MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da sauran abinci irin na zamani. A wasu lokutan kuma, sai dai in mun je ganin gida mu taho da abinda ya samu wanda saboda marmari, nan take yake Ƙarewa tunda an jima ba'a gamu ba.

Ana cikin wannan hali ne sai ga shi Allaah Ya kawo mana sauƙi har gida, domin kuwa an samu wani gawurtaccen kamfani wanda yake sarrafa ingantattun kayan haɗa abinci irin da dauri a mataki irin na zamani. Wannan kamfani kuwa shi ne MRJ INVESTMENT!

A MRJ Investment, kana iya samun abubuwa kamar haka:

 1. Garin Ɗan Wake: Wannan wani hamshaƙin gari ne da aka haɗa shi musamman domin masu sha'awar cin Ɗan Wake. A cikin wannan gari akwai rogo, Waken Suya, Gujiya, Dawa, Wake, Alkama da kuma kuka. A taƙaice dai, an riga an haɗa komai kanwa kawai za'a sa a kwaɓa shi a tsumbula ruwan zafi, daga nan kuma sai shagali kawai malam. Bugu da ƙari, shi wannan garin ana iya yin tubani da shi.
 2. GARIN KUNU: Shi Kuma wannan garin kunu ne mai ɗan karen daɗi da ga sinadarai masu inganci da gamsarwa kamar su gero, citta, kanunfari, barkono da dai sauransu. Shima wannan baya buƙatar wani sabon aiki, kawai tafasa ruwa za'a yi sai damawa.
 3. GARIN TUWO: Kasancewa kowa yasan muhimmancin tuwo ga rayuwar Bahaushe, hakan yasa Kamfanin MRJ INVESTMENT suka samar da nagartaccen garin tuwo domin amfanin yau da kullum. An riga an niƙa, an tankaɗe kuma an gyara. Tuwon kawai ya rage.
 4. TSAKIN FATE/DAMBU: Shima wannan wani samfuri ne sabo da aka fito da shi. Tsakin masara ne mai kyau da aka gyara domin mabuƙata. Ana iya yin fate da shi, kuma hakanan ana iya yin Dambu da shi. Riba biyu kenan.
 5. GARIN KUKA: Gari ne na asalin kuka 'yar dauri aka niƙa kuma aka tankaɗe shi tsaf domin masu son shan miyar kuka.

Tun da na gano wannan katafaren kamfani, shikenan sauƙi ya samu kuma buƙata ta biya.
Don haka kuma ku garzaya domin ku samu naku. Yana da inganci sosai.

Domin neman ƙarin bayani, sai ku tuntuɓe mu a lambobin waya kamar haka..

08110298305
08185819176

Share:

2 comments:

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive