SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 5

SARKIN SARAKAI BOOK 1. 05
Duk da kasancewarsa ba tsohoba jama a sun dade suna mamakin dalilin da yasa yake dogara sanda a duk sa adda yake tafiya alhali bai tsufa ba har Abu hakim ya rasu babu wanda yasan dalilin da yasa yake amfani da wannan sandan Lokacinda cutar Ajali ta kama abu hakim a wannan lokaci tuni matarsa ta dade da rasuwa kuma ta bar masa ya guda daya wato shulaiba saboda aminci da kaunar dake tsakanin sarki sahibul hairi da abu hakim saiyasa aka kawo shi cikin gidan sarauta ya zamana cewa shi da kansa yake jinyarsa sannan kuma yasa aka dinga kula da shulaiba tamkar yar cikinsa bayan kamar wata hudu da faruwar haka sai ciow ya kara tsanani wani yammaci sarki sahibul hairi da shulaiba na zaune a gaban abu hakim sun zuba masa ido suna kwalla sbd ganin halinda yake ciki sai abu hakim ya dubi sarki sahibul hairi yayi murmushi sannan ya dubi shulaiba ya fashe da kuka koda ganin haka sai hankalin sarki sahibul hairi ya dugunzuma yace yakai aminin mahaifina shin zaka iya gaya min dalilin da yasa ka dubeni kayi murmushi amma da ka dubi shulaiba saika fashe da kuka sa adda abu hakim yaji wannan tambaya saiya gyada kai yana mai alamun cewa zai iya amsa tambayar cikin karfin hali ya bude baki yace yakai wannan sarki mai adalci zanso ka tashi kafaduna ka jingina bayana a wannan gado da nake kwance domin naji dadin sanardakai abinda zai amfani rayuwarka data yata nan gaba koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya mike da sauri ya kama kafadun abu hakim ya tashe shi zaune ya jingina bayansa a jikin marikin gadon koda gama hakan sai abu hakim ya kira sunan shulaiba yace taho gareni yake yata shulaiba ta fada kan kirjinsa ya rungumeta a lokacinda duk su biyun suka fashe da kuka al amarinda ya sa sarki cikin tsananin tausayinsu kenan shima bai san sa adda ya fara kuka ba jim kadan sai abu hakim ya dubi shulaiba yace yake yata kiyi hakuri domin ciwonnan nawa bana tashi bane amma ki sani cewa ko a bayan raina baki da wani gata koda jin wannan batu sai mamaki ya kama sarki sahibul hairi yace haba yakai wannan aminin abbana saboda me kake irin wannan furuci alhali ina raye a matsayin sarkin misra Abu hakim ya dago kai ya dubi sarki sahibul hairi a lokacinda hawaye ya subuto masa yace yakai dan aminina ina mai bakin cikin sanar dakai cewa nan gaba awasu shekaru masu zuwa saikashiga cikin wani irin mummunan hali na rashi harta kai cewa ba zaka iya daukar nauyin kanka ba bare ka dauki nauyin wani dukda cewa kana matsayin sarki A wannan lokaci jama a zasu gujeka musamman fadawanka abokanka sauran sarakai zasu kyamaceka su dinga yi maka ba a da isgilanci ka kasance mai hakuri a duk matsayin da ka tsinci kanka kuma ka jajirce wajen neman mafita amanar da zan bar maka itace ga yata shulaiba lallai ka aurar da ita ga mafi soyuwa a ranka daga cikin fadawanka wanda ka tabbatar da cewa yana kaunarka dari bisa dari kuma lallai kada ka aurar da ita a lokacin da ta haura shekara tara a duniya ina nufin ka aurar da ita nan da shekara biyu. Sa adda abu hakim yazo nan a zancensa sai sarki ya cika da tsananin mamaki yace haba ya aminin abbana saboda me kace zanyi talauci alhalin ina da matsayin sarkin misra kuma taya za ayi kace na aurar da yarka a lokacinda take shekara tara alhalin ba a taba yin haka ba a garinnan? Abu hakim ya dubi sarki sahibul hairi yace shin ka yarda cewa kafin rasuwar mahaifinka bashi da abokin shawara wanda ya fini sarki yace gaskiya ne Abu hakim yace shin na taba baka shawara wacce ka bita kaga ba dai dai ba sarki yace A'a to abind anake so ka gane shine abinda na sani har abada ba zaka saniba face na sanar dakai abinda zan hango har abada ba zaka iya hangoshi ba abinda nake so aidakai shine ka kiyaye da duk abubuwanda na fada maka a baya kuma kayi aiki dasu idan kana so ka cimma nasara a rayuwarka lokacin da abu hakim yazo nan a zancensa sai ya janye shulaiba daga kan kirjinsa ya dubeta yace yake yata ki sani cewa nitalaka ne babu abinda zan bar miki na daga dukiya amma zan bar miki wadansu abubuwa guda biyu wadanda indai kina tare dasu har abada keda mijinki ba zakuyi talauci ba kuma babu wani tsautsayi da zai hau kanku wadannan abubuwa biyu ba komai bane face sandata da kuma takalmina nan take Abu hakim ya dauko takalminsa a karkashin gadonda yake kwance gami da sandarsa ya mikawa shulaiba ta karba sannan yace ki boye wadannan abubuwa biyu da kyau har zuwa ranar da kikaga mijinki ya sami babban matsayi a kasar nan to a sannan ne zaki dauki wannan sanda da takalmin ki bashi kuma ki umarceshi da yayi amfani dasu ko yaushe dare da rana koda kuwa yana kwance ne a kan gadonsa ina nufin kada ya kuskura yacire wannan takalmin daga kafarsa face zai shiga kewaye ita kuwa wannan sanda ko barci zaiyi ya ajiyeta a daf dashi lokacinda shulaiba tazo dai dai nan a tunaninta Sai aminul has ya girgiza kafadunta yace Wai shin wanne irin tunani kike yi ne haka??.
Aminul has ya girgizata yace tunanin me kikeyine haka kamar wacce ta farka daga bacci haka ta zabura koda tadawo cikin hayyacinta saita dubi Aminul has tace ka jirani Anan karka matsa ko ina zan shiga daki na fito nan take shulaiba ta juya ta nufi cikin dakinta shi kuwa sai yabita da kallo kawai jim kadan saiga shulaiba ta dawo rike da shohuwar takalmi a hannunta koda ta iso gaban Aminul has saita tsaya suka kurawa juna ido yana mai mamakin ganin tada wadannan tsofaffin abubuwa biyu shulaiba tayi murmushi mai taushi a gareshi tace yakai mijina shin kayi imani da kaunar da nake maka cewa ta cika dari bisa dari? Aminul has yace babu kokwanto ga hakan shulaiba tace idan har kayi imani da hakan toka rike wannan takalmi da wannan sanda daga yau ka kasance a tare dasu dare da rana ya zamana cewa babu abindake rabaka dasu hatta kwanciya bacci face idan zaka shiga kewaye tabbas idanka kiyaye da haka babu tsautsayin da zai sameka kodajin wannan batu sai aminul has ya kurawa wannan sanda da takalmi idanu kawai ya karbesu ya rungumesu a kirjinsa yana mai cewa hakika na gamsu cewa wadannan abubuwa biyu sun fito daga hannun wanda ba za a taba mantawa dashiba lallai zaki sameni mai kiyayewa da umarninki. Nan take aminul has ya cire takalmin dake kafarsa ya saka wannan tsofaffi sannan ya dogara wannan sanda ya nufi cikin turakarsa yana mai waigen shulaiba suna yiwa juna murmushi. Wannan shine abinda ya faru tsakanin aminul has da matarsa shulaiba bayan ya karbi rikon kasar misra daga hannun sarki sahibul hairi ++...
Al'amarin sarki sahibul hairi da bawa haluf kuwa tun da sarki ya kama barci a cikin tantinsa bai farka ba saida gari ya waye har rana ta iske koda budewar idanunsa sai yaji rurin gagarumar wuta a wajen tantinsa cikin sauri ya mike tsaye ya fita waje da hanzari yana mai zare takobinsa don tsammanin ko wadansu yan fashi ne suka kawo sumame da fitowarsa saiyaga ashe bawa haluf ne ya tara gawarwakin yan fashin da ya kashe jiya a waje daya ya kunna musu wuta, sarki sahibul hairi yayi murmushi sannan ya yafito bawa haluf da hannu cikin hanzari haluf ya rugo gareshi suka koma cikin tantin tare da shigarsa sai haluf yaga ashe har sarki ya fiddo abincin kalaci ya shirya shi bisa faranti. Sarki ya dubi haluf yace ina son muyi sauri mu gama kalaci domin muci gaba da tafiya ka san cewa a kalla nan gaba sai mun kwana talatin da bakwai kafin mu isa birnin Askandariyya ba tare da gardamar komai ba bawa haluf yabi umarni suka zauna tare suna masu fuskantar juna suna cikin cin abincin ne sarki sahibul hairi ya lura idanun bawa haluf yaga sunyi jawur kawai sai yayi murmushi yace yakai haluf kai kuwa menene ya hanaka yin barci jiya da daddare?. Koda jin wannan tambaya sai haluf yayi ajiyar zuciya yace ya shugabana hakika jiya naga bala'in da bantaba gani ba kuma naga jarumtaka a wajenka wacce inda zanje na bayar da labarinta baza a gasgata ni ba hakika ka cika sadauki uban sadaukai ka sani cewa ko a yanzu idan na runtse idanuna sai nayi ta ganin yadda ka dinga karya barayin jiya kana sawa suna sare kawunansu da soke juna. Yayinda sarki sahibul hairi yaji wannan batu saiya bushe da dariya yace yakai haluf hakika inda kana nan a lokacin da nayi wani yaki da mutanen birnin Rum da wata kila kwakwalwarka ta birkice ka sami tabin hankali A rayuwata ban taba yin yakin da na sha bakar wahala ba kamarsa domin saida na kwana na yini ina yaki ba tare da na sami damar hutawa ba daidai da dakika daya a wannan yakine na shiga tsakiyar abokan gaba mutum dubu dari uku ni kadai suka yanyameni suna kawo mini sara da suka nima ina maida martani A tsawon kwana da yinin ne nayi musu mummunar barna na kashe mutum dubu dari da talatin A wannan yaki gaba dayan dakaruna mutum dubu dari biyu da hamsin saida aka kashe su ni kadaine na rage Lokacinda abokan gaba sukaga inatayi musu barna amma sun kasa cimmani sai suka kara kaimi suna kokarin hallakani ta kowanne hali amma saina zame musu alakakai kaini kaina a wannan yaki saida na tausayawa abokan gaban saboda irin kisan gillar da nake musu. Wani lokacin idan na sari mutum saidai kaga gangar jikinta tsage gida biyu bari da bari duk inda nasa gaba sai daikaga sassan jikin bil'adama suna yawo a sararin sama gaba dayan jikina saida ya rine da jini ba a ganin komai sai idanuna tamkar anyi mini wanka a kogin jini babu abinda zai baka tausayi face ganin yawan gawarwakin a zube tuli a filin yakin tamkar yabanya a gona lokacin da muka kwana muka yini muna wannan yakin ya zamana cewa na kasa karar da abokan gaba sukuma sun kasa cimmani sai gajiya ta fara riskata a sannanne fa abokan gaba suka fara samun lagona har aka yi min sara uku a gadon bayana kuma aka sokeni a kwibin hagu na cikina nan fa jini ya fara zuba a jikina koda naga zan hallaka saina kwarara uban ihu wanda ya firgita gaba dayan abokan gabar suka jada baya suka tarwatse koda naga hanya ta samu saina ruga da gudu ina gudun ina saransu kafin abokan gaba su ankara nayi nisa
Zan Cigaba Insha Allah
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive