Skip to main content

HUKUNCIN ASKE SASHE NA GASHIN KAI A BAR WANI SASHE A MUSULUNCI

HUKUNCIN ASKE SASHE NA GASHIN KAI A BAR SASHE A MUSULUNCI

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Alhamdulillah, wassalatu wassalamu ala rasulillah, wa ba'ad.

Lallai yana daga abubuwan da aka jarabci da yawa daga cikin mutane a yau musamman matasa, canza wa kawunansu kamanni ta hanyar aske sashe na gashin Kansu da sunan ado musamman a bukukuwan sallah, Wanda galibinsu kwafoshi sukeyi daga wurin wasu mashahuran arna da kafurai, wadanda mafi yawansu sun jahilci hukuncin hakan a Musulunci, wanda da sun sani da sun nisanceshi.
Wanda hakan yasa naga ya dace nayi bincike akai don fa'idantar da yan'uwa matasa dama dukkanin mai aikata irin hakan da fatan Allah yasa a gyara.

Aciki akwai matsaloli guda uku (3) a dunkule:

1. DALILAN DA SUKAYI HANI KAN ASKE WANI BANGARE NA GASHIN KAI DA BARIN SAURA:

An karbo hadisi daga Ibn Umar Allah ya qara masa yarda yace: "lallai Annabi s.a.w yayi hani akan ALQAZA'U. Ubaidullah yace wa Nafi'u: menene kuma ALQAZA'U? Sai yace: shine a aske sashe na gashin kan yaro abar sashe."

Wannan hadisi Bukhari da Muslim suka rawaitoshi

A wani hadisin na Ibn Umar har wa yau yace: lallai Annabi s.a.w yaga wani yaro an aske wani sashe na gashin kansa aka bar sashe, Sai ya hanesu akan hakan, yace: "Ku askeshi gaba daya ko ku barshi gaba daya". 

Abu Dawuda da Ahmad suka rawaitoshi.

2. HUKUNCINSA:

Malamai sunyi sabani kan hukuncin irin wannan aski:

* Wasu sukace MAKARUHI ne, kamar mazhabar SHAFI'IYYAH da HANABILAH.
Kamar yadda Imam Annawawy ya tabbatar da hakan acikin littafinsa ALMAJMU' 1/347 Kuma ya naqalto ijma'insu akan haka.

* Wasu kuma sukace HARAMUN ne, saboda Annabi s.a.w yayi hani akan haka, sannan ya bada umurnin a askeshi gaba daya ko a barshi gaba daya a hadisai guda biyu da suka gabata.

Sukace: domin kalmar hani asali tana hukunta haramci ne, kamar yadda Kalmar umurni ke bada hukuncin wajibci.
Saboda haka sukace hadisan guda biyu suna nuni ne akan haramcin aske sashen kai da barin sashe.

LAJNATUD DA'IMAH LIL'IFTA'I 5/195 sukace: hatta rage ma wani bangare na gashin kai tsawo, daya bangaren kuma a barshi da tsayi bai halatta ba.
Sheikh Abdullahi Alibassam ya qara tabbatar da hakan acikin littafinsa TAISIRUL ALLAM sharhin Umdatul Ahkam inda yake cewa:

Abinda wasu matasa ke aikatawa a yanzu na saisaye wani sashe na gashin kansu da barin sashe, wanda suke kiranshi da suna (Toiletries) yace: bidi'ah ne wannan.

Shi yasa Ibn Taimiyya yace: yana daga kamalar son da Allah da Manzonsa ke yiwa adalci, shine umurtar mutum da yayi na ya tsaida adalci hatta a karan kansa, saboda hakane ma ya haneshi da kada ya aske wani sashe na gashin kansa ya bar sashe, 
Domin yin hakan zaluntar kai ne, yayin da yayi wa daya bangaren tsirara, daya bangaren kuma ya barshi lullube da gashi.

3. KAMANCECENIYA DA KAFURAI:

To idan kuma ya kasance mai yin irin wannan askin ya kwafoshi daga wurin kafurai ko fajirai ko kuma wasu wadanda shari'ah tayi hanin ayi koyi dasu, to wannan kai tsaye HARAMUN ne har a wurin malaman da suke ganin Makaruhi ne, domin illar kamanceceniya da kafurai haramci ke nunawa,
Saboda hadisin Ibn Umar Allah ya qara masa yarda yace: lallai Annabi s.a.w yace: "Duk Wanda yayi kamanceceniya da wasu mutane to yana tare dasu" (Abu Dawud)

Ibn Taimiyyah acikin littafinsa IQTIDA'I 1/269-270 yace: " isnadin hadisin mai kyau ne, yace: mafi qarancin hali na hukunci da wannan hadisi ke nunawa shine Haramcin kamanceceniya da kafirai, duk da a zahirinsa kafirci yake nunawa"

Yaci gaba da cewa a 1/271: " Ita wannan kamanceceniyar ta game dukkan Wanda ya aikata wani aiki da nufin kwaikwayan masu aikin, da kuma wanda ya yi aikin ne kawai dan buqatar Kansa ba da nufin kwaikwayan mai aikin ba"

Wannan ke nuna mana cewa iqirarin cewa Ni ina aikatawa ne ba da nufin koyi da mai aikin ba, wannan ba zaiyi tasiri cikin hukuncin Haramci da aka fada ba, matukar dai a wajen kafurai aka daukoshi,

Wanda kuma kowa shaida ne askin da yan'uwa matasa keyi yanzu a wajen shahararrun kafurai suka dauko,
Tunda wasu askin ma da sunan kafuran ake kiransu, wanda wannan Haramun ne!! Haramun ne!!!

Muna roqon Allah ya nuna mana gaskiya gaskiyace ya azurtamu da binta,
Ya nuna mana qarya qaryace ya azurtamu da nisantarta,
Ya kuma sanyamu cikin bayinsa shiryayyu.


Comments

Fitattu Goma

MATSATSUBI 1 COMPLETE

M


  atsatsubi 1
Complete book
Na Abdul Aziz Sani madakin gini.
Typing Suleiman Zidane kd.
Whatsapp.. 09064179602
Sarki Dujalu yayi gyaran murya sannan yace to sai ku kimtsa, kai mai rubutu ka aza alkalamin ka akan tkrd domin wannan hikayar da zan baku na dauke da matukar abubuwan al-ajabi.
Ni kai na ko tunowa nayi da lbrn sai nayi kuka.
Hikaya ce ta wani kyakykyawan saurayi kuma jarumi wanda ake kira nazmir bin halad da gimbiya luzaiya yar sarki fahalul bahafus.
A wani zamani can mai tsawo da ya shude anyi wata babbar Qasa wadda ake kira duhamul.
Wannan kasa ta bunkasa da girma karfi da kuma mayaka.
A bisa wannan dalili ne kasar duhamul ta shahara kuma ta zama gagara badau a ckn dukkanin kasashen kewayenta.
Ya zamana ana matuakar tsoranta.
Sarkin da ke mulkin a wannan kasa ta duhamun wani azzalumin sarki ne ana kiransa Bashakur.
Sarki bashakur ba tsoho bane kuma ba yaro bane domin shekarunsa ba zasu gaza ar'ba'in da hudu ba. Zuwa da biyar.
Sbd zalunci irin na bashakur ko a ck…

MATSE GABANKI CIKI DA WAJI TA YANDA MIJINKI ZAI JIKI KAMAR BUDURWA DA YANDA AKI AMFANI DA MUSKI 5

*MATSE GABANKI CIKI DA WAJI TA YANDA MIJINKI ZAI JIKI KAMAR BUDURWA DA YANDA AKI AMFANI DA MUSKI*🚫⭕🚫⭕🚫⭕🚫⭕🚫⭕
     ⚱⚱⚱⚱⚱⚱⚱⚱
🚫⭕🚫⭕🚫⭕🚫⭕🚫⭕
🀦🏻‍♀🀦🏻‍♂πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ

πŸ‘¨πŸ»‍⚕ *BY ADMIN MUSA MUSA*✍🏼
*KASHI KASHI HAR KASHI TARA (9)*
*Ga Kashi Na Biyar (5)*

