Sunday, 7 July 2019

FASSARAR WAƘAR PANCHADARA BOMMA

FASSARAR WAƘAR Panchadara Bomma

Sunan Waƙa: Panchadara Bomma

Sunan Shiri: Maghadheera

Haɗa Sauti: M. M Keeravani

 Rubutawa: Chandrabose

Rerawa: Anuj Gurwara & Reeta
Anuj Gurwara

Fassarawa: Haiman Khan Raees

* Panchadara bomma bomma

Ya ke 'ƴar tsana ta mai lulluɓin Sikari

*Pattuko vaddanakamma

Kada ki ce min kada in riƙe ki

* Manchu poola komma komma

Ya Ke igiya ta mai lulluɓin ƙanƙara

* Muttukovaddanakamma

Kada ki ce min kada in taɓa ki

* Chetine taakoddante chentake raavaddante

Idan Kika hanani taɓa hannunki ko kuma ƙarasowa wajen ki

* Yemavutanamma

Me zai faru da ni?

* Ninnu pondetanduke puttane gumma

An haife ni ne don in so ki

* Nuvvu andaka pote vrudhaa ee janma

Rayuwata bata da amfani Matuƙar ba zan iya kaiwa gare ki ba.

* Ninnu pondetanduke puttane gumma

An haife ni ne don in so ki

* Nuvvu andaka pote vrudhaa ee janma

Rayuwata bata da amfani Matuƙar ba zan iya kaiwa gare ki ba.

* Puvvu paina cheyyeste kasiri nannu tittinde

Yayinda na ɗaura hannuna a kan fure, sai furen ta kore ni da zagi

* Pasidi puvvu nuvvani pampinde

(kuma) Ta turo ni wajen ki domin ke ce fure mai fitar da tambarin zinari

* Nuvvu raaku naa ventaaye

Kada ka biyo ni

* Puvvu chuttoo mulluntaay

Ita fure zagaye take da ƙayoyi

* Antukunte mante vollantaa

Kuma idan ka sake ka taɓa, to raɗaɗi mai zafi zai zagaye jikin ka

* Teegapaina cheyyeste titti nannu nettinde

Yayinda na ɗaura Hannuna a kan wata 'ƴar ciyawa, sai ta kore ni da zagi

* Merupu teega nuvvani pampinde

(kum) ta aiko ni gare ki tana kwatanta ki da Walƙiya.

* Merupu venta urumantaa

Ita Walƙiya Aradu ce ke biye da ita

* Urumu venta varadantaa ne

Aradu kuma marka-marka ke biye da ita

* Varadalaagaa maarite muppantaa

Damuwa zata dirar maka idan na rikiɗe na zama ARADU ko marka-marka

* Varadainaa varamani varistaanamma

Na ɗauki damuwar a matsayin kyauta, don haka zan aure ki

* Munakaina sukhamani mudestaanamma

Domin samun auren ki, zan ji daɗi idan aka ce na nutse a cikin wannan ruwa na marka-marka

* Ninnu pondetanduke puttane gumma

An haife ni ne don in so ki

* Nuvvu andaka pote vrudhaa ee janma

Rayuwata bata da amfani Matuƙar ba zan iya kaiwa gare ki ba.

* Gaali ninnu taakindi nela ninnu taakindi

Sassanyar Iska ta taɓa ki, Ƙasa ma ta taɓa ki

* Nenu ninnu taakite tappa

To menene laifi don na taɓa ki?

* Gaali oopirayyindi

Iska ita ta zamo Numfashi na

* Nela nannu nadipindi

Ƙasa kuma ita ce ke yi min jagora a kowane taku da nake yi

* Yevitantaa neeloni goppaa

To kai menene abin birgewa a tare da kai?

* Velugu ninnu taakindi

Hasken rana tana taɓa ki

* Chinuku kooda taakindi

Ruwan sama shima yana taɓa ki

* Pakshapaata menduku naapainaa

Me yasa kike nuna Ƙiyayya a gare ni?

* Velugu daari choopindi

Haske shi ke nuna min hanya

* Chinuku laala posindi

Ruwan sama kuma shi ke tsaftace ni

* Vaatitona polika neekelaa

Me yasa kake haɗa kanka da su?

* Avi batikinappude toduntaayamma

Su waɗannan duk za su zama abokanki ne kawai idan kina raye.

* Nee chitilo todai nenostaanamma

Amma ni zan kasance tare da ke har bayan mutuwar ki. (saboda)...


* Ninnu pondetanduke puttane gumma

An haife ni ne don in so ki. (kuma)

* Nuvvu andaka pote vrudhaa ee janma

Rayuwata bata da amfani Matuƙar ba zan iya kaiwa gare ki ba.NA SADAUKAR DA WANNAN AIKI GA DUKKAN MASOYAN ASALI A KO INA SUKE A FAƊIN DUNIYA.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com


EmoticonEmoticon