Skip to main content

Posts

Showing posts from March, 2019

ALLAAH YA SANYA TSAYAR DA ADALCI A BAYAN ƘASA...

Allah Ya Sanya Tsayar Da Adalci A Bayan Kasa Ya Zama Sharadin Samun Zaman Lafiya Da Cigaba Mai Dorewa!

Daga Imam Murtadha Gusau

Talata, 12 Mayu, 2019

Bismillahir Rahmanir Rahim

Lallai dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna yabon sa, muna neman taimakon sa, kuma muna neman gafararsa. Muna neman tsarin Allah da kariyarsa daga sharrin munanan ayyukkanmu. Duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, kuma duk wanda Allah ya batar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa lallai babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad, bawan sa ne kuma Manzon sa ne. 

Salati da sallamawa da tsira su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da matansa da duk wanda yayi imani da shi kuma yayi aikin kwarai har zuwa ranar tashin kiyama.

Bayan haka:

Ya ku bayin Allah! Ku sani, lallai Allah Ya umarce mu da tsayar da adalci a bayan kasa, kuma ya sanar da mu cewa, da adalci ne sama da kasa suka tsayu. Kuma shine ginshiki da tushen samun zaman …

ALLAAH GIVES POWER AND LEADERSHIP TO WHOM HE WILLS

ƳAN NIJERIYA KU DAWO HANKALIN KU

*'YAN NIGERIA KU DAWO HANKALINKU.*


Assalamu Alaikum Warahmatullah. 

Barkanmu da safiya, dafatan mun wayi gari lafiya. Allah Madaukakin Sarki Ya sada mu da dukkan alkhairan da ke cikin wannan rana. 

Da fari ina taya Shugaba Muhammad Buhari murnar sake samun nasarar lashe za6e na zama shugaban kasar Nigeria. Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi ikon yin adalci. 

Sai dai wani hanzari ba gudu ba 'Yan uwa! 

Kada mu ta6a tunanin cewa don Buhari ya hau matsalolinmu sun kare a Nigeria. Kada mu ta6a tunanin Buhari zai iya azurtawa ko ba da kariya ga jama'ar Nigeria. Kawo karshen matsalolin Nigeria ya dogara ne ga yawan addu'o'inmu da ibadunmu da rashin sa6a wa Allah. 

'Yan uwa kamar yadda muka yi ta addu'a kafin za6e har Allah Ya ba Shugaba Buhari nasara, to mu ci gaba da yi masa addu'ar Allah Ya sawwake masa dukkan al'amuran mulkinsa kuma Ya ba shi ikon tabbatar da mulkin adalci ga Al'ummar Nigeria. 

Mu ci gaba da yi masa addu'ar Allah Ya kare shi daga kaidin …

ANYA AKWAI MAZA A GIDAJEN KUWA?

*ANYA AKWAI MAZA A GIDAJEN KUWA*?

🧕🏻Yanzu mata suna fita waje, suna bayyana surorin jikinsu ga mutanen waje, ba tare da sun rufe jikkunansu yadda shari'ah tace ba.Wasunsu ma matan Aure ne.

🤔 Abin tambaya anan : Shin anya akwai Maza acikin gidajen da matan nan suke kuwa? Shin kodai mazajen gidan sunaso ne Allah ya haramta musu Aljannah sbd Sun Zama *Dayyus* (Mara Kishin iyalansa). 

*" Dukkaninku makiyaya ne, kuma dukkaninku sai abintambaya ne dangane da kiwon da Aka bashi. "* 

_Allah yasa mudace kuma yakara tsare mana imaninmu kuma yasa mucika da kyau da Imani._

✍🏻 *Idris M Rismawy*

ƘARYACE-ƘARYACEN WATAN RAJAB

KARYECE-KARYACEN WATAN RAJAB 
*_HADISAI MARAR SA INGANCI DA HADISAN KARYA GAME DA FALALAR WATAN RAJAB_*
HADISI NA FARKO 1-(Yin azumin yinin farko na watan Rajab,yana kankare laifukan shekara ukku,a yini na biyu kaffarar shekara biyu,a yini na ukku kaffarar shekara guda,sannan daga nan kowane yini yana kaffarar wata guda)Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba@ﺿﻌﻔﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺿﻌﻴﻒ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ - ﺭﻗﻢ : ‏( 3500 )

HADISI NA BIYU2-(Ya kasance idan ya shiga watan Rajab yana cewa; ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺑﺎﺭِﻙْ ﻟﻨﺎ ﻓﻲ ﺭﺟﺐٍ ﻭﺷﻌﺒﺎﻥَ ، ﻭﺑﻠِّﻐﻨﺎ ﺭﻣﻀﺎﻥ )Shime Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba daga Manzon Allah SAW ba.@ﺿﻌﻔﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺿﻌﻴﻒ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ – ﺭﻗﻢ :‏( 4395 ).

HADISI NA UKKU3-(An kira watan Rajab ne da suna Rajab saboda yana tattaro alkhairi mai yawa ga watan Sha’aban da Ramadhana)*Shime Wannan Hadisine mai rauni bai inganta ba daga Manzon Allah SAW ba*.@ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻣﻮﺿﻮﻉ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﻀﻌﻴﻔﺔ - ﺭﻗﻢ :‏( 3708 )
HADISI NA HUDU4-(Fifiko da falalar watan Rajab akan sauran watanni,kamar fifiko da falalar alqur’ani ne akan…

SIYASAR JAHAR KADUNA, ADDINI KO JAM'IYYA?

*SIYASAR JIHAR KADUNA ADDINI KO JAM'IYYA?*

Duk mutumin da ke bibiya da lura da abinda ke faruwa na harkar siyasa a jihar Kaduna baya bukatar k'arin bayani. Domin abin a fili yake kamar misalin hasken rana ce ta fito, baka bukatar ace maka ta fito. Kuma yana da kyau duk wani mai hankaki d'an jihar Kaduna ya fahimci cewa: siyasar jihar Kaduna ba jam'iyya ba ce Addini ce, saboda haka dole mu fito a matsayin mu na Musulmai musu kishin Addinin mu mu nuna kishinmu kuma mu zabi wanda zai kare mana Addinin mu da rayukan mu.

Kuma mu sa ni cewa zaben jihar Kaduna:

1) Zabe ne tsakanin Imani da Kafirci.

2) Zabe ne tsakanin Musulunci da Kafirci.

3) Zabe ne tsakanin Mumunai da Munafikai.

4)Zabe ne tsakanin masu kishin kasarsu da marasa kishinta.

5) Zabe ne tsakanin masu kaunar sahabbai da masu zaginsu.

6) Zabe ne tsakanin masu son fadan addini da masu kyamatar fadan addini.

7) Zabe ne tsakanin masu son zaman lafiya da masu son tashin hankali.

8) Zabe ne tsakanin masu son cigabar jihar Kaduna …

Today In History

On This Day March9

1776 – The Wealth of Nations by Scottish political economist Adam Smith (bust pictured) was first published, becoming the first modern work in the field of economics.

1862 – American Civil War: In the world's first battle between two ironclad warships, USS Monitor and CSS Virginia fought to a draw near the mouth of Hampton Roads in Virginia.

1932 – Éamon de Valera, one of the dominant political figures in 20th-century Ireland, became President of the Executive Council of the Irish Free State.

1944 – World War II: As part of the Battle of Narva, the Soviet Air Forces heavily bombed Tallinn, Estonia, killing up to 800 people, mostly civilians.

2010 – The first legal U.S. same-sex marriages south of the Mason–Dixon line took place in Washington, D.C.UKU-BALA'I 30

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA TALATIN.

💕💕 *_Kibiyar Ajali Taken Sone, Ya Mamayen da Gangawa, Yai Min Barin Makauniya_* 💕💕
       -- *Hamisu Breaker*

Tunda ta dago labulan dakin ta sanyo kai take dubanta da kallo kamar wacce taga bakuwar fuska, sosai ta lura da Mariya cikin yan kwanakin nan gabadaya ta sauya kamar ba ita ba sai sanyi jiki da rashin son magana ko aiki take yi haka take zama wata sukuku duk ta rame sai idanu da sukayi mata zuru-zuru ga tsayi da takuma yi sosai.
Gyaɗa kai Umma tayi kafun ta kau da kanta daga kallon da takeyi mata sosai ta fahimta sosai ta gane akwai abin da ke dawainiya da 'yarta wanda yake haifar mata da damuwa sosai a zuciya da ma jiki baki daya ba ta san mai Mariya take nufi da hakan ba ba ta san wacce irin rayuwa ta daukarwa kanta ba na zama cikin damuwa sosai ita kanta abin ke damunta a zuciyarta sai dai tana boyewa ne saboda ita Mariyar domin ba ta …

UKU-BALA'I 29

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ASHIRIN DA TARA.

Cikin wani irin yanayi ta kai wayar kunnan ta sai faman jan numfashi take yi daƙyar idanuwanta sun kada sunyi jajir kamar an watsa mata barkono zuciyarta take ji tana mikata cikin wani irin waje mai dauke da tashin hankali mai girman gaske komai take ji ya tsaya mata cak! ji take yi kamar motar ta ta tuntsiran da ita ta mace ko ta huta da wannan tashin hankalin da kunar da zuciyarta ke yi tana babbaka duk wani sashi na kirjin ta ruhinta take ji yana wani irin fizga mai haifar mata da wani matsanan cin ciwo a dukkan sassan jikinta.
Girgiza kai take yi tana jin yarda yake wani irin sarawa da duk tashin hankalin da take ciki komai take ji a wannan lokacin yana barazana da duk ragowar farincikin da yayi sauya a gareta na filin duniyarta.
Ba ta san abin da ya sa ta fito yau ba bata san mai alkalamin ƙaddararta yake kokarin rubuto mata ba sosai take…

UKU-BALA'I 28

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS.

A hankali ta turo kofar dakin ta shigo tafiya take yi cikin natsuwa da kuma yanga da ta zame mata jiki da wuya kaga Areefa na tafiya da sauri-sauri a,a sai dai ka ga tafiyar ta kamar mai koyo duk hakan na cikin salo da take amfani dashi cikin filin duniyar rayuwarta sanye take da doguwar Riga Gown wanda tayi matukar amsar jikinta sosai da sosai ta fiddo mata da asalin kyanta da kuma fatarta mai haske wanda tayi Fresh sosai da sosai hutu da jindadi sun taimaka kwarai wajan bayyana a jikin ta kanta ba kallabi sai dai ta tufke gashinta ta sanya rinbos mai kalar pink ta saki jelar gashin na reto a bayan ta fuskar nan fayau ba alamun ko digon tabo na kuraje.
Ba ta shafa komai ba natural fatarta kawai ce ke kyalli manyan idanuwanta masu haske sun kara taimakawa waja fiddo da kyan fuskarta hancinta dan madaidaici shi dai ba za a kira shi dogo ba sa…

UKU-BALA'I 27

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI.Mariya ta jima tsaye bakin get domin daidai kanta, sosai ta shiga tashin hankali komai taji yana kwance mata. tsayuwar ta a nan shine kawai take ganin mafita domin in har ta cigaba da tafiya zubewa zatayi warwas a kasa, domin kuwa kafafuwanta take ji suna harɗewa kamar an narka roba.
Numfashi take ja ta na saukewa kafun ta sanya hannu tana kwankwasa Get din a yan sakanni mai gadi ya iso sai da ya leko ta 'yar karamar kofar dake jiki ya ga wacece sannan ya zo ya buɗe karamar kofar yana bin Mariya da kallo fuskarsa da fara'a da alamun ya santa dama.
Gaidashi tayi kafun ta juyo ta dubi in da Huzaif yake abin mamaki tsaye ta hango shi ya harɗe hannayensa idanuwansa na in da take tsaye saurin dauke kai tayi tana mai cusa kanta cikin gidan bayan ta gaida baba maigadi.
Huzaif ganin ta shige cikin gidan hakan ya sanya shi dukan jikin …