*IDAN KIN HAIHU*
sai ki Fara shirya jikinki don tarbar maigida, don in dai lafiya kika haihu Daga lokacin Zaki tsinci kanki cikin kuzari.
Duk wanda ya ganki zai ganki tas kamar ba ki haihu ba. Don haka tunda tafiyar ta samu sai a Fara shirya jiki, Kiyi kokarin a dafa miki kaza irin ta masu jego ki Fara ci, ( Inda babu kada ki matsawa mijinki ) cin kazar yana Kara gyaran kasan mace maigida yaji ta zam-zam kamar bata haihu ba. shan ya'yan itatuwa akai-akai baran ma ( kankana, abarba, gwada, lemon Zaki.
ki dinga yin Kunun aya kina sha. In zai samu Kiyi kullum, Amma karki dinga zuba sukari Dan kadan Zaki dinga sawa ko ki sha haka. shan maganin Mata mai kyau ( habbatus-sauda, Zuma , dabino, aya ,madara , nono Amma me kyau.
sh…

SIRRIN DAREN FARKO GA ANGO DA AMARYA

sirrin-daren-farko-ango-amarya☏+2348141722330

Daren angwanci wani dare da ake farinci, idan an wayi gari cikin sa rana ce masoya basa mantata ranar fari ciki.

zaku kasance awani hali mai tattare da shauki da zumudi na kasance warku a matsayin abu daya daren daraja ga ma’aurata kenan da zarar an kai amarya gidan mijinta ango kenan, Iyayanta da kawa yanta zasu barta a daki tana jimamin kasancewar ta a wannan yana yi Na zama amarya.

akan so bayan an watse ambar amarya ta tashi ta dan gyara abin da take ganin bazai kayatar mata DA ango ba a wasu guraran kawayan amarya suna tsayawa har sai an kawo ango wannan baya cikin al’ada an fison abar amarya daga ita sai ango.

ango Ya sani abubuwa da yawa Na iya ballewa mace murfin budurci ta daga cikinsu akwai

1. Jinin haila mai nauyi
2. hawa sama,itace,gini da sauran su.
3. tsalle-tsalle,kamar wasar tsalle-tsalle da sauran su.
4. Yawan hawan keke ko doki
5. Hawa jaki da dai sauran su.

Ya kamata iyaye su dinga hana yara mata irin wadannan matsalolin.

YADDA ZAKI DINGA KYALLI, SANTSI, KAMSHI, MAGANIN KURAJE {DA SABULU}

YADDA ZAKI DINGA KYALLI, SANTSI, KAMSHI, MAGANIN KURAJE {DA SABULU}*

GYARAN FATA DA JIKI HADIN SABILU

dole maigida ko saurayi yai tabinki zai-zai to yaga kin yi kyau.
ke dai yi wanka da

*SABULUN BITA ZAI-ZAI*

➜ dudu osun
➜ dettol
➜ sabulun Ghana
➜ garin zogale
➜ farar albasa

sai Ku hade su guri daya Ku kirba su a turmi ki mulmula Ku rinka wanke fuska zaku ga yadda fuskarku zata yi kyau.

*BITA ZAI-ZAI*

sunan hadin kenan idan dai kana yin wannan hadin zaki sha mamaki za kibani labarin amfani hadin tabbas idan amarya tayi wannan hadin zata kidima ango har yakasa gane ta sai yayi da gaske ke dai yi mugani domin gyaran jiki.

⇚ ayaba
⇚ lemon tsami
⇚ tataciyar madara
⇚ kwai uku

zaku sami ayaba mai kyau Ku bare Ku matse da hannun ko Ku markada yi laushi sai Ku zuba tataciyar madara Ku fasa kwai kamar uku amma farin zaku zuba sai Ku matse lemon tsami Ku gauraya shi Ku shafa a jikin Ku ya sami kamar tsayin ¹ daya sai kuyi wanka da ruwan zafi, idan har kuka lazimci yin haka ba magana.

*SABULUN GYARA FATA*

idan har…