SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 7

 SARKIN SARAKAI BOOK 1. 07
Ana cikin tsakiyar wannan haline akaga sarkin kofa ya shigo a guje yana ta faman haki Al amarinda ya dugunzuma hankalin kowa kenan akayi tsit kamar mutuwa ta gifta kowa ya kame kamar babu mai rai a wajen Da zuwan sarkin kofa saiya fadi gaban sarki yayi gaisuwa sannan yace ya shugabana kayi sani cewa yanzu haka jarumi uban jarumai ya shigo kasar nan ya banke kofar gari da karfin sadaukantakarsa kuma ya kashe dukkanin abokan aikina yana nan tafe izuwa nan fadarka don biyan wata bukata tasa ni kaina ya kyaleni ne kawai don nazo na isar da sako' cikin tsananin fushi sarki BARUSA ya dakawa sarkin fada tsawa wacce tasa dukkanin jamar wajan suka fadi kasa suka kwanta da ruf da ciki don tsananin razana sarki barusa ya kasance lafcecen katon mutum mai surar mutanen farko gashi dogo kuma gashi kakkaura duk jikinsa a murde yake ya tara jijiya da kwanji komai tsawon mutum sarki barusa na iya dora abinci a kansa yaci yana da jajayen idanuwa ababan tsoro yanada wawakeken hanci da katon baki a takaice dai idan ana batun muni to sarki BARUSA kurunkus ne! Sarki barusa ya nuna sarkin kofa da yatsa yace wai shin wanene jarumi uban jarumai harda ya isa ya banke kofar birnina ya kashe min dakaru har yace lallai sai ya shigo fadata bidar wani abu? Sarkin kofa yace Aiba wani fane face SARKI SAHIBUL HAIRI na birnin misra kodajin wannan batu sai sarki barusa ya mike tsaye ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya ita kanta dariyar abar tsoroce domin zata iya firgita mai ciki tayi bari :o zata iya sa mutum gudawa kuma zata iya zamo sanadin yin hijirar dukkanin tsuntsayen daji bayan sarki barusa yai dariya ya gaji saiya koma kan kujerarsa ya zauna su kuwa fadawanda gaba daya sun tsure sun dimauce tunda sukaji ance sarki sahibul hairine yazo wazirin sarki barusa wanda ake kira YARKUS ya matso daf da sarki yace ranka ya dade yanzu menene abinyi? Ka sani cewa sarki sahibul hairi ya shahara fagen jarumtaka da samun nasarar yaki shinefa mutuminda ya gagari rumawa da hindu shine wanda ya shiga har birnin farisa ya sare kan sarkinsu kuma shine sarkinda ba a taba cin kasarsa da yaki ba sai sau daya a yakin da suka gwaza da rumawa amma dukda cewa an kashe gaba daya dakarunsa saura shi kadai saida yayi musu mummunar barna kuma ya tsira da rayuwarsa lokacinda waziri yarkus yazo nan a zancensa sai sarki barusa ya sake bushewa da dariya a karo na biyu daga can kuma ya murtuke fuskarsa yace ya kai yarkus kayi sani cewa baka fini sanin ko waye sahibul hairi ba na sanshi kamar yadda na san kaina abinda nake so daku shine kowa ya nutsu ya koma mazauninsa idan sahibul hairi ya shigo nan ya iskemu muna harkokinmu kamar yadda muke yi dazu tamkar labarinsa bai riskemu ba ina son naji abinda ya zo nema a kasata sannan na san hukuncin da zan dauka akansa koda gama fadin haka saigaba daya jama ar dake fadar suka dawo cikin hayyacinsu aka ci gaba da sharholiya tamkar babu abinda ya faru jim kadan da faruwar haka saiga sarki sahibul hairi bisa taguwarsa ya shigo da ita har cikin fadar babu abinda zai baiwa mutum mamaki face ganin yadda ita kanta taguwar take tafiyar kasaita tamkar akan sahara shi kuwa sarki sahibul hairi na zaune a kanta cikin wannan shigata bakaken kaya fuskarsa arufe idanunsa kadai ake gani sbd tsabar kwarjinin sahibul hairi saida masu rawa da kida suka kasa cigaba da aikinsa fadawa da sauran jama ar gari kuwa saida kowa ya natsu ya kurawa sarki sahibul hairi idanu duk wanda ka duba saikaga bakinsa a bude tamkar shashasha. Taguwa taci gaba da tafiya har ta iso daf da karagar sarki barusa sannan ta tsaya cak aka fara kallon kallo a tsakanin sarakan biyu sarki barusa ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa dama tuniya kule saboda ganin jama arsa sun firgita da ganin sarki sahibul hairi.
Tsawon yan dakiku fadar tayi shiru kamar ba mai rai a cikinta daga can sai sarki sahibul hairi ya risina kadan ga sarki barusa yace tsakanin sarki da sarki akwai girmamawa yakai mai birnin Askandariyya kayi sani cewa ban shigo kasarka da nufin cin zarafinka ba ko zalunci ba zan la anta kowa ba face wanda yaso la antani ina hadaka da girma da arziki ka bani abu guda daya rak na tafi dashi idan kayi haka nayi alkawarin ba zan cutar da ko kazar garinnan ba idan kuma kaki nayi alkawari saina karar da dukkanin dakarunka na biya bukatata koda kuwa a sanadin hakan zan baje gidajenku su zamo turbaya koda jin wannan batu sai sarki barusa ya bushe da dariya sannan ya hade fuska yace yakai mai birnin misra ka fadi abinda kake bukata daga gareni na baka domin ina da labarin cewa fatara da talauci sun isheka idan na abinci ne zan sa a baka wanda zakaci kaida jama arka na shekara goma idan kuma sutura ce kake so zan baka wacce zata kaika shekara arba in kana sawa kullum sa adda sarki sahibul hairi yaji wannan batu sai ya murtuke fuskarsa yace ai ba bara nazo yi wajenka ba abinda nake bukata a wajenka ba komai bane face gatarin lu'u lu'u wanda kuke bautawa .
Koda jin wannan batu sai sarki barusa ya sake bushewa da dariya a karo na hudu sannan ya mike tsaye ya dubi sahibul hairi cikin murmushi yace ai wannan abune mai sauki kabi waccen hanyar zaka isa dakin da gatarin yake saika dauko cikin salama kazo kayi tafiyarka' ba tare da tsayawa yin wani nazari ko tunani ba kawai sarki sahibul hairi yabi wannan hanya wadda sarki barusa ya nuna masa koda ya kusa isa wata kofa sai kasa ta dare ya rufta cikin wani dakin kasa mai tsananin zurfi yana fadawa sai kasar ta hade ta rufe ruf tamkar bata taba darewa ba sarki barusa ya tuntsure da dariya yace lallai wannan ya cika mahaukaci to inbanda mahaukaci wane ne abokin gabarsa zai nuna masa hanya yabi? Tabbas yakai kansa izuwa mahallakarsa sa adda sauran fadawa da jama ar gari sukaji haka sai suma suka kama kyalkyala dariya suna cewa tabbas sarki sahibul hairi ya cika mahaukaci.
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A FADAR SARKI BARUSA ++.
AL AMARIN SARKI SAHIBUL HAIRI kuwa lokacinda kasa ta dare ya fada kasanta sai yaji ya fadi cikin wani faffadan daki mai tsananin zurfi fadowarsa keda wuya yaji ana tayin wani irin gurnani mai ban tsoro kasancewar dakin akwai duhun gaske baiga abubuwanda ke gurnanin ba.
Bazato ba tsammani sai dakin ya haske fayau yaga abubuwan dake gurnanin ba komai bane face wadansu rikakkun zakuna wadanda a kalla adadinsu yakai guda dubu dukkaninsu a kwance suke sunyi wa dakin kawanya ma ana a tsakiyarsu sarki sahibul hairi yafado koda zakunan nan sukayi arba dashi sai suka fara zazzago harshe suna tamde baki alamar cewa sun jima suna fama da yunwar abinci kawai suke nema tunda sahibul hairi yazo duniya bai taba ganin zakuna masu girma da tamkar wadannan dukda dakakkiyar zuciya ta mazan jiya saida hankalinsa ya dugunzuma yasan cewa lallai yau ya gamu da gamonsa sai abinda hali yayi kamar hadin baki sai zakuna suka daka tsalle lokaci guda gaba dayansu suka yi kan sarki sahibul hairi suka tumurmusheshi da nufin su cinyeshi sahibul hairi ya yunkura da dukkanin karfinsa ya watsar dasu sai gashi sun tarwatse a sama suna buguwa da garun dakin kafin su sake kawo masa farmaki tuni ya zare takubba biyu a jikinsa hagu da dama ya hausu da sara duk zakin da ya sara sai yaji kamar dutse ne saidai kaji wani irin sauti ya tashi kall.
Al amarinda ya dugunzuma hankalinsa kenan ya tabbatar da cewa lallai maganar sarki barusa ta tabbata cewa ya kawo kansa izuwa mahallakarsa nanfa zakunan nan suka kara kaimi wajen daka tsalle suna kai masa hari suna kokarin ya kusarsa da kokarin cinyeshi inba don sahibul hairi ya kasance mai tsananin zafin nama da sadaukantaka ba da tuni sun gama dashi amma dukda hakan saida suka fara karkarce jikinsa da faratan hannunsu kafin ya ankara tuni jini ya fara zuba a jikinsa koda ya fuskanci cewa zai hallaka ba da dadewa ba in akaci gaba da wannan gumurzu sai yayi jifa da takkubban hannunsa sannan ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa ihune ya sa zakunan sukaja da baya sukayi cirko cirko ihun yaci gaba da amsa kuwwa har sarki barusa da jama arsa dake zaune a can fada saida suka jiyo ihun amma sai sukayi zaton cewa wahala ce tasa sahibul hairi yake wannan ihu don haka sai suka kama kyalkyala dariyar mugunta lokacinda zakunan nan suka firgice da jin wannan ihu na sahibul hairi sai aka fara kallon kallo tsakaninsa dasu tamkar sunji tsoro bazasu sake afka masa ba daga can sai suka sake daka tsalle gaba dayansu sukayi masa rubdugu wohoho! A sannan ne fa tsagwaron karfi da jarumtaka sukayi ranarsu domin sahibul hairi wanzuwa yayi tamkar shaidani a tsakiyar zakunan nan duk wanda ya nausa sai dai kaga yai sama ya fado kasa kafin ya mike sai yasa kafa ya tatsile kansa take zakaga kan zakin ya dagwargwaje tamkar an kwankwatsa shida dutse wani lokacin idan ya naushi zaki a gadon baya saidai kaji bass! Wato ya karya masa kashi nan fa zakunan nan suka ringa bajewa a kasa suna zama gawa koda sahibul hairi yaga ya samo lagon zakunan saiya kara kaimi a kansu yaci gaba da ragargazarsu da karfin damtse cikin zafin nama da juriya da jarumtaka kai saida takai cewa yana kama kawunansu yana murde musu wuya da karfin tsiya saidai kaga yayi jifa da gawar zaki. Hakika karfi jarine domin inda sarki bai kasance sadaukin gaskeba da tuni zakunan sun zamo sanadiyar Ajalinsa duk da cewar ya samo lagon zakunan ba su fasa yi masa rauni ba domin kartar jikinsa suke da farata nan da nan jikin nasa yai fata fata tamkar da kaifin takobi ake saransa saboda zafin yankan da suke masa ne ya dinga kwarara ihu yana ci gaba da kakkarya gabban jikinsu. Saida aka shafe kusan rabin sa'a ana wannan dauki ba dadi sannan ya samu ya kashe gaba dayan zakunan nan aikuwa yana gamawa dasu ya yanke jiki ya fadi a lokacinda jiri da jini ke dibarsa, dama tun lokacinda aka fara wannan gumurzu su sarki barusa na jiyo ihunsu da gurnanin zakunan amma daga bisani sai sukaji shiru ba ihun sarki bana zakuna . .
Zan Cigaba Insha Allah
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive