DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 02

DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN

Kashi Na ɗaya 01

Fitowa Ta Biyu 02

Daga Haiman Khan Raees

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Barkan Mu da Warhaka.


 7. GIRMAN KAI RAWANIN TSIYA:

 Jarumi Shah Rukh Khan yana daga cikin Jaruman Indiya da suka fi saura sauƙin kai da iya mu'amala. Bugu da ƙari SRK bashi da girman kan tsayawa a nuna mishi abinda bai sani ba ko bai iya ba ko da kuwa ace wanda zai koya masa abin nan yana ƙasa da shi ne sosai. Domin mun ga hakan a fili Yayinda ake ɗaukan fim ɗin Zero inda ƴar cikin sa mai suna Suhana ta zo tana koya masa wasu al'amura dangane da aikin fim ɗin.

8. ƊAN UWA RABIN JIKI:

Mutane da yawa basu san cewa Jarumi Shah Rukh Khan yana da wata ƴar uwa ba, amma a zahiri yana da ita. Su biyu mahaifiyar su ta haifa. Bayan mutuwar iyayen su wannan ƴar uwa tasa ta faɗa cikin mawuyacin hali na rashin lafiya wanda wasu da dama ma sun yi tunanin mutuwa zata yi, amma hakan bai sa ɗan uwanta ya guje ta ba. Hasali ma, mafi yawancin ayyukan da ya karɓa a farko-farkon fitowar sa, ya karɓe su ne kawai domin ya samu abinda zai ci da kansa da iyalan sa da kuma nemawa ƴar Uwar sa lafiya.

9. ALLAAH NA TAIMAKON MAI TAIMAKO:

 Shah Rukh Khan ya kasance ɗaya daga cikin Jaruman da suka fi kowa tausayin Talakawa da waɗanda Iftila'i ya faɗawa. Yana taimakawa mutane a duk inda ya samu damar taimakawa, ko da yake baya son baiyanawa, amma duniya ta sani, domin har lambar yabo ya samu akan hakan.

10. A SAI DA RAI A NEMO SUNA:

 Jarumi Shah Rukh Khan Haƙiƙa ya cancanci a kira shi da suna ƊAN KASADA, domin kuwa yayi abinda a Tarihin Masana'antar Fina Finan India kusan in ka cire Jarumi Amitabh Bachchan, to za'a iya cewa ba'a taɓa samun jarumin da yayi kamar sa ba. Ba komai ne ba wannan abu ba face karɓar wasu ayyuka wanda jarumai da yawa suka gujewa domin tsoron zasu iya karya musu alƙadarin su a harkar Fina-Finai. Bisa sa'a kuwa sai gashi ya hau su kuma ya tsallake rijiya da baya. Kamar yadda jarumin yakan faɗa, "tari Aradu da ka, in ka yi Nasara zaka ji daɗi in kuma baka yi ba zaka ƙara ilimi".

11. DATTIJO:

Haƙiƙa Alamomin Dattijantaka sun bayyana a tattare da Jarumi Shah Rukh Khan. Domin kuwa banbancin tsoho da Dattijo abu ne mai muhimmanci da ya kamata mu sani. Tsoho shi ne wanda ya tsufa sakamakon shekarun sa sunyi nisa, amma zuciyar sa tana cike da yarinta. Dattijo kuwa shi ne tsohon da ya tsufa a shekaru, kuma ya tsufa a hankali da tunani. Jarumi Shah Rukh Khan yayi aure, kuma ya haihu, sannan shekaru sun ja kuma yasan da hakan. Sanin kowa ne cewa jarumin yana da kyakkyawan tarihi da ke bayyana cewa bai taɓa yaudara ko cin zarafin wata Jaruma ba, bai taɓa ha'intar wani abokin aikin sa ba kuma bai da mugunta. Sannan hankali da nutsuwar sa ne suka sa ake gayyatar sa zuwa taruka domin ya gabatar da jawabai. Bugu da ƙari yana daga cikin Jaruman da suka fi saura kula da yaransu musamman ta fuskar karatu da kuma ɗa'a.

12. BAYAN WUYA SAI DAƊI:

 Iyeyen Jarumi Shah Rukh Khan har Suka mutu basu mallaki gidan kansu ba, a gidan haya su ke. Asali ma, akwai lokacin da aka wayi gari sun gaza biyan kuɗin hayar gidan da suke zaune har aka watso musu kayan su waje. Amma a yau Jarumi Shah Rukh Khan yana da katafaren gida na gani na faɗa. Bugu da ƙari, gidan jarumin ya samu damar shiga cikin jerin gidajen da ko da nan gaba Gwamnatin India ta yanke Shawarar yin rusau domin gyara tsarin gine-ginen Ƙasar, to su ba za'a taɓa su ba. Lallai Allaah Shi ne mai yin yadda ya so.

13. GIDA BIYU MAGANIN GOBARA:

 Kasancewar Jarumin yana da ilimi a harkar kasuwanci da iya tallata haja, kamfanoni da dama sun sha ɗaukar sa a Matsayin mai tallata musu hajojin su. Hakanan kuma jarumin yana da Kamfanin shirya Fina-Finai mai suna Red Chillies Entertainment wanda a yanzu haka babu kamar su a kaf Bollywood wajen VFX. Har ila yau kuma dai, jarumin yana da kaso mafi tsoka a cikin kungiyar ƙwallon Cricket ɗin nan mai suna Kolkata Knight Riders. Kenan yau ko da ta Allaah ta kasance ya daina fim, to yana da abin yi.

14. KWALLIYA TA BIYA KUƊIN SABULU:

Tabbas Jajircewar wannan Jarumi ta jawo mishi suna da ɗaukaka mai tarin yawa a rayuwar sa. Domin a daidai lokacin da na ke wannan rubutu, alƙaluma sun bayyana cewa jarumin yana da lambobin yabo a ƙalla guda ɗari biyu da Casa'in da biyu (292). Lallai wannan ko ba'a faɗa maka ba kasan cewa banza bata kai zomo kasuwaA nan zan ɗan dakata dangane da Darussan rayuwar wannan Jarumi ba don sun Ƙare ba, sai dai don kada abin yayi yawa. In Shaa Allaahu Ta'ala a fitowa ta gaba zamu taɓa Darussan da ke tattare ne da wasu daga cikin finafinan sa.

Nagode.

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah
<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com

Share:

3 comments:

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive