Saturday, 6 July 2019

TA'ADDANCIN MASONIYYA 16

TA'ADDANCIN MASONIYYA 16


Wani Salon Yakin Sunkuru kuma da Masoniyya ke
amfani da shi wajen ganin sun cimma burin su shi ne,
kyale ko barin Ta'addanci ya wanzu a cikin jama'a, a wani lokacin ma harda daukar nauyin TA'ADDANCIN!
Hakan zai Wanzar da tsoro tare da bukatar kariya ta kai
da kai da kuma ta kasa baki daya.

 A wani bincike da
aka gudanar, an gano cewa, Kamfanonin dake hada
Miyagun Kwayoyi na daya daga cikin Kamfanonin da
suka fi kowa samun riba a Kasuwance. Kasashen
duniya da dama na nan suna ta fama wajen ganin sun
kawar da Matsalar Safarar kayan maye, kama daga cikin
gida har Izuwa sauran Kasashen ketare domin Safarar
Miyagun Kwayoyi ta addabi mutane.

 Amurka misali,
cike take da Matsalar Safarar Miyagun Kwayoyi da
sauran kayan maye, wannan na daya daga cikin dalilan
da suka sa Ta'addanci iri iri ke afkuwa a Kasar kamar
ba gobe. Saboda ganin goyon baya da kuma daurin
gindi da da Gwamnatin Amurka ta samu a wajen jama'a
don ganin an dau Tsatstsauran Mataki akan wannan
matsala ce yasa Gwamnatin yin amfani da Muggan
Makamai da kuma Miyagun Shirye Shirye don ganin an
Magance wannan Matsala a fili ko a bayyane. Sai dai
kuma Bayyanar wasu abubuwa da suka faru ta bayan
fage sun sa mutane sun fara Daurawa Gwamnatin
alamar Tambaya. Musamman dangane da irin Shirye
Shiryen da Gwamnatin ke yi akan wannan Al'amari.


Kusan kowa Yasan cewa a shekara ta alif dubu daya da
dari tara da sittin (1960) J. Edgar Hoover wanda shi ne
Ciyaman din FBI na wancan lokacin ya bar siye da siyar
da Miyagun Kwayoyi da kayan maye yana ta Wanzuwa
da gangan a tsakanin Bakaken fatar dake zaune a
kasar Amurka domin ayi musu kofar rago wajen dai
daitar da su saboda yawa da kuma karfin da ake ganin
suke Karawa a kullum. A Shekara ta alif dubu daya da
dari tara da tamanin (1980) , lokacin da Kwamunisanci
ya kusan Mamaye tsakiyar Amurka, sai ya Zamana ana
bukatar kudi Haikan domin a samar d Makaman Yakar
'Yan Kwamunisanci, don haka sai CIA suka bar siyar da
Miyagun Kwayoyi da sauran kayan maye sukai ta
Yawaita a cikin Amurka. Ta nan ne suka sami kudin
siyen wadannan Makamai da kuma kera wasun su.

Bayanai daga bakin Sanatan Amurka Jack Bloom
wanda yana daya daga cikin 'Yan Kwamitin bincike
akan wannan Lamarin ya tabbatar da faruwar hakan.

Zan ci gaba In Shaa Allah.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com


EmoticonEmoticon