Sunday, 7 July 2019

DABARUN SARRAFA NAMA 03

🌹Dake Ake🌹
Darajarki Abincinki

DABARUN SARRAFA NAMA -3
Dambun Nama

Dafarko zaki samo namanki zallah
bamai kitse ko kashi ba
 gyrashi
ki hada

Albasa
Attaruhu
kayan kanshi[Citta,kanunfari,masoro,cinnamon,maggi,gishiri,mangyada]
 bayn kin hadasu a tukunya ki zuba ruwa yadda naman zai hade da kayan da kika zuba su dahu sosai
bayan ya dahu kuma ya tsotse ruwansa
saiki sauke
hanya biyu ce
ko in zaki iya ki cigaba da juyashi harya fara ragargajewa [yafi wahala]
kodai ki juyeshi a turmi ki daka
ko kuma ki zuba a injin bature ki nika
daga nan saiki zuba mai a kasko yayi zafi kisa albsa ya soyu saiki zuba nikakken namanki
kita soyawa sai yayi yadda kike bukata
 daga nan saki juye a container mai tsafta
yawwa daga nan sai ci😋😋
nagode
19/8/2018
Rubutawa:-Binta Murtala[ummu Ahmd]

Yadawa:-Cibiyar wayar da kan mata
ta
🌹 Dake Ake Consultancy🌹


EmoticonEmoticon