Fassarar Waƙar Badla

Fassarar Waƙar Badla Title Song

Sunan Waƙa: Badla (Title Song)

Sunan Fim: Badla

Shekarar Fita: 2019

Sauti: Anupam Roy

Rubutawa: Manoj Yadav & Anupam Roy

Kamfani: Zee Music Company

Mawaƙi: Anupam Roy

Mai Fassara: Haiman Khan Raees

(Matashiya)

Wannan waƙa tana ƙunshe da sarƙakiyar Kalmomi inda Kalmar Badla ta ke yawan fitowa a ciki. Ita kuma Kalmar badla tana da manyan Ma'anoni guda biyu, Ma'ana ta farko ita ce FANSA, ma'ana ta biyu kuma Canji. Don haka a cikin wannan waƙa sun yi amfani da waɗannan ma'anoni dukkan su wajen tsara ta.

* Aye Barkhurdar Hoshiyaar Yeh Sansaar Badla

Ya kai yallaɓai! Ka nutsu Domin duniya Canjawa ta ke

* Zulfon Ki Style Jhoothi Smile Aur Profile Badla

Salon gyaran gashi, Murmushin bogi da Kundin bayanai suna ta Canjawa

* Koi Na Jaana Kab Kahaani Ka Kirdaar Badla Re

Babu wanda yasan yaushe ne ƴan Kafcen labarin suka sauya.

* Culture Purana Ghar Gharana Yeh Sanskaar Badla

Tsofaffin Al'adu da ɗabi'u duk sun canja

* Petrol Ka Price Assi Ab Pocket Ka Size Badla

Fetur ma ya ƙara kuɗi zuwa rupees 80, girman Aljihu ma ya canja

* Koi Na Jaana Maine Kab Haathon Ka Taash Badla Re

Babu wanda yasan yaushe ne na canja ƙasurgumin shirin.

* Door Se Koi Aaya Hai

Wani yazo daga nesa

* Kuch Aisi Baat Baaki Hai

Tsugunne bata Ƙare ba

* Majboor Hoke Aaya Hai

Mutumin can fa ya zo ne a tilasce

* Chhota Hisaab Baki Hai… Hai Na

Da sauran rina fa a kaba

* Ankhon Ko Ankhon Se Lena Badla

Idanuwa suna so su ɗauki Fansa akan Junan su

* Khwabon Ko Khwabon Se, Badla

Mafarkai suna so su ɗauki Fansa akan Junan su

* Baaton Ko Baaton Se Lena Badla

Zantuka na so su ɗauki Fansa akan Junan su

* Yaadon Ko Yaadon Se, Badla…

Tunanuka suna so su ɗauki Fansa akan Junan su

* News Aur Akhbaar Badla

Labarai da Jaridu sun canja

* Shubh Samachar

Labari mai kyau kenan

Jab Ye Jeena Marna Daily Dekha

Tun da naga mutuwa kullum

* Apna Bhagwan Badla Re…

Na canja ubangiji na/Imani na

* Sach Ka Avatar Badla

Gaskiyar ma an canja ta

* Ye Atyaachar Teri,
Jhoothi Moothi Duniya Dekhi

Wannan Azabtacciyar duniyar bogin taku da na ke gani

* Apna Usool Badla Re…

(ta sa ni) Nima na canja ɗabi'u na

* Door Se Koi Aaya Hai

Wani yazo daga nesa

* Kuch Aisi Baat Baaki Hai

Tsugunne bata Ƙare ba

* Majboor Hoke Aaya Hai

Mutumin can fa ya zo ne a tilasce

* Chhota Hisaab Baki Hai… Hai Na

Da sauran rina fa a kaba

* Ankhon Ko Ankhon Se Lena Badla

Idanuwa suna so su ɗauki Fansa akan Junan su

* Khwabon Ko Khwabon Se, Badla

Mafarkai suna so su ɗauki Fansa akan Junan su

* Baaton Ko Baaton Se Lena Badla

Zantuka na so su ɗauki Fansa akan Junan su

* Yaadon Ko Yaadon Se, Badla…

Tunanuka suna so su ɗauki Fansa akan Junan su

* Ankhon Ko Ankhon Se Lena Badla

Idanuwa suna so su ɗauki Fansa akan Junan su

* Khwabon Ko Khwabon Se, Badla

Mafarkai suna so su ɗauki Fansa akan Junan su

* Baaton Ko Baaton Se Lena Badla

Zantuka na so su ɗauki Fansa akan Junan su

* Yaadon Ko Yaadon Se, Badla…

Tunanuka suna so su ɗauki Fansa akan Junan su

* Dollar Ka Bhaav Bada

Farashin Dala ya tashi

* Pav Ka Aakar Badla

Ƙirar biredi ma kanta ta canja

* Monday Ke Bhai Dekho Sunday Ka Vyahvaar Badla

Yanayin Litinin ɗan Uwan Lahadi shima ya canja

* Aye Barkhurdar Hoshiyaar Yeh Sansaar Badla

Ya kai yallaɓai! Ka nutsu Domin duniya Canjawa ta ke

* Adhunik Pyaar Superstar Ka Baazaar Badla…

Soyayyar zamani da shaharar shahararru
Ita ma ta canja

<••••••••••••••••••••••••••••>
  ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive