Birnin Sahara 19

࿐​ *_​PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_* ࿐​

༄༄ *PWA* ༄༄࿐​❁✹✿​༄✺༄✿​✹❁࿐​
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
     *BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
࿐​❁✹✿​༄✺༄✿​✹❁࿐​         

____________________________________

   ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
         *ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Raees_* ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹

            (℘ᾰ❡ḙ 19)

Ba zan ɓoye muku ba, a wannan Lokaci gaba ɗaya kasa magana nayi. Can sai naji muryar Boka Nuna'u yana cewa: "Ƙarya kake ya kai wannan baƙo, baka isa kazo ka ce zaka gaje mana Sarautar birnin mu ba, har abada ba zan taɓa yi maka Mubaya'a ba!... Kafin ya gama wanna zance nashi sai na tare shi da cewa ;"to wa ya faɗa maka na zo nan ne domin in gaje muku sarauta? Kuma wa ya gaya maka ina buƙatar mubaya'ar ka?

Ko da Boka Nuna'u yaji waɗannan kalamai nawa sai yayi Kururuwa gami da Zunduma ashar yana cewa, 'Halaka ta tabbata a gare ka yakai Maƙiyin birnin mu, Dakaru, ku kamo min shi... Maimakon dakarun da ke cikin fadar su yo kaina su kama ni, ko ɗaya daga cikin su babu wanda ya nuna Alamun ma ya ji maganar sa balle ya motsa. Nan fa dariya ta ƙule ni nayi kamar in dara amma sai na kanne. Bayan haka, sai na nufi inda Sarauniya Diana take a durƙushe nace; "Please Diana get up, this is not right, you are a Queen. Ko da nazo nan a kalamai na, sai Sarauniya Diana ta ɗago daga durƙuson da tayi. A wannan lokaci Idanun ta sun cika da ƙwalla, amma kuma ga murmushi nan ya bayyana ƙarara a fuskar ta. Wai menene matsalar Diana ne? Na tambayi kaina, saboda Wannan abu ya Matuƙar ɗaure min kai. Sai dai Kafin in yi mata wannan tambayar, kawai sai ji nayi ta kama Hannuna ta ɗaga sama sannan ta ci gaba da cewa; "Ya ku jama'ar Birnin Sahara, ga yariman ku Haiman ina mai gabatar muku da shi! A gaban idon ku ya hau karagar mulki ba tare da wani abu ya same shi ba, kuma a Gabanku ya bayyana sunan shi da na Mahaifin Sa, lallai na yarda da sahihancin zancen sa don haka zan barshi yaje zuwa ga ahalin sa, idan har ya rayu to zai halarci zaman taron duk shekara wanda za'a yi a babban ɗakin gani nan da wata uku, duk wanda yake da tantama ko shakka dangane da wannan hukunci nawa, yana iya gabatar da ƙorafin sa Yayinda aka taru a bikin gani mai zuwa, na sallame ku!

Nasan cewa da yawan ku zaku iya tunanin, Dakyau! Wannan aiki yayi, ko kuma shikenan Haiman ya samu sarauta! Ina... Abinda ya fara fitowa daga bakina tambaya ce, me kike nufi da in na rayu? Na tambaye ta cikin alamun damuwa, "zaka gani da idon ka, ta bani amsa tare da sakin Hannuna. A wannan lokaci mutanen da suka halarci fadar sun fara Watsewa, dakarun da ke tsaron fadar ne kaɗai suka tsaya. Ba tare da jiran komai ba, sai Sarauniya Diana ta bada umurnin a kwance sadiya kuma a kawo ta inda nake.

Ko da Boka Nuna'u yazo fita daga cikin fadar, sai ya zo inda nake ya kalle ni ido cikin ido yace dani; "Ka sani cewa ya kai wannan baƙo, tabbas daga yau ka samu Maƙiyi mai suna Nuna'u, Maƙiyin da ba zai taɓa hutawa ba har sai ya ga bayan ka". Yayinda yazo nan a zancen sa, sai Sarauniya Diana ta buɗe baki da nufin ta bashi amsa amma sai na dakatar da ita, bata so hakan ba, amma babu yadda ta iya. Daga nan nima sai na fuskance shi ido cikin ido na mayar masa da amsa da cewa; "Ni kuma daga yau ka sa a ranka cewa ka samu Maƙiyin da a kullum zai ta buɗe maka Sabbin ƙofofin da zaku iya zama abokai, Maƙiyin da zai ci gaba da hana ka bacci amma kuma zai iya ceto rayuwar ka a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, Lallai zaka Gwammace mutuwa da yin gaba da ni!

Yayinda na zo nan a zance na, sai Boka Nuna'u ya turɓune fuska kamar an goyo biri a keke, sannan ya ɓace bat daga gaba na yana mai dalla min harara. "Amma dai ina fatar ba haka kake nufi har a cikin zuciyar ka ba ko? Sadiya ce tayi wannan tambaya cikin alamun damuwa. Gaba ɗaya tausayi take bani ma ni, ta jigata ƙwarai da gaske da ƙyar ma take iya tsayuwa bisa duga-dugan ta. Nayi murmushi a gare ta sannan nace mata, 'Kada ki damu'. Ina rufe baki sai ga sarkin yaƙi Dargazu yazo gaban mu, ya dubi Sarauniya Diana cikin fushi yace; 'Diana, wannan wane irin ɗanyen aiki ne haka kika shuka? Me kike nufi da ƙaddamar da wannan baƙo a matsayin yarima?... Kafin ya gama maganar sa, sai Sarauniya Diana ta tari Numfashin sa da cewa, "Kana iya yin duk waɗannan tambayoyi a ranar taron gani, Dargazu! Wannan amsa da ta bashi ba ita yaso ba, amma sai yayi shiru, can kuma sai yace 'koma dai menene kike Shiryawa, ki sani cewa ba zai Taɓa yin tasiri ba, da yardar kyanwa Shamawila. Daga nan kuma sai ya kalle ni, sannan ya ci gaba da cewa; 'Bar ganin ka bar ƴata da ranta, kada hakan yasa kayi tunanin gabar mu ta yanke kenan... Ƙaruwa ma tayi, ita kuma ƴata zata bayyana min yadda akayi har ɗan tatsitsin mutum kamar ka ya samu galaba akanta cikin sauƙi haka. Ko da ya gama rattabo zancen sa, sai nayi murmushi sannan nace masa; 'kada ka damu, nima haka na ɗauke ka, amma ƴar ka ta yi ƙoƙari domin Jaruma ce ta gaban kwatance, sai dai ta kasa samun abinda ya kamata ace ta samu, wannan shi ne matsalar ta. Dargazu ya yunƙura da nufin ya mazge ni, kawai sai gani muka yi wata katangar gilashi ta raba tsakani na da shi,ko da ya bugu da jikin Katangar, sai tayi mishi shokin, dole ya ja da baya, sannan yaja ƴar sa suka wuce.

Shi kuwa wannan mutumin na huɗu wanda bai duƙw min ba, Kallona kawai yayi ta yi har ya fita ba tare da ya ce min komai ba. Bayan fitar sa ne sai Sarauniya Diana ya Waigo gare ni tace da ni; "kayi haƙuri Haiman, wannan ba ita bace haɗuwar da nayi tsammanin zata faɗo mana a rayuwa, sai dai masu iya magana dama sun ce, ƙaddara ta riga fata, kayi haƙuri da duk wani irin ƙalubale da zaka fuskanta, ina tare da kai komai wuya komai rintsi. Waɗannan Kalamai na Sarauniya Diana sun sa Jikina yayi sanyi kuma na faɗa kogin tunanin Ma'anar maganar. Ban kai ga samo komai ba, sai naji tana cewa wannan baƙuwar Jarumar, "Ki Kula min dashi, kada ki bari ya mutu! Ita kuma sai tayi murmushi sannan tace;" zan yi iya ƙoƙarina, amma ki sani, Haiman fa ba ƙaramin ɗan Jarfa bane, da wuya yayi tsawon kwanaki uku ba tare da an sheƙe shi ba. Ko da tazo nan a zancen ta, sai Sarauniya Diana tayi mata godiya sannan ta ƙara baiwa Sadiya haƙuri, ganin haka yasa nace; "Hello, your Majesty, gani nan fa da raina, ya naji kuna ta maganar mutuwa ta ne? Sarauniya Diana tayi tattausan murmushi a gareni sannan tace;"ɗan uwa, nayi Matuƙar kewar ƙiriniyar ka, ka kula da kan ka. Daga nan bata sake cewa da mu komai ba sai kawai ta wuce ta bar mu tsaye.

Bayan tafiyar ta ne sai wannan baƙuwar Jaruma tayi mana Jagoranci izuwa ga wani ƙaton keken doki wanda wasu jibga-jibgan Raƙuma ke jan sa. (na zaɓi in kira shi da keken Raƙuma, ko ba haka ba?), inda muka shiga cikin sa mu uku, wato ni, Sadiya da kuma wannan baƙuwar Jaruma, wani bawa wanda yake gaban keken dokin ya ja akalar raƙuman muka fara tafiya zuwa inda Allaah kaɗai ya sani.

Mai karatu kafin in kaika da nisa, zan so a daidai wannan gaɓa in baka ɗan twƙaitaccen tarihi na, wataƙila hakan zai sa ka fahimci wasu al'amura dangane da ni a cikin wannan labari nawa, don haka, abin tambaya a nan shi ne, WANENE HAIMAN IBN HAMMADI?Zan Ci Gaba In Shaa Allaah.

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki
Share:

2 comments:

 1. Assalamu alaikum
  Barkanku da wannan lokaci mai albarka
  Ina bukatar abubuwanku da kuke wallafawa acikin wannan page a turumin a cikin email dina

  ReplyDelete
 2. OK in Shaa Allaah zamu bada damar yin hakan ta yadda zaku iya samu. Mun gode

  ReplyDelete

Popular Posts

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Recent Posts

Unordered List

 • Lorem ipsum dolor sit amet, consectetuer adipiscing elit.
 • Aliquam tincidunt mauris eu risus.
 • Vestibulum auctor dapibus neque.

Sample Text

Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipisicing elit, sed do eiusmod tempor incididunt ut labore et dolore magna aliqua.

Ut enim ad minim veniam, quis nostrud exercitation test link ullamco laboris nisi ut aliquip ex ea commodo consequat.

Pages

Theme Support

Need our help to upload or customize this blogger template? Contact me with details about the theme customization you need.