SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 1

 SARKIN SARAKAI BOOK 1. 01
A WANI ZAMANI can baya mai tsawo da ya shude anyi wani mashahurin sarki a birnin misra mai suna SAHIBUL HAIRI
Shidai wannan sarki ba a tabayin talakan sarki ba kamarsa a duniya saboda yawan kyautarsa da taimakon talakawa
akarshe da talauci ya isheshi sai ya shirya ya tafi wajen wani boka AWANI DAJI WAI shi HAZARIL DALFUR 
a yammacin misra Daga cikin birnin misra zuwa wurin wannan boka tafiya ce ta s'a biyu kacal sarki Sahibul hairi
bai tafi wannan daji ba sai da dare ya raba kuma saida ya saci jiki yayi bad da kama ya tafi a kasa ba tare da ya hau doki ba ko rakumi
Bayan tafiyar sa'a biyu ne dai dai ya iso kofar gidan boka HADIMUL ASUR
Wanda aka ginashi da zallan itatuwa bisa kan wani godon dutse faffada mai tsawon gaske
lokacin da sarki Sahibul hairi yazo gaban dutsen sai ya tsaya yana tunanin hanyar da zaibi ya hau kan dutsen ba zato ba tsammani sai yaga boka Hadimul Asur ya bayyana a gabansa yana mai murmushi
hadimul asur yayi sujjada ga sarki Sahibul hairi yace Lale marhaban da SARKIN SARAKAI na duniya baki daya kaine sarkin da zaiyi arziki da daukakar da ba a taba yin kamar su ba nan gaba idan har ka sami nasarar samo abubuwan da zan gaya maka yanzu
muje zuwa cikin turakata domin mu zanta a tsanake kafin sarki sahibul hairi yace wani abu tuni boka Hadimun Asur ya dafa kafadarsa take suka bace bat sai gashi sun
bayyana a cikin turakar boka hadimul asur Wadda akayi mata ado da fatun manyan dabbobin dawa da kwarangwal din kawunansu
nan take hadimul asur ya yiwa sarki nuni da wata shimfida mai taushi shi kuwa sai yaje ya zauna a kai zamansa keda wuya saiga wata zabgegiyar budurwa ta fito daga cikin
wani daki dauke da tambulan na ruwan inibi da kofin zinare a hannu
tun da sarki sahibul hairi yazo duniya bai taba ganin budurwa mai kuruciya da kyau kamarta ba duk da cewa sarki sahibul hairi yayi alkawarin cewa ba zai taba yin aure ba saida yaji yayi sha awar wannan budurwa
budurwar tazo gaban sarki ta tsugunna sannan ta zuba ruwan inibi a cikin kofin zinare ta mikawa sarki ya karba kofin yana mai kura mata ido da murmushi
ita kuwa saita sunkuyar da kanta ta fice daga cikin turakar fitarta keda wuya sai sarki ya bude baki da nufin yayi magana amma sai boka hadimul asur yai masa nuni da yayi shiru
yace dashi wannan 'yata ce ita kadai gareni a duniya kuma babu abinda na ke so sama da ita ka bar batunta yanzu zamuyi shi nan gaba
ya kai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa tuni na san abindake tafe dakai kuma kamar yadda na gaya maka cewa bukata zata biya idan harka sami nasarar samo abinda na umarceka da samowa
Sa'adda boka hadimul asur yazo nan a zancensa sai sarki ya dubeshi cikin kokwanto da mamaki yace yakai wannan boka hakika nayi mamakin jin yadda kake bayani tamkar kasan sirrin xuciyata
amma duk da haka ina so ka fada mini ainihin bukatar da nazo da ita gareka domin na kara samun natsuwa dakai
koda jin wannan batu sai boka hadimul Asur ya tuntsure da dariya sannan yace yakai wannan sarki na gani cewa kwanaki bakwai da suka shude
sarakai bakwai sun aiko maka da wasika A cikin wasikar sunyi bayanin cewa tunda ka zamo almajiri zasu rinka taimaka da sadaka domin kada ka dinga zubar da kimar sarakai a duniya kuma sunyi maka gorin baka da lafiya tunda baka da aure
lokacin da ka sami wannan sako saibakin ciki ya turnuke ka har ka shiga cikin turakarka kayita shara kuka a boye ba wanda ya sani bayan kayi kukanka ka gaji ne kayi rantsuwa da girman karagar mulkinka cewa 
saikafi dukkan sarakunan duniya mulki dukiya da mata to ka sani cewa idan har kana so ka sami wannan matsayi dolene ka nemo wadansu 'yan mata guda uku ka aura mace ta farko utace 'ya ga wata mace wadda duk duniya babu mai iliminta yanzu ita dai wannan mata tana jin yare guda dari ba daya haka kuma ta kasance malama a cikin addinai guda dari ba daya shekarunta dari ba daya cif-cif kuma ta boye kanta tare da 'yarta a inda babu wanda ya sani a halin yanzu in banda wannan 'ya tata duk duniya babu mai iliminta
mace ta biyu babu wanda yafi mahaifinta yawo a duniya mahaifinta bai mutuba saida ya ziyarci kasashe dari tara da casa'in da tara inda ya cika dubu da ya sami matsayin da kake son samu yanxu 'yar wannan mutum yanzu haka ta ziyarci kasashe dari takwas da sittin a cikin shekaru bayar kacal baisa taimakon wani Aljani waishi KALBURA a matsayin abin hawanta
wannan budurwa ta lashi takobin cewa saita ziyarci kasashe dubu dan cika burin mahaifinta wanda ajali ya hanashi cikawa duk kasar data ziyarta saita debo irin kasar da aka gina gidan farko a nahiyar idan ta kammala tara kasar guda dubu shine zata sami wannan daukakar
budurwata uku itace 'yaga wani mutum wanda yafi kowa sanin tarihin sarakunan duniya da mulkinsu itama wannan budurwa mahaifinta ya mutu kuma ta gajeshi A halin ynx itace kadai tasan adadin sarakan duniya da tarihin mulkinsu tun daga farko har karshe
wannan budurwa kwakwalwarta kamar littafi yake domin tarihin a rubuce yake a kanta zata iya baka lbrn shekara dari baya......
YAKAI WANNAN SARKI kayi sani cewa idan har kana son kafi dukkanin sarakunan duniya mulki dukiya dolene ka nemo wadannan yan mata uku ka auresu
sa adda boka Hadimun Asur yazo nan a zancensa sai yayi shiru ya kurawa sarki idanuwa kawai cikin tsananin damuwa sarki Sahibul hairi yace yanzu a ina zan ga wadannan yan mata kuma waye zai iya samo minsu
boka Hadimul Asur yace tambaya ta farko tafi karfina domin banida amsarta amma tambaya ta biyu itace a halin yanzu duk duniya babu wanda zai iya samo ma wadannan yan mata face wani jarumi saurayi kuma mafarauci wanda ake kira SADAUKI AWAISU
sadauki awaisu na zaune a can nahiyar kasar Hindu a cikin wani birni da ake kira HALRALI awaisu ya kasance matsafin gaske kuma yana da wani Aljani wanda ake kira SARMUDA
aljani sarmuda ya kasance matashi mai karfin gaske kuma a cuk cikin jama ar aljanun duniya babu kamar sa a fagen karfin gudu da sauri yayin tafiya a sararin sama Aljani KALBURA ne kadai ke iya yin rabin tafiyar sa a gudu
sadauki Awaisu bazai taba yarda ya samo maka wadannan 'yan mata uku ba face ka samo masa 'yarsa guda daya wata karamar yarinya yar shekara bakwai ALFILA 
WACCE aka saceta a shekaru uku da suka gabata babu irin neman da sadauki awaisu bai yiwa wannan ya tasa ba amma ya rasa inda take da yayi bincike a cikin tsafinsa sai ya gano cewa yarinyar na can hannun wani mashahurin bokan Aljanu ne a cikin wani gida dake tsakiyar tsibirin tekun BAHAR ZAILUS
sunan wannan boka SHAMZUBUL AZWAS ba komai bane yasa bokan ya sace Alfila ba sai don ya kwashe sirrikan tsafin dake jikinta guda dari tara domin shi yana da guda dari nasa da kansa idan ya hada da wannan sirrika zai zamo babu wani matsafi kamarsa a doron kasa 
Shamzubul Azwas ba zai iya kwashe wadannan sirrikan tsafin ba daga jikin Alfila har sai izuwa tsawon shekara biyar A halin yanzu saura shekara biyu kawai ya kammala debe sirrikan tsafin su kuwa sirrikan tsafin ainihinsu na Sadauki awaisu ne duk duniya babu mai irinsu face shi
bayan rasuwar mahaifiyar Alfila da shekara daya sadauki awaisu ya zuba wadannan sirrikan tsafi guda dari tara a cikin jikin Alfila domin burinsa a duniya shine ta gajeshi a fagen tsafi
lokacin da sadauki awaisu ya gano inda aka boye masa 'yarsa sai yayi shiri ya hau kan aljani Sarmula suka durfafi tsuburin bahar zallus daga birnin Hindu zuwa bahar zallus tafiyace ta shekara goma sha daya akan rakumi ko doki amma cikin wata uku aljani sarmuda ya isa can
koda suka sauka a kofar gidan boka shamzubul azwas sai suka iske cewa gidan an ginashi ne da zallan bakin karfe kuma bashi da kofa ko taga wacce za a iya bi a shiga cikinta kuma koda mutun ya shiga gidan ba zai iya kashe dakarun Aljanun dake ciki ba guda dubu dari wadanda suka kasance manyan zakwakuran mayaka masutaurin kai da dakakkiyar zuciya
nan da nan sadauki awaisu da aljani sarmuda sukayi ta kokarin shiga wannan gida ta hanyar amfani da karfin sihiri da kyar suka gano wata kofa guda daya wacce akayita da karfen lu u lu u nan take suka fara kokarin bude ta da karfin tsiya domin shiga
amma sai abu ya faskara saida suka kwana uku a wajan suna saran kofar da makamai iri iri amma kofar taki buduwa
tabbas inda kofar ta bude to sai sunsami nasarar shiga gidan kuma sai sun kashe dukkan dakarun ciki sun hallaka boka shamzubul azwas sannan su dauki Yarinya alfila
Yakai wannan sarki kayi sani cewa bincike ya nuna mini cewa akwai wani gatari guda daya a duniya wanda zai iya sare wannan kofa ta gidan boka shamzubul azwas shidai wannan gatari ya kasance mai girma da nauyin tsiya domin sai karti sittin sun taru suke iya daga shi sama kuma anyi shine da zallan lu'u lu'u bincike ya nuna mini cewa kaikadaine mutumin da zai iya sarrafa wannan gatari sbd sadaukantakarka tafi ta kowa a wannan zamani
A yanzu haka wannan gatari na can a ajiye a cikin fadar sarki BARUSA na birnin ASKANDARIYYA cikin mummunan tsaro Ainihin wannan gatari na sarkin farko ne na kasar don kowanne sarki zuwa yake ya tarar dashi a matsayin abin gado kai sbd ganin darajar gatarin ma har takai cewa mutanen kasar sun camfashi a matsayin indai yana nan ajiye a cikin gidan sarautarsu to har abada ba za a cisu da yaki ba bisa wannan dalili ne kullum dare da rana aka zuba dakaru dubu uku suke gadinsa
wadannan dakaru dubu uku sun kasance karfafa mayakan kwarai wadanda ake takama dasu a birnin Askandariyya yakai wannan sarki ya zama wajibi a gareka kayi shirin yaki ka tafi izuwa birnin domin ka dakko wannan gatari na sihiri ka dawo gareni sannan na kimtsaka ka tafi izuwa fadar boka shamzubul azwas don ka dauki Alfila yar sadauki awaisu idan ka daukota saikazo da ita nan mu ajiyeta har sai yaje ya samo mana wadannan yan mata uku wadanda sune bukataka zata biya
sa adda boka hadimul Asur yazo nan a zancensa sai sarki sahibul hairi yace to yanzu idan sadauki Awaisu yazo yaga 'yarsa baka tunanin cewa zai iya karbeta da karfin tsiya ba tare da ya biya muna bukatarmu ba?......
Zan Cigaba Insha Allah

Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive