FASSARAR WAƘAR SLOW MOTION


Fassarar Waƙar Slow Motion


Waƙa: Slow Motion
Fim: Bharat
Sauti: Meghdeep Bose
Rubutawa: Irshad Kamil
Kamfani : T-Series
Mawaƙa: Vishal & Shekhar tare da Nakash Aziz, Shreya Ghoshal
Fassarawa: Haiman Khan Raees

JAN HANKALI: wannan waƙa an yi ta ne da salon barkwanci dangane da abinda ya shafi shirin fim, don haka kada ku yi mamaki ko ku ruɗe in kun ji wasu kalmomin. Ina da Tabbacin Cewa zaku fahimci inda zancen ya nufa. Sannan zaku ga ina saka - da kuma +, to shi - yana matsayin Namiji ne Yayinda + kuma yake matsayin mace. In kuma na saka su duka, kenan mace da namijin ne suka faɗi hakan a tare.


- * Aaj Ki Shaam Lage Picture Ka Scene Koi

Yammacin yau yayi kama da wata fitowa a cikin Fim

- * Picture Ka Scene Koi, Picture Ka Scene Koi...

Kamar wata fitowa a cikin Fim, kamar wata fitowa a cikin Fim

- * Main Hero Jaisa Aur Tu Heroine Koi

Ni tamkar Jarumi ne ke kuma tamkar Jaruma

- * Tu Heroine Koi, Tu Heroine Koi...

Ke tamkar Jaruma ce, ke tamkar Jaruma ce

- * Story Kahaan Kahaan
 Se, Oh Ghoom-Ghaam Ke, Aa Gayi Motion Mein

Labarin ya daɗe yana yawo kuma yau gashi zai fara motsi

- * Aaja Doob Jaaun Teri Aankhon Ke Ocean Mein

Ina so in Dulmiye a cikin kogin idanunKi

- * Slow Motion Mein...

A hankali A hankali

- * Aaja Doob Jaaun Teri Aankhon Ke Ocean Mein

Ina so in Dulmiye a cikin kogin idanunKi

- * Slow Motion Mein...

A hankali A hankali

 Haan..

+ * Aaj Ki Shaam Lage Picture Ka Scene Koi

Yammacin yau yayi kama da wata fitowa a cikin Fim

+ * Picture Ka Scene Koi, Picture Ka Scene Koi...

Kamar wata fitowa a cikin Fim, kamar wata fitowa a cikin Fim

Haan…

+ * Main Bhi Rangeen Lagun, Tu Bhi Shauqeen Koi

Na zamo abar sha'awa kai kuma mai goyon baya.

+ * Tu Bhi Shauqeen Koi, Tu Bhi Shauqeen Koi...

Kayi kama da mai goyon baya, kayi kama da mai goyon baya

+ * Poori Party Hai Aaj Mood Mein, Aur Apne Emotion Mein...

Kowa sai shagali yake ana Nishaɗi Yayinda aka shiga yanayin caskaɗewa

+- * Aaja Doob Jaaun Teri Aankhon Ke Ocean Mein

Ina so in Dulmiye a cikin kogin idanunKi

+- * Slow Motion Mein...

A hankali A hankali

+- * Aaja Doob Jaaun Teri Aankhon Ke Ocean Mein

Ina so in Dulmiye a cikin kogin idanunKi

+- * Slow Motion Mein...

A hankali A hankali

- * Ring Leke Bade Waali Ek Din

Watarana zan siya miki zoben Lu'ulu'u

Hey Hey Hey Hey!

- * Tujhe Maine Kar Lena Hai Win

Ina so inyi nasara a kan ki

Hey Hey Hey Hey!

-* Ring Leke Bade Waali Ek Din

Watarana zan siya miki babban zobe

- * Tujhe Maine Kar Lena Hai Win

Ina so inyi nasara a kan ki

-* Phir Shaadi Hogi, Babies Honge, Badlenge Hum Napkin

Daga nan sai muyi aure, zamu haifi yara harma mu canza musu adiko a tare

+* Ab Ho Jaane Do Ji Meeting,

Da fari dai, bari ganin ya tabbata

+* Phir Hogi Humari Setting

Daga nan ne soyayyar mu zata fara

+ Phir Mummy Papa Ko Bolenge, Karo Humaari Wedding

A sannan ne zamu faɗawa iyayen mu a ɗaura mana aure.

+* Hoga Hill Pe Honeymoon

Yawan shakatawar bayan auran mu a saman tsibiri za'a yi

+* Delay Ismein Nahi Soon

Ba wani Jinkiri dangane da hakan

+* Din Thode Bache Hain, Relationship Ke Promotion Mein…

Ranaku kaɗan kawai suka rage don tallata tarayyar mu

+ Haan Aaja Aaja Aaja...

Maza Maza+- * Aaja Doob Jaaun Teri Aankhon Ke Ocean Mein

Ina so in Dulmiye a cikin kogin idanunKi

+- * Slow Motion Mein...

A hankali A hankali


+- * Aaja Doob Jaaun Teri Aankhon Ke Ocean Mein

Ina so in Dulmiye a cikin kogin idanunKi

+- * Slow Motion Mein...

A hankali A hankali

+- Slow Motion Mein…

A hankali A hankali

Hey Hey! Hey Hey! Hey Hey!

- Pyaar Ho To Aata Hai Maza Nahi Shoshan Mein…

Annushuwa na Samuwa ne kawai in da soyayya, babu jin daɗi a mugunta

- Slow Motion Mein…

A hankali A hankali+- * Aaja Doob Jaaun Teri Aankhon Ke Ocean Mein

Ina so in Dulmiye a cikin kogin idanunKi

+- * Slow Motion Mein...

A hankali A hankali


<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive