FASSARAR WAƘAR TERI MITTI

FASSARAR WAƘAR TERI MITTI 

Sunan waƙa: Teri Mitti

Sunan Shiri: Kesari

Shekarar fita: 2019

Sauti: Arko

Rubutawa: Manoj Muntashir

Kamfani: Zee Music Company

Mawaƙi: B Praak

Mai Fassara: Haiman Khan Raees 


(Matashiya) Kalmar Bhangra sunan wata Shahararriyar rawa ce da yaran mutanen Punjab ke yi. Su kuwa mutanen Punjabi suna zaune ne a arewacin India) 


* Talvaron Pe Sar Waar Diye

Mun Sanya Kawunan Mu Akan Takubba 

* Angaaron Mein Jism Jalaaya Hai

Mun sadaukar da Jikkunan Mu Munyi Yaƙi tuƙuru 

* Tab Jaake Kahin Humne Sar Pe

Kuma bayan haka, a Kawunan Mu Kuma 

* Yeh Kesari Rang Sajaaya Hai

 Mun Saka Waɗannan Rawunna Masu Ruwan Ɗorawa 

* Aye Meri Zameen Afsoss Nahi

Bani da wani Dana sani, Ya ke Ƙasata 

* Jo Tere Liye Sau Dard Sahe

Akan duk wani ƙunci da na jure 

* Mehfooz Rahe Teri Aan Sada

Ina fatar Martabar ki ta ci gaba da Wanzuwa har abada 

* Chaahe Jaan Meri Yeh Rahe Na Rahe

Ko da zan kasance a raye ko a'a 

* Aye Meri Zameen Mehboob Meri

Ke ce Abar Sona, Ya Ke Ƙasata 

* Meri Nass Nass Mein Tera Ishq Bahe

Soyayyar ki ce ke gudana a cikin kowace jijiya ta

* Pheenka Na Pade Kabhi Rang Tera

Ina Fatan kalan ki kada ya gushe 

* Jismon Se Nikal Ke Khoon Kahe…

Wannan shi ne abinda kowane ɗigon jini na da ke fita yake faɗ

* Teri Mitti Mein Mil Jawaan

Zan Zama Toka In Wanzu tare da ke, Ya ke Ƙasata 

* Gul Banke Main Khil Jawaan

Sannan Kuma in firfito kamar Fure 

* Itni Si Hai Dil Ki Aarzoo…

Wannan shi kaɗai ne muradin Zuciyata 

* Teri Nadiyon Mein Beh Jawaan

Ina so Inyi ninƙaya a cikin rafukan ki, ya ke Ƙasata 

* Teri Kheton Mein Lehrawaan

Ina so inyi rausaya (kamar Tsirrai) a filayen ki 

* Itni Si Hai Dil Ki Aarzoo…

Wannan shi kaɗai ne muradin Zuciyata

* Wo O… Ooo… Wo O… O… Ooo…
Sarson Se Bhare Khaliyaan Mere

Filaye na cike su ke da Korayen Ganyayyaki 

* Jahaan Jhoom Ke Bhangra Paa Na Saka

A inda ba zan iya taka rawar Bhangra ba 

* Aabad Rahe Woh Gaon Mera

Ina fata Ƙauyen Mu ya ci gaba da Wanzuwa a cike da mutane 

* Jahaan Laut Ke Wapas Jaa Na Saka

A inda ba zan taɓa dawowa ba 

* Ho Watna Ve, Mere Watna Ve

Wayyo Ƙasata! Wayyo Ƙasata 

* Tera Mera Pyaar Nirala Thha

Soyayyar da ke tsakanin mu tana da ban mamaki 

* Kurbaan Hua Teri Asmat Pe

Na Sadaukar da Kaina akan Tsarkakakiyar Ƙasar Ki 

* Main Kitna Naseebon Waala Thha

Kai! Amma fa nayi sa'a Matuƙa 

* Teri Mitti Mein Mil Jawaan

Zan Zama Toka In Wanzu tare da ke, Ya ke Ƙasata 

* Gul Banke Main Khil Jawaan

Sannan Kuma in firfito kamar Fure 

* Itni Si Hai Dil Ki Aarzoo…

Wannan shi kaɗai ne muradin Zuciyata 

* Teri Nadiyon Mein Beh Jawaan

Ina so Inyi ninƙaya a cikin rafukan ki, ya ke Ƙasata 

* Teri Kheton Mein Lehrawaan

Ina so inyi rausaya (kamar Tsirrai) a filayen ki 

* Itni Si Hai Dil Ki Aarzoo…

Wannan shi kaɗai ne muradin Zuciyata

* Kesari…

Ruwan Ɗorawa... 

* O Heer Meri Tu Hansti Rahe

Wayyo Abar ƙauna ta, ina fata ki kasance cikin farinciki har abada 

* Teri Aankh Ghadi Bhar Nam Na Ho

Ina fata kada ko alamun hawaye ma su bayyana a idanun ki har abada 

* Main Marta Thha Jis Mukhde Pe

A kan fuskar da na ke mutuwa 

* Kabhi Uska Ujaala Kam Na Ho

Ina fatar hasken fuskar nan kada ya taɓa raguwa 

* O Maai Meri Kya Fiqr Tujhe

Ya ke Uwata! Me yasa kike damuwa ne? 

* Kyun Aankh Se Dariya Behta Hai

Me yasa kogin hawaye yaje gudana daga idanuwan ki? 

* Tu Kehti Thhi Tera Chaand Hoon Main

Ki kan kira ni da cewa ni ne watan ki 

* Aur Chaand Hamesha Rehta Hai

To ki sani wannan watan naki zai wanzu har abada 

* Teri Mitti Mein Mil Jawaan

Zan Zama Toka In Wanzu tare da ke, Ya ke Ƙasata 

* Gul Banke Main Khil Jawaan

Sannan Kuma in firfito kamar Fure 

* Itni Si Hai Dil Ki Aarzoo…

Wannan shi kaɗai ne muradin Zuciyata 

* Teri Nadiyon Mein Beh Jawaan

Ina so Inyi ninƙaya a cikin rafukan ki, ya ke Ƙasata 

* Teri Kheton Mein Lehrawaan

Ina so inyi rausaya (kamar Tsirrai) a filayen ki 

* Itni Si Hai Dil Ki Aarzoo…

Wannan shi kaɗai ne muradin Zuciyata

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
 Instagram: Haimanraees 
 Infohaiman999@gmail.com

Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive