ABOTA DA MUTANEN KIRKI ALHERI NE


*ABOTA DA MUTANEN KIRKI ALHERI NE:*

Idan kaji kana son mutum a ranka, to ka bayyana masa.... yin hakan sunnah ne.

Idan ka fadawa dan uwan ka kana son sa, ana fatan hakan zai faranta masa rai daga nan insha Allahu dankon Zumunci zai yi karfi a tsakaninku.

Hakika wadanda suka so juna saboda Allah zasu hadu a inuwar al'arshin Allah a ranar alkiyama.

Mu sani mafi alherin abota da son juna shine wanda aka yi don Allah ba don abin duniya ba.

'Yan uwa mu kula da zumunta, muna sada zumunci a tsakanin dangi da masoya.

Muyi abota da mutanen kirki. Hakika alaka da salihan bayin da zama da mutanen kirki yana kara imani, yana gyara tarbiyya.

Mafi alheri makusanci shine wanda zama dashi zai kara maka tsoron Allah. Wadda in ka ganshi zaka ji farin ciki kuma alaka dashi ya sanya ka zama mai kula da addini.

Addinin mu ya nuna mana muna mu so alheri ga 'yan uwan mu kamar yadda muke son alheri ga kawunan mu.

Allah ya hadamu da masoya na kwarai, Allah ya hadamu da masoyan mu a aljannah, amin

*Rubutawa:*✍🏻
*Sheik Aliyu Said Gamawa*
(Hafizahullah)

```DAGA ZAUREN DARUL-ISLAM```
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive