Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

MANYAN HANYOYI GUDA GOMA NA NEMAN ARZIKI

MANYAN HANYOYI GUDA GOMA-(10) NA SAMUN ARZIKI

Arziqi yana da manyan hanyoyin samunsa guda biyu sune;
*A-Hanyar samun Arziqi na Al'ada Wanda ya hada noma da kiyo da kasuwanci da kwadago*.

*B-Hanyar samun arziqi na shari'a,sune wadan nan hanyoyi guda goma,wadanda suka tabbata daga Alqurani da Hadisan Manzon AllahSAW ingantattu*

Dukkan Wanda yake neman Arziqi to wajibine ya bi daya ko wasu daga cikin wadan nan hanyoyi tare da doguwa ga Allah,sannan ya kuma yarda da abinda Allah ya bashi na kason arziqinsa.

Daga Cikin ayoyin da suke bayani a akan arziqi da hanyar samun sun hada da;-

ﻳﻘﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ;(ﻭَﻓِﻲ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ
ﺭِﺯْﻗُﻜُﻢْ ﻭَﻣَﺎ ﺗُﻮﻋَﺪُﻭﻥَ‏) .
*(Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari)*.
@ﺳﻮﺭﺓ:ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ.

ﻭﻳﻘﻮﻝﺗﻌﺎﻟﻰ (ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻫُﻮَ ﺍﻟﺮَّﺯَّﺍﻕُ ﺫُﻭ ﺍﻟْﻘُﻮَّﺓِ ﺍﻟْﻤَﺘِﻴﻦُ ‏) .
*(Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi)*.
@ﺳﻮﺭﺓ : ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ

ﻭﻳﻘﻮﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ ‏(ﻫُﻮَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺟَﻌَﻞَ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﺫَﻟُﻮﻟًﺎ ﻓَﺎﻣْﺸُﻮﺍ ﻓِﻲ ﻣَﻨَﺎﻛِﺒِﻬَﺎ ﻭَﻛُﻠُﻮﺍ ﻣِﻦ ﺭِّﺯْﻗِﻪِ ۖ ﻭَﺇِﻟَﻴْﻪِ ﺍﻟﻨُّﺸُﻮﺭُ).
*(Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya,sai ku tafi cikin sãsanninta,kuma ku ci daga arzikinSa,kuma zuwa gare shi ne tãshin yake)*
@ﺳﻮﺭﺓ : ﺍﻟﻤﻠﻚ .

HANYOYIN ARZIQI NA SHARI'A

1-HANYA TA FARKO
*Yawaita Istighfari*
Kaicon ga Wanda yake neman arziqi amma ya manta da hanya mafi sauki ta samun arziqi a wajen Allah,wato yawaita *ISTIGHFARI*.

ALLAH YANA CEWA
‏(ﻓَﻘُﻠْﺖُ ﺍﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻭﺍ ﺭَﺑَّﻜُﻢْ ﺇِﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﻏَﻔَّﺎﺭًﺍ
‏( 10 ‏) ﻳُﺮْﺳِﻞِ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀَ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﻣِﺪْﺭَﺍﺭًﺍ( 11 ‏) ﻭَﻳُﻤْﺪِﺩْﻛُﻢْ ﺑِﺄَﻣْﻮَﺍﻝٍ ﻭَﺑَﻨِﻴﻦَ ﻭَﻳَﺠْﻌَﻞْ ﻟَﻜُﻢْ ﺟَﻨَّﺎﺕٍ ﻭَﻳَﺠْﻌَﻞْ ﻟَﻜُﻢْ ﺃَﻧْﻬَﺎﺭًﺍ ‏) .
*(Shi na ce,'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku,lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne.""Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga.""Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna)*.
@ﺳﻮﺭﺓ ﻧﻮﺡ ‏]

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Dukkan Wanda ya lazumci yawaita ISTIGHFARI,to Allah zai Sanya masa mafita a duk lokacin da yake cikin qunci,kuma ya kawo masa farin ciki a duk lokacin da yake cikin damuwa,kuma ya azurta shi daga Inda baya tsammani)*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ.

2-HANYA TA BIYU
*Taqwa,wato jin tsoran Allah da kiyaye dokokin Allah,ta hanyar barin abinda yayi hani da aikata abinda yayi umarni*

Allah yana cewa
(وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِبُ ۚ وَمَن يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ بَالِغُ أَمْرِهِ ۚ قَدْ جَعَلَ اللَّهُ لِكُلِّ شَيْءٍ قَدْرًا )
*(Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato.Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma'ishinsa. Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne.Haƙĩƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kõme)*
@ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻄﻼﻕ ‏

Kuma Allah yana cewa:
‏(ﻭَﻟَﻮْ ﺃَﻥَّ ﺃَﻫْﻞَ ﺍﻟْﻘُﺮَﻯٰ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﻭَﺍﺗَّﻘَﻮْﺍ ﻟَﻔَﺘَﺤْﻨَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢ ﺑَﺮَﻛَﺎﺕٍ ﻣِّﻦَ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْض‏) .
@ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻷﻋﺮﺍﻑ
Jin tsoron Allah hanya CE ta samun arzikin duniya dana lahira,jin tsoran Allah shine mabudin dukkan alkhairi,yawan sabon Allah itace makullin alkhairi kuma mabudin dukkan sharri.

3-HANYA TA UKKU
*Dogaro ga Allah da sallamawa Allah ta hanyar yarda da samu da rashi daga Allah yake,tare da bin hanyoyin da Allah ya sanya na cin nasara da samun arziki sai kuma zuciyarka ta sallama tare da amincewa da yardar akan Allah kadai yake Qaddara samu ko rashi*.

Allah yana cewa;
‏(وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِبُ ۚ وَمَن يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ بَالِغُ أَمْرِهِ ۚ قَدْ جَعَلَ اللَّهُ لِكُلِّ شَيْءٍ قَدْرًا )
*(Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to,Allah ne Ma'ishinsa.Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kõme)*
@ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻄﻼﻕ ‏

Manzon Allah ﷺ yana cewa:
*(Da dai zaku yi dogaro da Allah matuqar dogaro,da Allah ya azurta Ku kamar yadda yake azurta tsuntsu,zai wayi gari cikinsa babu komai,amma yayi yammaci cikinsa a cike)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ


        Allah ne mafi sani


Mu hadu A darasi na gaba insha Allah.
Share:

MIJIN BAHAUSHIYA

➡MIJIN BAHAUSHIYA

KAFIN AURE

Na kiraki dazu da sassafe ba'a dauka a l0kacin nasan baki tashi ba na katse miki barci S00RY

murya KASA KASA jiya na miki tambaya amma baki amsamin tambayata ba, ina jira SWEETY

Ranki ya dade wanka kikayi yanzu da sanyinnan koda yake kedin ai yar gayu ce BABYNAH

DA ALLAH kada kici wake da shinkafa yanzu bari na aik0 miki KAZA da MaltinA kinji H0NEY

Ah Ah haba dan ALLAH my LADY tah0 a hankali mana kada kiji ciw0 ki sani a tara mana my S0UL

BAYAN AURE

kina da matsala WALLAHI TALATUWA dan rainin way0 ayi ta kiranki kina ta shegen barcinnaki k0

MURYA A SAMA wai me yasa baki da biyayyane na miki tambaya jiya baki cemin k0mai ba

In banda tsabar rashin sanin ciw0n KAI ina ke ina wanka da sanyin nan k0 da yake ai jikinki ne

 Rainin way0 ke ba zaki ci tuw0 ba kaina zaki dafa kici kada ALLAH sa kici cikin waye

Wai kina inane ke baki san kiyi sauri bane kina ganin yanda na kwas0 bala'in yunwa haba

😂😂😂😂😂😂
Send to mazan Hausawa and see their response SHIN DAGASKENE HAKA KUKE MAZAN HAUSAWA?
Share:

KA NEMI SOYAYYAR ALLAAH TA ISHE KA

*KA NEMI SOYAYYAR ALLAH YA ISHEKA !!!*
.
Yazo cikin hadith cewa: Wani mutum yazo wajen Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: Ya Rasulullah shiryar dani ga wani aiki da zanyi wanda idan nayi shi ALLAH zai so ni, Mutane ma zasu so ni? Sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: Ka guji duniya ALLAH zai soka, kuma ka guji abun hannun mutane, mutane zasu soka.” [Ibn majah da wasunsu suka ruwaito shi.]
.
→Kada ka sanya soyayyar mutane itace agabanka, saboda mutane zukatansu na jujjuyawa yau su soka gobe su qika.
.
→Kada ka qwallafawa ranka kwad'ayin abun hannun mutane, domin ba zasu qare ka da komai ba haka kuma baza su rage ka da komai ba face abunda ALLAH Ya rubuta maka.
.
→Ka kau da kai daga kwad'ayin Abun duniya na hannun mutane, ka dogara ga ALLAH su ma ALLAH ne ya basu kuma bai manta da kai ba, ka gode masa acikin duk yanayin da ka tsinci rayuwarka, hakan zaisa ya qara maka ya kuma kaika inda baka yi zato ba.
.
→ka sanya soyayyar ALLAH a gabanka saboda idan ALLAH ya soka zai sanya zukatan mutane su karkata zuwa gareka.
.
→ka nemi Yardar ALLAH, Idan ALLAH Ya yarda da kai ya isheka.
.
Ya ALLAH Ka so mu ka yarda damu (Ameen)

Share:

'YANUWANTAKA A MUSULUNCI

*'YAN UWANTAKA A MUSULUNCI*
______________
Manzon Allah (S.A.W) yace: "Dangantaka da take tsakanin mumini...
kamar gini ne wanda sashe yake karfafa sashe." (Bukhari/Muslim)
An karbo daga 'Dan Umar (R.A) cewa Manzon Allah (S.A.W) yace: "Musulmi dan uwan Musulmi ne, kada ya zalunce shi, kada ya mika shi ga abokin gaba.
Wanda ya tsaya da biyan bukatar dan uwansa, to, kuwa Allah zai tsaya masa (da biyan bukatarsa). Wanda kuwa ya yaye wa Musulmi wani abu da yake damunsa, to, Allah zai yaye masa wata damuwa daga damuwar ranar Alkiyama.
Kuma wanda ya suturta Musulmi, to, Allah zai yi masa sutura ranar Alkiyama." (Bukhari/Muslim)
Manzon Allah (S.A.W) yace: "Misalin muminai a cikin soyayyarsu da jin 'kansu da tausasawarsu a tsakaninsu, kamar misalin jiki ne. Idan gaba daga cikin ta yaji ciwo, sauran jikin sai rashin bacci da zazzabi ya same shi." (Bukhari/Muslim)
Ya Allah muna rokonka ka hada kan dukkan musulmi baki daya.
 ka bamu ikon yin soyayya da tausayin juna saboda Allah.
Allah yasa mudace.

*Zauren Sheikh Ja'afar*
Share:

IMANI DA ƘADDARA

━━━━•✿✍🏼✿•━━━━
IMANI DA 'KADDARA
━━━━•✿✍🏼✿•━━━━

Imani da 'kaddara alkhairinsa da sharrinsa rukuni ne cikin rukunan imani, kuma imanin musulmi ba ya cika har sai ya san cewa abin da ya sameshi bai kasance zai kuskure masa ba, haka abin da ya kuskure masa dama bai kasance zai sameshi ba,
Allah Madaukaki yace:

"إِنَّا كُلَّ شَيْءٍ خَلَقْنَاهُ بِقَدَرٍ"

"Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri."[Al-Qamar:49]

Kuma yace:
"وَخَلَقَ كُلَّ شَيْءٍ فَقَدَّرَهُ تَقْدِيرًا"

"Sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa." [Alfurqan:2]

"K'addara na nufin:Tsarin da Allah ya tsara halittu a kansa, gwargwadon yanda iliminSa ya gabata kuma hikimarSa ta hukunta. Wannan tsari na 'Kaddara ya samo asali ne daga sifar Allah ta "K'udura", wato ikonSa da kasancewarSa Mai cikakken iko ne a kan komai da komai, kuma mai cikakkiyar damar aikata duk abin da ya ga damar aikatawa ne"(Littafin Arkanul Iman).

A cikin wannan rukuni na Imani, wato imani da k'addara alkhairinsa da sharrinsa akwai lada mai yawa da sakamako mai girma ga wanda yayi imani cikakkiyar imani, yayi hakuri, ya yi tawakkali ya fawwalawa Ubangiji lamarinsa.

MARTABOBIN IMANI DA K'ADDARA

Imani da 'Kaddara alkhairinsa da sharrinsa ba ya cika har sai mutum ya tabbatar da wasu abubuwa guda hudu:

1- ILIMI
Imani cewa lallai Allah ya san kowane abu, a dunkule, da kuma a d'aid'aikunsa. Allah Madaukaki yace:

"أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ ۗ إِنَّ ذَٰلِكَ فِي كِتَابٍ ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ"

"Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yanã cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne."[Al-Hajj:70]

Kuma yace:

"وَعِندَهُ مَفَاتِحُ الْغَيْبِ لَا يَعْلَمُهَا إِلَّا هُوَ ۚ وَيَعْلَمُ مَا فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ ۚ وَمَا تَسْقُطُ مِن وَرَقَةٍ إِلَّا يَعْلَمُهَا وَلَا حَبَّةٍ فِي ظُلُمَاتِ الْأَرْضِ وَلَا رَطْبٍ وَلَا يَابِسٍ إِلَّا فِي كِتَابٍ مُّبِينٍ "

"Kuma a wurinSa mabũdan gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce Shi, kuma Yanã sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce Yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa."[Al-An'aam:59]

2-RUBUTU
Imani cewa lallai Allah ya rubuta k'addaran kowane abu, har zuwa tashin Alk'iyama.
Allah Madaukaki yace:

"مَّا فَرَّطْنَا فِي الْكِتَابِ مِن شَيْءٍ..."

"Ba Mu yi sakacin barin kõme ba a cikin Littãfi..."[Al-An'aam:38]

3-NUFI
Imani cewa, dukkan abin da Allah ya nufa, shi yake kasancewa, abin da bai nufa ba kuma ba ya kasancewa, sannan kuma lallai bawa yana da nufi, amma tana a k'arkashin nufin Allah ne, ko yayi nufi toh kuma sai Allah ya nufata. Allah Madaukaki yace:

"وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ"

"Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda."[At-Takweer:29]

4-HALITTA
Imani cewa, lallai dukkan halittu, bawa dashi da ayyukansa dukansu halitta ne..
Allah yace:

"اللَّهُ خَالِقُ كُلِّ شَيْءٍ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ وَكِيلٌ".

"Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme." [Az-Zumar:62]

Kuma yace:

"وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ"

"Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"[As-Saffaat:96].

Mai waqe ya kawo wadannan martabobi gabaki dayansu cikin baiti yace:

علم كتابة مولانا مشيئته وخلقة وهو إيجاد وتكوين

Ma'ana

Ilimi, da rubutun Majibincinmu (Allah), da nufinSa da halittarSa, wanda shine samarwa da kasantarwa.
Share:

DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 01

DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 

Kashi Na ɗaya 01

Fitowa Ta Ɗaya 01

Daga Haiman Khan Raees 

Bismillahir Rahmanir Raheem. 

Barkan Mu da Warhaka. 

   Jarumi Shah Rukh Khan yana ɗaya daga cikin Manya-manyan Jaruman Fina Finan Ƙasar India. Na san cewa wannan Jarumi baya buƙatar a bayyana ko shi wanene a harkar Fina-Finan India 🇮🇳, domin kuwa duniya ta riga ta san da wanzuwar sa. Babu wani waje da ake kallon fim ko da a cikin rijiya ne da sunan wannan bawan Allaah bai je ba, to amma ba wannan ne abin mamakin ba, hatta ma waɗanda basu san da wanzuwar kallace-kallacen Fina-Finai ba ma sun san shi a hoto ko kuma labari. Misali, an kai wani mataki da a nan arewacin Nijeriya da zarar ka faɗi wata kalma ta soyayya ko kuma ka aikata wani gagarumin abu da ya danganci soyayya, nan take sai kaji ana cewa 'hmm su sharukhan baban soyayya, uhm kaji su sharukhan da dai abubuwa Makamantan haka masu Alamta cewa jarumin ya samu isa zuwa wajen waɗannan mutane. Wannan kuma har wa yau alama ce da ke nuna tsantsar suna da kuma shahara da wannan bawan Allaah yayi a duniya. 

To a Zahirin gaskiya babu wani mutum da za'a ce gashi ya shahara a duniya face sai ka samu wasu darussa da za'a iya koya daga gare shi, Darussan nan kuwa suna iya zama na kirki ne wanda za'a ɗabi'antu da su ko kuma akasin haka. Wannan dalili yasa na yanke Shawarar tsakuro mana wasu daga cikin kyawawan Darussan da suka zagaye rayuwar wannan Jarumi tun daga rayuwar sa ta kansa da kuma Fina Finan sa domin su zame mana ababen lura saboda rayuwar yau da kullum. Sai dai kuma fa, mai karatu ya kamata ya sani cewa ba wai na kawo waɗannan darussa bane don in wanke jarumin daga wasu kurakurai da yake aikatawa ko kuma in nuna shi yafi wani bane, abinda na sani shi ne, shima yana laifi kamar yadda kowa ke yi kuma yafi wani wani abun shima wani ya fishi wani abun. Sannan ina fata wannan muƙala Tawa ta zamo amsa ga masu tambaya dangane da Jarumi Shah Rukh Khan. 

Na Kasa wannan Muƙala Tawa izuwa gida huɗu. Ga su Kamar haka:
 1. Darussa daga Rayuwar Sa kai Tsaye. 
 2. Darussa daga Fina Finan sa kai tsaye. 
 3. Darussa daga Kalaman sa kai tsaye. 
 4. Darussa daga kalaman Fina Finan sa. 

Don haka yanzu zamu fara bayani ne akan kashi na Ɗaya: ga kaɗan daga cikin Darussan da zamu iya koya daga rayuwar Jarumin Kai tsaye. 

1. MARAICI BA HUJJA BACE TA RAGONCI: 

Mai Yiwuwa mai karatu ya kasance baƙo ne a harkar Tarihin jarumai, mai yiwuwa kuma ba baƙo bane. To idan har ba baƙo bane, nasan kana da Masaniya akan wannan. Idan kuma kai baƙo ne to yau ka sani. Mahaifan Jarumi Shah Rukh Khan duk sun mutu tun kafin ya zama wani abu a duniya, amma hakan bai karya masa zuciya ba, bai sa ya langaɓe ya ɗora hannu a kai yana Wayyo Wayyo Jama'a ku zo ku taimaka min na shiga uku ba. Hasali ma hakan ƙara masa ƙwarin gwuiwa yayi wajen ganin ya cimma burin sa a rayuwa. 

2. IDAN BA ZASU IYA TAFA MAKA BA, TAFA WA KANKA:

 Jarumi Shah Rukh Khan yana ɗaya daga cikin ɗaiɗaikun Jaruman da basu da uwa a gindin murhu a Masana'antar Fina-Finai ta Bollywood, kuma mafi Shahara daga cikin su. Yayin da ya shigo harkar bai san kowa ba kuma babu wanda ya san shi, amma haka ya dage har Allaah Ya kawo shi matakin da yake a yau. Rashin wani wanda zai masa alfarma a harkar bai hanashi jajircewa wajen ganin ya cimma muradin sa ba. 

3. NACI DAMBEN KUTURU: 

Kowa yasan cewa Jarumi Shah Rukh Khan bai kai irin su Hrithik Roshan iya rawa ba, amma hakan bai hana shi dagewa wajen ganin ya taka iya rawar da zai iya a cikin Fina Finan sa ba. Bai kai irin su Salman Khan iya faɗa ba, amma hakan bai hana shi jajircewa wajen ganin ya kafta ba. Shin ko kun san Jarumi Shah Rukh baccin da yake samun damar yi a yini bai wuce awa huɗu zuwa shida ba? Sauran duk yana tafiyar da su ne wajen baiwa aikin sa muhimmanci? 

4. JAHILCI BA HUJJA BA CE:

 Jarumi Shah Rukh Khan yana ɗaya daga cikin jarumai waɗanda suka fi sauran tarin ilimi a cikin Masana'antar Fina Finan India. Duk da cewa iyayen sa Talakawa ne, hakan bai hana su dagewa wajen ganin sun bashi ilimin da ya dace ba. Hakanan bayan rasuwar su ma, ya dage har sai da ya kammala karatun sa a Fannin tsimi da tanadi watau economics. Baya ga haka, jarumin ya kasance mai yawan karance-karance wanda hakan ya sa ya zama gwani wajen iya tsara zance da kuma saita kalamai. Bugu da ƙari kuma, a halin yanzu jarumin yana da Digirorin girmamawa guda huɗu wanda ya samu daga Jami'o'i Mabanbanta a faɗin duniya. Kenan hakan na nuna mana cewa, lallai ne ko me zaka yi in har ka zama ma ilimi, lallai ne al'amura za su zo maka da sauƙi kuma cikin lumana. 

5. BIN NA GABA BIN ALLAAH:

 Jarumi Shah Rukh Khan ya kasance mutum mai Matuƙar biyayya ga na gaba da shi, hakan yasa jama'a da dama suke son shi fiye da wasu Jaruman. Yana girmama na gaba da shi kuma yana mutunta su sosai. Haka kuma yana mutunta na ƙasa da shi. 

6. MUTUM BABU MUTUM IN BAI DA MATA: 

Kamar yadda wani mawaƙin Hausa yake cewa "Gida babu gida in babu mata, mutum babu mutum in bai da mata". Tabbas wannan magana haka take, domin kuwa Jarumin ya fahimci Muhimmancin mace a rayuwar sa kuma yayi aure tun da sauran Ƙuruciyar sa. Hakanan kuma matar Jarumi Shah Rukh Khan watau Gauri Chibber Khan ta bashi gudunmuwa sosai a rayuwar sa. Duk da kasancewar sa mutum mai tsoron mata, hakan bai hana shi girmama su ba. Duk duniya ta aminta da cewa yana ɗaya daga cikin Jarumai mafiya kyawawan Ɗabi'u da kuma ɗa'a ga mata. A shekarun da suka gabata ne ma ya fitar da wani tsari na duk fim ɗin sa da zai fitar, to lallai a fara saka sunan Jarumar da zasu fito tare a cikin Fim ɗin kafin Nasa saboda girmamawa.

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah. 
<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
 Instagram: Haimanraees 
 Infohaiman999@gmail.com


Share:

IDAN NA FARA AL'ADA CIKINA YANA MIN CIWO

*IDAN NAFARA AL'ADA CIKINA YANA MUN CIWO???!*
:
Daga zauren
Kulafa'ur rashidun
:
Assalamu alaikum idan na fara Al'ada cikina Ciwo yakemin randa nafara yini nakeyi akwance komotsi banayi wasu lokuta ma sainayi awa 3 bansan ma inda nakeba kuma har tsawon kwanakin da zan gama??
:

: *****
Walaikumussalam......
.
Ki samusamu gauta da tsohuwar tsamiya ki jiqashi kina sha tun kafin saura 2 days ki fara al'ada kuma kina sha harki gama sannan ki tafasa "ya"yan habbatussauda kina sha sosai da zafi zafi amma shikam sekin ga al'adar kaman tafara zuwa
.
Duk mai fama da ciwo lokacin al'ada anason tarege shan Abu mai zaqi musamman alokacin da date nata ya kusa kokuma intana cikin yin al'adar kuma ta dinga shan ruwan mai dumi harta gama banda shan ruwan sanyi. Insha Allah zata ga ta samu sauqinsa
.
➡ Jamila Dahiru Muhsinat Datti
========================
*```Date* ```[29-08-1439]Hj {16-05-2018}
  Kuna iya samun mu ta Internet/website http://khulafau.cf
_Masu buqatan Group suyima daya daga cikin Number's innan maga ta whatsApp_
+2349033206238
+2347035269582
+2348063796175
           *```Kuna iya samun mu ta facebook*```
facebook.com/khulafaurrashidun
((سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أشْهَدُ أنْ لَا إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ، أسْتَغْفِرُكَ وأَتُوبُ إِلَيْكَ))
〰〰〰〰〰〰〰〰✔
*Wanda yaga gyara, yasanar damu !*
Share:

INA MASU SUNA ANISAH

*INA MASU SUNA ANISAH❓*
   
 *❓TAMBAYA❓*
Assalamu alaikum Dan Allah Mlm INA da tambaya. Dan Allah Mlm sunan Anisa (Aneesa) me yake nufi Allah ya kara ilimi ameen

      *📝AMSA*
AMSA Wa alaikumus salamu warahmatullah.

Anisa yana nufin *MAI DEBE KEWA,* wato wanda za'azauna tare dashi kuma aji dadin zaman, wannan itace bayyananniyar ma'anarsa.
Atasgirisa sai ace: *Unaisah.*
Ansamo kalmar ne daga: *ANAS,* tasgirinsa : *UNAISU*.
Akwai Sahabin Annabi *Anas* kuma akwai *Unaisu.*
1. ANAS. ➖ 2. UNAISU.

1. ANISAH. ➖2. UNAISAH.

Saboda haka za'a iya sawa yara sunan.
Sunan *Unais* yana Buhari:2696. Muslim:1698. Annabi ya aikashi yajefe wata mata da tayi zina.

Daga cikin ya yan Abdullahi Dan Amr Allah yakara masa yarda akwai ANISAH. Al Isabah na Ibnu Hajar(9/31). Sahabiya ta:10876.


=============
Wallahu ta ala a alam.
Shafi'u Shehu Minna.
Daga Islamic Group.
Share:

GAISUWA DA YAREN HINDI

GARAM MASALA HINDI SCHOOL |Introduction |

*Gaisuwa da yaran Hindi*

Good morning - *suph prabhat hai*

Fine-
*Prabhat hai*

Good afternoon - *suph dapehaar hai*

Fine- *achcha depehaar hai*

Good Day - *suph din*

The day is fine- *achcha din hai*

Good evening - *suph sandhyaan*

Fine. - *Achcha sandhyaan hai*

Good night - *suph raatri*

Assalamu Alaikum - *Shanti par ho*
Share:

MAFIYA ALKHAIRIN MUTANE

MAFIYA ALKHAIRIN MUTANE.


Annabi SAW yana bayyana mana siffofi da Wadansu Halaye na Mutanan da suke zababbu awajan Allah.

Ga kadan daga cikinsu:

*1-Wanda yafiku kyawawan Halaye*

Daga Ibn Abas R.A Manzon Allah SAWyana cewa:
*(Zababbunku sune wadanda suke da kyawawan Halaye.......)* @Albany Ya Ingantashi

*2-Wanda yafi kowa kyawun biyan bashi*

Daga. Abi Hurairata R.A :Annabi SAW yana cewa:
*(Zababbe acikin ku shine wanda yafi kyawun biyan bashi)*
@ASSaheeha

*3-Wanda yafi alkhairi awajan iyalinsa*

Annabi SAW yana cewa:
*(Zababbe acikinku shine wanda yake abin alfahari awajan iyalinsa)*
@Albany ya Ingantashi.

*4-Wanda ya iya karatun alqurani kuma yake koyar dashi*

Manzon Allah SAW
yana cewa:
*(Zababbunku shine wanda ya iya karatun alqur'ani kuma yake koyar dashi)*
@Albany ya Ingantashi

*5-Wanda Musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa*

Annabi SAW Yana cewa:
*(Mafi alkhairin acikin musulmi shine wanda musulmi suka kubuta daga sharrin Harshensa da Hannayansa)*
@Saheehul Jami'i.

*6-Wadanda sukayi rayuwa tare da Manzon Allah SAW*

Manzon Allah SAW yana cewa:
*(Mafi alkhairin mutane sune Mutanan da sukayi zamani da Annabi SAW, sannan wadanda suka biyo bayansu,sannan wadanda suka biyo bayansu)*
@Albany ya Ingantashi.

*7-Wanda yafi amfanar da al'umma*

Annabi SAW yana cewa:
*(mafi alkhairin mutane shine wanda yafi amfanar mutane)*
@Albany ya ingantashi.

*8-Wanda zuciyarsa ta tabbata akan tsoron Allah*

Manzon Allah SAW yana ccewa:
*(Mafi mafi alkhairin mutane shine mai zuciyar datake jin tsoran Allah,da harshen da ya tabbata akan fadar gaskiya akowane lokaci.........)*
@Albany Ya ingantasa

*9-Macen da idan mijinta ya kalleta zata faranta masa rai*

Annnabi SAW. Yana. Fada:
*(Mafi alkhairi acikin Mata,itace Macen da idan ka kalleta zata faranta maka rai,idan kuma kayi mata Umarni zatayi maka Da'a, sannan bazata ci amarnarka ba. Idan bakanan)*
@Saheehul Jami'i.

*10-Wanda ake tsammanin alkhairinsa*

Manzon Allah SAW yana fada:
*(Mafi alkhairi acikinku shine:wanda ake tsammanin alkhairi. Daga wajansa,kuma aka aminta daga sharrinsa........)*
@Albany ya ingantashi.

*11-Mafi alkhairin Matan Duniya*

Annabi SAW yana cewa:
"Mafi alkhairin Matan duniya guda hudune:
¤Maryam Bint IIIMRANA
-¤Khadijatu Bint KKKKhuwaid
¤Fadhimatu Bint MMuhammad
¤Asiyatu Matar fir'auna
@Silsilatus Saheeha
Allah ya kara masu yarda.

    Allah ne mafi sani

Allah ka sanya mu cikin bayinka mafiya alkhairi acikin mutane.
Share:

SIRRIN RIKE MIJI

*SIRRIN RIKE MIJI*


ina son kara jan hankalin ku mata game da zaman takewar ku ta aure

A cikin zaman takewar ku ki kasance me gsky duk abinda za'ayi karki yadda kisa zalunci ciki, komai yana tafiya amma banda zalunci, daga mijinki har kishiyar kamoki ne dai bazatayi ba karki yi abinda mutuncinki zai zube a idon mijinku. Kowacce mace tanaso ace mijinta yafi sonta akan kishiya to dataga cewa kece komai awajensa ita baya daukakata zata nemi hanyar waje ba taga wajen zama ba 󟰊
bayan nan

karki yadda yaranki su fahimci bakwa zaman lpy da babansu, karki fada da mijinki agaban yara zasu dauka wannan abune me kyau tunda kema kinayi mamansu (musamman mata) sannan bazasu ringa ganin kimar mahaifinsu ba,
karki sako yaranki acikin fadanki da kishiya shima training kike musu karki zaunar da yaranki kike gaya musu laifin babansu kuskurene babba
Domin kuwa koda yaushe zasu rikan ganin sa a marar tsoron allah

kisan mi zaki yi ma kishiyar ki da abu mai kyau

Ki dafa kishiyar nan da ruwan jikinta ta hanyar janta ajiki kamar ba kishi a tsakaninku ki nuna mata komai na tsarin gidan cikin ruwan sanyi bada rigima ba wallahi kawata yanda kikace haka zatayi sabida tazo gidan taga yanda mijinki ke baki girma kowa nakine dole zatabi itama ayi da ita, ko kadan karki yadda wani raini ya shiga tsakaninki da ita da wannan damar zakiyi amfani ki juyata kamar baiwa karki bada kofar da wani zai shiga tsakaninku


Dr bodmas
+2348039347743
Share:

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA 03

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
(KASHI NA UKU)
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
Bunkasar Harshen Hausa
Abisa fahimta irin tamu, yaren hausa gamayya ce ta haifar dashi. Littafin Babil mai tsarki ya faɗi cewar shekaru da dama da suka gabata (misalin shekaru dubu takwas da suka gabata), mutanen duniya da harshe ɗaya kurum suke amfani, sai daga baya yaruka suka rinka samuwa ta yadda zuwa yanzu akwai kimanin yaruka dubu bakwai a faɗin duniyar nan. Ina tsammanin Littafin Alqur'ani maigirma bai yi magana irin wannan ba, amma duk da haka maganar data fito daga Babil na iya tabbatuwa a kimiyance tunda dai munsan cewa Allah Ubangiji ne ya saukar da littattafan duka guda biyu.
Samuwar harshen hausa na iya zamowa daga haɗakar kalmomi na waɗansu yaruka mabanbanta. Ma'ana, tana iya kasancewa karo-karon kalmomi daga yaruka daban-daban ne ya haɗu ya samar da yaren hausa kachokan ɗinsa, hakan kuwa na iya faruwa ne idan muka kalli hausawan su kansu zamuga cewa kabilu ne da dama suka cakuɗu suka rikiɗe tare da zamowa hausawa lokaci mai tsawo daya shuɗe.
Misali, bari mu ɗauki manyan garuruwan hausa mu ɗanyi karamin nazari akansu:-
A tarihin kafuwar kano, ance wani mai suna Dala ne ya fara zama akan wani dutse wanda daga bisani aka sanya masa suna dala. A hasashe, hakan ta faru tun a wajajen karni na bakwai. Littafin tarihin kano da ake kira 'Kano Chronicle' (Tarih baladil Laziy Musamma Kano) ya ruwaito kwatankwacin haka, har kuma ya rubuta a shafin farko "La na'alamu k'abilatihi'. Ma'ana, bamu san kabilar shi wannan Dala ɗinba wanda hakan ke nuna cewar sam-sam Dala ba Bahaushe bane. Hakan kuma na nuna cewa asalin kalmar Dala itama ba hausa bace.
Daga lokacin Dala da lokacin rayuwar zuriyarsa, kalmomi mabanbanta sun shigo cikin harshen hausa. Kamar misalin Girgije (Sunan Kakan Barbushe, kalmar kuma da hausawa ke nufin Hadari), Magaji daga Magajin Dala, da makamantansu.
Daga bisani akace Bagauda yazo Maɗatai ta kano ya kama noma. A bisa mafi rinjayen magana, Bagauda Bamaguje ne. Shima watakila Sunan kabilar sa Maguzawa, ko kuma sunan kabilar tasa ya zama yana da wani lakabi na zahiri na daban, amma an sakaya shine da sunan 'Maguzanci', kalmar da a hausa ake nufin mutanen da basu da addini. Daga wajen su kalmomi irinsu Noma, Guguwa, Hadari, Shekara da Shekarau suka fito. Waɗannan jinsi na maguzawa kuma, sune suka kafa kusan kafatanin tsoffin biranen dake kasar kano ayau, misalin Rano, Gaya, Gwarzo, Kiru da wasunsu. Koda yake, duk da muna da karancin fahimta akan jinsin Maguzawa, amma da alama suna iya zamowa kabilu mararraba tamkar yadda jinsin fulani suke ayau.
Sannan dai, a littafin 'Kano ta dabo', marubuci marigayi Alh Abubakar Dokaji (Allah ya gafarta masa amin) ya faɗi cewa a tsohuwar kano akwai kabilun Gazargawa dake zaune a jakara, Zadawa dake tsakanin jakara zuwa sontolo, Fangon dake tsakanin Sontolo da Burkum, Zaura dake tsakankanin Bompai da wasai, Dundunzuru dake tsakanin watari zuwa Ɗdutsen karya, Shiriya dake tsakanin sontolo zuwa Shinke, Sheme dake tsakanin Damargu zuwa kazaure, Tokarawa dake tsakanin karmami zuwa Ringim da wasunsu. Dukkan mafi rinjayen waɗannan kabilu sun haɗe guri ɗaya lokaci mai tsawo daya gabata, har takai yaren hausa kurum akeyi a kano, kuma a duk duniya idan kace kano, za'ace maka birnin Hausawa ne.
Mu kalli Katsina. Suma ance Durɓawa ne suka kafa garin tun a karni na sha uku. Wamban Katsina Alhaji Abba Khali ya taɓa faɗa a wata firar sa da gidan radiyon (RFi: Radio france international) cewa waɗanda suka kafa garin katsina sunzo ne daga wani gari mai suna Mani. Garin mani yana nan har yanzu a jihar katsina, to amma ana tsammanin mutanen garin Mani na farko ba hausawa bane, wata kabila ce wadda ta taso daga yankin Mali.
Haka abin yake a zaria. Littafin 'History of Zaria (1350-1902)' na Yakub Hassan ya nuna cewa asalin Birnin Zazzau mutane ne daga Kufena, kuchichchiri, Turanku, Madarkachi, Kargi da Tukur-Tukur sukayi haɗaka wajen kafashi.
Domin kuwa, duk kan waɗancan garuruwa tsoffin gurare ne da binciken akiyoloji ya tabbatar da wanzuwar mutane tun da jimawa kafin kafuwar zazzau a karni na sha uku, kuma akasari waɗancan mutanen kabilu ne mabanbanta misalin Kadarawa, da wasunsu, har dai daga bisani aka samu cewa kabilar Torankawa suka zo suka kwace iko da wurin. A yanzu kuma garin ya rikiɗe izuwa kasar hausa, masarautar su da al'adunsu duk na hausa ne. Suma dai Watakila jikokin waɗancan kabilun ne kusan zamu iyacewa suka ajiye yarukansu da al'adunsu tare da zamowa hausawa zuryan.
Itama kasar Damagaram (Zinder) wadda a yanzu da kasar hausa ake kiranta. Asalinta ance wani mafarauci ne mai suna Zundurma ya fara zama a wurin. Sannu a hankali Barnawa suka rinka kwararowa yankin saboda ance wajen ya kasance turbar kasuwanci ce, har kuma daga bisani aka samu karin kabilu mabanbanta waɗanda mafi akasari yanzu duk sun rikiɗe sun koma hausawa.
A hakika a cikin hausa ta yau akwai Barnawa da yawa. Yawan nasu ma bazai lissafu ba. Tunda an samu cewa akwai garuruwa da dama waɗanda bare-bari ne suka kafasu. yawa-yawan waɗancan bare-bari, wani dalilai ne ya taso dasu izuwa kasashen hausa, sai gashi kuma bayan zamani mai tsawo ya shuɗe, jikokin su duk sun zama hausawa, jinin jikinsu kaɗai ne na kanuri (duk da shima ya gauraya dana sauran kabilu) amma harshe da al'ada duk dana hausa suke amfani.
Irin waɗannan misalan ne a Daura, Zamfara, Gobir, Maraɗi da mafi yawan jihohin hausawa. Abin nema dai anan shine yaya akayi harshen hausa ya haɗiye yarukan waɗancan kabilu ta yadda a yanzu suka zama tarihi?
To, abisa ga falsafar marubucin tarihi Ibn Khaldun, ana gane abinda ya faru a baya ta hanyar fahimtar abinda ke faruwa a yanzu, sannan za'a iya gane menene zai faru anan gaba idan akayi duba na tsanaki bisa abubuwan dake faruwa a yanzu.
A saboda haka, nafi ganin abubuwa biyu ne manya wajen zamowa silar bunkasar harshen hausa.
Na farkon su shine rashin kyamar bakon (mutum) abu matukar bai zo da abu saɓanin fahimtar suba.
Na biyun su kuwa shine karɓar bako tare da maida shi ɗangida.
Ga abinda aka rubuta a Littafin 'waka a bakin mai ita' dangane da wannan:-
"Wani abin sha'awa shine, harshen hausa harshe ne mai iya karɓar kowanne irin salo da harshen larabci yazo dashi ya zauna daram-dam kamar anan aka halicce shi.."
Da yake littafin yana magana ne akan kamanceceniyar ma'aunan gwajin waka na larabci da namu na hausa, amma muna iya cewa wannan abin ba akan larabci da waka kaɗai ya tsaya ba. Domin idan za'a yi bincike za'a samu cewa harshen hausa yayi aro na kalmomi da hikimai daga yaruka mabanbanta, kuma sannu a hankali ya mayar da abinda ya aro ɗin ya zauna daram kamar daman tun can asali akwai shi.
A wani gagarumin bincike da akayi, Dr Aliyu Abubakar ya rubuta a littafinsa 'Al-thakafatul Arabiyya fi Nigeria' cewa yawan kalmomin larabci a cikin hausa sun kai kumusi. (kashi ɗaya bisa biyar, kamar ace aduk kalma biyar ta hausa, ɗaya daga larabci aka aro ta, to idan kuwa da za'a auna da sauran yaruka, da watakila aga wai ina ainihin hausar take?).
Ko kuma idan zamuyi hasashe, zamu iya duba cewar larabawa sun fara shigowa kasashen hausawa don mu'amala tun a wuraren karni na goma sha uku ne. Don haka muna iya cewa a iya shekaru ɗari bakwai na mu'amala tsakanin hausawa da larabawa (1300-2000), tarin kalmomin da hausa ta ara yakai 'khumusi'. Kenan, idan muka ɗauki wancan ma'aunin auna lamurori da Ibn Khaldun ya bamu zamu iyacewa daga karni na bakwai zuwa na goma sha uku (700-1300, wasu shekaru ɗari bakwai baya kenan), hausa ta ari wasu kalmomin da adadinsu zai iya riskar khumusi ko wani abu dake sama ko kasa da haka daga wasu harsunan waɗanda zuwa yanzu zaiyi wuya mu gane su..
A baya-bayan nan kuma,shigowar turawa zuryan da fara mu'amalar su a kasar hausa ta soma ne daga shekarar 1900. Zuwa yanzu Muna iya cewa yaren ingilishi ya shiga cikin hausa a iya waɗannan shekaru ɗari biyun da adadin kalmomi masu tarin yawa, tayadda zaka samu matasan mu zaiyi wuya suyi sa'a guda suna fira ba tare da sunyi amfani da kalmar aro ta ingilishi ba. Watakila kamar haka hausa ta soma a sauran yarukan, kuma muna iya cewa nan da shekaru ɗari biyar masu zuwa tsoffin kalmomin hausa da yawa na iya dulmiyewa tunda an samu musayarsu dana ingilishi.
Don haka, muna iya ganin cewa ɗaukacin kabilun dake tare da hausawa tun tale-tale sun rinka aron kalmomin hausa ne, yayin da suma kuma hausawa na dauri suka rinka aro kalmomi daga garesu, a haka har lokaci yayi da hausa ta haɗiye yawa-yawan yarukan, ta kuma mayarda yawa-yawan kalmomin aro mallakinta.
Watakila kuma saukin hausa wajen yarawa da arowar kalmomi yasa makwabtan hausawa suka fara koyon hausa a hankali-a hankali lokaci mai tsawo daya shuɗe har takai jallin da harshen hausa ya zame musu ɗan tsakiya wajen saduwa tsakanin kabilun dake da banbancin yare da juna.
Zuwa yanzu dai akwai kabilun da sun ma mance da ainihin harshensu, da hausa kurum suke amfani, yayin da wasu kuma suka rike nasu harshen suka kuma riki harshen hausa tayadda idan basuyi hankali ba, shekaru da dama masu zuwa harshen hausa zai haɗiye harshen nasu kamar yadda yayiwa waɗancan yaruka na baya.
Wannan a takaice na iya zama wani abin kamawa dangane da bunkasar harshen hausa a wannan yanki namu..
Zan tsaya anan.. Godiya da yabo ya tabbata ga Allah. Allah yyi daɗin tsira ga Annabi Muhammad (sallalahu alaihi wa sallam).
Share:

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA 02

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
(kashi na biyu)
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Faruwar wannan lamari yasa Gwamna Lugga ya tura sako ga kasarsu Ingila a rohoton da yake turawa gami da labarta musu abinda ya sami Kyaftin Moloney. Shine har yake faɗa musu cewa ba lalle ne ace tafintan Kyaftin Moloney da gayya yayi wannan kasassaɓar ba, amma watakila hakan ta faru ne saboda rashin samun wata fahimta da Kyaftin Moleney yayi dangane da yaren hausa tayadda har ya kasa tantance tsakanin abinda yake karantawa da abinda tafintan sa yake faɗa.
Don haka a karshe Lugga ya bada shawarar cewa a ganinsa mafitar kare aukuwar irin wannan hadari anan gaba shine turawan mulki 'yan uwansa su koyi hausa.
(D.J.M Muffet, concerning Brave Captain, London 1964.)
Ai kuwa hakan akayi, domin an samu cewa Ingila ta bada odar kowanne jami'inta ya fara koyon harshen hausa, an buga sanarwar fara yiwa jami'an mulkin mallaka jarabawar auna fahimtar harshen hausa a jaridar Northern Gazette ta ranar 30 ga watan satumbar shekarar 1902.
Sai dai, abu ne mai matukar wuya a gane wanda yafara rubuta hausa da haruffan romawa (Rubutun Boko) kasancewar bauta ta sanya hausawa sun shiga kasashen larabawa lokaci mai tsawo daya gabata, daga can kuma an tsallaka da wasu izuwa turai da sauran sassan duniya masu nisan gaske duk da zimmar yin bauta.
Kowa yasan anyi zamunna na cinikin bayi a baya, sannan shaharar masautar Borno ba karamar aba bace. Itace akace sarakunan ta sun shahara, har ma akace a wajajen karni na goma sha ɗaya suka fara hurɗa da larabawa, sannan kuma idan yakinsu ya motsa, mamaya suke kawowa dukkanin makwabtan kasashe, ciki kuwa harda kasar hausa. Tana iya kasancewa wani daga turawa ko girkawa ya taba jarraba amsar labaru daga wani bahaushe gami da rubutashi da romanci (boko) amma abin bai fito ga duniya har mun riske shi ba, amma dai mafi dadewar abinda aka samu shine wanda Marubuci Ibrahim Yaro Yahaya (Allah yajikansa da rahama) ya kawo a shafi na 74 na littafinsa mai suna 'Hausa A Rubuce..' inda yakecewa "Watakila za'ayi mamaki aji cewa a kasar Denmark ta turai aka fara samun an rubuta kalmomin hausa acikin rubutun boko tun a karni na goma shatakwas. Yadda abin yafaru shine a cikin shekarar 1772 sarkin Denmark ya tura wakilansa izuwa Arabiya don gudanar da bincike na kimiyya. Acikin wakilan harda wani mai suna B.G Neibuhr, wanda shine kadai ya tsira kuma har ya dawo gida kasarsa. To a wannan shekarar sai wani balaraben Tunis yaje Denmark ziyara, sunan sa Abdurrahman, a tare dashi akwai wani bawansa Bahaushe. Sai sarkin Denmark yasa aka kira Niebuhr domin ya zama tafinta tsakanin sa da balaraben nan kasancewar shi Niebuhr ya koyi larabci a tafiyar da yayi izuwa Arabia. To a wannan gamin ne har abota ta-kullu tsakanin Niebuhr da Abdurrahman, har kuma Niebuhr yayi sha'awar koyon Barbarci da Hausa daga wannan Bawa. Anan ya dukufa yana koyo, ana fada masa kalmomi yana rubutawa.
Ga wasu kalmomi da aka samu Niebuhr ya rubuta a hausar boko kamar yadda yaji daga bakin wannan bawa bahaushe.
Dudsji. Dutse
Ghaui. Gari
Dsjenari. Zinari
Ghurasa. Gurasa
Crua. Ruwa
Sirki. Sarki
Schensali. Shaidani
Berni. Birni
Baya da wannan kuma, sai rubuce-rubucen da J.F Schon yayi da hausa a wuraren 1856 lokacin daya roki Dr. Barth ya bashi aron Yaransa Dorugu da Abega don su taimaka masa wajen yin rubututtukan hausa.
A wancan lokacin ne Dorugu ya rinka faɗar labarun hausa, shikuma yana rubutawa, har aka samu cewa J. F Schon din ya rubuta litttattafai misalin Magana Hausa, Letafin Musa na fari, Labari Nagari, Dictionary of the Hausa da sauransu.
Amma dai idan muka dawo maganar asalin soma rubuta hausa da boko irin wadda har yau muke amfani da ita, to zaifi kyau mu koma kan maganar mu ta sama cewa turawan mulkin mallaka ne suka assasa tare da tabbatar mana da ita.
Farfesa Mahdi Adamu ya tabbatar mana da hakan a shafi na 55 na littafinsa mai suna 'The Hausa factor In West African History'. Kuma ga kadan daga abinda yace :- Karatu da rubutu ta hanyar boko ya samu ga hausawa ne a farkon karni na 20. Saboda a shekarar 1900AD ne gwamnatin Ingila ta karɓe ragamar mulki daga hannun sarakunan hausawa, amma sai a 1903 sojojin Gwamna Lugga suka cinye Kano da Sakkwato a yaki, sanna suka buɗe makaranta ta farko a sokoto tare da malamai biyu watau Mr. Kurdan da mataimakinsa Malam Ibrahim, amma makarantar bata daɗe ba saboda iyaye sunki sanya 'ya'yansu don gudun kada acusa musu akidar kiristanci.
Tun kafin wannan ma, shi kanshi Lugga sai daya kalli Hausawa da yadda sukayi riko da addini tun a lokacin, sannan yayi amannar cewa bai yiwuwa ace za'a koyar dasu boko kamar yadda ake koyar dashi a kasarsu Ingila.
A wani kaulin kuma, cewa akayi tun sa'ar da Lugga yake yaki a kasar nan ya fara sanyawa ana rubuta hausa ta hanyar amfani da rubutun romawa (boko). Saboda kamar yadda muka faɗa tun a baya, Lugga ya fahimci tasiri da bunkasar yaren hausa a wannan yanki na arewa, amma kuma a wurinsa bai yiwuwa ya rubuta hausa da ajami kamar yadda ya samu hausawan lokacin sunayi. Dalilan yin hakan suna da yawa, daga ciki akwai fadin cewa idan za'a rubuta hausa da ajami, sai an koyi yare biyu maimakon ɗaya, watau sai an koyi hausa, sannan kuma an koyi larabci. Amma watakila babban dalilin yafi ga kiyayyar su ga larabawa ko kuma ace kiyayyarsu ga musulunci (kamar yadda babban dalilin kin jinin boko daga hausawa shine kiyayyarsu da kiristanci). Wannan abune da ba sai an ɓoye ba. Lugga ya faɗa cewa baya ganin rashin sanya musulmai a sojinsa a matsayin siyasa, amma a zahiri siyasar ne. Tunda dai kusan ɗaukacin Sojojin nasa ba musulmai bane, mutane ne gwarawa da sauran kabilu marasa addini wadanda suke adawa da musulunci, waɗanda kuma yawa-yawansu suna da matsala daa musulmai tun a lokacin jihadi, don haka suna zucci-zuccin karya daulolin da musulmai suka kafa domin ɗaukar fansa.
A ɗaya ɓangaren kuma, akwai kwatankwacin wannan kiyayyar a zukatan hausawa, kuma tana daga manyan dalilan da yasa hausawa suka kyamaci ilimin boko. Shiyasa sai da aka sha-burtu aka soma sanya yara a makarantun zamani a wancan lokacin, koda yake har izuwa yanzu (kusan shekaru 114 kenan) wasu daga cikin mu hausawa na kallon ilimin boko a matsayin haramtaccen abu kuma gurɓatacce.
Ai a zahirin yakin da turawa sukayi a zamanin mulkin mallaka da 'yan kasa akayi, domin mafi yawan dakarunsu 'yan kasa ne bakaken fata, tunda turawa ba yawa garesu ba a rundunonin, hasali ma wannan yanki namu kamar makabarta ya zamewa turawa saboda yawaitar cututtuka dake musu lahani a yankin.
Shi kuwa rubutun Ajami, turawa da waɗanda ba musulmai ba sna ɗaukarsa a matsayin rubutu ne na Larabci kuma na musulunci, daman kuwa da tun da jimawa turawa da larabawa ba wata ɗasawa suke ta azo agani ba. Idan kuma ba haka ba, to zamu iya cewa baya daga cikin manufar turawa a zuwan su wannan yanki su inganta addinin Islama. Dalili kenan da ba zasu yadda suyi aiki da rubutun ajami ba ballantana har su inganta shi.
Don haka akace babbar sadarwar da sojojin Lugga sukafi fahimta daga gareshi shine rashin sonsa ga musulunci. A zahiri, ban jin an taɓa ruwaito wata kalma ta ɓatanci da Lugga yayiwa Islama, amma a baɗini, ayyukansa nason ganin bayan addinin ne, shiyasa kuma sojojin nasa sukafi kaunar kome za'a rubuta musu, a rubuta musu shi ɗin da yaren hausa, yaren da sukafi sha'awar yarawaa sama da nasu, amma kuma cikin haruffan sabuwar wayewa da kiristocin mulkin mallaka suka kawo, watau romanci.
Bayan anci kano da sokoto da yaki, sai Gwamna Lugga ya sa akayi masa hasashen ɗaliban dake makarantun allo a wannan yanki, inda kintace yanuna cewa akwai misalin makarantun Allo da ake karantar da Addinin musulunci cikin rubutun arabi da ajami misalin dubu 25, sannan ɗaliban dake cikin makarantun sun tasamma dubu 250. Wannan tasa Lugga fahimtar Cewa akwai aiki ja agabansa, amma dai ance da taimakonsa aka kafa makarantar mishan a Bidda a cikin shekara ta 1904, inda aka fara koyawa wasu mutane aciki harda tsirarun musulmai rubutun hausar boko, gami da harshen turanci. Ance ana koyar da daliban ne cikin harsunan mu na gida, watau hausa da nufanci. Gwamna Lugga ya sanar da Ingila yunkurin daya fara na juya rubutun ajami izuwa haruffan Rumawa (Boko) kamar yadda aka samu a kundin takardun dayasha turawa izuwa ingila (Annual Report, Northern Nigeria no. 476, 1903, 332-3)
Daga sanda aka fara samun gagarumar Nasara a fannin boko a kasar hausa kuwa shine wajajen shekara ta 1908, sa'ar da Lugga ya tura Dr. Hans Vischer wanda akafi sani da 'ɗan Hausa' izuwa kasashen Sudan, Misira (Egypt) da Gwalkwas (Ghana) domin yin nazari akan yadda kasashen ke bayar da ilimi ga mutanensu waɗanda akasari musulmai ne, saboda kasancewar hausawa musulmai sunki tura 'ya'yansu a harkar boko. Bayan Dr. Vischer ya dawo gida ne akace ya bude makarantar elementary da ake kira Makarantar ɗan Hausa a Nassarawan jihar kano, wadda akace da dalibai 30 ta soma, sai a hankali daliban suka rinka yawaita. Amma dai daga wannan lokacin ne aka samu cewar an fara fassara littattafai na ilimi wadanda aka rubuta su a wasu yarukan duniya izuwa hausa, aka rubuta su kuma da boko, a sannan gwamnati ta mayar da gausa a arewa a matsayin yaren sadarwa, sannan kuma a hankali har hukumar Norla tazo wadda itama ta bada gagarumar gudunmuwa wajen fassara littattafan ilimi izuwa harshen hausa.
Daga littattafan farko da aka soma fassarawa izuwa harshen hausa da rubutun boko akwai misalin :- Koyon Lissafi, Dare Dubu da ɗaya, Tarihin Garuruwan Borno, da wasu littattafan da dama.
Share:

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA 01

ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
(kashi na ɗaya)
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
Kafin karni na sha tara, kuma kafin zuwan turawan mulkin mallaka kasar hausa, ɗaukacin masana sun haɗu akan cewa babu rubutun AaBaCaDa a kasar hausa, rubutun hausa da larabci (Ajami) kaɗai aka sani.
Shi kansa rubutun na Ajami, dattijo Marigayi Alh Muhammad Koki ya faɗa mana cewa yaji kaka-da-kakanni cewa asalin hausa babu rubutu har sai lokacin da larabawa suka kawo musulunci. A lokacin ne aka rinka amfani da rubutun larabci wajen sadarwa a rubuce. Har ma yace a wancan zamanin, idan kanaso ka tura wani sako ga wani ɗan uwanka dake rayuwa acan nesa dakai, sai dai kaje ka samu malami daya kware a fannin larabci, ka faɗi masa sakon shikuma yana rubutawa da alkalami a takarda, sannan ka biya lada, kai kuma ka naɗe sakon ka turawa ɗanuwan naka ta hanyar fatake. Shima ɗan uwan idan ya samu sakon, haka zaije ga malami wanda ya iya karatun larabci ya karanta masa sakon gami da fassarawa.
Sai Alhaji Muhammad Koki yace:- sai a wajajen karni na sha shidda zuwa na sha bakwai wani Sarki a Zaria ya kirkiro da dabarar rubuta zantukan hausa da haruffan larabci domin saukakewa da kuma bunkasa harshen na hausa.
Watakila kafin wancan lokacin, malumman bogi sunyi sharafi masu fassara sako gwargwadon abinda suka ga mutum yanaso, ko kuma muce karancin fahimtar wasu kalmomi na larabci sun taka muhimmiyar rawa wajen dakile harkar sadarwa a kasar hausa, amma samar da ajami sai ya kawo sauyi a harkar.
John Edward Philips ya rubuta a littafin 'Hausa in the Twentieth century' cewa: Fara Rubuta ɗai-ɗaikun kalmomin hausa da haruffan larabci ya samo asali ne tun lokacin da aka fara rubuta littafi da larabci a yankin. Tund a cewar sa Littattafan da aka rubuta na kunshe da sunayen Hausawa kamar misalin Muhammad Rumfa, sarkin kano dayayi mulki a karni na goma sha biyar.
Amma dai, littafi mafi daɗewa da aka samu wanda aka rubuta da Ajami shine littafin 'Riwayar Annabi Musa' da akace wani bakano mai suna Abdullahi Suka ya rubuta tun a wajajen karni na goma sha bakwai.
Daga nan kuma sai wakokin da aka samu Malaman nan na katsina sun rubuta, watau Dan Marina da Dan Masani, waɗanda suma ake hasashen anyi rubutun a zamani ɗaya da wancan na Abdullahi Suka, ko kuma wasu shekaru kaɗan baya da nashi. Daga nan ne kuma littattafai suka rinka samuwa da hausar Ajami, ta inda ake kara bunkasa rubutut-tukan da abubuwan da abaya babu su tun usuli, tun daga karni na sha takwas har zuwa na ashirin.
Marubuci John Edward Philips yayi hasashen cewa hausar boko ta fara ne a lokacin da turawan mulkin mallaka suka iso kasar hausa. A cewar sa Sa'ar da Fredrick Lugard ya zama shugaban 'Royal Niger Company' a ranar ɗaya ga watan janairun 1900, kaɗan daga sojojinsa ke jin yaren Ingilishi, tunda an samu cewa ana fassarawa sojojin Jawabin da Sarauniyar Ingila Victoria ta aiko a karanta musu da yaren Hausa dana Nupe ne.
Tun alokacin, ance Lugard ya fahimci nisan da yaren hausa yayi a zukatan kabilu dake zaune a arewacin Nigeria. Tunda an samu cewa zaka riski mutum yana magana da harshen kabilar sa, yana kuma magana da harshen hausa. Har ma takai jallin da idan hurɗa ta haɗa wasu mutane masu mabam-bantan kabila da harshe, sai kaga sun ajiye harshen su sunyi amfani da hausa wajen sadarwa.
Ga abinda aka taba jiyo Lugard yana cewa dangane da wannan batu:-
Na gamsu matuka wajen samar da daidaito a ɗibar sojoji ba kawai tsakanin kabilu ba, sai dai tsakanin mabiya addinin (Annabi) Muhammad da kuma sauran mutane marasa addini. Ina matukar girmama addinin (Annabi) Muhammadu, don haka bana ɗaukar rashin sanya mabiya addinin na (Annabi) Muhammadu a harkar soji a matsayin siyasa.. A yanzu mun fahimci cewar Kabilu marasa addini irinsu Gwari, Kedar da sauransu duk suna iya magana da harshen hausa, don haka zanfi so nasanyasu a aikin da zarar babban wurin atisayen mu ya Kammala..
Amma dai, duk da kasancewar Lugard yafi son ɗaukar sojoji daga kabilun da bana Hausa ba, ko kuma ace yafi son ɗaukar mutane marasa addini sama da mabiya Addinin musulunci, amma sam-sam baya koyar da sojin sa harshen su na Ingilishi.
Wannan kuma wani wayo ne da masu dabarar yaki suka nakalta. Domin shi yare ai kamar sirri ne, idan har baka jin yaren da ake yarawa, ba zaka iya fahimtar sirrin da ake tattaunawa ba. Wayon anan kuwa shine, su turawa da sojojin su suna jin harshen hausa, harshen da mafi yawan waɗanda suke yak'a ke fuskanta, amma kuma sunki bada wata kafa dasu waɗanda ake yaka zasu koyi turanci balle har su san wani abu daga sirrikan da turawa ke yaɗawa a tsakanin su.
Da wannan Lugard ya nunawa 'yan uwansa turawa muhimmancin kowannensu yakoyi harshen hausa. Ance ma shine asalin wanda ya kirkiro da jarabawar auna fahimtar hausa ga ma'aikatansa turawa kwatankwacin wadda akace Marigayi Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello ya kirkiro ga ma'aikatan gwamnati a zamaninsa. Sai dai turawa da yawa sunga baiken Lugard, sai sukayi turjiya kuma akan wannan bukata.
Daga cikin futattun su akwai Kyaftin C. W Moloney, wanda akace ya nuna kyamar sa a fili ga yaren hausa tunda acewar sa Larabawa masu yaɗa addinin Islama ne suka kafa shi, ai kuwa shine wanda akace ya haɗu da hatsarin rashin koyon hausa a Fadar sarkin zariya.
Yadda abin ya auku shine, ance Kyaftin Moloney na gabatar da Jawabi ga jama'ar Zazzau ne a fadar sarkin Zariya a ranar uku ga watan oktoba na shekarar 1902 (tun kafin turawa su gangaro Kano da yaki) shikuma mai tafinta yana fassarawa ga jama'a. Sai rashin fahimta ta dabaibaye tafinta, inda ya rinka sauya zantukan da Kyaftin Moloney ke karantawa da wasu zantukan na daban gwargwadon fahimtarsa. ( Watakila saboda tsauraran kalmomin dake cikin jawabin ko kuma saboda karancin ilimin fassara ga tafintan) A ciki ne yake nunawa jama'ar zazzau cewa Matayensu mallakin turawa ne, kuma turawa na matukar bukatar su, duk wanda yaki amincewa da hakan kuwa zai haɗu da fushin turawa.. Haba, kafin a ankara sai ganin kan Kyaftin Moloney akayi yana mirgin-mirgin a kasa, wani zakakuri ya sare shi saboda bacin ran abinda yaji... Nan take kuwa sai faɗa ya kaure...
Share:

Fassarar Waƙar Agar Tum Saath Ho

Fassarar Waƙar Agar Tum Saath Ho

Sunan Waƙa: Agar Tum Saath Ho

Sunan Shiri: Tamasha

Shekarar Fita: 2015

Sauti: A.R.Rahman

Rubutawa: Irshad Kamil

Kamfani: T-Series

Mawaƙa: Alka Yagnik & Arijit Singh

Mai Fassara: Haiman Khan Raees

* Pal Bhar Theher Jao, Dil Ye Sambhal Jaaye

Ka ɗan dakata na wasu 'Yan Lokuta domin wannan zuciyar ta samu ta nutsu

* Kaise Tumhe Roka Karoon…

Ta yaya zan iya hana ka tafiya?

* Meri Taraf Aata, Har Gham Phisal Jaaye

Kowace damuwa in ta tunkaro ni sai ta zame

* Aankhon Mein Tum Ko Bharoon...

Ina so in Kama ka a cikin idanuwana

* Bin Bole Baatein Tumse Karoon

Na kan yi magana da kai, Ba tare da furta kalamai ba

* Agar Tum Saath Ho...

In Kana Tare da ni

* Agar Tum Saath Ho...

In Kana Tare da ni

* Behti Rehti… Neher Nadiya Si, Teri Duniya Mein

Tamkar Ruwa, haka na ke tafiya a cikin duniyar ka

* Meri Duniya Hai Teri Chaahaton Mein

Duniyata ta ta'allaƙa ne da soyayyar Ka

* Main Dhal Jaati Hoon Teri Aadaton Mein

Na kan Narke A cikin halayen ka

* Agar Tum Saath Ho...

In Kana Tare da ni

* Teri Nazron Mein Hai Tere Sapne

Akwai Mafarkai a idanuwan ki

* Tere Sapnon Mein Hai Naaraazi

Akwai rashin gamsuwa a cikin waɗannan Mafarkan

* Mujhe Lagta Hai Ke Baatein Dil Ki Hoti Lafzon Ki Dhokebaazi

Ina jin cewa zantukan Zuciya duk bogi ne

* Tum Saath Ho Ya Na Ho Kya Fark Hai

Ko da kina tare da ni ko a'a

* Bedard Thi Zindagi Bedard Hai

Rayuwa (ta) cike take da ƙunci ta kowace hanya

* Agar Tum Saath Ho (x2)
Ko Da ace kina tare da ni

* Palkein Jhapakte Hi, Din Ye Nikal Jaaye

Cikin Ƙiftawar ido, ranaku su ke wucewa

* Baithi Baithi Bhaagi Phiroon

Duk da cewa a zaune nake, ji nake yi tamkar gudu nake yi

* Meri Taraf Aata, Har Gham Phisal Jaaye

Kowace damuwa in ta tunkaro ni sai ta zame

* Aankhon Mein Tum Ko Bharoon...

Ina so in Kama ka a cikin idanuwana

* Bin Bole Baatein Tumse Karoon

Na kan yi magana da kai, Ba tare da furta kalamai ba

* Agar Tum Saath Ho...

In Kana Tare da ni

* Agar Tum Saath Ho...

In Kana Tare da ni

* Teri Nazron Mein Hai Tere Sapne

Akwai Mafarkai a idanuwan ki

* Tere Sapnon Mein Hai Naaraazi

Akwai rashin gamsuwa a cikin waɗannan Mafarkan

* Mujhe Lagta Hai Ke Baatein Dil Ki Hoti Lafzon Ki Dhokebaazi

Ina jin cewa zantukan Zuciya duk bogi ne

* Tum Saath Ho Ya Na Ho Kya Fark Hai

Ko da kina tare da ni ko a'a

* Bedard Thi Zindagi Bedard Hai

Rayuwa (ta) cike take da ƙunci ta kowace hanya

* Agar Tum Saath Ho (x2)
Ko Da ace kina tare da ni

* Dil Yeh Sambhal Jaaye

Zuciyata Kan nutsu

* Agar Tum Saath Ho...

In Kina Tare da ni

* Har Gham Phisal Jaaye

Duk Baƙin cikin da ya tunkaro ni yakan zame

* Agar Tum Saath Ho...

In Kina Tare da ni

* Din Ye Nikal Jaaye

Ranaku Suna Wucewa

* Agar Tum Saath Ho...

In Kina Tare da ni

* Har Gham Phisal Jaaye

Duk Baƙin cikin da ya tunkaro ni yakan zame

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com
Share:

DU'A FOR PROTECTION AND CURE

DUA Dua for protection and cure

 أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ الله التَّامَّا تِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ

I seek protection in the perfect words of Allah from every evil that He has
created.

A'oozu bi kalimaati alllahi attaammaati min sharri maa khalaq

 (Recite three times) . Aboo Hurayrah (may Allah be pleased with him) narrates from the Prophet : “Whoever recites in the evening three times; I seek protection in the perfect words of Allah from every evil that He has created, then not so much as a stinger (humah) will harm him that evening.” In Muslim there is a similar wording without mention of reciting the supplication thrice (#2709) and at-Tirmidhee (#3898), and al-‘Alaamah Ibn Baaz (may Allah have mercy upon him) mentioned it in Tuhfat-ul-Akhyaar, saying: “The noun al-Humah denotes an animal that possess a stinger filled with poison like a scorpion, snake or something similar. And Suhayl bin Saalih who is one of the narrators of this narration said: “Our people had learned this supplication and we used to recite it every evening when a teenage girl was stung but suffered no pain or affliction (from the sting)”. Taken from The Precious Remembrance Written by ash-Shaykh Ibn ‘Uthaymeen


🐏 *ARAFAZ FARM* 🐏
*_As-salaam Alaykum Waramotullaih Wabarakatuh_*
Share:

ITA TA KAI KANTA

ITA TA KAI KANTA
{Kurma mai ciki}

Wata kurma ce Allah Ya Jarrabe ta da masifar son aure kamar ta kai kanta gidan miji. Ana cikin haka ta sami saurayi suka kulla soyayya har Allah Ya nufe su da aure,bayan tarewa ba da jimawa ba sai Allah Ya ba amarya kurma ciki,tun ba'a je ko'ina ba ta fara laulayin ciki amaye-amaye zazzabi da ciwon kai tabi duk ta rame da kyar dai har lokacin haihuwa yayi, Kurma dai ta haihu a daddafe taji irin abin da 'Yan'uwa mata keji wurin haihuwa,akai suna ta tafi gida wanka bayan ta gama wanka akai-akai ta dawo tace bata komawa ta sake shan irin wannan wuya, karshe dole sai dai auren ya mutu.
Yanzu haka zancen nan da nike da ku kurma na nan gida kememe taki aure kwata-kwata sai dai kawai in an ce mata zo muje barka wance ta haihu ta tambaya ''Haihuwar farko ce koko bata farko bace? In ance ta fari ce sai tace''WAYYO BA TA SANI MUJE AI MATA BARKA'' Inko taji ba haihuwar fari bace sai tace''BANI ZUWA ITA TAKAI KANTA''
Nima ina jin labarin na bushe da dariya sannan nace''KURMA KEMA KE KIKA KAI KANKI''ehe.
Share:

Fassarar Waƙar Manwa Laage

Fassarar Waƙar Manwa Laage

Sunan Waƙa: Manwa Laage

Sunan Shiri: Happy New Year

Shekarar Fita: 2014

Sauti: Vishal-Shekhar

Rubutawa: Irshad Kamil

Kamfani: T-Series

Mawaƙa: Shreya Ghoshal, Arijit Singh

Mai Fassara: Haiman Khan Raees

* Manwa Laage… O Manwa Laage

Wannan Zuciyar Yanzu Ta Manne

* Laage Re Saanwre (x2)

Wannan Zuciyar Yanzu Ta Manne da kai masoyi

* Le Tera Hua Jiya Ka, Jiya Ka, Jiya Ka Yeh Gaaov Re

Duba ka gani, wannan ƙauyen zuciyar Tawa yanzu ya zama naka

* Manwa Laage… O Manwa Laage

Wannan Zuciyar Yanzu Ta Manne

* Laage Re Saanwre (x2)

Wannan Zuciyar Yanzu Ta Manne da kai masoyi

* Le Khela Maine Jiya Ka, Jiya Ka, Jiya Ka Hain Daav Re

Duba ka gani, nayi kasada da rayuwata kamar yadda nake wasa da Hannuwana

* Musaifir Hoon Main Door Ka

Ni matafiyi ne daga nesa

* Deewana Hoon Main Dhoop Ka
Ina haukan son hasken rana

* Mujhe Na Bhaayein… Na Bhaayein… Na Bhaayein… Chaaon Re…

Bana son Inuwa

* Manwa Laage… O Manwa Laage

Wannan Zuciyar Yanzu Ta Manne

* Laage Re Saanwre (x2)

Wannan Zuciyar Yanzu Ta Manne da kai masoyi

* Le Tera Hua Jiya Ka, Jiya Ka, Jiya Ka Yeh Gaaov Re

Duba ka gani, wannan ƙauyen zuciyar Tawa yanzu ya zama naka

Hey… Hey…

* Aisi Waisi Boli Tere Naino Ne Boli

Wai shin wane irin yare ne idanunka suke yi

* Jaane Kyun Main Doli Aisa Laage Teri Holi Main…

Da suka sa na kama rawa haka kuma har ma nake ji kamar na zama taka?

* Tu Mera...

Kai kuma ka zama nawa

* Mmm... Tune Baatein Kholi Kacche Dhaago Mein Piroli

Kin fara wannan maganar ne ta hanyar ƙulla ta da zare mara ƙwari

* Baaton Ki Rangoli Se Na Kheloon Aise Holi

Da waɗannan kyawawan Kalaman naki, ai ko bikin Holi ba zan iya yi ba

* Main... Na Tera…

Ni ba naki bane

* Ho... Kisi Ka Toh Hoga Hi Tu

Watarana zaka zama na wata

* Kyun Na Tujhe Main Hi Jeetoon

Me zai hana na same ka?

* Khule Khwaabon Mein… Jeetey Hain… Jeetey Hain… Baawarein…

A faffaɗar duniyar Mafarkansu ne kaɗai zararru suke yin rayuwa cikin nasara

* Mann Ke Dhaage, O Mann Ke Dhaage

A jikin zaren zuciya

* Dhaage Pe Saaware (x2)

A jikin zaren zuciya, masoyi

* Hain Likha Maine Tera Hi, Tera Hi, Tera Hi Toh Naam Re…

Sunanka kaɗai na rubuta

* Ras Boondiya Nain Piya Raas Rache

Da idanuwa cike da ɓoyayyun albarkatu masoyina yake taka rawar Raas

* Dil Dhad Dhad Dhadke Shor Mache

Zuciya tana bugawa fa sauri kuma tana fitar da hayaniya sosai

* Yun Dekh Sekh Sa Lag Jaye

Duk sanda na kalle shi sai inji wani irin zafi na ketowa

* Main Jal Jaaoon Bas Pyaar Bachein

A Ƙarshe dai na ƙone ƙurmus babu abinda ya rage face soyayyar shi

* Aise Dore Dale Kaala Jaadu Naina Kaale

Waɗannan mayun Baƙaƙen idanuwan naki sun furta ɗalasiman tsafi a kaina

* Tere Main Hawale Hua Seene Se Lagale

Na zama naki yanzu, Zo ki rungume ni

* Aaa... Main Tera...

Taho yanzu, ni naki ne

* Ho… Dono Dheeme Dheeme Jaley

Bari kawai dukkanmu mu ƙone a hankali

* Aaja Dono Aise Mile

Kawai mu haɗe a hakan

* Zameen Pe Laage… Na Tere… Na Mere… Paaon Re…

Ta yadda ƙafata da ƙafarki ba zasu taɓa ƙasa ba

* Manwa Laage… O Manwa Laage

Wannan Zuciyar Yanzu Ta Manne

* Laage Re Saanwre (x2)

Wannan Zuciyar Yanzu Ta Manne da kai masoyi

* Le Tera Hua Jiya Ka, Jiya Ka, Jiya Ka Yeh Gaaov Re

Duba ka gani, wannan ƙauyen zuciyar Tawa yanzu ya zama naka

* Rahun Main Tere Naino Ki, Naino Ki, Naino Ki Chaaov Re...

Fatan kullum in kasance a ƙarƙashin inuwar Idanunka

* Le Tera Hua Jiya Ka, Jiya Ka, Jiya Ka Yeh Gaaov Re

Duba ka gani, wannan ƙauyen zuciyar Tawa yanzu ya zama naka

* Rahun Main Tere Naino Ki, Naino Ki, Naino Ki Chaaov Re...

Fatan kullum in kasance a ƙarƙashin inuwar Idanunka.

ƘARIN BAYANI: Raas wata irin rawa ce da yaran Ƙasar India suke yi, musamman Mazauna yankin Gujarat. Ita wannan rawa a wasu lakuta akan kira ta da rawar ƙaddara, wacce Ubangiji Krishna ke Lura da ita kamar yadda suka ce.

Na Sadaukar da Wannan waƙa ga ɗaukacin Masoya Shah Rukh Khan da Kuma Deepika Padukone.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com
Share:

FASSARAR WAƘAR AANKHEIN KHULI

Fassarar Waƙar Aankhein Khuli

Sunan Waƙa: Aankhein Khuli

Sunan Shiri: Mohabbatein

Shekarar Fita: 2000

Sauti: Jatin Lalit

Rubutawa: Anand Bakshi

Kamfani: YRF Music

Mawaƙa: Lata Mangeshkar, Udit Narayan, Shweta Pandit, Sonali Bhatawdekar, Pritha Mazumdar, Udhbav, Manohar Shetty, Shahrukh Khan & Ishaan

Mai Fassara: Haiman Khan Raees

* Ek ladki thi deewani si

Anyi wata yarinya mai wauta

* Ek ladke pe woh marti thi

Ta kamu da Son wani yaro da dukkan zuciyar ta

* Nazrein jhuka ke

(Da) Idanun ta a Ƙasa/tana mai sadda kai ƙasa

* Sharma ke galiyon se guzarti thi

Cikin jin kunya, haka take tsallaka hanya

* Chori chori chupke chuke

A Sirrance kuma cikin shiru

* Chitthiyan likha karti thi

Ta kan rubuta Wasiƙu

* Kuchh kehna tha shayad usko

Da Yiwuwar dai wani abu take son faɗi

* Jaane kisse darti thi

Ko tsoron wa take ji?

* Jab bhi milti thi mujhse

A duk lokacin da ta haɗu da ni

* Mujhse poochha karti thi

Ta kan tambaye ni

* Pyaar kaise hota hai

Ta Yaya so yake faruwa ne?

* Yeh pyaar kaise hota hai

Ta Yaya wannan soyayyar ta soma ne?

* Aur main sirf yehi keh paata tha

Ni kuma abinda nake iya faɗa mata kawai shi ne

* Aankhein khuli ho ya ho band

Ko Idanuwa a buɗe su ke, ko a Kulle suke

* Deedar unka hota hai

A koda yaushe suna kallon wanda suke so

*Kaise kahoon main o yaara

Ta yaya zan iya faɗa muku hakan Yaku abokai?

* Yeh pyaar kaise hota hai

Ta Yaya wannan soyayyar ta soma ne?


* Aankhein khuli ho ya ho band

Ko Idanuwa a buɗe su ke, ko a Kulle suke

* Deedar unka hota hai

A koda yaushe suna kallon wanda suke so

* Aankhein khuli ho ya ho band

Ko Idanuwa a buɗe su ke, ko a Kulle suke

* Deedar unka hota hai

A koda yaushe suna kallon wanda suke so

*Kaise kahoon main o yaara

Ta yaya zan iya faɗa muku hakan Yaku abokai?

* Yeh pyaar kaise hota hai

Ta Yaya wannan soyayyar ta soma ne?

* Aankhein khuli ho ya ho band

Ko Idanuwa a buɗe su ke, ko a Kulle suke

* Deedar unka hota hai

A koda yaushe suna kallon wanda suke so

*Kaise kahoon main o yaara

Ta yaya zan iya faɗa muku hakan Yaku abokai?

* Yeh pyaar kaise hota hai

Ta Yaya wannan soyayyar ta soma ne?


* Aaj hi yaaron kisi pe marke dekhenge hum

Abokai, ayau, mu faɗa son wata kawai don mu gane wa idanuwan mu.

* Pyar hota hai ye kaise kar ke dekhenge hum

Ta yaya wannan soyayyar ta fara ne? Bari mu jaraba domin mu gane wa idanuwan mu

* Kisi ki yaadon mein khoye hue

A ɓace cikin tunanin wata

* Khaabon ko hum ne saja liya

Na saƙa kuma na ƙawata Mafarkai na

* Kisi ki baahon mein soye hue, apna usse bana liya

Kishingiɗe a kafaɗar wani, na maida shi nawa

* Aye yaar pyar mein koi

Yaku abokai, a yayin soyayya

* Aye yaar pyar mein koi Na jaagta na sota hai

Yaku abokai, a yayin soyayya babu wanda yake barci kuma babu wanda yake Farke

*Kaise kahoon main o yaara

Ta yaya zan iya faɗa muku hakan Yaku abokai?

* Yeh pyaar kaise hota hai

Ta Yaya wannan soyayyar ta soma ne?

* Aankhein khuli ho ya ho band

Ko Idanuwa a buɗe su ke, ko a Kulle suke

* Deedar unka hota hai

A koda yaushe suna kallon wanda suke so

*Kaise kahoon main o yaara

Ta yaya zan iya faɗa muku hakan Yaku abokai?

* Yeh pyaar kaise hota hai

Ta Yaya wannan soyayyar ta soma ne?


* Kya hai jaadu hai koi, bas jo chal jaata hai

Shin wai tsafi ne wannan ko kuma hakan na faruwa ne da kansa?

* Tod ke pehre hazaaron, dil nikal jaata hai

Ta hanyar ɓalle dubunnan iyakoki, wannan zuciyar ta tsere

* Door kahin aasmanon par hote hain ye saare faisale

Can da nisa a Samaniya/Lahira, waɗannan ƙaddarorin/hukunce-hukuncen ake yanke su

* Kaun jaane koi humsafar kab kaise kahan mile

Wa ya san yaushe kuma a ina zaka haɗu da wanda ƙaddarar ku tazo ɗaya?

* Jo naam dil pe ho likha

Duk sunan wanda aka rubuta a Zuciyar ka

* Jo naam dil pe ho likha, ikrar ussi se hota hai

Duk sunan wanda aka rubuta a zuciyar ka, shi/ita kake/kike kamuwa da so


*Kaise kahoon main o yaara

Ta yaya zan iya faɗa muku hakan Yaku abokai?

* Yeh pyaar kaise hota hai

Ta Yaya wannan soyayyar ta soma ne?

* Aankhein khuli ho ya ho band

Ko Idanuwa a buɗe su ke, ko a Kulle suke

* Deedar unka hota hai

A koda yaushe suna kallon wanda suke so

* Aankhein khuli ho ya ho band

Ko Idanuwa a buɗe su ke, ko a Kulle suke

* Deedar unka hota hai

A koda yaushe suna kallon wanda suke so

*Kaise kahoon main o yaara

Ta yaya zan iya faɗa muku hakan Yaku abokai?

* Yeh pyaar kaise hota hai

Ta Yaya wannan soyayyar ta soma ne?


<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com
Share:

SHARHIN FIM ƊIN AVENGERS AGE OF ULTRON

SHARHIN FIM ƊIN AVENGERS: AGE OF ULTRON


Avengers: Age of Ultron Fim ɗin jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2015 a Ƙasar Amurka. Labarin fim ɗin ya samo asali ne daga littattafan almara mai suna Avengers wanda Stan Lee da Jack Kirby Suka rubuta a ƙarƙashin Kamfanin Marvel Comics. Kamfanin Marvel Studios ne suka ɗauki nauyin shirya shi, yayin da Kamfanin Walt Disney Motion Pictures suka rarrabashi. Fim ɗin shi ne na biyun The Avengers (2012) kuma Fim na goma sha ɗaya daga cikin Fina Finan Duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe (MCU). Joss Whedon ne ya rubuta kuma ya bada umurnin Fim ɗin.

An fara Ɗaukar Fim ɗin ne a cikin watan Fabarairu 2014 a, yayin da sauran aikin ya ci gaba a tsakanin watan Maris da Agusta. Wuraren da aka ɗauki Fim ɗin sun haɗa da Shepperton Studios dake
Surrey, Italy, South Korea, Bangladesh , New York City, da sauran wasu wurare dake Ingila. An mayar da fim ɗin izuwa zubin 3D tun kafin a fitar da shi. Kasancewa an kashewa Fim ɗin kuɗi kimanin dala miliyan $365, hakan yasa ya zama Fim na biyu da aka fi kashewa kuɗi a Tarihin Fina Finan duniya baki ɗaya. An saki wannan Fim ne a ranar 13 ga watan Afrilu 2015 A Los Angeles, Sannan aka sake shi a duniya baki ɗaya a ranar 1 ga watan Mayu 2015 a zubin 3D da IMAX 3D.

 Fim ɗin ya samu yabo sosai daga masana harkar Fina Finai sannan 'yan kallo ma ya burge su, bugu da ƙari, fim ɗin ya kawo maƙudan kuɗaɗe kimanin Dala Biliyan $1.4 a Kasuwancin Fina Finan duniya baki ɗaya, hakan yasa ya zama Fim na huɗu da yafi kowanne kawo kuɗi a 2015 kuma yafi kowanne kawo kuɗi a duniya.

Anyi na ukun sa mai suna Avengers: Infinity War a 2018, sannan ana sa ran fitar na huɗun sa a 2019.

LABARIN FIM ƊIN

Mayaƙan tawagar Avengers sun kai wani hari a Ƙasar Sokovia da ke gabashin Yurofiya domin ruguza wata mafakar jami'an Hydra wanda Baron Wolfgang Von Srucker Yake Jagoranta.

Wolfgang ashe yana ta sarrafa tsafin da ke cikin sandar tsafin Loki ne ta hanyar baiwa mutane ƙarfin da ke cikin ta. A nan ne tawagar Avengers ta ci karo da wasu 'yan biyu waɗanda suka samu irin wannan ƙarfin. Pietro Maximoff wanda ya samu ƙarfin gudu kamar tauraruwa mai Wutsiya, sai kuma ƙanwar sa Wanda Maximoff wacce take iya sarrafa tsafi yadda taga dama. Tawagar ta samu nasara akan Wolfgang inda Tony Stark ya ɗauke sandar tsafin Loki ɗin

Bayan sun koma gida ne sai Stark da Banner suka gano cewa wannan sandar tsafi tana da wani hankali na wucin gadi a cikin dutsen da ke jikinta. Saboda haka sai sukayi Shawarar su kammala haɗa wani saƙago da Stark ya fara haɗawa mai suna ULTRON da shi a asirce domin ya taimaka musu wajen yaƙi da 'yan ta'adda. Shi kuma Ultron sai yayi tunanin ya wanzu ne kawai domin ya ƙarar da' yan adam baki ɗaya a maimakon kare 'yan adam baki ɗaya da Stark ya ƙirƙireshi a kai.

Don haka sai nan take ya kashe saƙagon dake taimakon Stark wato J.A.R.V.I.S. Sannan ya kaiwa tawagar hari a Hedikwatar su, sannan ya fece da sandar tsafin Loki. Bayan nan sai kuma Ultron yayi amfani da ragowar kayan aikin Wolfgang a Sokovia ya inganta jikin sa, sannan kuma ya ƙirƙiro wasu ƙananan saƙagai irin nasa domin su taya shi aiki. Hakan fa bai ishe shi ba, sai kuma ya je ya ɗauko waɗannan 'yan biyun domin su zama mataimakan sa, su kuma dama suna jin haushin Stark saboda Kamfanin sa ne ya ƙera makamin da yayi sanadiyyar mutuwar iyayen su.

Daga nan kuma sai ya je wajen fitaccen ɗan harƙallar miyagun makamai Ulysses Klaue domin ya samu Sinadarin Vibranium wanda aka samo daga Wakanda. Tawagar suma sai suka kaiwa Ultron hari a can tare da muƙarraban sa. Sai dai Wanda ta yi amfani da ƙarfin tsafin ta wajen rikita su da hangen abubuwa iri daban daban sannan ta sa Hulk ya fita hayyacin sa ya kama yiwa jama'a ɓarna, da ƙyar Stark ya samu ya sumar da shi bayan yayi amfani da wata rigar ƙarfe ta musamman wanda ya Sana'anta saboda hakan

Ta'adin da Hulk yayi wa jama'a da kuma tsoron da Wanda ta dasa musu a zuciya ne yasa tawagar suka ɓoye a wani keɓaɓɓen gida na ɗan wani lokaci. Shi kuma Thor sai ya nemi taimakon Dakta Erik selvig dangane da munanan abubuwan da ya gani yayin da wanda ta rikita masa tunani. Shi kuma Nick Fury sai ya je maɓoyar tawagar ya ƙara musu ƙwarin guiwa kan yadda zasu samu nasara akan Ultron.

Can kuma a Seoul, Ultron ya matsawa abokiyar tawagar Avengers wato Dr. Helen Cho Domin tayi amfani da na'urar ta wajen Samar masa da wani sabon cikakken jiki mafi inganci. Yayinda Ultron yake ƙoƙarin ɗaura kansa a wannan sabon gangar jiki ne sai wanda ta samu damar karanta zuciyar sa, a nan ne fa ta gano shirin sa na son ganin ya hallaka gaba ɗayan mutanen duniya don haka sai ita da yayanta suka juya masa baya.

Daga nan sai Rogers, Romanoff da Barton suka tunkari Ultron suka ƙwace gangar jikin, sai dai sunyi rashin sa'a domin ya kama Romanoff ya tafi da ita. Rikici kuma sai ya sake ɓallewa a tsakanin tawagar bayan Tony Stark ya ɗaura J.A.R.V.I.S. a kan wannan sabon jiki. Ashe Jarvis ba mutuwa yayi ba, ya ɓoyewa Ultron ne. Ana cikin hakane Thor yazo ya taimaka wajen kunna gangar jikin, tare da yi musu bayanin cewa wannan dutse da ke goshin gangar jikin ɗaya ne daga cikin duwatsun al'ajabi shida da ake da su, kuma su ne duwatsun da suka fi kowanne ƙarfin tsafi a duniya kuma ya gansu a cikin hangen nesan da yayi.

Daga nan sai " Vision " tare da waɗannan 'yan biyu suka raka tawagar Avengers zuwa Sokovia inda Ultron yayi amfani da ragowar Sinadarin Vibranium ɗin da ya siyo wajen samar da wata Muguwar na'ura wacce zata iya ɗaga ilahirin Ƙasar sama tun daga ƙasa ta kifar da ita kowa ya mutu. Banner ya samu damar ceto Romanoff wacce ta farkar da Hulk domin yin wannan yaƙi. Tawagar avengers sunyi baƙin gumurzu a tsakanin su da Ultron Yayinda Nick Fury, Maria Hill, James Rhodes da kuma wasu Jami'an S.H.I.E.L.D. Suka zo a wani babban jirgi suka kwashe mutanen Ƙasar. Ana cikin hakane Pietro ya mutu a lokacin da ya kare Clint Barton daga harsasai, jin haushin haka ne yasa wanda ta bar inda aka ajiye ta domin ta ruguza jikin Ultron, wannan ya baiwa ɗaya daga cikin saƙagan Ultron damar kunna wannan Mummunar Na'ura. Nan take birnin ya fara ɓuɓɓugowa gaba ɗaya amma sai Stark da Thor suka haɗa ƙarfi suka tarwatsa komai.

Bayan ƙura ta lafa ne sai Hulk ya gudu a wani jirgin sama saboda baya son ya cutar da Romanoff idan ya ci gaba da kasancewa tare da ita, shi kuma vision sai ya Fuskanci Ultron ya tarwatsa shi. Bayan nan sai tawagar ta kafa sabon wurin zama inda Nick Fury Maria Hill da Rhodes zasu dinga kulawa da shi, thor kuma ya koma Asgard domin ya ƙara bincike dangane da Al'amuran da suka jawo faruwar waɗannan yaƙe-yaƙe. Shi kuma Clint Barton Sai yayi ritaya, Yayinda Steve Rogers da Romanoff su kuma suke koyar da sabbin Membobin tawagar wato Wanda, Sam Wilson, Rhodes da Kuma vision.

A wata fitowa ta ƙarshe, an nuno Thanos wanda ransa ya ɓaci da rashin nasarar da karnukan farautarsa suke haifar masa, inda yasa wata safar hannun Ƙarfe kuma ya sha alwashin samo duwatsun al'ajabin dukkan su da kansa.


JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA


* Robert Downey Jr. - Tony Stark / Iron Man

* Chris Hemsworth - Thor


* Mark Ruffalo - Bruce Banner / Hulk


* Chris Evans G Steve Rogers / Captain America


* Scarlett Johansson - Natasha Romanoff / Black Widow :


* Jeremy Renner - Clint Barton / Hawkeye:


* Don Cheadle - James "Rhodey" Rhodes / War Machine

* Aron Taylor-Johnson - Pietro Maximoff / Quicksilver


* Elizabeth Olsen - Wanda Maximoff / Scarlet Witch

* Paul Bettany - J.A.R.V.I.S. / Vision

* Cobie Smulders - Maria Hill

* Anthony Mackie - Sam Wilson / Falcon

* Hayley Atwell - Peggy Carter

* Stellan Skarsgård as Erik Selvig

* James Spader - Ultron

* Samuel L. Jackson - Nick Fury

* Thomas Kretschmann - Baron Wolfgang von Strucker

* Henry Goodman - Dr. List

* Linda Cardellini - Laura Barton

* Claudia Kim - Helen Cho

Andy Serkis - Ulysses Klaue


* Julie Delpy - as Madame B.

* Kerry Condon - F.R.I.D.A.Y

* Josh Brolin - Thanos


<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com
Share:

FATALWAR SINU 02


*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              FATALWAR SINU 02
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              A Short Story
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
   
                      ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
         *ѕtσrч/wríttєn ɮʏ✍🏻:*
👉🏻© *_Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹

Haka dai wannan iska tayi ta gudu da ni kamar zamu bar duniya har sai da na manta iya lokacin da ta ɗauka tana wannan gudu dani. Bayan mun daɗe a cikin wannan yanayi, sai can na jini Tim! Na faɗo kan wani abu mai kama da tarin raugar gyaɗa wanda ina kyautata zaton laushin sa ne kawai ya hana ƙasusuwana karyewa tare da yin rugu-rugu. Kasancewar na galaɓaita ainun, ban ma fahimci cewa wannan Igiyar da ta ɗaure ni ta kwance ni da kanta ba balle in lura da inda nake, hakanan dai na langaɓe ina numfashi sama-sama sai kace tsohon karen da cuta ta kwantar da shi.

Ina nan kwance ina tunanin ta yaya akayi har wannan al'amari ya faru da ni? Yaya daga buɗa littafi kawai shikenan waƙi'a irin wannan zata antayo kaina? Ban kai ga gama wannan tunani ba sai naji wata murya na cewa: "Barka da zuwa Hãïmâñ, lake-lale marhabin da makafcin zamani, aminci ya kaiwa tsafin gidan mu, Haƙiƙa na tabbatar da cewa zaka zo, kuma gashi kazo ɗin. Hahah! Tsabar galaɓaitar da nayi, tare da rashin ƙwarin jikina suka sa na kasa furta komai kuma na kasa Waigawa inda wannan murya ke fitowa domin inga ko wanene, kuma na kasa furta komai. Ko da mai maganar yaji shiru, sai naji yace: "a'a, ya naji yayi shiru kuma, Ko dai ya mutu ne? Bari mu gani". Ko da yazo nan a zancen sa sai naji wata irin iska mai sanyi tana shiga cikin Jikina, ba'a daɗe da yin haka ba sai naji duk gajiyar da ke jikina ta gushe, wahalar da na sha ta kau, sannan wani gagarumin Ƙarfi ya shige ni tamkar nayi baccin awa goma na tashi nayi wanka kuma na ci abinci. Ko da naji wannan canji a jikina, sai nayi zumbur na miƙe tare da Waigawa inda wannan murya take fitowa domin ganin kowanene.

Tooooofah! Mai zan gani haka? Ba kowa na gani ba face Kwarkwar sinu zaune cikin sigar Kafcen sa na fim ɗin Racha (Hatsabibi). Kujerar da yake zaune a kanta kyakkyawa ce ba laifi, Singiletin da ke wuyar sa kuma Koriya ce, Yayinda ya ɗaura wani farin zane a ƙugunsa ya kuma ɗauki ƙafa ɗaya ya ɗaura a kan ɗayan. A hannunsa na dama kuma kwalbar barasa ce wacce a daidai wannan lokaci yayi rabin ta, ko da muka haɗa ido sai yayi min wani azzalumin murmushi.

Tsananin mamakin ganina tare da shi a wannan wuri kuma a daidai wannan lokaci yasa yasa na wangame baki kawai ina kallon sa. Bayan mun an samu ɗan lokaci muna kallon juna ba tare da ɗayan mu ya ce da ɗayan komai ba. Sai ya ce da ni: "zauna mana". Kafin in ƙyafta ido sai ga kujera ta bayyana a gabana alhalin da can babu ita. Har na yunƙura da nufin in zauna sai na lura cewa ashe duk allurai ne soke a jikin kujerar, zama kawai suke jira in yi su tsire ni, don haka sai na ƙi zama. Ko da yaga haka, sai ya ɓarke da dariya kamar sabon hauka, yayi ta yi har ya gaji, daga baya kuma sai ya murtuke fuska kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa. A daidai lokacin da ya ɗaure fuskar ne kuma kayan jikinsa suka canja launi izuwa ƙananan kaya. Daga nan sai ya miƙe tsaye ya nufo inda nake yana kaɗa kai cikin murmushin antakaranci kamar dai yadda ya dinga yi a cikin shirin Nayaak (masheƙi). Ko da yazo dab da ni sai ya buɗe baki da nufin yin magana. Ai kuwa nan take naji wani wari, ɗoyi gami da hamami sun Durfafo ni, ba shiri na kau da kaina daga saitin inda yake don naga warin na neman yin barazana wa lafiya ta.

Ganin abinda nayi yasa ya sake fashewa da dariya sannan yace: "Watau baka son warin barasa, amma ka iya yamaɗiɗi da ni kan cewa ni mashayinta ne ko a zahiri, ko ba haka ba? Lallai ka cika Maras kunya, Tir da kai! Ko da naji wanna kalami sai raina ya ɓaci, amma saboda ban san me ke faruwa ba sai na danne zuciyata ban nuna mishi ba. Maganar farko da ta fito daga baki na ita ce: "Waye kai?". Ko da yaji wannan tambaya, sai naga yayi tsalle ya koma gefe tare da riƙe baki wai shi yayi alamar mamaki, sannan yace: "ai iyye! To in baka sani ba ka sani, ni ne nan Mailavarapu Surya Narayana, watau Kwarkwar sinu kamar yadda ku Ƴan fassare-fassaren nan kuka liƙa min". Yayin da yazo nan a zancen sa, sai naga ya sake murtuke fuska yana harara na.

Ni kuwa wannan bayani da yayi ba ƙaramin mamaki ya bani ba, na sake duban shi da kyau naga dai tabbas shi ɗin ne, sai nace da shi: "To amma ba ka mutu ba? Ya kuma aka yi ka ci gaba da rayuwa?" ko da yaji waɗannan tambayoyi nawa sai ya ƙara ƙyalƙyalewa da dariya sannan yace: "Ai fatalwa ta ce kake gani yanzu, kasancewa ta ɗaya daga cikin Mabiya ubangiji Rama da kuma kasancewata ɗaya daga cikin mutanen da aka fi zolaya a duniya, shi ne Ubangiji Rama ya bani damar dawowa duniya a matsayin fatalwa bayan mutuwa ta domin in rama abinda aka yi min wanda kai da ire-iren ka kuke sahun gaba wajen aikatawa! Na daɗe ina kafawa masu zolayata tarko suna shallakewa ba tare da na tarka ko ɗaya ba, sai fa kai yau. Don haka ya zama dole in gana maka azaba mai raɗaɗi don hakan ya zama sharar fage na taron Ɗaukar fansata da zan yi. Mamaki da taraddadin abinda ka iya biyo bayan wannan batu nasa ne suka sa nayi shiru na kasa cewa komai. Can dai sai na yanke Shawarar jan shi da labari ko wataƙila hakan yasa ya bayyana min wasu al'amuran, don haka sai nace: "Eermm... Kaga Kwarkwar ɗan Dakata kaji... Ai iyye! Watau ni kake kira da Kwarkwar ko? Lallai ka cika maras kunya yaron nan! Sinu ne ya katse ni da wannan jawabi nasa ta hanyar daka min tsawa. Cikin rawar baki nace "Erm... To Sinu ka ɗan saurare ni... Kai! Kada ka raina min wayau, sunan ba Sinu bane Srinu ne, kuma kada ka sake kirana da wannan sunan ka kira ni da sunana na asali watau Mailavarapu Surya Narayana! " To Mailavarapu Surya Narayana... Erm.. Ina ganin kamar an samu saɓanin fahimta ne, ina so ka sani cewa ni ba kowa bane a harkar fassara, domin ayyukan da aka yi dani basu da yawa, hasali ma ni aikin shirin ka ɗaya zan iya tunawa nayi. Bugu da ƙari ni ban ga ta yadda za'a yi ace wannan abu ya zafafe ka ba da har zaka dawo duniya a matsayin fatalwa kace zaka ɗauki fansa. Laifin me masu fassara suka yi maka? Hasali ma dai, shin wai wannan Karon ne aka fara fassara ne? In gaskiya ne me yasa waɗancan basu zafafe ka ba sai wannan?


Zan Ci Gaba In Shaa Allaah.<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com
Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form