FALALAR ZIYARA DA SON 'YAN UWA

FALALAR ZIYARAR YAN UWA DA KUMA SAN JUNA SABODA ALLAH.

Zayara da sadar da zuminci da yn soyayya dan Allah,yana cikin mafi girman aiyukan alkhairi da suke samu soyuwa da matsayi awajan Allah, shiyasa Annabi s.a.w ya kwadaitar damu yinsu agurare masu yawa kuma shima yayi hakan a aikace.

1-Manzon Allah s.a.w yace:
(Lallai Allah zai ce a ranar Alqiyama:Ina masu yin Soyayya dan girmana "ma'ana masu yin soyayya dan Allah dan girman Allah" a yau zan sanya su a inuwata ranar da babu wata Inuwa sai Inuwata).
@صحيح مسلم

2-Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Abubuwa guda ukku wanda ya samesu ya sami dandanon zakin Imani,
-Allah da Manzonsa su sukafi soyuwa agare shi fiye da dukkan komai.
-Kuma yana son bawane badan komai ba sai dan Allah.
-Kuma yana kyamata a koma cikin kafirci bayan Allah ya tsamoshi daga cikinsa kamar yadda yake kyamatar a sanya shi wuta).
@صحيح البخاري - رقم: (21)

3-Annabi s.a.w yana cewa:
(Lallai wani mutum ya tafi ziyarar dan uwansa zuwa wani gari,sai Allah ya tura masa Mala'ika akan hanyarsa,sai Mala'inkan ya tambayesa ina zakaje?? Sai yace: zanje ziyarar dan uwana a wancan gari,sai Mala'ikan yace:Shin zakajene dan kwadayin wani abu da kakeso ya baka?sai yace: A'a babu abinda zai kaini zuwa wajan sai dan ina sonsa dan Allah kadai.sai Mala'ikan yace da shi: Ni dan Sakon Allah ne,hakika Allah yana sanka kamar yadda kake son dan uwanka dashi).
@صحيح مسلم - رقم: (2567)

4- 3-Annabi s.a.w yana cewa:
(Imanin dayanku baya cika har sai ya soma dan uwansa irin abinda yake soma kansa).
@صحيح البخاري - رقم: (13-45)

5-Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Duk wanda yaje duba marar lafiya ko ya kaiwa dan uwansa ziyara dan Allah,sai wani mai kira yayi kira yace:
Ka dace ka rabauta kuma an tanada maka mazauni acikin aljanna) حسنه الألباني ف صحيح الترمذی @

6-Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Mutumin da ya kai ziyara ga dan uwansa wani gari dan Allah,yana samun aljanna).
@حسنه الألباني في صحيح الجامع - رقم: (2604)

7-Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Allah madaukakin sarki yana fada:
Soyayyata ta wajaba ga masoya guda biyu da sukeyin soyayya sabodani,da masu jama da junansu sabodani,...... da kuma masu ziyartar junansu sabodani).
@صححه الألباني في
📚 صحيح الجامع - رقم: (4331)

8-Annabi s.a.w yana cewa:
(Lallai mafi cikar samun matsayi a musulinci shine mutum yayi soyayya dan Allah kuma yayi kiyayya saboda Allah).
@الألباني في صحيح الجامع - رقم: (2009)

Allah ka bamu ikon yi soyayya da kuma ziyarar yan uwanmu da abokin arziki da sauran musulmai dan Allah.
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive