Wednesday, 23 January 2019

UKU-BALA'I 19

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
BABI NA GOMA SHA TARA.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'una mai nake shirin gani ni marka? Hafsi! Hafsi!! Hafsi!!!."
Goggo Marka dake zaune bakin kofa tana kadin zarenta ta mike tana tafa hannaye tana fadin haka idanuwa warwaje lokacin da ta ji sallamar su Mariya jikin ta har ɓari yake yi ta shiga dubansu kamar wanda ta ga wani mugun abu.
Cak! Suka tsaya suma suna dubanta musamman Mariya da idanuwanta su kayo waje tana duban ta ganin yanayin da ta nuna juyawa tayi ta dubi Umma kafun ta sake mai da kallonta zuwa wajan Goggo Marka.
"Mariya Habeeba daga ina kuma haka?".
Ta fadi cikin yanayi na mamakin ganin su.
Suma mamaki ne ya cika musu zuciya sosai da sosai sun rasa abin yi gabakidayan su sai bin ta da kallo kawai suke yi suna faman gyaɗa kai a hankali Mariya ta ja jiki a sanyaye ta isa bakin kofar dakin su da yayi kaca-kaca kamar wani kudundubi kofar dakin su har an girgiɗe ta labulan kuwa an yi fata-fata dashi ta na hango tsakar dakin yarda ya zama kamar wajan wasan yara sosai taji ranta ya sosu matuka gaya tsaki ta ja kadan kafun ta ajje kayan da suke hannunta wani irin duba tayi wa Goggo Marka da tayi tsaye fuska cike da mamaki sosai Hafsi da ta fito da daurin kirji kai ba dan kwali gashin kan nan nata yayi wani kerere kamar dambun karangiya sai fama yawatawa da idanunta take tsakanin Umma da Mariya cikin yanayi na mamaki kallo daya zakayi mata ka gane a firgice ta fito daga cikin dakin barci ne a idonta.
Kau da kai Mariya tayi kafun ta isa in da Umma tayi tsaye kamar wacce aka dasa kallo daya zakayi wa fuskarta ka gane bacin ran dake kunshe a zuciyarta ansar Mu'azzam tayi ta goya sannan ta dubi Umma tana mai rike mata hannu suka baro wajan suka iso kofar dakin nan bari ta samu damar dan gyara wajan sannan ta dauko zani cikin kayansu ta shimfiɗa wa Umma ta zaunar da ita daga nan ta shiga dakin tsaye tayi tana bin sa da kallo wani haushi da takaici gami da tukukin bakin ciki suka cika mata zuciya sosai take ganin yarda dakin ya sauya gabadaya kamar dakin mahaukata kallo take tana tunanin ta ina ma zata fara gyaransa don ta san tabbas wannan dakin ba zaunuwa zai yi ba haka kwafa tayi sannan ta fito daga cikin dakin Umma ta duba cikin yanayi na damuwa.
"Bari na siyo tsintsiya Umma domin wannan dakin ba zaunuwa zai yi ba dole a gyara shi".
Gyada mata kai kawai tayi itama ba tare da ta sake cewa komai ba ta duba cikin kayan su gudan duba ta dauko cikin kudin da Dr.Aqeel ya bata ta fice daga cikin gidan bisa mamaki har yanzu suna nan ba su tafi ba baki ta saki tana duban su kafun ta taka ta isa wajan su.
"Uhmm wai har yanzu...".
sai kuma tayi shiru ba tare da ta karasa abin da tayi niyyar cewa ba ganin irin kallon da Dr.Karami yake yi mata na alamun tuhuma.
"ina zaki je kuma da wannan ranar daga dawowarku?".
Shiru tayi kamar ba za tayi magana ba can ta nisa.
"tsintsiya zan sayo dakin zan share yayi kura ne sosai da sosai ba zai zaunu ba".
ta karashe tana mai yatsine fuska kamar za tayi kuka sosai take jin wani iri a ranta ba ta so ta fito ta tadda su ba ba ta so a wanna lokacin ta sake saka su a idanuwanta ba ta so ace yarda ta baiwa zuciyarta hakurin kewarsu na dan lokacin nan suma sun yi hakan sun tafi ba za ta so wani sabon lamari ya sake afkuwa ba a nan wajan domin ba zata manta tsawon lokacin da suka shafe a nan wajan ba tun isowarsu ake abu daya sai da Umma tayi da gaske sannan suka shiga cikin gidan bayan sun yi sallama amma kuma abin mamaki ta fito ta tadda su.
"Bari naje na sayo Umma na jira na".
Ta fadi cikin yanayi na damuwa domin ba za iya tsayuwa tana kallon su ba sosai take jin zuciyarta na zafi da raɗaɗi ba ta jira cewarsu ba ta fara tafiya cikin yanayi na sanyi jiki sosai ko da ta isa shagon mai tazara kadan da gidan su makalewa tayi taki dawowa tana hango su ba ta ga alamun suna da niyya tafiya ba sam! ita kuma ba ta so su sake gamuwa a cikin halin da take ciki a yanzu so take ta bai wa zuciyarta hakuri so take ta fara koyon zaman kadaici tun yanzu don ta san tabbas dole wata rana su dau lokaci mai tsayi kafun su hadu kuma ya zame mata tilas ta yi abin da Ummanta ba za ta shiga damuwa ba dole ta kau duk wata damuwa a zuciyarta don ganin walwala ga Ummanta.
Numfashi taja kafun ta hango sun shiga motarsu ta lura sosai kamar sun damu da rashin dawowarta kuma ta san saboda su taki dawowa don haka suka yanke hukunci tafiya hakan yayi mata dadi sosai da sosai sai da taga sun fice daga layin su sannan ta tako cikin sarsarfa domin a tunanin ta kila su dawo.
*****
"Mun shiga uku".
Cewar Hafsi tana daura hannu akai idanuwa warwaje kafun ta sake jan numfashi mai dauke da tashin hankali.
"ki ka ce mani sun tafi kenan har abada ba za su dawo ba, amma kuma ga su sun dawo kuma kin ce mani Habeeba ta zama MAHAUKACIYA amma dube ta kalau ba alamun hauka a tare da ita".
Goggo Marka da ta yi zaman yan bori kofar daki ta zabga tagumi tana duban Habeeba da ɗan dake hannunta wasu katangun tashin hankali taji suna rigizo mata akai ji take yi duniyar na juya mata ba ta yi zaton haka zata faru ba bata taba kawo hakan akan ta ba ta yi zaton sun tafi kenan ko duriyar su ba za a sake ji ba a duniyar nan tuni ta saki jiki take shan sharafin ta ganin lokaci sai tafiya yake yi kuma ba su dawo ba hakan ya kara gasgata mata zatonta amma yau rana tsaka irin wanna mugun abu ya zo mata wani numfashi taja ta fesar kafun ta dubi Hafsi murya kasa-kasa domin bata so Habeeba ta ji maganganun da suke yi.
"tuni fa aka tabbatar mani da ta haukace ita da 'yar ta ta da mijin nata...".
Da sauri Hafsi ta katse ta.
"Injiwa ya fada miki to wallahi duk wanda ya fada miki hakan karya ne ki dube su fa su duka kalau suke ba abin da ke damun su".
Nisawa tayi ta kai hannunta ta na susar kanta.
"ina ganin mugun abu kenan da gaske Habeeba ba hauka tay...".
Sallamar da Mariya tayi ne ya katse musu hirar da suke yi sukayi wuri-wuri da ido alamun rashin gaskiya kallo daya tayi musu ta kau da kanta a jikinta take ji akwai maganar da suke yi wanda ya dangance su kunuwanta sun jiyo mata kalmar hauka da Goggo Marka take fadi a zancen hakan ya tabbatar mata da Ummanta suke yi wato hauka tayi kenan daukar ta suke a matsayin mahaukaciya wani kunci taji ya tokare mata kirji sosai taji ranta na ɓaci amma sai ta share su ta baiwa banza ajiyarsu ta isa in da Umma kenan zaune ta zabga tagumi da alamun ita ma ta ji hira da suke yi a kanta don idanunta har sun tara kwalla kadan.
Sauko da Mu'azzam tayi barci ya ke yi hankali kwance a haka ta mikawa Umma shi ba tare da tace da ita kala ba ta dauki tsintsiyar da ta sayo ta shiga dakin a hankali ta fara tattara kayan su waje daya ta na fitowa da su waje zuciyarta na kunci da bakin ciki sosai take jin tausayin kan su sosai take hango irin kalar zaman da za suyi a gidan nan duba da tayi da halin Goggo Marka yana nan yarda yake ba sauyawa tayi ba sai abin da ya ci uban na da sosai take ganin za su fuskanci yanayin rayuwa a gidan musamman yanzu da suka kasance su kadai ba mahaifinta wanda shi kadai suke samun sauki a wajan sa to yanzu baya nan Allah kadai yasan halin da za su shiga cikin wannan halin ta hau tsaftace dakin yayi kura sosai bayan ta kwashe komi ta samo ruwa ta yayyafa a dakin saboda ba simitin in tana sharewa kuma kura na tashi sosai a haka cikin jarumta ta kammala sharewa sannan ta fito ta barshi ya sha iska kayan su ta ajje su gefe domin sun yi datti sosai suna bukatar zama na musamman domin wanke su sai da ta zauna ta huta sannan ta sake fita ta sayo kayan wanki sabulu da omo ta zo ta ja ruwa sosai ta jika kayan duk abin da take yi akan idon Goggo Marka da Hafsi sai faman bin ta da kallo suke suna faman yatsine fuska kamar sun ga abin kyankyami..
*********
Satin su Mariya biyu da dawo gida izuwa lokacin mutanan unguwa da yawa sun san sun dawo ana ta zuwa musu barka da arzuki da kuma ya mai jiki a nan suke samun labari wajan mutanan gari wai ai Habeeba hauka cewa tayi ta shiga duniya tun da ta haihu cutar hauka ta same ta ba a san in da take ba Mariya da babanta kuma suma sun ba zama duniya ne neman ta tun da suka tafi ba labarin su.
Abin yayi matukar daurewa Umma da Mariya kai sosai suka ji a ransu bisa wannan mugun fata da akayi musu na halaka ko daya ke ba suyi mamaki ba tun da sun san halin wacce ta kulla musu wannan makircin kadan daga aikin ta.
Ba su ce da ita komai ba sai dai suka barta da Allah domin kuwa halinta yafi karfin su.
Kamar ko yaushe yau ma Mariya na goye da Mu'azzam tana dauraye musu kayansu domin tun da suka dawo ko tsinke ba ta bari Umma ta dauke komai ba ita take yi rainon Mu'azzam duk yana wajan ta tun da ba nono yake sha ba sai madara anyi anyi amma ina yaki kamawa ko ya kama ya fara sha sai ya saki dole ta kasance madara ake bashi.
"Mariya".
Ta jiyo muryar Umma ta na kiranta da sauri ta ajje wanki tana amsawa ta doshi dakin.
"Yawwa yar Albarka amshi nan maza ki je gidan kultum ki sayo mani tafarnuwa".
Da mamaki Mariya ta dubeta.
"Umma Tafarnuwa kuma, me zakiyi da ita?".
"Yaa Allah! Mariya kenan. ba fa wani abu bane zan yi da ita kawai kafafuwa na ne naji suna rikewa na san kuma sanyi ne ba wani abu ba shine fa zan yi amfani da ita".
dan tsuke fuska tayi alamun rashin son abin da Umma tace.
"kawai ki bari Yah Dr.Karami ya zo sai a fada masa ƙafarki na ciwo nasan zai baki magani ni kam ban yarda ki yi amfani da tafarnuwar nan ba tun da ba likita bane yace ki yi amfani da ita".
Murmushi tayi ta san halin Mariya sarai tun da ta warke a cutar nan in dai za tayi abu to tabbas sai taji daga bakin Dr.Karami tun da yana zuwa musu lokaci lokaci ya duba jikin Umma.
"Shikenan naji taimaka dai ki sayo mani na ajje in ya zo duk abin da ya ce dashi zan yi amfani".
Fuskar a dan tsuke ta amshi kudin ta ficewarta Umma na bin ta da ido murmushi a fuskarta sosai take jin kaunar 'yar ta ta a ranta sosai yanayin rayuwarta take burgeta da komai na ta godiya take yi wa Allah da ya bata 'ya kamilalliya mai natsuwa da sanin ya kamata duk da karancin shekarun ta hakan bai hana ta sanin ya kamata ba idanuwanta lokaci guda suka kawo kwalla.
"Ina ka shiga ne ina son ganin ka a duniyata ya Allah duk in da wannan bawan naka yake Allah ka tsareshi ka tsare masa rayuwarsa ya Allah ka karkato masa da hankali ya dawo gaban iyalansa suna matukar buƙatarsa".
A bayyane take zancen zuciyarta take ji tana yi mata zafi tun lokacin da ta tsinci labarin tafiyar mijinta shikenan komai ya kara jagule mata ta rasa ina zata sa kanta abubuwa da yawa sun rikita mata rayuwa ita ba dangi ba ita ba iyaye ba sannan gashi yanzu miji ba ta san a halin da yake ba sosai take godewa Allah da irin ƙaddarar da ta samun kan ta a ciki sosai take goɗewa Allah da irin jarabtar da ya jeho mata cikin rayuwarta.
Dauke hawayen ta sake yi tana mai gyaɗa kai ita kadai ta san abin da take ji a zuciyar ta da kasan ruhin ta sosai rayuwar duniyar nan ke tsorata ta sosai take tsorota da komai na duniyar nan baki dayan sa.
*******
Sosai zuciyarta ta buga lokacin da idanuwanta suka hango mata shi zaune saman motarsa ya tallaɓe haba kamar wanda aka aikowa da mutuwa cikin dangin sa runtse idanuwa tayi gani take kamar a mafarki ba gaske ba laɓɓanta ta tura cikin baki tana cizawa a hankali zafin da take ji yana ratsa ta ya tabbatar mata da gaske shi din ne ba wani ba.
Kallon sa take da duk wani yanayi da ta tsinci kanta sosai ta hango sauyin yanayi game dashi sosai ta hango canji a gareshi ba kamar kwanakin baya ba wani abu taji yana mata yawo a zuciya sosai take jin jikinta na sakin wani irin yanayi yana kaiwa ga kafafuwanta kamar ba za su dauki gangar jikin ta ba.
"Yaa Rabbi!".
Ta fadi tana mai kau da kanta tana gargaɗin zuciyarta da ta daina abin da take yi akan Huzaif...
"Mariyaaa!".
Kamar daga sama ta jiyo sautin amon muryarsa mai cike da wani irin yanayi wanda ba ta san yarda zata ce yake ba amma dai da alamun rauni a cikin ta dago kanta tayi ta hango ya sauko daga kan motarsa ya doso in da take da sauri ta juya za ta koma cikin gida domin ba zata iya tsayuwa dashi ba sosai take jin ta a wani mataki wanda ya canza mata komai nata yake yaki da natsuwarta yake haifar mata da abubuwa masu tsoratar mata da zuciya da gangar jiki.
"Don Allah...".
Tsak! ta tsaya ba tare da ta waigo ba jin abin da yace sosai taji wani abu a muryarsa wanda ya kara rikita mata zuciya da kwakwalwa.
"Ban san mai zance miki ba, ban san abin da ya dace na fada miki ba wanda zai canza komai da komai a idanuwanki".
Nisawa yayi yana mai dafe kansa da yaji yana wani irin juya masa kamar zai watsar dashi a kasa bai san abin da zai ce da ita ba bai san abin da ya dace yace da ita ba bai san ya akayi ya zo nan wajan ba bai san akan abin da kawo shi nan ba gashi dai ga Mariya amma shi a karan kan sa bai san mai zai ce mata ba.
Sosai ta gane inda ya dosa sosai ta fahimci akwai abin da ke addabar zuciyarsa.
"Kayi hakuri na san ban kyauta maka ba...".
"Please Mariya mana".
Ya yi saurin katse ta jin abin da take fadi sosai ya ji wani iri a zuciyarsa.
"Ni ya dace na baki hakuri ni ne nayi miki laifi ni ne na aikata miki ba daidai ba afuwarki nake nema ba ban yi zaton kalamai na za su sanya ki ki tsane ni ba...ko da yake komai ya faru ni na jawa kai na don Allah kiyi hakuri".
Wani irin nauyi taji kanta yayi mata sosai taji rashin dacewa sosai taji kunya ta kamata ace mutum kamar Huzaif yake bata hakuri ta ya ya hankali zai dauka anya kuwa ba wata manufa a zuciyarsa anya kuwa zata yarda da maganarsa domin ita tun haduwarsu ta farko ta raina wa a zancin sa sosai ta gane bai iya lafuza ba...
"na san dole ki ji ba dadi a ranki amma duk da hakan ki daure ki yafe mani Mariya sosai da sosai na shiga tashin hankali a rayuwa tun haduwa dake na kasa sukuni komai nawa na rasa gane kan sa na sani kece...kece silar komai ya faru kuma na sani nine ban da gaskiya".
"Na yafe maka Allah ya yafe mana baki daya ni dama ba kayi mani komai ba".
Sosai ta gaji da maganganunsa shiyasa ta katse masa hanzari da amsar bukatarsa.
Wata irin a jiyar zuciya yayi kafun ya dubeta da wani irin kallo.
"Na gode sosai Mariya".
