BIRNIN SAHARA 17

࿐​ *_​PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_* ࿐​

༄༄ *PWA* ༄༄࿐​❁✹✿​༄✺༄✿​✹❁࿐​
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
     *BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
࿐​❁✹✿​༄✺༄✿​✹❁࿐​          

____________________________________

   ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
         *ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Raees_* ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹

            (℘ᾰ❡ḙ 17)

Ko da na Shafo kaina naga jini, sai nan take zuciyata ta harzuƙa raina ya ɓaci. Zumbur! Na Miƙe tare da goge wani ɗigon jini dake ƙoƙarin shiga min idanuwana. A daidai wannan lokaci ita kuma Dardira ta koma kefe kawai tana Kai-komo tare da jiran ganin na taso. Daga nan sai nayi wani abu wanda ni kaina sai da ya bani mamaki.

Wata Irin Tsyuwar yaƙi nayi wacce tafi kama da tsugunno, ita irin wannan tsayawa ita ce tsayuwar salon yaƙi na Ƙarshe da mahaifina ya koya min kafin rasuwar sa, kuma har ya rasu ban gama Ƙwarewa irin yadda yake so ba. Wani irin salon faɗa ne wanda Mukan yiwa juna dariya akan shi a wasu lokutan saboda sunan da muka sa masa na 'MALAM BUƊE MANA LITTAFI'. Shi irin wannan salon yaƙi, mutum yakan tsuguna ne kamar yana kan Babur, ƙafar sa ɗaya tana gaba ɗaya tana baya. Hannuwan sa ma haka, sai dai hannun gaba zai kasance ne a ƙasa-ƙasa, hannun baya kuma a sama. A haka, abokin Karawar ka zai kasa tantance da wannene zaka kai masa hari, in yayi can kai sai kayi nan, in kuma yayi nan sai ka taro shi ta can.

Magana ta gaskiya wannan salon faɗa ba ƙaramin wahalar Koyo yake da shi ba, balle kuma ace a Ƙware a kanshi. Mahaifina ya faɗa min cewa shi kanshi ya ɗauke shi tsawon shekaru kafin ya Ƙware kuma yakan yaba min ma dangane da ƙoƙarin domin yakan ce na fishi saurin ɗaukar abu idan aka koya min. Bugu da ƙari, duk iya Karance-karance na, da Bincike-bincike na, da Kallace-kallace na, sau Ɗaya na taɓa samun wani wanda naga yana yin irin wannan faɗan a cikin wani fim mai suna Queens Of Lankasuka.

Don haka yin wannan tsayuwa a daidai wannan lokacin sai ya zamo abin mamaki a gare ni, musamman duba da cewa ban Ƙware akan sa ba. Sai dai bisa ga Mamakina, wannan tsayuwa da nayi ta Matuƙar firgita Dardira tare da Sauran mutanen fadar, domin Dardira sai da ta ja da baya jikin Firgici kafin daga baya ta shiga taitayinta. Ina kallon wasu daga cikin mutanen ta Wutsiyar ido daga cikin ƴan fadar suma sun Mimmiƙe, amma naƙi yarda in waiga gare su domin Dardira tana iya kawo min hari a kowane lokaci.

Kamar haɗin baki kuwa, sai Dardira ta sake nufo ni da wani sabon azababben gudu, nima na tare ta muka fara fafatawa. Nan fa faɗan ya zamo samu, ya zamana muna kaiwa juna muggan hare-hare. Sai da muka kwashe sama da daƙiƙa ɗari da sittin muna wannan fafatawa amma Dardira ko lakutar hanci na bata samu damar yi ba, Yayinda ni kuma gaba ɗaya na rikitata da duka da sanda ta. A ƙalla nayi mata ƙwararan bugu guda shida a manyan gaɓoɓin jikinta. Hakan yasa da ƙyar take iya tsayawa da ƙafafunta, kuma da ƙyar take iya kare farmakin da nake kawo mata.

Yayinda dai na fahimci cewa tayi tiɓis, sai na kai mata wani wawan duka a kai, ta sa Takobinta ta kare, kafin ta ankara na daki ƙafafuwanta guda biyu a tare, nan fa tayi taga-taga zata faɗi, tun kafin ta kai ƙasa na rarumeta makai ƙasan tare. Ya zamana ta faɗi akan fuskar ta, Yayinda ni kuma na jawo hannayenta baya tare da taɗiye ƙafafuwanta a cikin nawa kamar ɗan Wrestling, ya zamana ta kasa koda motsin kirki. Nanfa fadar ta ƙara yin tsit. Na kalli Dardira dakayu ina mai ajiyar zuciya nace:
"ki miƙa wuya mu bar yaƙin nan"
"bazan taɓa miƙa wuya" tace dani. 
"Ba burina bane in kashe kowa, kawai ki miƙa wuya ni gida nake so in koma! 
"Kawai ka kashe ni tunda kayi nasara" 
" AHALIN ki suna buƙatar ki, kuma kina da amfani ga mutanen Ƙasar nan, ki miƙa wuya kawai! 

Daganan sai shiru ya ɗan gudana a tsakanin mu, bayan wani ɗan lokaci sai Dardira ta aje wani gwauron Numfashi sannan ta gyaɗa kai alamar ta amince. Nan take na sake ta sannan na matsa gefe ina haki. Sai a wannan lokaci ne na fuskanci mutanen fadar waɗanda da yawansu sun Miƙe tsaye tare da wangale baki suna kallona, wasu cikin mamaki wasu cikin Firgici. Ita kanta Sarauniya Diana sai da ta tsaya kawai tana kallona cikin rashin sanin me ya kamata tace. A daidai wannan lokaci ne kuma Dardira ta Miƙe tsaye, ta kalle ni Dakyau, sannan tayi min gaisuwar bangirma ta hanyar risinawa kaɗan, sannan ta koma bayan mahaifinta ta tsaya. Shiru ya ɗan ƙara gudana aka rasa wanda zai ce ƙala! 

Da dai naga kowa yayi tsit, sai na maida dubana zuwa ga Sarauniya Diana nace da ita; "Yake wannan Sarauniya mai Karamci, ina mai roƙon ki da ki gabatar min da Jarabawata ta gaba". Wannan kalami nawa ne ya dawo da gaba daƴan mutanen dake cikin fadar hayyacin hayyacin su, nan take Boka Nuna'u Ya nufo ni yana mai cewa: 'Wannan Al'amarin akwai ƙwange a ciki, a Ƙa'idar irin wannan Fafatawa dole ne ɗaya ya kashe ɗaya sannan ya wanzu a matsayin mai nasara... Kafin ya gama rufe bakin sa sai nan take Sarkin yaƙi Dargazu ya Katse Shi da cewa' kana nufin kace da ya sani ya kashe ƴata kenan Ko yaya? Boka Nuna'u sai ya juya gare shi yana cewa Amma kaima kasan haka wannan dokar ta ke... Nan dai suka fara kace-na-ce da dai naga abin nasu ba mai Ƙarewa bane sai nayi gyaran murya sannan nace;
'Hem.. Idan ba zaku damu ba, wannan matsalar ku ce, na zaɓi in bar ta da ranta ne don ni ba rigima nazo nema da ku ba, don haka kuji da ni tukun, daga baya sai ku ci gaba da gardamar taƙu! Cikin ɓacin rai Boka Nuna'u ya juyo gare yana magana cikin fushi;' kai kuma wa ya kasa da kai? Kai har ka isa manya suna magana kana saka musu?... Ai kafin ya gama maganar ni tuni ma zuciyata har ta fara tafasa don haka na maida mishi da martani da cewa,' ai naga manyan ne sun koma wasan yara, don haka naga ya dace inyi magana! 
"KAI har ni kake gayawa magana?" 
"to sai me don an gaya maka maganar? So kayi ɗayan mu ya mutu kuma hakan bai faru ba kawai shi ne kake jin haushi, kenan ko dai ka tsaneni ko kuma ka tsani ahalin sarkin yaƙi shi yasa kake so mu kashe juna! Hayyasa, ashe na tono Tsuliyar Dodo, nan take Boka Nuna'u ya Jeho ni da wata wuƙar Tsafi, nayi sauri na goce, kafin in ankara sai gani kawai nayi wasu Kibiyoyi guda biyar sun fito daga cikin ƴan yatsunsa sun nufo ni a fusace. Nan take na sa sandar dake Hannuna na kaɗe kibiyoyin gaba daƴa, nan take suka zube ƙasa suna huci tare da narka shatin inda suka faɗo. 


Ko da ganin haka sai Boka Nuna'u Ya Nuno ni da yatsun hannunsa yana mai karanta wasu ɗalasiman tsafi, nan take sai wata ƙaƙƙarfar Iska ta Tunkaro ni. Tun kafin ta iso gare ni na fara jin hucin ta, wani abun mamaki sai naji jikina ya ƙame na kasa motsa ko da yatsar ƙafata. Nan dai na zubawa Sarautar Allaah ido kawai na tsaya ina jiran abinda zai faru dani, domin nasan cewa sai yadda ta yiwu. Ko da ya rage bai fi taku uku a tsakanina da wannan iska ba, kawai sai naga wata Jaruma Sanye da wasu baƙaƙen Ƙaya waɗanɗa sun rufe gaba ɗaya jikinta idanuwanta kawai ake iya gani, ta diro gabana sannan ta sa wata garkuwa dake hannunta ta tare wannan iska. Ko da wannan iska ta bugi wannan garkuwa, sai nan take ta koma da baya a fusace ta ɗaga Boka Nuna'u sama ta buga shi da ƙasa, take ya faɗo magashiyan baya iya ko motsi. Nan fa kowa yayi Cirko-cirko ana kallon-Kallo Yayinda Jarumai suka fara zare makaman su da nufin su kaiwa wannan Jaruma hari, ita kuwa ta Tsaya ƙyam a gabana ba tare da ta yi wani ƙwaƙƙwaran Motsi ba. Ganin haka yasa Sarauniya Diana ta Miƙe tsaye tare da umartar waɗannan Dakaru da su Dakata.

Bayan Dakarun Sun dakata daga kai wa wannan baƙuwar Jaruma harin da sukayi nufi, sai Sarauniya Diana Ta Tako da kanta tazo gaban wannan Jaruma, Kasancewar ina bayan wannan Jaruma ina iya ganin yanayin fuskar Sarauniya Diana, sai dai bana iya ganin yanayin na ita wannan Jaruma. A wannan lokaci Sarauniya Diana bata nuna wata alama ta rashin jin daɗi ko murnar bayyanar wannan Jaruma ba, amma ina iya ganin alamun damuwa rututu a cikin ƙwayar Idanun ta. Bayan sun Ƙarewa juna kallo na wani ɗan lokaci sai Sarauniya Diana ta dubi wannan Jaruma da Kyau tace; 'Shin ko Zan iya sanin dalilin da ya fito da Damisa daga Maɓoyar ta? Ba tare da Jarumar tayi wani motsi ba sai ta baiwa Sarauniya Diana amsa da cewa: "Damisar ta biyo bayan ɗan Marayan Zaki ne, kuma tana fata za'a barta ta tafi da shi ba tare da Ja-in-ja ba! 

Ko da jin wannan furuci sai alamun rashin fahimta suka yi dirar mikiya a fuskar Sarauniya Diana, don haka sai ta sake Tambayar wannan Jaruma tana mai cewa: 'shin dama akan samu alaƙa tsakanin Wuta da ruwa? Yayinda Jarumar taji wannan tambaya sai tayi ajiyar zuciya sannan tace; 'Tabbas waɗannan halittu ne da ba sa jituwa da juna, amma alaƙar su anan ita ce dai irin alaƙar da ke Samuwa a duk lokacin da wani yayi nufin amfani da su. Misali, Yana iya dafa abinci da wuta kuma yana iya shan ruwan hakanan don biyan buƙatar sa, sannan yana iya kashe wutar da ruwan ko kuma ya dafa ruwan da wutar don biyan wwta buƙata nasa'. Wannan Kalami da Jarumar tayi ne yasa kyakkyawar Fuskar Sarauniya Diana ta ƙara faɗawa cikin yanayin Damuwa, nan fa ta fara kaiwa da komowa tana tunanin hukuncin da ya kamata ta yanke. Ni kuma nayi kasaƙe... Ina kallon ta. Suma sauran Jamar fadar sai sukayi Tsit, Yayinda suka zubawa wannan Jaruma ido kawai ba tare da ɗayan su yace komai ba. Da dai naga abin nayi ne, sai na buɗe baki nace; 'Kuyi haƙuri da Kutse na, ina godiya mai tarin yawa a Gareki yake wannan Jaruma, amma idan ba zaki damu ba zan so ki bari sarauniya ta fara sallamata tukunna, in yaso daga baya sai ku ci gaba da zancen naku'. Ko da na zo daidai nan a zance na sai wannan Jaruma ta juyo ta fuskance ni sannan ta buɗe baki cikin sassanyar Murya tace dani; 'Kada ka damu ɗan Uwa, Komai Zai yi daidai, ka ɗan ƙara haƙuri kaɗan'. 

Ko da naji wannan batu ya fito daga bakin wannan baƙuwar Jaruma sai Tunanina ya dagule, hankali na ya dugunzuma har ma na fara yiwa kaina wasu tambayoyi Sababbi waɗanda su ma kamar kullum bani da amsar su. Shin ita wannan baƙuwar Jaruma Wacece ita? Menene alaƙarta da sarauniya Diana? Kuma me yasa ta tausasa kalami a gare ni har ma ta kirani da ƊAN UWA? Lallai ina buƙatar sanin waɗannan amsoshi, ko da Yake ban san me yasa nake son sanin su ba, balle in san ta yaya zan same su. Ina can ina wannan zancen zuci, sai naji muryar Sarauniya Diana Yayinda ta ci gaba da magana tana mai cewa; 'Yake Ƴar Uwa, Na kasa ajiye maganganun ki a kowane bagire na ƙwaƙwalwa ta, domin duk inda na nufa da zancen, sai in ga bai dace da wajen ba, don haka zan so ki warware min zare da abawar kafin in yanke hukuncin da ya kamata'. Yayin da Sarauniya Diana tazo nan a zancen ta. Sai na ƙara shiga wata sabuwar damuwa, shin wane hukunci Sarauniya Diana take son yankewa? Kuma me yasa ta kira wannan baƙuwar da ƳAR UWA? ni dai a iya Sanina da ita, bata da wata ƴar uwa mace, hasali ma ita kaɗai Mahaifin ta ya haifa. Ko da nazo daidai nan a Tunanina, sai wata ƙaramar Muryar daga cikin kaina ta ce dani, 'amma kaima dai ka cika soko? Shin abubuwa nawa ne Diana ta faɗa maka waɗanda daga baya ka gano cewa ba gaskiya bane? Kuma abubuwa nawa ne bata gaya maka ba? Eh kuma fa Hakane, don haka sai na kauda wannan zance daga cikin raina. 

Wannan baƙuwar Jaruma sai ta ƙara yin ajiyar Zuciya a karo na biyu sannan tace; 'Bayanin Abu ne mai sauƙi, Ɗan Uwan Mu ne ya Dawo gida', ko da jin haka sai Sarauniya Diana ta ɗago kai cikin alamun mamaki ta dube ni sannan ta sake duban wannan baƙuwar Jaruma, kai da gani ka san cewa lissafi take yi a Ƙwaƙwalwarta. Bayan wani ɗan lokaci sai tace; 'Shin ko kina da dalilin da yasa kika ce hakan? 

Ko da jin wannan Tambaya sai wannan. Baƙuwar Jaruma Tace;


Zan Ci Gaba In Shaa Allaah

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring 


Share:

MA'AURATA ZASU IYA GANIN TSARAICIN JUNAN SU?

*_MA'AURATA ZASU IYA KALLON TSARAICIN JUNANSU?!_*


                         *Tambaya?*
Assalamu alaikum mallam menene matsayin kallon tsaraicin ma aurata?


                             *Amsa:*
Wa'alaykumussalam. Ya halatta ma'aurata su kalli tsaraicin junansu, Saboda Annabi S.A.W yana wanka da matansa, kamar yadda hadisai suka tabbata.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑 _*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.
Share:

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...