Wednesday, 16 January 2019

YA MUSULUNTA, YA MUTU, YA BAR MATA BAKWAI, YAYA ZA'A RABA GADONSA???
YA MUSULUNTA, YA MUTU, YA BAR MATA BAKWAI, YAYA ZA'A RABA GADONSA???


                         *Tambaya:*
Assalamu Alaikum. Da fatan Malam ya na lafiya. Malam don Allah ina da tambaya; Mutum ne ya musulunta, bayan ya karbi musulunci ya kira matansa a waya suma suka musulunta kafin yadawo sai ya rasu. Matan Kuma su bakwai ne. Yaya za ayi wajen rabon gado?                             *Amsa:*
Wa'alaikumus Salam Wa Rahmatullah. Toh dan uwa Lallai ya wajaba a gare su dukkansu su yı idda, Sannan Za su yı sulhu a tsakaninsu su barwa mata hudu su ci gado, in kuma suka ki yin sulhu sai ayi Kuri'a a tsakaninsu, a zabi guda hudu ta hanyar Kuri'a, a basu gado.

Don neman karin bayani duba: Al-mugni na Ibnu Khudaamah 7/540.

Allah ne mafi sani.

22-02-2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑 _*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.


EmoticonEmoticon