SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 2

 SARKIN SARAKAI Book 1. 02
Book 1
KODA jin wannan batu sai boka Hadimun asur ya tuntsure da dariya sannan yace ai kowa a gidansa sarki ne ina tabbatar maka da cewa indai kazo da Alfila cikin wannan gida nawa babu wanda ya isa ya tafi da ita face da yarda ta
da wannan kalmomi nake maka sallama dan haka sai ka tafi kayi shirin zuwa fadar sarki Barusa na birnin Askandariya don dauko gatarin sihiri zan kasance mai sauraronka a nan
kuma ina yi maka tuni da cewa shima wannan gatarin sihiri karka barshi a can fadar boka Shamzubul azwas lallai ka taho da shi nan gareni tare da yarinya Alfila
koda gama fadin wannan batu sai boka hadimul asur ya sake dafa kafadar sarki sahibul hairi nan take sarki sahibul hairi ya tsinci kansa a wajen gidan boka hadimul asur kuma a kasan dogon dutsen nan kawai sai sarki sahibul hairi ya juya ya tafi ya nufi cikin birnin misra yana mai tafiya da sauri don ya isa gida kafin fitowar Alfijir
kashe gari da sassafe sarki sahibul hairi ya tura aka kirawo masa dukkanin fadawaLabarai farko sunyi tsammanin cewa wani abu zai nema a hannunsu don haka sai wadannsu suka noke suka ki zuwa da wuri suna karyar fadin cewa suna nan tafe
koda ganin haka sai sarki ya fusata yace a gaya musu cewa duk wanda baizo ba a yanzu a bakacin ransa koda jin haka sai yan majalisar suka rude nan da nan suka iso fadar suna masu rawar jiki bayan sun hallara sai kowa ya nutsu yayi shiru baka jin motsin komai a dakin face sautin numfashi
daga can sai sarki sahibul hairi ya mike tsaye fuskarsa a murtuke babu alamar fara a Al amarin da ya kara firgita fadawan ke nan gaba daya suka sunkuyar da kawunansu kasa don gudun fushinsa sarki yace dasu
''yaku yan majalisa kuyi sani cewa raina ya baci bisa halaiyarku ta kina da guduna sbd halin da na shiga na babu wannan ya nuna min cewa babu soyayyar gaskiya a tsakanina daku kuma kuna tsoron kada ku talauce ne shiyasa kuke guduna? To ku sani cewa daga yau bana bukatarkomai daga hannun ku kuma nayi muku Alkawari cewa ba zan sake neman komai ba a wajenku
kuyi sani cewa ba wani abu bane yasa na taraku a nan ba sai don na gaya muku cewa zan tafi yaki izuwa birnin Askandariyya domin dauko gatarin nan na sihiri wanda suka baiwa kyakkyawan tsaro zanyi amfani da wannan gatari ne don kawo karshen wannan talauci da nake famda dashi kunga kuwa idan na rabu da talauci kuma kun huta da fargabar komai
kuyi sani cewa bayan na sami wannan gatarin kuma zan wuce izuwa tsibirin zallus inda boka shamzubul azwas yake domin na dauko wata karamar yarinya wacce ya saceta shekaru uku da suka gabata wadda ta kasance yaga babban matsafi sadauki Awasisu
a kalla zan sami shekara guda kafin na kammala wannan tafiya na dawo sabo da haka yanzu ina son ku zabi wanda zai rike mini kasa daga cikinku kafin na dawo koda jin haka sai gaba dayan suka kidime suka haukace nace kowa na cewa shine zai rike kasar shikuwa sarki sahibul hairi sai yai shiru ya zuba musu idanu kawai yana nazarinsu ya fuskanci cewa gaba dayansu babu abin yarda a gareshi
yayi da sarki yaga sun kaure da gardama sai ya daka musu tsawa nan take suka kame kamar gumaka kowa ya yi tsit sarki ya kira wani barde dake can kofar shigowa dakin da suke ciki barden ya rugo da gudu ya zube kasa gabansa sarki yace da barden maza kaje dakin ajiya ka debo mini akwatunan karfe iya adadin fadawan nan nawa
barden ya mike da sauri yace an gama ranka ya dade koda ficewar barden sai cikin yan majalisar nan ya duri ruwa domin a zatonda suke shi ne sarki zaisa su a cikin akwatunan ne ya kulle domin akwatunan sn kasance darma darma baisa wannan daliline jikinsu ya kama kyarma gaba daya kamar ace kyat su fita da gudu
barden ya dinga shigowa da akwatunan daya bayan daya yana saukewa da jerawa a waje guda har saida ya gama tara guda taran koda ya gama ajiye akwatunan sai sarki ya dubi yan majalisar yace gaba dayanku ku fita su rufe kofar kuma su tsaya a bakin kofar cikin rawar jiki suka bi umarni fitarsu keda wuya sai sarki ya dauki kwagirinsa na sarauta ya saka a cikin daya daga cikin akwatunan bayan ya bame akwatun saiya yiwa yan majalisar nan izini su shigo cikin hanzari suka shigo suka tsaitsaya a jere waje guda sarki ya dubesu a natse yace
yaku yan majalisa kuyi sani cewa kwagirin sarautata na cikin daya daga cikin akwatunan nan guda tara daya bayan daya zakuzo ku zabi akwati dai dai ku budeta wanda ya dauko kwagirin sarautata shine zai rike mun kasata har na dawo daga doguwar tafiya
koda jin wannan batu sai gabadayansu hankalinsu ya dugunzuma wazirin Akiyanu ya dubi sarki sahibul hairi yace ya shugabana ni a tunanina bai kamata ayi haka ba ni da nake a matsayin wazirinka nine na dace na rike maka kasa
koda jin haka sai sarki ya yi murmushi yace na sani cewa ka dace ka wakilceni to amma fa ka sani cewa ban taba yin tafiya irin wannan ba kuma gaba dayanku babu wanda hankalina ya kwanta da shi don haka kawai sa'a naga mai rabo dole ne abi wannan tsari nawa....
KAFIN WAZIRI ya kara cewa wani abu tuni Sarki sahibul hairi ya dubi yan majalisar na farko ya umarceshi da yaje kan akwatunan ya zaba hannayensa na karkarwa sai ya tsaya ya kasa zabar akwatin da zai bude sai da sarki ya daka masa tsawa sannan yaje ya bude akwatin farko
aikuwa yana budewa sai yaga wayan babu komai ciki koda ganin haka sai kwalla ta ciko idanun dan majalisar ya fara kukan zuci don takaicin rashin samun nasara daya bayan daya suka rinka bude akwatunan har akazo kan mutum na tara shine wanda na kashe wanda ake kira AMINUL HAS
Aminul has ya kasance shine galadiman sarki kuma duk a cikin yan majalisar shine wanda baya gajiya da yiwa sarki hidima duk sa adda sarki ya aika masa da bukatar abinci ko sutura take yake aiko masa har saida takai cewa sarki sahibul hairi ya kure Aminul has ya talautar dashi duk ya siyar da kadarorinsa
wani lokacin ma idan aka turo da bukatar sarki sai yayi rance sannan ya aika wajan yaransa da suke tafiya fatauci a kawo masa kudi ya biya bashin gaba daya yan majalisar mutum takwas babu wanda ya sami nasarar dauko kwagirin sarautar kuma duk su takwas din babu wanda bai zub da hawaye ba da fargaba lokacin da ya zo bude akwatinshi
Shikuwa Aminul has cikin nutsuwa ba da fargabar komai ba ya zo ya bude akwatin ta karshe wadda ba a bude ba bisa mamaki sai shima yaga babu komai a cikin akwatin
yan majalisar suka dubi sarki sahibul hairi waziri Akiyanu yace ranka ya dade yazaka yaudaremu kace akwai kwagirinka a cikin daya daga cikin akwatunan nan alhali babu?
Koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya bushe da dariya sannan yace hakika na yaudareku amma ba dan komai nayi hakaba sai don na gane wanda ke kaunata a tsakaninku gaba dayanku nan kun sani cewa wannan tafiya da zanyi mai hadarin gaske ce kuma na tabbata cewa duk kuna ganin cewa idan natafi ba zan dawo da raina ba don haka duk wanda ya hau kan karagata ya haukenan
gaba dayanku takwas din nan babu wanda baiyi kukan takaici ba a nan da fargabar rashin samun nasara face Galadima kuma a cikinku shi kadai ne bai gajiya da bukatata lallai yanzu na dad gamsuwa cewa Galadima masoyina neh na kwarai tunda baya harin kujerata
batun kwagirin sarautata kuwa hakika da farko na sanya shi a cikin akwatin tsakiya amma kafin ku shigo sai na sauya shawara na dauke abina sakamakon wannan hikimar da tazo cikin gaggawa koda gama fadin haka sai sarki sahibul hairi ya fiddo kwagirin sarautarsa daga cikin alkyabbarsa ya baiwa aminul has ya karba sannan yace dashi
daga yau kaine sarkin misra kafin na dawo daga tafiyata ko shakka babu zan dawo kuma na umarceka da kayi adalci a cikin harkokin mulki kamar yadda na sabayi
nan take sarki ya sallamesu gaba daya suka tafi cikin bakin ciki galadima ne kadai ya zamo a cikin dumbin farin ciki mara misaltuwa domin dama yana da wani babban buri a zuciyarsa wanda ba zai taba cika shiba face ya zama sarkin misra
bayan sarki ya sallami yan majalisa sai yasa aka shirya masa doki da guzuri amma sai bawan dake wannan aiki ya sanar dashi cewa guzurin fa ba zai isheshi ba har ya isa birnin Askandariyya
kafin bawan ya gama rufe bakinsa saiga manzo daga gidan Galadima janye da wata doguwar taguwa akan taguwar kuwa guzurin tafiya ne mai yawa ga sarki Sahibul hairi
yayinda sarki yaga wannan sako sai ya cika da tsananin farin ciki kuma yaji cewa kaunar Aminul has ta karu a zuciyarsa ainun nan take yayi alkawari a zuciyarsa cewa randa duk bukatarsa ta biya sai ya maishe da galadima waziri kuma zai bashi dukiya mai tarin yawa da bazasu iya cinyeta ba har zuwa karshen rayuwarsu
bayan an gama kimtsa taguwar sarki da guzurinsa sai ya umarci wani bakin bawa nasa mai suna HALUF daya shirya suyi wannan tafiya tare cikin murna da zumudi Haluf yaje ya kimtsa koda fitowarsa sai ya iske yayi shigar yaki mai tsananin kwarjini da ban tsoro gaba daya shigar bakaken kaya sarki yayi sannan ya sanya bakin sulke da bakaken takalma dogaye na fata iya gwuiwa hatta kufen takobinsa da garkuwarsa ma bakakene fuskarsa ya rufeta ruf da bakin rawani ba aganin komai face idanunsa nan take sarki da haluf suka fito daga cikin gida
sarki ya hau taguwa shi kuwa bawa haluf yahau doki ba tare da bata lokaci ba suka kama hanya suka bar cikin birnin misra A wannan lokaci kuwa rana na gaf da faduwa domin gari ya soma duhu haka dai sarki da bawa haluf sukaci gaba da tafiya harsuka nausa cikin dokar daji
basu gusheba suna tafiya har saida sukaga duhu yayi sosai sannan suka yada zango a bakin wata bishiyar dabino cikin gaggawa bawa haluf ya kafawa sarki tanti sannan yayi masa shimfida a cikin tantin ya kunna masa fitila
koda gama wannan shiri sai ya mike tsaye da nufin ya fita daga cikin tantin sarki Sahibul hairi ya kira sunansa yana mai cewa
Ina zaka ya Haluf??
Bawa haluf yace ya shugabana ai zan fita wajan tantin nanne natsaya don na tabbatar da tsaro kada wani mugun abu ya sumamemu.......
Zan Cigaba Insha Allah
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive