Skip to main content

Posts

Showing posts from September, 2019

TAYA KAI MURNA

TAYA KAI MURNA
Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu. 'Yan uwana Makafta kamar yadda kuka sani cewa na saba antayo kafcaccaki iri daban daban a kuma lokuta Mabanbanta, yau kam ba sabon Kafce na kawo muku ba, wannan maƙala ce kawai na yi domin in taya kaina murnar Fassara waƙoƙin Fina Finan India har guda ɗari. Na san ba lallai bane ku ku ga girman abin ko muhimmancinsa, amma a wajena, hakan babban al'amari ne. Hakan yasa nake gayar farinciki a wannan rana, ga jerin waƙoƙin da na fassara nan zan antayo muku. Fatan zaku faɗa min wacce tafi muku daɗi da kuma wacce kuke muradin in fassara muku, hallau kuma dai. Ƙofofin shawari da ƙorafi a buɗe suke. Nagode.
 1. Aaraha Hoon Palatke  2. Hawayein  3. Jeene Laga Hoon  4. Jeena Jeena  5. Zinda  6. Mere Humsafar  7. Suraj Hua Maddham  8. Tum Hi Ho  9. Saari Saari Raat 10. Jiya 11. Baaton Ko Teri 12. Saware 13. Jeete Hain Chal 14. Hasi Bangaye 15. Bande Hain Hum Uske 16. Selfie Lelere 17. Tu Milade 18. Teri Khushboo 19. Baatein Yeh Kabhina 20. O Zaalim…

FASSARAR WAƘAR ADHURI ZINDAGI

FASSARAR WAƘAR ADHURI ZINDAGI 
* Sunan Waƙa - Adhuri Zindagi
* Sunan Fim - Teraa Surroor
* Shekarar Fita - 2016
* Haɗa Sauti - Himesh Reshammiya
* Rubutawa - Sameer Anjaan
* Sunan Kamfani - T-Series
* Mawaƙi - Rituraj Mohanty
* Mai Fassara - Haiman Khan Raees 
* Dil Akela Hai Bada Haan…
Zuciyata tana cikin kaɗaici 
* Kyun Rahoon Main Tanha Haan…
Me yasa zan ci gaba da kasancewa a cikin kaɗaici? 
* Yeh Ilteja Hai, Tujhse Meri…
Wannan shi ne roƙo na a gare ki 
* Adhuri Zindagi Hai, Tu Karde Muqammal (x2)
Rayuwa ta ba a cike take ba, ki cika min ita (ta hanyar kasancewa tare da ni) 
* Yeh Ilteja Hai, Tujhse Meri…
Wannan shi ne roƙo na a gare ki 
* Adhuri Zindagi Hai, Tu Karde Muqammal (x2)
Rayuwa ta ba a cike take ba, ki cika min ita (ta hanyar kasancewa tare da ni) 

* Dil Akela Hai Bada Haan…
Zuciyata tana cikin kaɗaici 
* Kyun Rahoon Main Tanha Haan…
Me yasa zan ci gaba da kasancewa a cikin kaɗaici? 
* Yeh Ilteja Hai, Tujhse Meri…
Wannan shi ne roƙo na a gare ki 
* Adhuri Zindagi Hai, Tu Karde Muqammal (x2)
Rayuw…

HANYOYI GOMA DON FITA DAGA BALA'I DA ƘUNCIN RAYUWA

HANYOYI GOMA DON FITA DAGA BALA’I DA KUNCIDA DAMUWA
_(Sheikh Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)_
Babu ko shakka kowa a yau ya san al’ummar musulmi a duniya suna cikin halin kunci da damuwa,don haka wajibi ne malamai da daliban ilimi su ci gaba da haskawa al’umma hanyoyin da ya kamata su bi don samun mafita daga wannan bala’i da musifa. Ga wasu hanyoyi goma da zamu runguma da izinin Allah,Allah zai yaye mana wadannan musifu:

1-Kyautata imani da Allah da nisantar abin da yake tauye imani. Allah ya yi alkawarin taimakon bayinsa muminai, da basu nasara akan abokan gabarsu.Don haka matukar akwai imani da Allah a zukatan bayi to Allah ba zai tozarta su ba.
2-Tuba da Istigfari da Komawa zuwa ga Allah.
3-Yawaita ayyuka na kwarai,saboda ayyukan kwarai sukan kawo wa zuciya nutsuwa,kamar yadda munanan ayyuka sukan kawo wa zuciya bakin ciki da damuwa da kunci.
4-Yawaita Sadaka : musammam ma a boye ba tare da an sani ba,ya tabbata a hadisi Manzon Allah S.A.W ya ce “Aikata kyawawan ayyuka suna kawar da munanan abubuwa,sadakar b…

Hadith of the day

*Hadith about Love!*
Narrated Abu Huraira (ra): The Prophet (saw) said,
"If Allah loves a person, He calls Gabriel saying: 'Allah loves so and so; O Gabriel, love him.' Gabriel would love him, and then Gabriel would make an announcement among the residents of the Heaven, 'Allah loves so-and-so, therefore, you should love him also.' So, all the residents of the Heavens would love him and then he is granted the pleasure of the people of the earth."
(Sahih al-Bukhari, Vol. 8, Bk 78, Hadith 70)!
Jumaat Mubarak to you all out there.

ƘA'IDOJIN HADDACE ƘUR'ANI

KA’IDOJIN HADDACE AL-QUR’ANI
Tambaya : Assalamu alaikum, malam don Allah ni karamin dalibi ne, ban dade da fara hadda ba, shi ne nake so a taimaka min da hanyar da zata kai ni zuwa haddace Alqur'ani.
Amsa :  To dan'uwa, ina fatan Allah ya datar da kai zuwa alkairi, ga wasu daga cikin hanyoyin da za su taimaka maka, wajan hadda, mutukar ka kiyaye su, to za ka samu hadda mai kwari :  1. Ya wajaba ka rinka yin hadda a wajan malami saboda ya dinga gyara maka.   2. Idan za ka fara hadda ka fara daga suratu Annas saboda ta fi sauki.        3. Ka da ka dinga haddace abu mai yawa, musamman farkon fara haddarka, saboda wannan zai jawo ka yi hadda mara karfi, ya kamata ka dinga yi daidai yadda zaka iya yin muraja’a , don ka inganta haddarka .  4. Ka rinka yin hadda da al-qur’ani iri daya, saboda hakan zai taimaka ka dinga tuna gurin da kowacce aya take, da kuma tuna inda kowanne shafi ya ke karewa. 5. Duk lokacin da ka haddace izu daya, to kar ka wuce shi, har sai ka maimaita shi a kalla sau a…

MATSALAR GAMSAR DA JUNA

/matsalolin-gamsar-da-juna sirrin rike miji WhatsApp: ☏+2348037538596
Wani mutumin ba ruwansa; da zarar ya sami gamsuwa da matarsa koda a iya wasan da su ke yi ne, to fa shi ya gama, ba ruwansa da ita. Shi ba abinsa ya yi ma sa zafi. Kun ga wannan shi ne karshen rashin adalci. Wata matar kuma ta na da doguwar sha’awa, saboda haka, idan mijinta bai yi wasa da ita ba, sannnn bai jira ta samu gamsuwa daga gare shi ba, to maniyyin da ya ke jikinta ba zai sauko ya hadu da nasa ba, sai dai ya tsaya ma ta a mararta. Daga nan kuma sai ciwon mara, sai ciwon ciki, sai ciwon kai, sai warin gaba. Daga nan sai mace ta dinga tsintar kanta da rashun kuzari da rashin walwala. Ta rasa abin da ya ke yi ma ta dadi, kuma wannan ke sa mace ta dinga jin haushin mijin da tsanar mijin. Sai ka ga mace ba ta girmama miji yadda ya kamata. A rasa dalili. Nan kuwa rashin ba ta hakkinta a shimfida ne ya jawo ma sa.
Sannan ya kamata mu sani cewar mata kala-kala ne kamar yadda maza su ke kala-kala. Akwai mai karfin sha…

AMFANIN ƁAWON ALBASA

AMFANIN BAWON ALBASA
Daga yau kada kisake jefarda bawon albasa.... Bawon albasa yanada amfani matuka ajikin mutum, shikadai yana kunsheda sinadarai masu fada da cututtuka ajiki.
       Idan aka samu bawon albasa aka wankeshi sosai dattin yafita sai azubashi acikin tafasasshen ruwa abarshi yajika daga bisani sai asha kofi daya dasafe kofi daya dayamma wannan zai taimaka wajen:
- Rage kiba.
- Yana magance ciwon mara lokacin al'ada namata.
- Yana magance rashin bacci ko karancinsa.
-Yana magance hawan jini.
- Yana magance ciwon hakori ko dadashi idan ana kurkure baki dashi.
- Yana magance matsalan yankewar numfashi.
- yana magance matsalan dandruff ko tsinkewar gashi idan aka wanke gashin dashi kafin ashiga ayi wanka.
           Wallahi amfanin bai tsaya dagananba wannan dan kadan muka kawo, domin karin bayani kuma sai kubincika sauran.

THE IMPORTANCE OF GIRL CHILD EDUCATION IN ISLAM

[Friday Sermon] The Importance Of A Girl Child Education In Islam
By Imam Murtadha Gusau
In the name of Allah, Most Merciful, Bestower of Mercy.
All praise is for Allah. And may the peace and blessings of Allah be upon the Messenger, his Companions and those who follow his guidance.
To proceed:
Dear brothers and sisters, Islam advocates educating women and enlightening them about the teachings of religion, as this greatly influences the life of women as well as that of their children in the future. As Hafiz Ibrahim, the Poet of the Nile said:
"The mother is a school; if she is well-prepared, a noble nation is prepared."
Besides, the Prophet Muhammad (Peace be upon him) addressed women saying:
"O womenfolk…."
He even specified a day on which he used to address them; when some female Companions said to him:
"Men are always with you. So, specify a day for us."
He indeed specified a day on which he met them, admonished them and commanded them… [Imams Al-Bukhari and Musl…

ILLOLIN SHAN RUWAN SANYI

ILLOLIN SHAN RUWAN SANYI 

1. TSAIDA BUGUN ZUCIYA:- bugun zuciya shike gyara dumin jiki da daidaita numfashi to ruwan sanyi yana sa bugun zuciya ya rika raguwa har takai ga tsayawa. Ko kunsan yawancin yan film na kasar indiya da yan ball da boxing da wrestling tsayawar bugun zuciya ke ajalinsu kuma bincike ya nuna yawancin shan ruwa mai sanyi yayin da suke aikine yake jawo musu..
2. LALATA TSARIN KAYAN CIKI:- shan ruwa mai sanyi yana tattare hanji guri daya sai ya sanya abinci yaki narkewa da wuri hakan kan jawo matsalar hanji ulcer kenan ko kuma tashin zuciya. Yawancin masu shan ruwan sanyi suna yawan zubda yawu ko tashin zuciya ko saurin kullewar ciki
3. DAUKE KARFIN JIKI:- Duk da cewa shan ruwan sanyi kan sa mutum yaji dadi amma a hankali yana dauke masa karfin jiki sakamakon cewa yayinda ruwan mai sanyi ya shiga jikinsa dole sai naurorin jikin sunyi kokarinsu na ganin sun maida wannan ruwan ya daidaita da dumin jikin hakan yanasa suyi rauni sakamakon kokarin da suke yana wuce haddi. K…

BAMBANCI TSAKANIN GAFARAR ALLAAH DA TA MUTANE

*BAMBANCIN GAFARAR ALLAH DA GAFARAR MUTANE*
A dabi'ar mutane in kana kyautata masu na kwanaki 99, sai kayi kuskure na kwana daya suna nan suna bibiyar wannan kuskuren naka. Ba su kallon wadannan kyautatawar.
Amma Allah Ta'ala da za kayi ta saba masa na kwanaki 99, sai ka tuba ka nemi gafararsa na kwana 1 zai gafarta maka.
*Ɗan uwanku a Musulunci: ✍* *Abu Ja'afar* *Yusuf Lawal Yusuf* 17th Muharram, 1440AH {27/09/2018}.

FRIDAY MESSAGES 300

Almighty! On this blessed day, keep us safe from hypocrites & those who have bad intention towards us. Surround us with good people; those who spread positivity & constantly remind us of You. Guide us in all that we do; all the way to our ultimate destination, Paradise! Aameen.
 *Jumm'at Kareem!*

AMFANIN SHAN RUWAN ZAFI KAFIN KARIN KUMALLO

AMFANIN SHAN RUWAN ZAFI☕ KAFIN A KARYA🍝 DA SAFE
☎08060606050☎
Wannan maudu'i ne mai muhimmancin da na ke fatan isar da shi ga jamaa, Babu abinda ya fi tsada bayan addininmu fiye da lafiyar jiki💪🏻 Likitocin zuciya❤ suna fada cewa: Da za'a isar da wannan fatawa ga mutane da an ceto rayuka masu yawa. Ga yadda ake yin magani da ruwan dumi☕: Abin mamaki🤔 shine da yawa daga cututtukan da Allah ya saukar babu shakka maganinta🍵 yana cikin ruwa💧 kuma Bayan haka Allah ya Fada a cikin Alqur'ani cewa ya Samar da rai ne daga Ruwa💧 to kaga Ashe kenan in Muka duba zamu Ga dukkan JIKIN mutum ruwane, misali kamar Jinin jikinsa ai Ruwa ne, haka kuma da Wani Abu zai sami mutum misali ko hadarin Mota in aka Kai shi asibiti za a Ga abinda likita zai fara masa shine Daura masa Ruwa (Drip)💧
A kasar japan an sami wasu da suka gudanar da bincike kuma sun tabbatar da cewa ruwa yana maganin cututtuka kamar haka : Ciwon kai, hawan jini, ciwon sanyi, ciwon gabobi, ciwon shanyewar jiki, bugun zuci…

ZAN IYA BIN LIMAN YAYIN IƘAMA?

*_ZAN IYA BI-BIYAR LADANI LOKACIN DA YAKE TADA IKAMA?_*

                        *Tambaya:* Assalamu alaikum, ina fata malam yana lafiya, bayan haka malam don Allah inada tambaya kamar haka..menene hukuncin maimaita ikama awajen mamu ayayin tada sallah???

                            *Amsa* To dan'uwa akwai hadisin da yake nuni da cewa: ana bi-biyar ladani lokacin da yake ikama, saidai hadisin bai inganta ba, wasu malaman hadisin sun raunana shi, don haka ba za'a iya gina hukunci akansa ba. Saidai akwai malamai da yawa da suke ganin za'a bi-biyi mai ikama saboda Annabi ﷺ ya kira tad a sunan kiran sallah a cikin hadisin Bukhari mai lamba ta: 601, don haka za ta dau hukuncinta. 
Zance mafi inganci shi ne: ba za'a bi-biyi mai ikama ba, saboda ibada tana bukatar dalili tabbatacce. Kasancewar Annabi ﷺ ya kira Ikama da kiran sallah da suna daya, ba ya nuna hukuncinsu daya ne, saboda idan abubuwa biyu suka hadu ana iya kiransu da sunan daya daga ciki, kamar yadda ake cewa Wata da ra…

SHIN YA HALATTA ARNIYA TA YIWA MUSULMA KITSO

*SHIN YA HALATTA ARNIYA TA YIWA MUSULMA KITSO ?*

*Tambaya*
Assalamu alaikum, shin ya halatta Arniyya ta yiwa musulma Kitso ?

*Amsa*
Wa'alaikumus salam  Ya halatta macen da ba musulma ba ta yiwa musulma kitso, saboda a zancen mafi inganci, al'aurar mace ga 'yar'uwarta mace, shi ne daga guiwa zuwa cibiya, babu bambanci tsakanin kafira da musulma a cikin haka, domin a zamanin Annabi s.a.w. Yahudawa mata suna shiga gidan Annabi s.a.w., kuma ba'a samu suna yin shiga ta musamman ba idan suka ga za su shigo, saidai in kafirar tana da wani sharri da ake jin tsoro, to wannan mace za ta iya suturta daga ita, sannan kuma mutukar akwai musulma to ita ta fi dacewa ayi hulda da ita .
ALLAH NE MA FI SANI
*Amsawa*✍🏻
*DR JAMILU YUSUF ZAREWA*
5/1/2014

FRIDAY MESSAGES 299

Ya Allah! All good is on Ur hands alone. And the disposal of all matters ultimately rests in U alone. Grant us our prayers & forgive our shortcomings. Pardon those who have gone before us. Teach us to always care 4 one another & protect us from evil.

RAYUWAR ƘABARI 01

*RAYUWAR ƘABARI*
 *Rubutu na 1* 
بسم الله الرحمن الرحيم 
Da hantsi (kusan ƙarfe 10: 00 na safe) a ranar Lahadi 24/Zul-Hijjah/1440 (25/8/2019) ne na gabatar da wa’azi ga taron mata: Tsofaffi da dattijai da matan aure da yaran mata mai taken: *Rayuwar Ƙabari* , a babban masallacin Jumma’a da ke cikin garinmu: Zangon Katab. 
Bayan kammala darasin ne aka gabatar da tambayoyin da suka rubuto, waɗanda kuma na bayar da amsoshinsu a taƙaice.
To, bayan gama karatu littafin: *RAYUWAR ƘABARI* a nan, sai na ga ya dace in sake kawo tambayoyin da amsoshin. Me yiwuwa su yi amfani ga sauran jama’a, _wal Laahu A'lam:_ 
 *T1- Menene hukuncin wanda ke haɗa mutane faɗa?* 
 *A1-* Haram yake yi, saboda dalilai masu yawa kamar haka: 
1. A rayuwar nan babu mai ƙaunarsa ko son zama da shi a cikin al’umma, muddin dai aka gano shi.
2. Yana da matsanancin azaba a cikin ƙabarinsa a bayan mutuwarsa, kamar yadda hadisin nan sahihi na matar da Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya tarar da ita tana kuka a …

AN GAISHE DA EL-RUFA'I

An Gaishe Ka Namijin Duniya, Gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i
Daga Imam Murtadha Gusau
Talata, 24/09/2019
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin kai
Assalamu Alaikum
Ya ku 'yan uwana 'yan Najeriya masu girma, masu daraja! Wallahi, Allah ya sani, kuma shine shaida, na dade ina kwakkwaran bincike da kuma bibiyar ayukka da tsare-tsare, da salon mulki irin na gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagorancin mai girma adalin gwamna, masoyin talakawa, mai kaunar kawo canji na gaskiya a cikin al'ummah, wato Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i; sai daga karshe sakamakon bincike na ya tabbatar mani da cewa, lallai wannan mutum alkhairi yake nufi ga jihar sa ta Kaduna da kuma kasar nan baki daya. Na gano cewa wannan gwamna wallahi, wallahi, wallahi, talaka ne a gaban sa ba aljihun sa ba, kuma na gano, burin sa shine, yaya za'a yi a gyara tsarin kasar nan, ta dawo kamar yadda ake tafiya a can da, ya zamanto babu banbanci tsakanin dan mai kudi da dan talaka; tsakanin 'ya 'yan masu m…

TSINTUWAR DA AKE YIN CIGIYA

*TSINTUWAR DA AKE YIMA CIGIYA ?* *Tambaya:*                                                                                                         Assalamu alaikum malam wani bawan Allah ne ya tsinci Naira: #500#, a wurin kuma bai ga wadanda zai yi wa cikiya ba... Ya ya kamata yayi da kudin tsintuwar ?, suna ajiye yanzu haka kusan wata daya .  
*Amsa:*                                                                                                                                                                                     Wa alakum assalam To dan'uwa idan mutum ya yi tsintuwa ya wajaba a gare shi ya yi cigiya har tsawon shekara guda, idan bai samu mai ita ba, daga nan zai iya amfani da ita, amma in mai ita ya zo daga baya zai biya shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 5761. Amma idan abin da ya tsinta dan kadan ne ba shi da yawa, to ya halatta ya yi amfani da shi ko da …

SHEIK PANTAMI DA KWANKWASO DUK ƳAN UWAN MU NE

Sheikh Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami Da Engineer Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso Duk 'Yan uwan Mu Ne!
Daga Imam Murtadha Gusau
Laraba, 25/09/2019
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
Ya ku 'yan uwana masu kima da daraja! Kamar yadda kuka sani, sanannen dan siyasar nan, tsohon Gwamnan Kano, tsohon Minista, tsohon Sanata, dan jihar Kano kuma dan arewacin Najeriya, Engineer Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da bikin tura 'ya'yan talakawa har su dari biyu da arba'in da biyu (242) zuwa kasar India domin karatun digiri na biyu, wanda gidauniyar sa ta Kwankkwasiyya Foundation ta shirya, muna rokon Allah ya saka masa da alkhairi, kuma ya yawaita muna irin su a arewacin Najeriya, amin.
A daidai lokacin da suka tafi filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano, da ke cikin birnin Kano, wato Malam Aminu Kano International Airport, domin yin rakkiya ga wadannan yara, kwatsam, sai ga mai girma Ministan Sadarwar Nigeria, Abu Abdir-Rahman, Dr. Isa Ali Ibrah…

HANYOYI 10 DA MACE ZATA BI DOMIN SAMUN LAMBAR YABO A WAJEN MIJINTA

*HANYOYIN GOMA {10} DA MACE ZATA BI DOMIN SAMUN LAMBAR YABO A WURIN MIJINTA*
*1-* Yin hakuri da shi a halin da akwai da halin rashi. *2-* Girmama iyayensa da ƴan uwansa ta hanyar kyautata musu.  *3-* Bin umurninsa da yi masa biyayya a duk abinda bai saɓawa Allah ba. *4-* Faɗa masa kalamai masu kwantar da hankali da sanyaya zuciya. *5-* Ki kasance mai ɓoye masa sirrinsa na gida dana waje. *6-* Ki kasance a koda yaushe cikin tsabta, haka cikin gidanki.  *7-* Ki zama mai lura a kowani yanayi, a wani ya fita gida da kuma halin da ya dawo.  *8-* Idan ya yi niyyar ƙara aure karki hana shi. *9-* In kuma har ya ƙara miki abokiyar zamar, ki zauna da ita lafiya domin faranta masa rai da neman aljannarki.  *10-* Daga ƙarshe kuma ki kasance mai yawan addu'a da sauran ibadu, kamarsu; azumi, salla, sadaka, zumunta.
*Ɗan uwanku a Musulunci: ✍* *Abu Ja'afar* *Yusuf Lawal Yusuf* 24th Almuharram 1441H {24/09/2019} .

ABUBUWA GUDA GOMA DA MATA ZA SU YI DOMIN FARANTAWA MAZAJEN SUY

*Abubuwa 10 da mata za su yi don faranta wa mijinsu*


*Ga wadannan abubuwa 10 kamar haka*
─━━━━━━░★░━━━━━━─
*1-Jima’i* Hanya ta farko da mata za su faranta wa mijinsu ita ce, ta bangaren jima’i. Sau da yawa mata babu ruwansu da nuna wa mijinsu suna bukatar jima’i, akwai abokina da ya fada mini ya shekara fiye da 10 da yin aure amma matarsa ba ta taba neman ya sadu da ita ba, kullum idan har suka yi jima’i to shi ne ya neme ta, hakan ya sanya ya daina jin dadin jima’in domin ba ya ganin matarsa tana shaukin jima’in, hakan ya sa ko ya sadu da matarsa ba ya jin gamsuwa. Don haka idan mata tana son ta rika faranta wa mijinta, to ta rika nemansa, idan ba za ta iya kai tsaye ba, to ta kirkiro hanyar aika dan sako. Mace za ta iya aika dan sako ta hanyar sanya tufafin mai daukar hankali, mace za ta iya aika dan sako ta hanyar kissa da kwarkwasa da kuma kisisina. Motsa gabobi ga mace kan iya tura dan sako cikin kankanen lokaci. Mata su rika ba da kansu ga mijinsu a duk lokacin da ya bukaci hakan, kad…

FASSARAR WAƘAR JASHN-E-ISHQA

Fassarar Waƙar Jashn-E-Ishqa 
Sunan Waƙa: Jashn-E-Ishqa
Sunan Fim: Gunday
Shekara: 2014
Haɗa Sauti: Sohail Sen
Rubutawa: Irshad Kamil
Kamfani: T-Series
Rerawa: Javed Ali & Shadab Faridi
Fassarawa: Haiman Raees 
* Jashn-E-Ishqa… Jashn-E-Ishqa...
Bikin Soyayya... Bikin Soyayya Ne 
* Jashn-E-Ishqa… Jashn-E-Ishqa...
Bikin Soyayya... Bikin Soyayya Ne 
* Jashn-E-Ishqa… Jashn-E-Ishqa...
Bikin Soyayya... Bikin Soyayya Ne 
* Jashn-E-Ishqa… Jashn-E-Ishqa...
Bikin Soyayya... Bikin Soyayya Ne 
* Daur-E-Ishqa Ek Jashan Hai
Wannan Zamanin Son Tamkar Biki Yake 
* Lekin Apna Alag Tashan Hai
Amma Mu Muna Da Namu Salon Na Musamman 
* Khoon Mein Sulgi Ek Agan Hai
Wuta Ce Ke Gudana A Jinin Mu 
* Beh Ke Dikhlaayega Yeh Tevar
Zafin Ran Mu Shi Zai Alamta Hakan 
* Daur-E-Ishqa Ek Jashan Hai
Wannan Zamanin Son Tamkar Biki Yake 
* Lekin Apna Alag Tashan Hai
Amma Mu Muna Da Namu Salon Na Musamman 
* Khoon Mein Sulgi Ek Agan Hai
Wuta Ce Ke Gudana A Jinin Mu 
* Beh Ke Dikhlaayega Yeh Tevar
Zafin Ran Mu Shi Zai Alamta Hakan 
* Chaahat Ke Dar …

ABOTA DA MUTANEN KIRKI ALHERI NE

*ABOTA DA MUTANEN KIRKI ALHERI NE:*
Idan kaji kana son mutum a ranka, to ka bayyana masa.... yin hakan sunnah ne.
Idan ka fadawa dan uwan ka kana son sa, ana fatan hakan zai faranta masa rai daga nan insha Allahu dankon Zumunci zai yi karfi a tsakaninku.
Hakika wadanda suka so juna saboda Allah zasu hadu a inuwar al'arshin Allah a ranar alkiyama.
Mu sani mafi alherin abota da son juna shine wanda aka yi don Allah ba don abin duniya ba.
'Yan uwa mu kula da zumunta, muna sada zumunci a tsakanin dangi da masoya.
Muyi abota da mutanen kirki. Hakika alaka da salihan bayin da zama da mutanen kirki yana kara imani, yana gyara tarbiyya.
Mafi alheri makusanci shine wanda zama dashi zai kara maka tsoron Allah. Wadda in ka ganshi zaka ji farin ciki kuma alaka dashi ya sanya ka zama mai kula da addini.
Addinin mu ya nuna mana muna mu so alheri ga 'yan uwan mu kamar yadda muke son alheri ga kawunan mu.
Allah ya hadamu da masoya na kwarai, Allah ya hadamu da masoyan mu a aljannah, amin
*Rubutawa…

BIN JAM'IN ISHA'I DA NIYYAR MAGARIBA

*BIN JAM'IN ISHA'I DA NIYYAN MAGRIBA !!*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum, nine nazo masallaci natarar imam yana sallar isha'i nikuma banyi magriba ba shin zan iya binshi da niyyar magriba? Kuma yaya zanyi da sallama tunda adadin raka'o'in ba dayaba? 
*Amsa*

   Eh ya halatta kabishi in yayi raka'o'i 3 kazauna kayi tahiyya kasallame sai katashi dawuri kabishi a raka'ar karshen da niyyar shine raka'arka ta farko a isha'i in yasallame sai kakawo cikin ukun,     irin wannan amsar SHEIKH BN BAAZ yabayar yayinda akayi masa irin tambayarnan gawanda yazo yatarar ana hada sallar magrib da isha'i don ruwan sama kuma dayazon an idarda Magrib ana kan isha'i kuma yakara dacewa= inma raka'a daya na isha'in ya subuce musa sai yssami 3 sai yayi sallama tareda imam su amatsayin isha'i shi kuma amatsayin Magrib, inma yasami isha'in kasada raka'o'i 3 shi kuma da niyyar biyan magrib yabisu in sunyi sallama sai yakawo cikotonda zai cikeshi raka&…

LEƘA NAKA KAFIN NA WANI

🕸 *LEKA NAKA KAFIN NA WANINKA*🕸
Kai dai kawai ka kyautata Tsakaninka da Ubangijinka, domin hakanne kawai za ka iya tsira da mutuncinka anan duniya da kuma gobe Alkiyama. 
Amma idan katsaya bincike da leke-leken tare da qaqalen dole sai ka ga no laifin wasu, to zaka dauwama a cikin damuwa, da bata lokacinka a haka kurum, kuma rashin ganin laifin kanka wata alama ce ta MUNAFURCI. 
Sai kaga har lokaci ya Kure maka a wajan leqen laifuffukan mutane kai kuma kakasa gyara naka laifin, har mai zuwa tazo maka. Allah ya kyautata. 
Idan kaga gemun dan uwanka ya kama da wuta, kai ma sai ka yayyafawa naka ruwa, gudun kar ta kama shi, ba wai tsayawa zakayi leken shin ya kone da yawa ne ko kuwa.
_Ya Allah ka shagaltar da zuciyoyin mu wajan ganin laifuffukan mu sama da na wasun mu, kuma kabamu ikon gyarawa da kuma taubatun nasuha cikin lokaci,_
 ✍🏻Rubutawa *Idris M Rismawy* Rismawy86@gmail.com

KADA KI BIJIREWA MAI KYAUTATA MIKI

🍀 *KARKI BIJIREWA MAI KYUTATA MIKI* 🍀
🍀Idan kika samu MIJI mai kula da ke kuma yana cika miki haqqoqinki yadda yakamata, to ki godewa Allah,  kuma ki rikeshi kataman da hannu biyu.  🍀Saboda idan har kika bijirewa kyuatatawar da yake miki, kikayi butulci, to fa kisani akwai 10 irinki a waje da kuma 40 wadanda suka fiki komai, duk  suna nan suna jiranshi yashigo da su dakinki. 
🍀Idan kinyi Sa'a ahadaku idan kuma akasin haka sai  kuma kiyi waje , abaki Red Card.  Allah yakiyaye.
🍀Kirika duba makomarsu mana, wasu fa irin yadda kikeyiwa mijinki haka sukayiwa nasu,  da tunanin cewa: ai idan ma sun fita akwai masu jiransu.
🍀Shaidan yayi musu alkawarin bogi,  kuma akarshe suka kare ahaka babu wanda ya shinshina su balle adaukesu, gararanbar dai kawai suke tayi,  da kuma yin bara a kufai. 
🍀Matukar kin godewa Allah, to Allah zai kara miki jim dadi doriya akan wanda kike kai, ku ma duk wanda bai godewa kadan ba ko anbashi mai yawa ma bazai gode ba.
🍀 Akarshe dai duk wanda bai godewa Mutan…

FASSARAR WAƘAR KYA KHOYA

Fassarar Wakar Kya Khoya 

 Sunan Waka : Kya Khoya
Sunan Fim: Khamoshiyan
Shekarar Fita: 2015
Hada Sauti: Jeet Ganguly
Rubutawa: Rashmi Singh
Sunan Kamfani: Sony Music Entertainment India Pvt. Ltd.
Rerawa: Naved Jafar

Fassarawa: Haiman Raees 

* Mere Mann Chal Duniya Se Ab Door Chale
Yake Zuciya ta Mu tafi muyi nisa daga wannan duniyar. 
* Raahon Ki Ungli Thaamein Chalte Chale
Mu rike yatsun hanya kawai mu fara tafiya. 
* Mere Mann Chal Duniya Se Ab Door Chale
Yake Zuciya ta Mu tafi muyi nisa daga wannan duniyar. 
* Raahon Ki Ungli Thaamein Chalte Chale
Mu rike yatsun hanya kawai mu fara tafiya. 
* Na Khushi… Aur Na Gham Ho Jahaan
Wurin da babu bakin ciki babu farin ciki. 
* Dhoond Le… Koi Aisi Jagah
Wurin da zamu nema kenan 
* Kya Khoya, Kya Paaya, Itna Kyun Soche Hai
Abinda ka samu kuma ka rasa, menene na wani Damuwa akan shi? 
* Tu Hai Nadiya, Tu Hai Dariya, Kyun Khudko Roke Hai
Kai rafi ne, kai kogi ne, me yasa kake Dankwafar da kanka? 

* Kya Khoya, Kya Paaya, Itna Kyun Soche Hai
Abinda ka samu kuma ka rasa,…