Skip to main content

Posts

Showing posts from August, 2019

FASSARAR WAƘAR SUN SAATHIYA

Fassarar Waƙar Sunn Saathiyaa

* Sunan Waƙa - Sunn Saathiyaa

* Sunan Fim - ABCD – Any Body Can Dance 2

Shekarar Fita - 2013

* Haɗa Sauti - Sachin-Jigar

* Rubutawa - Mayur Puri

* Kamfani - Sony Music

* Mawaƙiya - Priya Panchal

* Mai Fassara - Haiman Khan Raees

Haan... Aaaa Haan… Haan…

* Sun Saathiya Mahiya

Saurara Masoyina, abin ƙaunata

* Barsa De Ishqa Di Syahiyaa...

Ka sa tawadar so ta koma ruwan sama

* Hoon Piya Bas Teri Main

Ya kai Masoyina, ni taka ce kai kaɗai

* Ho O... Chhule Toh Khari Mein

Idan ka taɓa ni ne kawai zan zamo mai karamci

Haan... Aaaa Haan… Haan…

* Hoon Piya Bas Teri Main

Ya kai Masoyina, ni taka ce kai kaɗai

* Ho O... Chhule Toh Khari Mein

Idan ka taɓa ni ne kawai zan zamo mai karamci

* Toh Khari Main, Khari Main, Khari Main…

A sannan ne kaɗai zan zama mai Karamci

* Sun Saathiya Mahiya

Saurara Masoyina, abin ƙaunata

* Barsa De Ishqa Di Syahiyaa...

Ka sa tawadar so ta koma ruwan sama

* Rang Jaaun, Rang Rang Jaaun Re, Haari Mein

Ya kamata inyi kwalliya, na manta da …

FASSARAR WAƘAR CHUNAR

Fassarar Wakar Chunar

Sunan Waƙa: Chunar

Sunan Fim: ABCD 2

Shekara: 2015

Haɗa Sauti: Sachin – Jigar

Rubutawa: Mayur Puri

Kamfani : Zee Music Company

Mawaƙi: Arijit Singh

Mai Fassara: Haiman Khan Raees


* O Jheena Jheena Jheena Re Udaa Gulaal

Ga Alamu Kyawawan Ƙwayoyin Zarra Sun Fara Tashi Sama

* Maai Teri Chunariya Lehraayi

Ya Ke Uwa! Mayafin Ki Na Tashi Sama

* O Jheena Jheena Jheena Re Udaa Gulaal

Ga Alamu Kyawawan Ƙwayoyin Zarra Sun Fara Tashi Sama

* Maai Teri Chunariya Lehraayi

Ya Ke Uwa! Mayafin Ki Na Tashi Sama

* Rang Teri Reet Ka, Rang Teri Preet Ka

Kalan Al'adun Ki, Kalan Soyayyar Ki

* Rang Teri Jeet Ka Hai Laayi, Laayi, Laayi

Sun Taho Tare da Kalar Nasarar Ki

* Rang Teri Reet Ka, Rang Teri Preet Ka

Kalan Al'adun Ki, Kalan Soyayyar Ki

* Maai Teri Chunariya Lehraayi

Ya Ke Uwa! Mayafin Ki Na Tashi Sama

* Jab Jab Mujhpe Hai, Utha Sawaal

 A Duk Sa'adda Aka Jeho Min Wata Tambaya

* Maai Teri Chunariya Lehraayi

Ya Ke Uwa! Mayafin Ki Na Tashi Sama

* O Jheena Jheena Jheena R…

SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 10

SARKIN SARAKAI BOOK 1. 10

GIMBIYA SHUKURA tacigaba da cewa aibazan bari ka mutu ba face na cika burina dakai ka kwantar da hankalinka ka sani cewa maigidanka sarki sahibul hairii na nan a raye bai mutuba.
Yanzun nan zan nuna maka zahiri ka gani, gama fadin haka keda wuya saitayi nuni da dan yatsanta guda izuwa jikin bango take wani irin haske ya fito daga cikin dan yatsanta ya dira a jikin bangon saiga hoton sahibul hairi kwance a sume cikin dakin nan na maridai a tsakiyar gawarwakin maridan A lokacinne ya farfado daga dogon suman da yayi ya mike ya zauna da kyar yana ta faman haki kamar zai mutu.
Ko ina a jikinsa rauni ne yai kaca kaca da jini gimbiya shukura ta dubi bawa haluf tace kaga halin da maigidanka ke ciki akwai dakuna goma sha biyu kowanne dakina dauke da masifa iri iri masifunda suke dakunan gaba sun ninka na baya yanzu ya wuce dakuna biyu saura goma a gabansa. Idan har ya wuce ta cikin ragowar dakunan goma yana raye yaci jarrabawata, don haka zan taimaka masa m…

SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 9

SARKIN SARAKAI BOOK 1. 09
DUK DA kasancewarsa bakin fata saiyaga ya zamo farar fata kuma ya juye zuwa kyakkyawar budurwa hatta gashin kansa anmaidashi dogo.
kuma baki sidik mai kyalli kirjinsa ya cika fam irin na mata ita kanta rigar da aka sanya masa irinta sarakaice abar a tsaya a kalla haluf ya dubi kansa da kyau sai yace a ransa lallai ashe inda mace aka yoni da na kasance daya daga cikin kyawawan duniya koda kuwa an barni a matsayin bakar fata koda aka kammala sauyawa haluf kamanni daga da namiji izuwa ya mace sai jamhas ya tafi dashi izuwa keken dokin gimbiye shukura tunkafin su karasa gareta ta zubo musu idanu tana murmushi gami da yiwa haluf wani irin kallo mai cike da alamomin tambaya bisa dole ya tsargu cewa lallai wannan mace nada wata babbar manufa a kansa ba tare da ya bata lokaci ba gimbiya shukura ta umarci haluf daya shiga cikin keken dokinta haluf ya waiga gaba da baya yaga gaba daya jama ar ayarin shi suke kallo cikin tsananin mamaki kawai saiya shiga cikin ke…

SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 8

SARKIN SARAKAI BOOK 1. 08

Dama tun lokacin da aka fara wannan gumurzu tsakanin sahibul Haiti da zakunan su sarku barusa Na jiyo ihunsu da gurnaninsu amma daga bisani sukaji shuru ma ana babu ihun sahibul Haiti kuma babu Na zakunan Al,amarinda ya baiwa sarki barusa mamaki kenan kawai sai ya dubi wadansu dakaru dubu uku tace maza kuje cikin wannan dakin Kasan su gano masa abindake faruwa shinn zakunann nan sunn kashee sarki sahibul hairii ko kuwa shine yakarkashesu. Yayinda dakaru sukaji wannan umarni Na sarki barusa sai hankalinsu ya dugunnzuma suka tsaya suka yi charko charko suna kallon junansu aka rasa Wanda zai wuce gaba Ba wani dalili bane yasa wadannann dakaru suka kasa zuwa wqnnan daki ba sai saboda bala,in dake cikinsa Shidai wannan wuri an tanadeshine musamman son hallaka iron mutanan da aka yankewa hukunncin kisa hakika sarrki barusaa karyaa yayiwa sahibull hairi cewaa a wannan bangareen gatarinn sihirinn yakee A cikin wannan gidaan kasa India sarki sahibul hairii ya fadaa …

SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 7

SARKIN SARAKAI BOOK 1. 07
Ana cikin tsakiyar wannan haline akaga sarkin kofa ya shigo a guje yana ta faman haki Al amarinda ya dugunzuma hankalin kowa kenan akayi tsit kamar mutuwa ta gifta kowa ya kame kamar babu mai rai a wajen Da zuwan sarkin kofa saiya fadi gaban sarki yayi gaisuwa sannan yace ya shugabana kayi sani cewa yanzu haka jarumi uban jarumai ya shigo kasar nan ya banke kofar gari da karfin sadaukantakarsa kuma ya kashe dukkanin abokan aikina yana nan tafe izuwa nan fadarka don biyan wata bukata tasa ni kaina ya kyaleni ne kawai don nazo na isar da sako' cikin tsananin fushi sarki BARUSA ya dakawa sarkin fada tsawa wacce tasa dukkanin jamar wajan suka fadi kasa suka kwanta da ruf da ciki don tsananin razana sarki barusa ya kasance lafcecen katon mutum mai surar mutanen farko gashi dogo kuma gashi kakkaura duk jikinsa a murde yake ya tara jijiya da kwanji komai tsawon mutum sarki barusa na iya dora abinci a kansa yaci yana da jajayen idanuwa ababan tsoro yanada waw…

SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 6

SARKIN SARAKAI BOOK 1. 06
suka jada baya suka tarwatse koda naga hanya ta samu saina ruga da gudu ina gudun ina saransu kafin abokan gaba su ankara nayi nisa.
Ai kuwa sai suka biyoni cikin matsanancin gudu amma na gaba yai gaba na baya sai labari lokacin da nake wannan gudu ina yinsane cikin takaici domin a rayuwata ban taba guduwa ba daga filin yaki yau gashi bala'i yakai har gudu ya zamadole a gareni inba haka ba kuwa na rasa rayuwata shidai wannan yaki muna yinsa ne a wani daji wanda ake kira BAHARUL SHARUL dajin na dauke da manyan tsaunuka da manyan koguna inda ruwa ke bulbulowa daga cikin duwatsu yana kwaranya yana gudu sa adda abokan gaba suka tasoni a gaba na ga babu matsera kawai saina durfafi wani katon tsauni wanda nidai a rayuwata ban taba ganin tsauni mai tsawonsa ba ina kyautata zaton cewa duk duniya babu tsauni mai fadi da tsawonsa nan fa naci gaba da gudu suna biye dani har muka isa can saman tsaunin muka kureshi koda na leqo kasan tsaunin na ga zurfinsa sai …

SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 5

SARKIN SARAKAI BOOK 1. 05
Duk da kasancewarsa ba tsohoba jama a sun dade suna mamakin dalilin da yasa yake dogara sanda a duk sa adda yake tafiya alhali bai tsufa ba har Abu hakim ya rasu babu wanda yasan dalilin da yasa yake amfani da wannan sandan Lokacinda cutar Ajali ta kama abu hakim a wannan lokaci tuni matarsa ta dade da rasuwa kuma ta bar masa ya guda daya wato shulaiba saboda aminci da kaunar dake tsakanin sarki sahibul hairi da abu hakim saiyasa aka kawo shi cikin gidan sarauta ya zamana cewa shi da kansa yake jinyarsa sannan kuma yasa aka dinga kula da shulaiba tamkar yar cikinsa bayan kamar wata hudu da faruwar haka sai ciow ya kara tsanani wani yammaci sarki sahibul hairi da shulaiba na zaune a gaban abu hakim sun zuba masa ido suna kwalla sbd ganin halinda yake ciki sai abu hakim ya dubi sarki sahibul hairi yayi murmushi sannan ya dubi shulaiba ya fashe da kuka koda ganin haka sai hankalin sarki sahibul hairi ya dugunzuma yace yakai aminin mahaifina shin zaka iya gaya…

SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 4

SARKIN SARAKAI BOOK 1. 04

Shugaban yan fashin ya sake rugawa da gudu kan sarki sahibul hairi da nufin ya sake kai masa sara shikuwa sai ya daka tsalle sama ya doki kirjinsa da kafa guda karfin dukanne yasa shugaban kartin yai sama ya fado kasa ya baje kamar an shanya tsumma koda ganin haka saigaba dayan dakarun nan suka zare maka mansu sukayi kan sarki sahibul hairi babu wanda ya kula da batun bawa Haluf wanda ya bude baki yana kallon abinda ke faruwa cikin tsananin mamaki nanfa karti da sarki sahibul hairi suka kacame da azababben yaki suna kai masa sara da suka yana gocewa amma duk wanda ya nausa saikaga ya zube kasa sumamme wani lokacin kuma in ya kama hannun mutum ko kafarsa sai dai kaji ya karya basss! Tamkar ya karya silin kara babu abinda zai baiwa mutum mamaki face tsananin zafin naman sarki sahibul hairi da iya kauciya da zilliya sai da aka shafe kusan rabin sa a yana turmutsa yan fashin nan amma baiyi tunanin zare makami ba da makaman nasu suka dinga sarar junansu saida yac…

SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 3

SARKIN SARAKAI BOOK 1. 3
KODA SARKI YAJI HAKA saiyayi murmushi yace yakai haluf ka sani cewa muddin kana tare dani babu wani abu mai rai da ya isa ya cutar dakai abinda nake so dakai shine ka kwance guzurinmu ka dauka abinci mu ci tare cikin tsananin mamaki bawa haluf ya dubi sarki yace haba ranka ya dade ina ni ina cin abinci tare dakai? Ai fiye da shekaru goma baya ma sa adda na fara yimaka bauta ban taba samun kusanci da kaiba kamar yanzu sarki sahibul hairi yayi murmushi a karo na biyu yace yakai haluf ka sani cewa wannan tafiya da ka samu ikonyi tare dani ba karamar matsayi ta janyo maka ba don haka ina so ka yaye dukkanin wani hijabi dake tsakaninmu na bawa da maigidansa ka dauka cewa tare da abokinka ne in kuwa kana sabawa hakan zan umarceka da komawa birnin misra in yaso nayi tafiyata ni kadai koda jin haka sai bawa haluf ya nutsu cikin hanzari ya bude guzuri ya fidda abinci ya zuba a faranti sannan ya dauko salkar ruwa ya tsiyaya a cikin kofi guda ya ajiye a gaban sarki, s…

SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 2

SARKIN SARAKAI Book 1. 02
Book 1
KODA jin wannan batu sai boka Hadimun asur ya tuntsure da dariya sannan yace ai kowa a gidansa sarki ne ina tabbatar maka da cewa indai kazo da Alfila cikin wannan gida nawa babu wanda ya isa ya tafi da ita face da yarda ta
da wannan kalmomi nake maka sallama dan haka sai ka tafi kayi shirin zuwa fadar sarki Barusa na birnin Askandariya don dauko gatarin sihiri zan kasance mai sauraronka a nan
kuma ina yi maka tuni da cewa shima wannan gatarin sihiri karka barshi a can fadar boka Shamzubul azwas lallai ka taho da shi nan gareni tare da yarinya Alfila
koda gama fadin wannan batu sai boka hadimul asur ya sake dafa kafadar sarki sahibul hairi nan take sarki sahibul hairi ya tsinci kansa a wajen gidan boka hadimul asur kuma a kasan dogon dutsen nan kawai sai sarki sahibul hairi ya juya ya tafi ya nufi cikin birnin misra yana mai tafiya da sauri don ya isa gida kafin fitowar Alfijir
kashe gari da sassafe sarki sahibul hairi ya tura aka kirawo mas…

SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 1

SARKIN SARAKAI BOOK 1. 01 A WANI ZAMANI can baya mai tsawo da ya shude anyi wani mashahurin sarki a birnin misra mai suna SAHIBUL HAIRI Shidai wannan sarki ba a tabayin talakan sarki ba kamarsa a duniya saboda yawan kyautarsa da taimakon talakawa akarshe da talauci ya isheshi sai ya shirya ya tafi wajen wani boka AWANI DAJI WAI shi HAZARIL DALFUR  a yammacin misra Daga cikin birnin misra zuwa wurin wannan boka tafiya ce ta s'a biyu kacal sarki Sahibul hairi bai tafi wannan daji ba sai da dare ya raba kuma saida ya saci jiki yayi bad da kama ya tafi a kasa ba tare da ya hau doki ba ko rakumi Bayan tafiyar sa'a biyu ne dai dai ya iso kofar gidan boka HADIMUL ASUR Wanda aka ginashi da zallan itatuwa bisa kan wani godon dutse faffada mai tsawon gaske lokacin da sarki Sahibul hairi yazo gaban dutsen sai ya tsaya yana tunanin hanyar da zaibi ya hau kan dutsen ba zato ba tsammani sai yaga boka Hadimul Asur ya bayyana a gabansa yana mai murmushi hadimul asur yayi sujjada ga …