Gyaɗa kai tayi kafun ta dago idanuwanta ta dube shi sosai taji gabanta ya fadi saboda wani irin kallo da taga yana yi mata sosai taji wani iri a ko ina nata da sauri tayi kasa da kai.
"So Fine Boy waye wannan yaro mai kyau dashi".
Ya fadi yana shafar kansa.
"Kanina ne".
Ta fadi a hankali sosai taji dadi da yabon da yayi wa Mu'azzam hakan ya kara rage haushin sa da take ji.
"Don Allah bani shi mana mu gaisa".
Ya fadi yana mai kasa da murya gami da mika mata hannu a hankali ta kwance Mu'azzam ba tare da komai ba ta mika masa wata irin runguma yayi masa gami da manna masa kiss a fuskarsa a daidai lokacin Mu'azzam ya buɗe idanuwansa yana kallon Huzaif murmushi yayi masa shima nan da nan ya wangale masa baki hakan ba karamin burge Huzaif yayi ba sosai ya shagala da kallonsa yana yi masa wasa har ya so mantawa da Mariya ma a wajan.
Sai da tayi gyarar murya sannan ya dago ya dube ta da murmushi a fuskarsa.
"Yana da kyau sosai ina son sa.
Ya sunansa?".
"Ibrahim amma Mu'azzam muke kiran sa".
"Nice Name sunan nashi ya dace dashi sosai, ya fi ki kyau fa".
Ya fadi da sigar zolaya
Dariya tayi kadan kafun ta mika masa hannu.
"kawo sa Umma ce ta aike mu fa?".
Ba musu ya mika mata shi
Kamar daga sama sai ga Hafsi tsaye akan su ta na duban su daya bayan daya a sheke Huzaif ya dube ta sannan ya dubi Mariya kau da kan ta tayi hakan da ta nuna sai ya karanci wani abu game da ita shima sai ya tsuke fuska kamar ba shi bane yake yiwa Mu'azzam wasa yanzu.
Tsaki ta ja ganin sun ba banza ajiyar ta tayi cikin gidan tana kunkuni.
"Sai anjima ma ko nagode".
Ta fadi tana juyawa da sauri ya tsaida ita yana mai sanya hannu cikin aljihunsa kudi ya zaro masu dan dama ya mika mata.
"Gashi ki sai wa Mu'azzam cakulat sannan don Allah in kin shiga ki gaida Umma".
Irin kallon da ya ga ta na yi masa ne mai cike da tuhuma da ban so abin da kayi mani ba duk sai ya tsargu jikin sa yayi sanyi duk sai ya ji ya rikice ya rasa ma mai zai yi.
Girgiza kai tayi kafun ta saki wani murmushi.
"Uhmm rike kudin ka na gode sosai".
Ta na fadin haka ta taka kafa da sauri ta bar wajan kallo ya bita dashi yana faman gyada kai kamar wani kadangare har takule a sabule ya mai da kudin sa aljihu ya jima a tsaye cikin nazari kafun ya ja kafarsa ya isa wajan motarsa ya bar unguwar cike da abubuwa masu girma da suka saka zuciyarsa nauyi.
Duk abin da yake yi Mariya na laɓe a zauren gidan da tashige tana kallonsa sosai taji ya bata tausayi sosai take jin wani irin abu game dashi a zuciyarta musamman yarda ya baiwa Mu'azzam kulawa duk sai taji duk wani kunci da take ji game dashi yana bacewa daga filin zuciyarta gyaɗa kai tayi ta kara sa cikin gidan ta sayo tafarnuwar ta fito a hankali take tafiya zuciyarta na ta kawo mata abubuwa masu yawa suna samun gurbin zama a kofar gida ta ja burki ta tsaya tana gyara goyon Mu'azzam.
Horn taji anyi mata a bayanta da sauri ta juya gabanta na faduwa duk a tunaninta Huzaif ne ya dawo amma sai ta ga akasin hakan Dr.Karami ne zaune cikin motarsa ya zuru kafafuwansa waje ya sauke gilas din yana kafe ta da idanu sai faman murmushi yake yi ita ma murmushi tayi tana mai yin kasa da kai.
A hankali ya mike kan kafafuwansa ya karasa fitowa ya kulle motar yana takowa zuwa gareta har lokacin kanta na kasa
"My Boy ya kake?".
Ya fadi yana taba Mu'azzam shi kuma sai faman zillo yake yi alamun yana so yaje wajan sa sosai suka saba tsakaninsu sosai Dr.karami yake son Mu'azzam in dai ya zo gidan to tabbas Mu'azzam na hannunsa har sai ya tashi tafiya.
"Ina yini".
Ta fadi kanta a kasa bai kula ta ba illa kokarin zare Mu'azzam da yake yi a bayan ta ganin haka ya sanya ta kwance shi.
Daukarsa yayi ya rungume shi yana mai manna masa kiss shikuwa sai faman Dariya yake yi.
"me kika fito yi waje tare dashi da ranar nan?".
"Umma ce ta aike ne sayan tafarnuwa".
Kallon hannunta yayi ba tare da ya ce da ita komai ba ya fara taka kafafuwan sa zuwa cikin gidan domin ba ai masa shamaki ba Umma ta bashi dama ya dinga shigowa duk lokacin da ya zo ya daina tsayawa a waje.
Mariya bin sa tayi a baya har suka isa cikin gidan bakin Kofa suka hango Hafsi baje tana cin awara tayi ɗaiɗai da kafafuwanta sai faman jan hanci take yi tana gumi alamun yaji yayi yawa ko kallon su ba tayi ba su ma ba su bi ta kan ta ba sukayi sallama dakin Umma su ka shiga bayan ta ba su izini.
Bayan sun gaisa nan Mariya ta shiga korawa Dr.karami bayani akan tafarnuwar da ta sayo wa Umma dariya yayi sosai kafun ya numfasa.
"Mariya iyayen tsari to ai ba wani abu bane tafarnuwa tana da amfani sosai a jikin mutum ba ta da illar komai ana so mutane suke amfani da ita sosai ko a cikin abinci ne domin magani ce kamar yarda kika ji Umma ta fadi don haka sai ki kyale tayi amfani da kayanta".
Dariya Umma tayi mata itama dariya tayi tana mikawa Umma tafarnuwar.
Shiru ne ya gifta tsakanin su na yan dakiku kafun Dr.Karami ya ja numfashi ya dubi Mariya sannan ya dubi Umma.
"Umma dama akwai maganar da nake so muyi game da Mariya akan karatun ta ya kamata ace ta koma makaranta zaman ta hakan ba zai yuwuwa ba ya kamata ace a yarda take da kuruciyar ta ace tana makaranta yanzu".
shiru Umma tayi tana gyaɗa kai sosai taji dadin maganar Dr.Karami domin tafi kowa son Mariya tayi karatu domin karatun Mariya abu ne mai muhimmanci a garesu dama al'umma baki daya sai dai WANI HANZARI ba gudu ba ba a nan gizo ke saƙar ba...
"Umma karki damu nasan abin da kike tunani wannan duk ba wani abun da zai gagara ba ne ni aka ran kai na nayi alkawari zan dauki nauyin karatun Mariya tun daga yanzu har zuwa lokacin da zata kammala shi".
Wani irin duban hanzari Umma tayi masa tana girgiza kai ba ta san wani irin mutum bane shi sosai ta fuskanci mutum ne shi mai yaƙana da alheri a rayuwarsa ba abin da ya hada su ba dangin iya babu na baba amma jibi yarda yake dawaniya da su tun daga lokacin da ta shiga matsalar cutar ta har zuwa wannan lokaci bai gajiya ba ga shi yanzu ya dauko wani gagarumin aiki wanda ya kamata ace su iyayenta ya dace ace duk sun yi sa.
rintse idanu tayi wasu hawaye suka zubo mata ganin hakan ya sanya Dr.Karami saurin dubanta.
"Don Allah Ki daina wannan kukan bai dace da ke ba sam! Addu'a ya kamata ace kin yi kawai Allah ya tabbatar da alheri".
"Hisham ban san da bakin da zan gode maka ba kayi mani komai na rayuwa ba tare da kasan su waye mu ba nagode sosai Allah ya saka maka da alheri ya cika maka burukan ka na alheri ya kare maka rayuwa da zuri'a" .
"Ameen Summa Ameen".
Ya fadi yana duban Mariya wacce tayi kasa da kai tana faman hawaye sosai ya ji ba dadi a ransa ba zai iya cigaba da zama yana ganin hawayen su ba don haka ya mike ya na mai ajje Mu'azzam.
"Zan tafi Sai gobe kuma in Allah ya kai mu zan zo domin yin abin da ya dace".
Ya na fadin haka ya fice daga cikin dakin ya bar su Mariya shanye da baki suna duban junansu...
*KAMALA MINNA*😎😎EmoticonEmoticon