UKU-BALA'I 26

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
 
BABI NA ASHIRIN DA SHIDA.
Ta jima sosai cikin soron gidan nasu tana jan numfashi, yanayin da take jin kanta a ciki a wannan lokacin ba zata iya cewa ga yarda yake ba ta san dai tana cikin wani irin yanayi na rashin natsuwa gami da ciwon rai.
Bata san ya zata yi da Dr.Aqeel ba bata san mai ya kamata tayi masa ba zuciyarta take jin tana shiga wani irin mataki mai raunin gaske yana haifar mata da yanayi na shiga ruɗani sosai take jin wani fili a zuciyarta ya na baiwa Dr.Aqeel matsayi da kalamansa wanda take jin su sun fi komai daga mata hankalin a wannan rana.
Hannunta daya ta saka cikin baki tana cizawa kafun ta fiddo shi tana yarfewa fuskarta na ya mutsewa da wani irin yanayi mai girman gaske a gareta. Ta jima kafun ta fara jan kafafuwanta da take jin su kamar ba nata ba kamar ba jikinta suke ba sosai take jin gajiya a cikin su ji take yi kamar za su watsar da ita kasa a hankali ta kai hannunta ta dafa bango tana tafiya a hankali har ta karasa shigewa cikin gidan.
"Na ce karuwanci kike koyawa 'yarki tana bin gardawa kamar wata karya kin ce ba haka ba yanzu me ne ne wannan Iyee nace yanzu menene wannan ai duk wanda ya ga wadannan kayan ya san da walakin goro a miya ba yarda za ayi a dauki wannan uba uban kayan a baku su haka zikau ba tare da kuma an ci ribar ku ba".
Maganganun da suka shiga dukan kunnuwan Mariya kenan a daidai lokacin da ta iso tsakar gidan ta tsinkayo muryar Goggo Marka cikin dakin su wani tashin hankali ne taji zuciyarta da kwanyarta sun dauka lokaci guda sun tsaya cak! da aikin da sukeyi lokaci guda duk wani magudanan jinin ta suka tsaya komai nata take jin sa ya sauya ji take yi kamar ba a duniyar nan take ba ji take yi kamar ba RAI DA RUHI a gangar jikinta juwa taji ta fara daukarta lokaci guda ta durkushe a wajan cikin wani yanayi tana mai jan numfashi da k'yar yana fizgar kansa shi kuka take so tayi amma zuciyarta da idanuwanta sun ki bata damar haka sai zafi da raɗaɗi da take jin sunayi kamar zasu tayar da kan su daga gareta.
Hannayenta ta saka a saman kirjinta tana shafawa domin ji take kamar ya tarwatse gabadaya idanuwanta a runtse a hankali ta fara kokarin tashi tana jin yarda kirjin nata yayi mata wani irin nauyi da abu mai girman gaske wanda take jin yana rinjayarta.
"Kin ce 'yar ki makaranta take yi ita ga wacce ta fi kowa son ilmi ko yanzu tsakanin ki da Allah Habeeba wannan shine makarantar da take zuwa don na tabbata a hanyar fitar da take yi ne ta hadu da wanda yayi mata wannan hidimar kuma na tabbata ba haka kawai bane sai da ta biyasa kafun ya bayar".
'Yaa zuljalalu wal'Ikram Ya Hayyu Yaa Kayyum'.
Abin da take jin wani sashi na zuciyarta na fadi kenan har ta iso bakin kofar ta tokare hannayenta a saman goshinta ji take yi kanta kamar zai tarwatse idanuwanta a runtse ta shiga ajje numfashi mai girma gaske wani abu taji ya zo mata makoshi ya tsaya tana jin yarda yake kartar mata ko ina na kirjinta har zuwa makoshi.
"Haba mana Goggo Marka ta ya kike tunanin zan jefa 'yar da na haifa a cikina cikin wannan mugun yanayi ribar mai zan samu a ciki".
Muryar Umma ta tsinkayo ta fadin haka muryarta cikin yanayi mai kama da kuka da sauri ta dago kanta ta ware idanunta kafun ta dage labulan dakin tsaye ta hango Goggo Marka sai faman tsaki take ja tana jifan Umma da mugun kallo jin motsi ne ya sanyata juyowa ganin Mariya ya sanya ta sakin wani murmushi na mugun kafun ta shiga tafa hannayenta.
"Uhmm a hakan kamar gaske musa a baki fir'auna a zuci".
Ta fadi tana yatsine fuska kafun ta dan rangwafa inda kayan suke tana bincike kafun ta shiga ware wasu a gefe guda sai da ta ware masu isarta sannan ta sunguma tana duban su Umma.
"To mu ma dai bari mu ci albarkar kacin bariki ko kin san ko ina kayan alheri suke dadi gare su Allah ya karo mana irin su masu kyautatawa".
Ta na gama fadin haka tayi hanyar yo wa waje Mariya da tayi sumar tsaye bangazar da taji anyi mata ya dawo da ita hayyacinta a rikice ta dubi Goggo Marka sannan ta dubi Umma wacce ta zabga tagumi hawaye sai shatata suke yi a fuskarta bakin ciki da takaicin duniya duk sun cike mata zuciya gabadaya ta hargitse sosai fuskarta ta ke nuni da tsananin tashin hankalin da take ciki ganin Mariya na dubanta ya sanyata saurin dauke hawayen da suke zubo mata tana sakin wani yake wanda yafi kuka ciwo.
Wani irin kuka ne Mariya taji yana zo mata a daidai wannan lokacin hannu ta saka ta toshe bakinta tana karasawa cikin dakin durkushewa tayi gaban Umma da wani irin yanayi na tashin hankali mai girman gaske laɓɓanta na rawa ta shiga motsa su.
"Na Shiga Uku wanna wacce irin rayuwa ce take kokarin tunkaromu a daidai wannan lokacin wannan wani irin yanayi ne mai sanya ciwon rai ya sanyo mu gaba".
Hannu Umma ta daga mata alamun tayi shiru kafun ta fara magana cikin yanayi na rauni.
"Ni ban ga abin shiga uku ba don haka ki daina ambatar mana Uku a nan kin ji ko kina dai bata hawayenki ki share su domin in har kika ce zaki cigaba da zubda su to na tabbata zaki shekara dubu a haka in dai kina cikin wannan rayuwar duniyar nan".
Fakare tayi da kunnuwa ta zubawa Umma idanu kamar wacce taga bakuwar fuska kafun ta shiga jan hanci kamar zata fizgeshi daga fuskanta.
"Haka nake nufi domin kuwa in har kace ba zaka dauki abin da ALKALAMIN ƘADDARA ya kawo maka rayuwa ba to kana tare da tashin hankali mai girman gaske".
Hawaye suka sake balle mata domin ji tayi komai ya kwance mata zuciyarta na wani irin zugi da raɗaɗi.
"Amma Umma..".
"Haba mana Mariya".
Tayi sauri katseta kafun ta ja numfashi da take jin sa da wani irin yanayi mai zafi gaske.
"Ina kika baro shi".
Runtse idanu tayi jin zuciya ta bugu kafun ta ciza laɓɓanta tana jin wani abu mai nauyin gaske na danne mata kirji da zuciya.
"Ba shi bane".
Ta fadi a raunane kamar zata fashe da wani sabon kukan wanda ya fi wanda ta gama ciwo.
Ware idanu Umma tayi cike da mamaki jin abin da Mariya tace.
"Kamar ya bashi bane to waye?".
Kamar ba zata ansa ta ba sai kuma tana ja numfashi ta fesar.
"Dr.Aqeel ne".
Duban sosai Umma ta shiga yi mata kamar mai son karin bayani akan abin da ta fadi yanayin da ta nuna ya tabbatar mata akwai abin da yake faruwa ganin sai yatsi ne fuska take yi tana cizon laɓɓa.
"Me ke faruwa na ga sai dakune fuska ki ke yi?".
"Bakomai yace yana gaishe ki".
"Mariya!".
Umma tafadi cikin wata irin murya mai zurfi har sai da gaban Mariya ya yanke ya fadi dago idanuwanta tayi da suke kasa ta dubi Umma da tayi mata kuri da Idanu da tuhuma cikinsu.
"Akwai abinda ke damun ki bayan Dr.Karami ki fada min ina bukatar sanin ko mene ne na gaji da wannan halin da kika aro ki ka saka a filin rayuwarki wanda sam! ban ga amfaninsa ba".
Gyaɗa kai ta shiga yi kamar zata rushe da kuka zuciyarta da kwakwalwarta take jin su kamar za su kama da wuta saboda wani irin tashin hankali mai dauke da turiri take ji yana wanzuwa acikinsu.
"da ke nake magana Mariya na gaji fa".
"Umma!".
Ta fadi cikin wani irin yanayi da rauri a muryarta kafun ta nisa ta na cizon laɓɓanta.
"ba abin da yake damu na...".
"ban yarda ba...shikenan ma komai ya shige ki bar komai a zuciyar ki hakan daidai ne".
Umma ta fadi tana mai kokarin mikewa kayan dake tsakar dakin ta shiga janyewa tana ajewa gefe guda ganin haka da Mariya tayi ta san Umma haushin taji shiyasa ta rabu da ita da sauri ta mike tana kokarin taya Umma kwashe kayan hannu ta daga mata ba tare da ta kalle ta ba.
"Bar shi kawai ki zauna ki yi tunanin abin da ya dace ki fidda kan ki daga damuwar da kike ciki tun da bakya bukatar abokin shawara a filin a rayuwarki".
Jikin ta lokaci guda yayi sanyi jin abin da Umma tace hannu ta sa tana goge kwallar da taji sun kawo mata ziyara idanuwa.
"Kiyi hakuri Umma..".
"ni ba kiyi mani komai ba Mariya ki je ki zauna ki huta ni na bukaci haka".
Ba yarda ta iya domin yarda ta ga Umma na maganar ta san har kasar zuciyarta don haka a hankali ta ja jiki ta zauna in da Mu'azzam ke kwance yana faman barci abun sa.
Bata san mai ya dace tayi ba, ba ta san mai ya kamata ace tayi a filin duniyar rayuwarta a yanzu ba komai take ji yana sauya wa komai take ji yana canzawa a filin rayuwarta ji take yi kamar ba ita ba jikinta take ji yana yi mata wani iri kamar wacce bata da lafiya zuciyarta take ji tana yi mata nauyi kamar wacce aka daura dutsen dala.
Ta jima cikin wannan yanayin kafun ta lura da har Umma ta gama kwashe kayan ta bar mata daki hannu bibbiyu ta daura a fuskarta ta zabga tagumi domin kuwa gabadaya take jin tunanin ta ya tsaya komai na ta ya tsaya cak! ba abin da take hangowa sai tashin hankalin dake gabanta yanzu bata san ina Dr.Karami yake ba a yanzu tsoron ta daya kar ya sake komawa ba tare da sun hadu da juna ba.
*******
"Umma Zan je gidan su Baseera".
Mariya ta fadi cikin yanayi na fargaban abin da Umma zata ce domin tun jiya da ta shareta har yau bata sake tsayawa sun yi wata magana mai tsayi ba bayan gaisuwa da tayi mata da safe.
"Allah ya kiyaye hanya ki gaida Hajiyar ta Baseera".
Abin da ta fadi kenan ba tare da ta dube ta ba hakan ya sanyayata jikin Mariya ta shiga gyaɗa kai da susar gefen fuskarta kafun ta shiga motsa baki.
"Umma don Allah kiyi hakuri...".
"Mariya haba mana nace miki bakomai ki tafi kawai".
Jin abin da tace ya sanya ta duban Mu'azzam dake hannun Umma hannunta kai ta shafi fuskarsa tana sakar masa murmushi kafun taja jiki ta fice daga cikin dakin.
A tsakar gida ta tsaya tana gyara hijabin dake jikinta domin ji take yi kamar bai zauna daidai ba a hankalinta juya ta dubi bangaren su Goggo Marka Hafsi ta hango tsaye daga ita sai daurin kirji kamar wata uwar mata ta kafe ta da idanu tana faman yatsine fuska kau da kai tayi kamar bata ganta ba da sauri ta zira takalmanta ta fice daga cikin gidan domin a yarda take jin kanta ba ta bukatar wata magana ta sake shiga tsakanin ta da wani har ta isa gidan su Baseera.
Tafiya take yi a hankali domin isa bakin layi ko za ta samu napep din da zai kai ta Unguwarsu Baseera taji take yi zuciyarta da kwanyarta sai faman dauko mata tunani suke yi wanda sam bata so ace sune a kanta ba yanzu.
Kamar daga sama taji ana yi mata Horn bata yi tunanin da ita ake ba hakan ya sanyata kara sauri tana komawa gefe duk a tunanin ta wani ne a bayan ta yake mata horn domin ta bashi hanya amma ina ta ji an ci gaba da yi ba kankautawa hakan ya sanyata tsaya wa cak! waje daya tana daga kanta don dubin ganin abin da ke faruwa motar Huzaif ta hango yayi parking yana kokarin fitowa wata irin faduwar gaba taji tana zo mata lokaci guda wanda ita a karan kanta ba zata ce ga dalili.
Dubansa ta shiga yi cikin wani irin yanayi wanda ba za ta ce gashi ba amma dai tana jin yarda zuciyarta ke bugawa a dukkanin sakan idanuwanta take yawatawa a kasa tana tunano yaushe rabon ta dashi sun kwana biyu ba su hadu ba sosai ta lura da yanayinsa kamar mara lafiya domin tafiyar ma kamar mai koyanta haka yake yin ta har ya iso in da take tsaye tana faman jan numfashi.
Lokaci guda idanuwansu suka sarƙe da juna aka rasa mai dauke nasa tsayin lokaci suna a haka kafun Mariya ta ja dogon numfashi ta fesar fuskar ta cikin yanayi na karan kadahan.
"Uhmm Huzaif dama kana duniyar nan".
Hakan da ta fadi da yanayin da tayi maganar ba karamin sanya Huzaif cikin wani irin yanayi mai armashi a hankali ya shiga motsa laɓɓansa fuskarsa na wanzar da wani farinciki mai dauke da fara'a jan numfashi yake yi yana fesar wa idanunsa akan Mariya zuciyarsa yake ji tana daukar kanta tana kaiwa wani mataki mai girman gaske yanayin da yake kallon Mariya wani farin ciki da muradan jindadi yake jin sa a ciki.
Ya sani yayi kewar Mariya ba kadan ba zuciyarsa tayi jinyar rashin ta sosai ya shiga cikin wani hali na rashin jindadi sosai duniyar yake jin ta wani mataki a kwanakin baya da yake zaune yana jinyar kan sa dalilin rashin lafiyar da ta same shi.
" Baki damu dani ba Mariya shiyasa sam rashi na bai d'ad'a ki da kasa ba".
Ya fadi yana mai dan haɗe rai kanta ta dago ta dube shi tana mai yatsine fuska kafun ta ja numfashi.
"akan mi zaka ce haka wa na sani na ka da zan tambaya ina kake so naje ko so kake yi na bi layi ina cigiyar ka Huzaif bai dace ka yi mani wannan maganar ba sam".
Kuri yayi mata da idanu yana kallon yarda take motsa laɓɓanta kalamai na fitowa wani irin farin ciki yake ji yana sake zundumawa a ciki.
"Allah ya baki hakuri amma dai zaman tare ai bai ce haka ba ko?".
Ya fadi yana murmushi kau da kai tayi tana mai yatsine fuska sam bata bukatar magana ba ta so ace ta sake gamuwa da wani a daidai wannan lokacin ba tafi bukatar su hadu da Baseera domin ita kadai ne take so su zauna domin sanin abin da ya dace ita kadai take tunanin zata fada wa abin da yake kokarin faruwa da ita ko ma tace ya faru da ita...
"Ina su Umma da Mu'azzam?".
Maganar Huzaif ta katse mata tunanin da ta jefa kanta a ciki.
"Uhmm suna gida suna lafiya".
Ta fadi tana kokarin raɓashi ta wuce ganin haka ya sanya shi saurin dubanta.
"Meye haka kuma Mariya yake kike kokarin tafiya...wai ma ina zaki kike wannan saurin".
Yanayin da yayi maganar kamar da bacin rai a ciki ita hakan ita ma ya so bata mata rai jin irin tambayar da yake yi mata kamar shi ne ya ajje ta ba ta ansa shi ba illa duban sa da tayi ta kau da kanta.
"Ina Zaki je ne?".
Ya fadi ganin kamar ranta ya so baci yayi kasa da muryar.
"Unguwa zani shiyasa nake sauri bana so na bata lokaci a bakin titi".
Gyaɗa kai yayi yana dubanta kafun ya numfasa cikin d'ard'dar.
"muje mana in kai ki ko".
Wani duba tayi masa wanda sai da yaji yan cikin sa sun motsa dama ya san za ayi haka da sauri ya kau da kai don ba zai iya jure irin kallon da take masa ba zuciyarsa wani irin yanayi take fadawa mai girman gaske.
"Don Allah mana".
Ya sake fadi yana mai hada hannayensa waje daya alamun roko.
Girgiza kai tashiga yi tana mai taku a hankali za ta bar wajan gabanta yasha yana mai harɗe hannayensa a kirjinsa idanuwansa ana ta tana watsa masa kallon ban son haka.
"Mariya wai shin ko laifi na sake yi ne ake kokarin hukunta ni ta wannan hanyar?".
"ko daya kawai dai bana ra'ayin abin da ka zo mani dashi ne nagode kawai kayi tafiyarka".
Ware idanu yayi jin abin da tace sosai yake dubanta yana kallon yadda ta kara haɗe fuska kamar hadari amma hakan bai hana kyanta ƙara bayyana ba wani irin kwarjini yake ganin tana yi masa wanda ya shagalar dashi ga kallon ta har bai san lokacin da ta raɓashi ta wuce ba.
Firgigin yayi ya dawo hayyacin sa ganin bata wajan ya yi saurin juyawa can ya hange ta tayi nisa dashi kadan.'Yaa Rabbi'.
Ya ambata yana takunsa cikin hanzari ya isa in da motasa take ya shige tare da yi mata key bayan yayi ribas ya bi bayan ta da gudu cikin yan sakanni ya isa in da take tsaye tana kokarin tsaida wani mai Napep parking yayi ya fito ya iso in da take tsaye suna magana da mai Napep din ba tare da yace mata komai ba yace dubi mai Napep din.
"Yi hakuri don Allah yi tafiyarka".
Ya fadi yana mai hade fuska da sauri Mariya ta juyo ta dubeshi da wani irin kallo ganin yarda ya hade fuska ita ma sai ta hade.
"Ya haka ya za ayi in tsaida abun hawa ka ce ya tafi ina ruwan ka dashi?".
Bai tanka mata ba illa nuni da yayi mata da motarsa alamun ta je ta shiga.
"Ba zan shiga ba kaji ko Allah ba in da zani Huzaif bana bukatar takurawa bana son abin da zai bata mutuncin junanmu".
"kawai Malama ki je ki shiga mu tafi ya za ayi ace ina waje kuma ga abin hawa a tare dani amma ki tare wani mai Napep wannan ai ba mutuncin ki bake".
'Ikon Allah'.
Ta fadi a ranta ta na sakin guntun murmushi kafun ta dubi Huzaif da ya haɗe rai kamar wani hadarin dake shirin zubda ruwa.
"wai don Allah Huzaif me yasa kake son takura mani ne na ce maka nagode ba zan shiga motarka ba to ka hakura mana".
"Ban san wannan zancen ba kisan Allah in har baki shiga mun je ba sai dai mu kwana a nan in zaki tsaida Napep dari sai na kore su".
Ware idanu tayi cikin yanayi na mamaki na karfi halin Huzaif ita abin ma dariya ya so ya bata.
Bata ga dalilin da zai sanya shi takura mata ba akan sai tayi abin da yake so shi ba mijinta ba shi ba ubanta ba amma ya kafe da bata Umarni.
Duban sa tayi ganin ya harɗe hannayenda ya jingina da gaban motarsa sai faman kaɗa kafa yake yi fuska a tamke ba alamun wasa kuma ta lura da gaske yake yi din sai dai su kwana a nan.
Wani tunani ne ya fado mata da sauri ta dube shi cikin mika wuya domin ta tabbata maganarsa da ya fadi tsaf zai aikata ita kuwa ta tsani tsayawa bakin titi ba ma wannan ba lokaci tafiya yake yi kuma in har ta jima bata koma gida ba dole ta fuskanci fushi a wajan Umma da ma ya ya ta barota balle kuma yanzu ta kara wani laifin ai sai abin yayi yawa shege da hauka.
Tsuke fuska tayi kamar hadari ita ma sannan ta isa wajansa tana mai kau da kai tana turo baki gaba hakan ba karamar dariya ya baiwa Huzaif ba amma sai ya kanne domin ya san in har yayi dariya zainl iya bata shirin nasa a hankali ya dube ta cikin danne dariyar da take kawo masa hari.
"To ya yan mata muje ne ko kuma mu cigaba da zama a nan har mahadi ya bayyana?".
wata harara ta watsa masa bai san lokacin da ya saki dariya ba har da buga kafa ya isa ya bude mata gidan gama yayi mata alamun ta zo ta shiga.
Ware idanu tayi kafun ta kau da kai.
"nikam ba zan shiga gaba ba baya zan shiga".
Dubanta yayi ganin da gaske take ba za tashiga ba cikin yanayi na zolaya ya dube ta.
"Kuturu mana..."
"A'uzubillahi minal shaidanir rajim zagi Huzaif".
Ta fadi tana ware idanunwanta akansa shima zaro idanu yayi yana faman gyada kai.
"Uhm Uhm fa kar ki fassara ni Malama ni ba zagi zan yi ba".
Harara ta wurga masa kafun ta isa wajan motar ta buɗe gidan baya ta shige.
Dariya yake yi mata ganin yanayin da ta nuna kamar zai hana ta shiga.
Shiga yayi shima ya na fadin.
"wato kin mai dani direban ki ko?".
Ko kallon sa ba tayi ba kanta na bakin kofar tana kallon waje har yayi wa motar key kafun ya tambaya ne ta in da sukayi
"Pabeyi".
Yanayin da ta fadi sunan Unguwar tana turo baki gaba sai ya bashi dariya ita ala dole fushi take yi dashi da gasken gaske.
Tafiya sukayi ta tsayin mintuna biyu ba wanda ya yi magana a tsakanin su ba abin da ke tashi cikin motar sai wakar 'Because of You' ta Amanda Mena sosai wakar ta tafi da hankalin Mariya don sosai taji muryar mawakiyar da yarda take sarrafa kalaman ta sun burgeta lokaci guda taji kaunar mawakiyar ya dalsu a zuciyarta ji take yi kamar ta tambayi Huzaif wace ce ita amma ba za ta iya wannan ganganci ba yanzu ji take yi kamar tana zaune akan k'aya.
"Mariya"
Kamar daga sama taji muryar Huzaif ya furta hakan gabanta taji ya yanke ya fadi ta madubin gaban motar ta hango irin kallon da yake yi mata ba tare da sani ba ba ta ansa shi ba illa idanu da suka hada da sauri ta dauke kanta tana jin gabanta na cigaba da bugawa.
"me yasa wai har yanzu baki yarda dani bane na lura mafi akasari in muna tare bakya sakin jikin dani kamar zan cutar dake".
Gyada kai tayi ba tare da tayi masa magana ba lokaci guda ta shashantar da maganar ma ta na nuna masa hanyar da za ta kai su layin su Baseera.
"Ya kamata ki bani hankalin ki nan magana nake so muyi ta fahimtar juna a tsakanina da ke".
Da sauri ta dubeshi jin abin da yace gabanta lokaci guda ya yanke ya fadi ba wanda ta tuna a wannan lokacin sai Dr.Aqeel da yanayin da suka kasance a tsakanin ta dashi a jiya maganganun sa ne suka shiga dawo mata kamar yanzu suka yi su gabanta ya cigaba da tsanar ta faduwa zuciyarta na dauko mata wani lamari mai girman gaske wanda yake kara sanyaya mata jiki numfashi ta shiga ja a hankali kafun ta sake daga kai ta dubeshi har zuwa lokacin idanuwansa na kanta wani abu mai girman gaske take hangowa a idanuwansa wanda suke ruɗa mata nata idanun da sauri ta dauke kai jin da tayi numfashin ta na fizga kamar zai fice daga gangar jikin ta lokaci guda ta ji nadama ta saukar mata ba ta san abin da yasa ta tsaya da Huzaif ba ta san abin da ya kai ta shiga motarsa ba har yake kokarin firgita ta.
"ba zan boye miki ba Mariya ina cikin wani irin hali mai wuyar fassaruwa ban san ta ya ya zan fada miki halin da nake ciki ba zuciyata tana cikin wani hali mai girman gaske Mariya komai na faruwa ne a dalilinki".
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".
Abin da taji bakin ta na fadi kenan daga nan bata san wata duniyar kuma ta fada ba sai da ta shafe sakanni kafun ta dawo hayyacin ta dauke da tashin hankali sosai taji ana hajijiya da ita ji take yi kamar tana saman gajimare ana yawo da ita kwanyarta taji ta tsaya cak! da aiki zuciyarta na wani irin bugu kamar zata faso kirji ta fito a hankali ta dago kanta tana duban kofar motar Huzaif ganin sun shiga layin su Baseera ta fara kokarin tsaida shi domin ya sauke ta a yanayin da take jin kanta ko sakan bata fata ta sake yi a cikin wannan motar domin kuwa ji take yi kamar an daura ta a kan KASKON WUTA.
Idanuwanta ne sauka sauka kan wata dalleliyar mota sabuwa fil sai kyalli take yi haska rana na kara haskata hannu ta sa ta rufe idanuwanta domin sosai motar ta haske mata fuska da kyallin haka kawai taji gabanta ya fadi sannan kuma tana son kallon motar ware idanu tayi har motar ta karasa fitowa daga get din gidan su Baseera tana kokarin barin layin sosai take kallon motar har ta iso daidai in da suke shi kansa Huzaif hankalinsa ya tafi wajan motar sosai.
"Yaa Allah".
Mariya ta furta da wani irin yanayi domin bugun da taji gabanta yayi sosai glass din motar a dage yake kuma gashi mai duhu ba ka gano wanda yake cikin motar hakan ya dan bata ran Mariya duk da tashin hankalin da take ciki ta so ace ta ga waye a cikin motar domin zuciyarta sosai ta kwadaitu da son ganin ko waye.
"ajje ni a nan".
Mariya ta fadi tana mai dafe kanta da sauri ya dawo da hankalinsa gareta ya dubanta ganin hankalinta bai gareshi hakan ya bashi damar sake kare mata kallo kafun yace.
"Ina son magana dake Mariya ki bani lokaci ko ya ya ne".
"Please don Allah Huzaif ka barni da naji da abin da yake damu na bani da lokacin da zan iya zama naji abin da zaka fadi don Allah ka kyale ni".
Ta karashe tana kokarin buɗe motar ta fice.
"Mariya!".
Cak! ta tsaya ba tare da ta karasa ficewa ba a hankali ta juya ta dubeshi ganin yanayin da yake ba karamin faduwa gaba taji ba da sauri ta fice daga cikin motar har tana kokarin faduwa ko tsayawa dubansa bata yi ba ta doshi gidan su Baseera cikin yanayi na rashin hayyaci sai faman hada hanya take yi kamar wacce ta sha kaya maye...
  
 *_KAMALA MINNA_*😍😍😍

Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...