah! Nida masu sauraro baza a barmu a baya ba, zamu garzaya dan Neman Littafin NA TSANI AURE dan muma Mu karu…Allah ya Kara baseera malama Beebah_.
_*Beebah Wadata* yawwa Ameen_
_*Asy Khaleel* Ga Tambayan mu ta gaba, wani kalubali kika taba fuskanta daga bangaren readers harma dasu Kansu writers din_?
_*Beebah Wadata* Eh toh…gaskiya ban wani fuskance wani kalubale ba a gurin readers ba,sai sau daya da wata ta zageni akan banyi mata sending buk ba,A bangaren writers ma ba laifi ko da irin rayuwarsa._
_*Asy Khaleel* Mungode da wannan bayanin, Allah ya kyauta gaba….Allah ya Kara hada kanku wrtrs_.
_*Beebah Wadata* Ameen ya rabbi_
_*Asy Khaleel* Acikin Online Hausa Writers wacece kika taba kaima ziyara? Wacece ta kawo maki ziyara har gida_?
_*Beebah Wadata* Xee Yabour ita na kaiwa and ita ta kawomin_
_*Asy Khaleel*: Allah ya kara zumunci tsakaninki da Zee yabour, Ga tambayanmu ta gaba…Jarumar tamu wani garuruka kika taba ziyarta anan gida Nigeria da kuma kasar ketare_?
_*Beebah Wadata* gaskiya ban taba ketarawa waje ba amma naje katsina,bauchi,Gusau,birnin kebbi,Kaduna,kano,sokoto da abuja_
_*Asy Khaleel*: Gaskia kinsha tafiye tafiye amma da sauranki tunda bakizo garin Lagos ba
_
_*Beebah Wadata* insh Allah zaki ganni idan naxo_
_*Asy Khaleel*: Kai amma naji dadi…Allah ya kawoki lfy_
_*Beebah Wadata* Ameen _
_*Asy Khaleel*: To Malama Beebah wani kaya kika fisan sawa, a fannin Abinci me kikafi sha’awan ci, bangaran drinks fa_?
_Ta bangaren fina-fina wanne kikafisan kallo etc Hausa, Nigeria da dai saueansu_
_Bangaren Kid’a kidai fa_
_*Beebah Wadata* A fannin kaya both Native n English,Abinci kuma pounded yam with vegetables soup,drinks kuma Tamareen juice_
_Ina matukar son indian series,Philippines n Korean film_
_Nafison naija music most especially na team din Don jazzy_
_*Asy Khaleel*: Madallah da wannan bayanin, Ashe raayinmu yazo daya Indian series ba baya ba gurin Asy _
_Karki damu daga yau Don Jazzy zesan da zamanki tunda ke yar team dinsace_
_*Beebah Wadata* ….hmmm to shikenan_
_*Asy Khaleel*: Masha Allah….Malama Beebaah wacece Mentor dinki dangane da harkan rubuce-rubucenki na novels_?
_*Beebah Wadata* mentor dina a bangaren rubuce-rubuce *Ayusha iliasu*_
_*Asy Khaleel*: Ayusha Iliasu barka da kokari Allah yakara baseera_
_*Beebah Wadata* Ameen ya Allah_
_*Asy Khaleel* Acikin Online Hausa Writers zamuso jin suwaye GWANAYANKI dan nasan baza’a rasa ba_?
_*Beebah Wadata* Dukkan writers gwanaye nane duk ina kaunarsu sai da akwai yan gaban goshi ayusha iliasu,mumeety,mamu(maryam) n asy khaleel_
_*Asy Khaleel*: Gareku Wrtrs dukkanku gwanayan tane kamar yanda jarumar tamu ta fada, Kai Masha Allah, Allah yabar xumunci tsakaninki da yan gaban goshinki da fatan Beebaah ma tanada wanna matsayin a gunku_
_*Beebah Wadata* Ameen_
_*Asy Khaleel*: Ga wata tambaya Wanda masu sauraro da masoyanki suka baza kunne danji…Malama Beebah Nada Aure KO da sauran lokaci_?
_*Beebah Wadata* Aa har ynx ina tsakiyar kasuwa lokaci Mike jira_
_*Asy Khaleel*: Allah ubanjigi ya kawo lkcn, Allah ya baki miji nagari mafi Alkhairi a rayuwarki_
_*Beebah Wadata* Ameen ya rabbi _
_*Asy Khaleel* To Wani Shawara Zaki bama Writers dan ganin an samu cigaba a hakan ONLINE HAUSA WRITERS_?
_*Beebah wadata* Shawarar dazan bawa OHW Dan Allah mu hada kanmu muzama tsintsiya madaurinki daya,mu zama yan uwan tare da qaunar juna_
_*Asy Khaleel*: Ga shawaran Jarumarmu ta wannan Rana BEEBAH WADATA da fatan OHW zakuyi amfanin da shawaranta_
_*Asy Khaleel*: Ga tambayanmu ta karshe…Wani Sako zaki mikawa Fans dinka_?
_*Beebah Wadata* sakon da zan mika ga masoyana Wanda na sani da Wanda bansani,sakone na godia da jinjina hade da gaisuwa mai tarin yawa,Idan bada Ku ba bazan kai haka ba,ina matukar qaunarku,Allah ya biya maku bukatun ku na alkhairi,har makiyana ma ina qaunar kuma_
_*Asy Khaleel*: Masoyan Beebah Wadata da fatan sakon gaisuwan jarumar taku se isa gareku_
_*Asy Khaleel*: Masu Sauraranmu duka-duka anan , muka kawo karshen shirinmu na hira da marubuta Wanda ni Asy Khaleel najagoranci shirin….Ku kasance tare damu a shirinmu na gaba…..Bissalam_
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive