FARKON ABINDA YA ZAMA WAJIBI AKAN BAWA


FARKON ABINDA YA ZAMA WAJIBI AKAN BAWA

An tambayi Shiek Muhammad Sãlihul Usaimeen Allah yayi masa rahama:
"Minene farkon wajibi akan bawa"??

Sai ya bada amsa da cewe:
"Farkon wajibi akan bawa shine farkon Abinda ake kiran ake kiran bawa akansa,wanda Manzanni da Annabawa suke kiran bayi akansa, wato kira zuwa ga Kadaita Allah shi kadai acikin bauta.

Annabi s.a.w ya bayyana hakan acikin Hadisin Mu'azu bin Jabal R.A 
Lokacin da ya turasa zuwa Yamen sai yace masa:
(Lallai kai zakaje zuwa ga wasu al'ummar Ma'abuta littafi:wato yahudu da Nasara,ya kasance farkon abinda zaka fara kiransu akai shine:
Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,kuma Annabi s.a.w Manzon Allah ne,...)
@Saheehul Jami'i

Dan haka:
-Farkon abinda yake wajibi akan bawa shine:
"Shaidawa babu abin bautawa bisa chanchanta da gaskiya sai Allah shi kadai,kuma Annabi Muhammad s.a.w Manzon Allah ne". 

-Wannan baya tabbata sai ha hanya guda biyu:-

1-Tsarkake dukkan wani nau'in bauta zuwa ga Allah shi kadai da kuma yarda akan babu wanda ya chanchanci bauta sai Allah shi kadai. 

2-Kadaita Annabi s.a.w cikin biyayya da Dha'a da kuma koyin Ibada.  
@ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﻭﺭﺳﺎﺋﻞ ﻓﻀﻴﻠﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﺻﺎﻟﺢ

Kuma wannan shine abinda ya wajaba mu fara karantar da dukkan ya'yanmu da matanmu da dukkan sauran musulmai baki daya,domin shine foundation na addinin Allah tun zamin Annabi Adamu s.a.w har ya zuwa kan Manzon Allah na karshe kuma mafifice acikinsu zababban masoyin Allah,Annabi Muhammad s.a.w

Kuma Annabi s.a.w ya fara da'awar sane da fara kiran mutane zuwa ga Kadaita Allah acikin bauta shi kadai da kuma nisantar bautar gumaka. 

Allah ya tabbatar da mu akan wannan tafarki na Aqeeda ingantacciya har zuwa mutuwar mu 

Amin.
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive